Skip to content
Part 5 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Ummu Hani bata san sa’adda ta ce “Kawu ina za ka da shinkafar nan, kar dai kuce min tafiya zaku yi da ita, ina mu aka kawowa?”

Ta ɗan nisa cike da takaici kamin ta ci gaba, “Ku baku kawo mana ba tsabar rashin adalci wanda aka kawo mana kun ɗebe, to ya kuke so mu rayu? Tsakani da Allah, ni naɗauka kun rabane tun da ku zaku ɗaukemu.”

Tsawa Kawu ya daka mata “Ke yimun shiru ni ba ubanku bane.” Ya yi waje.

Aisha ta miƙawa Muhammad, ta ce Kairiyya su ɗebe ta gaban su gwaggo ta bi kawo.

Da sauri ta bi shi, “Kai ba ubanmu bane, kai wan ubanmu ne, dan mahaifin mu ba zai taɓa barinmu ba gata ba, kuma wallahi in baka kawo shinkafar nan ba yadda ba kuji nauyin kin daukanmu ba kuka barmu mu rayu da kanmu, matsayinku na wanda haƙƙinmu ke kanku, toni ma bazan ji nauyin kaiku karaba, kan yi mana sata, karkayi zaton zani hizba, a’a ba zani inda za’ai silhu asa dole ku ɗaukemu ba, zani inda duk sai kun dana sani.”

“Lallai yarinyar nan bata da mutunci.” Inji Inna, “Ka ga yaya mu aje musu abincin nan. Ni na fasama yin sallar agidan nan.” Inna Gaje ta faɗa.

Dire shinkafar ya yi, har tana zubewa ya yi waje cikin fishi Ummu Hani ta sunkuya, ta ɗauki shinkafar ta yi ciki ta aje a ɗaki.

Gwaggo na shirin fita, “Ummu ta ce Gwaggo kuɗin da na baki ɗazu shi za ki bani, na ga ba’ayi sadakar ba kuma muna buƙatarsu.” Sauran jiyowa su ka yi suna kallon Gwaggo irin kallon zargin nan wato daman an bada kuɗi baki bamu ba.

Jiki a sanyaye Gwaggo ta curo kuɗi a gefen zaninta ta miƙawa Ummu Hani.

Hannu tasa ta amsa ta hau lissafawa, kamin ta ɗago kai “Sauran dubu biyu” Ta ce.

Takaici ne ya kama Gwaggo bata ce komai ba ta ciro ta bawa Ummu Hani.

Gida ya watse sai su kaɗai, ran Ummu Hani duk babu daɗi, ta sani bata kyauta ba dai dai in har ba haka tai ba to tayaya zasu rayu susu bakwai ba abinci ba hanyar samu.

Miƙewa ta yi ta zari buhun hunan tace su Khairiyya suzo su riƙe mata.

Duk ta cikin ledojin ta maida buhun hunan ta zauna tana hawaye tana ɗinkewa.

Shiko Kawu tunda yaje gida yake masifa, wai yarinya ƙarama ta ci masa mutunci, bacin shi yamanta da yara ƙanana ɗinne yabarsu surayu sukaɗai.

Matarsa ke ta tausarsa tana ce masa karya damu yana nan zaune zasu  nemeshi, ba mata bane duk tsiya shine maɗaurin aurensu, shima sai ya rama kunji fa maimakon ta nuna masa kuskurensa saima kulla masa wata tsiyar take, mata muji tsoron Allah wallahi.

Tun safe Ummu ke jin ranta babu daɗi toilet ta shiga ta kulle, ta hau kuka har ga Allah bata san ya za ta yi da ƙannenta ba, yanzu ace itace uwa itace uba gare su, ita kanta ji take tana buƙatar iyaye, sannan kuma ace ita zata zama dukka biyun ga mutun har shida.

Muhammad tafijin tausayi shi ba abin ta bashi abinci ba, ta lissafa kuɗin da suke gunsu batajin zasu isa ko madarar wata biyu ne su siya masa, wanda tasan tabbas in suka ƙare bata da gun samu hakama shinkafar tasu in ta ƙare tasan bata da gun samu, in su Aisha sun san babu Mohd da su Hasana ba su sani ba kuka ya kuma kwace mata.

“Yaya” Ta ji Aisha ta kira ta, wanke fuskar ta ta yi, ta ɗan nutsu sannan ta fito, kallon ta Aisha ta yi a tsanake kamin ta ce, “Kinga Muhammad na kuka,” Ta amsheshi ta goya ta zari mayafi, bari inje in dawo, nan yan biyu suka sa kuka muma ki tafi damu,  dan duk da Aisha itama yayarsu ce sunfi shakuwa da Ummu Hani, rike musu hannu ta yi, sannan ta dubi Aisha, “Ki kula da su Khairi, zan je in nemo abinda zamu dinga bawa Muhammad,” A’isha ta ce “To yaya sai kin dawo.” Ta ja su Hasana suka fice.

Kai tsaye bakin titi sukai inda ta samu adai dai ta sahu sai kasuwar rimi.

Gun masu magungunan hausa tai dan ta yanke shawarar ita zata shayar da muhd, dan in ba haka ba tasan yunwa ce zata kashe mata shi.

Bayani taiwa mai maganin kan abinda take so, wato ta haɗa mata maganin da zaisa wadda bata taɓa haihuwa ba ta samu ruwan nono yazo dan shayarwa.

Tashi matar ta yi ta haɗa mata komai, sannan ta dawo ta zauna ta mata bayani, nasha da wanka Ummu ta biyata suka baro gurin.

Sai da ta siyawa su Husaina yar tsana sabida yadda suka azzaba mata sannan suka samu mota suka yo gida.

Mamaki ne ya cika Aisha ganin yayar tasu da magunguna, ta ce “Yaya me zamuyi da magani, waye ba lafiya?”

“Ni ce.” Ta faɗa a takaice, tai maka ki haɗamin, ki dafan ta nuna mata yadda za’ayi.

Nan da nan A’isha ta haɗa ita ce kan kace me har magani ya dahu, tas Ummu ta riƙe yadda za’a ta miƙe ta shiga wanka, ta ce a dora mata ɗayan bayan ta kwantar da Mohd a katifar da makociyarsu ta basu, dansu basu da komai sai matattun tabarmi tun mutuwar Abbansu Ummansu ta saida kayanta duk dan su rayu…

Cikin kwana biyun da Ummu Hani ta fara anfani da maganin har yanma ruwan baizo ba, hakan yasa ta ɗauki ɗanmarar komawa gun mai maganin dan gashi dai komai ya nuna kamar tana shayarwa, sai dai ba ruwa, ga kuɗi babu ta fara gajiya da roƙon madarar da zasu bawa Muh’d a maƙota.

Da alamu yunwa ma Muh’d ɗin yake ji, yadda tun ɗazu yake tsanyara kuka, Aisha ta tafi makarantar ita da su Khairiyya ba kowa a gidan daga Ummu sai ƴan biyu.

Kwantar da Muhd tai a katifarsa ta zaunar da Usaina dan ta fi hankali, tace Usai ga ƙaninku nan kimai wasa, banda ɗauka kinaji na ko, to kawai yarinyar tace ta hau taɓa kumatun muhd.

Wanka Ummu ta shiga yadda takejin zafi ga gumi da tai sharkaf jikinta, sabida tuwon da ta tuƙa icen ɗanye ne ta sha wuya, hakan yasa taga gwanda tai wanka kamin ta tafi gun mai maganin duk da kuwa ɗazu tai wankan.

Hasana ce ta shigo riƙe da tarkacenta, hango Usaina da ta yi kusa da Muhd yasa ta tafi da gudu tana murna, dan ita burinta ta ɗauki yaron tako sa hannu za ta ɗaukeshi, Usaina ta figi gashinta tana faɗin kar ki taɓa shi, yaya ta ce kar a ɗaukeshi.

Zafin figar gashin yasa Hasana ɗaukan kwano ta kwaɗawa Usaina, suka hau faɗa irin nasu na yara.

Da gudu Ummu ta ƙaraso ta raba haba, “My girls mene na faɗa.” Ba ita ce muguwa ba ta jamin gashi Hasana ta faɗa tana kuka.

Rarrashi Ummu Hani ta hau yi, da kyar dukkanninsu su ka yi shiru, shima sai da dabara, dan Usaina taƙi ɗaukan laifin ta, ita kuma Hasana bata haƙuri sai ka yadda ka mata ba dai dai ba.

Sai da Ummu Hani ta ce ta zauna, ta ɗora mata Muhd a cinya, ta ce “Kinga ke babba ce, Usaina ƙanwarki ce, ga kuma baby kinga mutun mai ƙanne biyu ai dole ya dinga haƙuri.” Daɗi ya cika Hasana dan mutunce mai san ace ta girmi Usaina duk da kuwa girmansu ɗaya komai na su ɗaya, amma ba abinda ke mata daɗi sama da ace ta girmi Usai ɗin. 

Samun da Ummu Hani ta yi sukai shiru yasa ta amshi Muhd, dan abinda ya fito da ita bawai rabon faɗa bane, dan bama ta ji su ba, hasali data shiga wankan rigarta data jike sharkaf take tunanin gumi ne taga ashe bashi bane, ruwan nono ne, daɗi ya cika ta ta fito da niyar bawa Muhd, taga sarakan rikicin na kanyi ta bige da rabo.

Da bisimillah ta sanya masa a baki, daurewa kawai ta yi yadda ta ji, shiko ɗan bawan Allah tuni ya kama har wani ajiyar zuciya ya ke.

Hasana ta matso kusa, kawai kallon yayar take da Muhd, da alamu mamakin yadda yayar ta su ke shayar da ɗan ƙani take, kamar yadda suke ce masa.

Usaina sarkin wayo ce ta ce, “Ya ya ki ka ce Ummanmu ce ta haifeshi.” Dariya Ummu Hani ta yi, “Eh mana ita ta haifeshi.”

“To na ga Ummansu Walidi ita ta ke ba shi nono ba yaya Fatima ba.”

Murmushin ƙarfin hali Ummu Hani ta yi, ai ita ummansu walidi bata tafi ba, mukuma Ummanmu ta barmin Muhd yanzu ni ce Ummansa.

“Kai to mu wace ummanmu?” Suka haɗa baki, “Ummu ta shafa kansu kuma ta barminku, duk nice umman ku, su Aisha kuma yayyenku.” Suka sa ihu abun ƙuruciya yey shi kenan Umma zamu dinga ce miki ko.

Ta gyaɗa kai, eh, Hasana ta yi waje tana murna Usaina ta zauna gefe tana shafa kan Muhd wanda da alamu shikam yau ya samu abinci mai daɗi.

Aisha da ta dawo daga makaranta ne, ta rugo da gudu gurin Ummu Hani, “Yaya me kike haka kar dai ki ce mun shayar da shi kike.”

Murmushin Ummu Hani ta yi, “To me idonki ya nuna miki ta faɗa tana ƙoƙarin gyara rigarta, bayan ta cire Muhd ta saɓa shi a kafaɗa.”

“Anman yaya tayyaya zakima kanki haka, bacin kinaji ana faɗe in mutun ya shayar zubewa suke.”

“Kajimin A’isha to dan kar abu ya zube sai kawai inbar mutun ya mutu, ko so kike inje in karuwanci in nemo abin da zamu bashi.” “A’a ni bance haka ba Allah ya baki haƙuri.” In ji A’isha.

“Amin” Ummu Hani ta ce, gami da miƙewa kinga na kai ruwa zan wanka ki kaɗa mana miyar can na gama komai, kan in fito karki bari su tashe shi.

Harta kai bakin ƙofa, ta ce, ina su Kairiyya ta tambaya da hanzari.

“Au ba su dawo ba.” Aisha ta tambaya, “In sun dawo zan tambaye ki ne, wato me yaran nan ke nufi” Ummu Hani ta faɗa rai a ɓace, gami da zarar hijabinta zan dawo yanzu kar ku sake ku fita ta ce gami da yin waje..,”

Ranta aɓa ce ta yi makarantar ƙannen nata, wanda take itama ɗaliba ce a cikin ta, mutuwar nan yasa dole ta haƙura da zuwa, duk da tanason karatun anman dole ta haƙura dan kula da ƙannenta.

Tana tafe tana mita a ranta, “Dole in magananin yaran nan, dan ta fahimci tun mutuwar nan suka koyi rashin dawowa gida da wuri.”

A hanya ta gansu, Khairiyya ce ta ce “Lah, yaya” Aiko wata uwar harara ta watsa musu, ba tare da ta ce komai ba kawai ta juya suka bi bayan ta.

Tana shiga cikin gida ta juyo a fusace, “Ina kuka je eyyi?” Su ka yi tsuru suna kallon ta. “Ba tambayar ku nake ba ina kuka je?”

“Yaya makaranta fa mukaje,” inji Khairiyya, “Makarantar gidanku, Aisha tun ɗazun ta dawo, ta ce kuma an riga tashinku za ku, faɗan inda kuka je ko kuwa.” Ummu ta faɗa a zafafe.

“Yaya wallahi makaranta muka je,” Sajida ta faɗa, cikin karaji ta ce “To daman na ce ba ita kuka je ba ina kuka biya?”

“Daman ba yaya Kairiyya ba ce ta tsaya hira,” Sajida ta faɗa cikin rawar murya ganin yadda taga yayar tasu ta tada hankalin ta.

Khairiyya ta kalla rai ɓace, “Wato kunga Umma ba ta nan shi ne kuke san zama ƴaƴan kanku ko, to wallahi bazan laminta ba, in mutum nasan hira ya fara dawowa gida inga lokacin da aka tashe ku, in yaso in naga ya da ce sai in bar mutun yaje hirar.”

Har ta shiga toilet tai wani tunani ta fito da hanzari, “Tsaya waima da wa ta tsaya hirar?” Ta faɗa tana maida hankalinta ga Sajida.

“Ita da ƴan ajinsu ne,” sajida ta bada amsa.

Ajiyar zuciya Ummu Hani ta saki, dan haƙiƙanin gaskiya ta yi wani mummunar tunani ne, watakan kar dai da namiji ta tsaya, dan tana tsoron kar wani ya yi anfani da rashin gatansu ya cutar mata da ƴan uwa.

Zama tai sannan ta dube su baki ɗaya, “Bawai ina san takura muku ba ne a’a inaso ne kawai mu zamto yaran da su Umma zasu yi alfaharin haifa, ku daure ku tayani kula da mutuncinmu, ni kaɗai bazan iya ba, ɗayanmu in ya lalace tamkar dukkanmu ne a idanun duniya, kar kuyi zaton dan muna zaune haka mu kaɗai bazamu iya zamowa na gari ba, karku bari wani ko wata ya yi amfani da rashin galihunmu ya cutar daku kunji ko.” Suka ce to baki ɗaya, ta miƙe ta shiga wanka.

Sai da ta shafe jikin ta da mai sannan ta ma Muhd wankan yanma ta shafe shi da mai ta goyawa Sajida shi, kasancewar bata salla ranar ɗaki ta shiga bayan ta rufe musu gidan, duk da mangari ba ce anman tana tsoron kar bacci ya rufeta su fi ce.

Batafi minti biyar da kwanciya ba bacci mai nauyi ya ɗauke ta, dan agajiye take sosai sabida tashin safe, tama su Sajida abincin tafiya makaranta wani zubin kuma Muhd sai yaita ihu da daddaren bata iya bacci sosai.

Aisha ce ta zubawa su Hasana tuwonsu da ta ga takwas ta yi, suna gama ci su ka yi bacci ta ɗauki Hasana taje ta kwantar ta dawo ta ɗauki Usaina.

Hira suke tayi tsakanin su, ganin har goma Ummu Hani bata fito bane yasa A’isha ta je ta tasota, dan tasam halinta sarai naƙin cin abinci.

Cikin bacci Ummu Hani ta ce, “Dan Allah ki kyaleni Aisha na ƙoshi, cikin fishi Aisha ta ce wallahi yaya ki tashi, sai kinci, haba wannan wane irin abu ne, ina lura da ke rabonda ki wani ci abin kirki tun kan Umma ta ta rasu.”

“Kinga malama ki kyaleni cikin ki ko nawa na ce na ƙoshi ummu ta faɗa tana gyara kwanciyar ta.”

Hannu A’isha tasa ta ɗago ta, “Wallahi sai kin taso kin ci, haba ya ki ke son muyi kinzo kina kwana da yunwa, in cuta ta kamaki bamu da kuɗin magani, in kuma kika mutu ni yazanyi da sauran, gaskiya inke ba kya bukatar lafiyar ki mu muna bukatarki.”

Jiki a sanyaye Ummu Hani ta taso ta fito, idanunta a lumshe alamun bacci, kusa da Khairiyya ta zauna Sajida ta miko mata kwanon abincin nata, tana ci tana bacci, in ya ɗan ɗauketa ɗaya cikin su ne zai ce “Yaya ba kya ci fa.” Sai ta yi sauri ta yi loma kamar suyi dariya suka daure.

Sai da suka ga ta cinye suka miƙe su ka yi ɗaki Aisha da Sajida da Khairiyya ɗaki ɗaya suke kwana, inda ita kuma Ummu ke kwana da ƙananan dan in sun tashi rikici suke su Aisha kuma ba haƙuri.

Muhammad nata wutsul wutsul a katifarsa ta same shi, ta ce “kaga ɗan albarka wato an tashi kenan, tashin hana bacci.” Sai da ta fara bashi mama sannan ta goyashi jikin filo ta jingine a bango, sannan ta kwanta ganin ya yi luf duk da ba bacci yake ba.

Motsi kaɗan take buɗe ido, duk da gidan a kulle yake haka ɗa kunan da suke dan tana tsoron kar wani ya shigo ya cutar da su.

Kamar kullum tun bayan mutuwar ummansu yauma da wuri ta tashi, ta fara dumama tuwo sannan ta azama ƙannen nata ruwan wanka, shida da arba’in kamar kullum ta tashe su, Aisha na wanka, Khairiyya da Sajida na cin abinci duk dan tattalin lokacin suke haka.

Kamar kullum yauma babu wanda ya makara cikin ɗari biyar ɗin data musu saura ta basu ashirin ashirin, suka mata sallama suka fice.

Tana ƙoƙarin haɗa ruwan da zatawa su Hasana wanka kamin Muhd ya farka, yaro ya shigo “Wai Ummu ta zo.” Gabanta ya faɗi ko waye zai zo nemanta, cikin ƴan sakannin da ta yi tunani ta kasa gano ko waye, ta dubi yaron “Ummaru jeka ka ce wai wane?” Ya ce “To” yai waje.

Dawowa ya yi wai inji Alhaji Ubale, Daram gabanta ya faɗi “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” ta faɗa.

Ba kowa bane fa ce mutumin da suke haya gidansa, gabanta ya faɗi ne tunawa da ta yi cewar kwanaki yazo amsar kuɗin sa Ummansu ta yi ta roƙonsa ya basu wata ɗaya in lissalinta dai dai ne yau wata uku kenan.

Jiki a saluɓe ta shiga ɗaki dan ɗauko mayafinta, fatanta kar ya kore su tunda dai ita bata da kuɗin bashi ba kuma ta bada ajiya ba.

<< Ummu Hani 4Ummu Hani 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×