Skip to content
Part 6 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Saida ta goya Muhd sannan ta yo waje riƙe da tabarma, su Hasana suka amsa suka bi bayanta.

Mutumin yana tsaye daga jikin motarsa, Ummu Hani ta ƙarasa har ƙas ta gaida shi, kamin ta ce, “Ga tabarma can na shinfiɗa a soro.” Ba musu ya bi bayanta dan ko yaushe ya zo tun Abbansu na da rai a soro ake masa shinfiɗa.

Kuma gaisawa su ka yi, kamin ya ce, “Ashe kuma abinda ya faru kenan? Allah ya jiƙanta ban sani ba sai da na shigo garin nake jin labari, Allah ya mata rahama.”

“Amin” Ummu Hani ta ce har lokacin gabanta faɗuwa yake, shiru su ka yi tana tsammanin batun kuɗin haya zai yi.

Gyaran murya ya yi, kamin ya ce, “Yau sauri nake, kiramin wadda kuke tare in mata gaisuwa.”

Ɗagowa tai kamin ta ce, “Wa?”

“Ina nufin wadda take kula daku mana.”

“Oh ai ba kowa, mu kaɗai ne.” Ta faɗa jiki a saluɓe.

“What!!?” Ya faɗa a tsorace.

“E, da ya ke dangin namu duk basu da hali, sannan babu tsoffin da zasu zauna damu.” Ummun ta kuma fadi ranta na suya.

Gyaɗa kai ya yi, “Anman duk da haka wannan ba dai dai bane, ta yaya za su bakku ku kaɗai yanzu a ina manyan suke?” Ya tambaya.

Girgiza kai ta yi “Dan Allah ka kyale su inma ansa sun ɗaukemu nasan ba zasu kula da mu ba, banda kuma gashi an rarrabamu in muna tare ko yaya ne zamuyi iyawar mu dan taimakon juna zakuma mufi shakuwa.” Ta fada a marai-raice.

“Shi kenan, akwai wata mata an faɗamin mijin ta ne ya rasu, basu haihu ba danginsa sun saida gidan da take ta na neman haya, da zan sata a wani shikenan yanzu zan mata magana, in zata karɓi wannan da kuke ciki ta biya kuɗin rabi, sai ku zauna tare ku ba sai kun bada ba, a ƙalla kuna da wadda zata ganku babba.”

Tunda ya fara maganar sai yanzu ta ji sanyi a ranta, hawayen farin ciki ya zuraro mata, godiya kawai take masa.

“Jaririn ne a baya?” Ya faɗa, murya a sanyaye tausayin yaran duk ya cika shi. Cikin sauri ta ce, “Eh.”

“Kawo shi muganshi” Ta kwantoshi ji ki na rawa.

“Masha Allah, ya sunansa?” Ummu Hani ta ce, “Muhd” Usaina tai saurin cewa, “Ɗan ƙani.”

Murmushin ya yi, “Ah ki ce Ɗan ƙani ne.” “Eh mana.” Hasana ta faɗa tana matsawa kusa dashi.

“Kasan mene? Yaran suka faɗa, girgiza kai ya yi alamar a’a, “Ummanmu ce ta haifeshi, kan ta tafi yanzu yaya ce Ummanmu.” Shiru kawai ya yi ya kasa magana, yanzu inba zalincin danginsu yarannan ba ta yaya za’a ce yarinya ƙarama haka ita zata kula da yara harda jariri.

Miƙo mata shi ya yi, “Ni zan wu ce in ta amince matar zaku ga ta zo, ku gyara daya ɗakin.” Ya faɗa yana zira hannu a aljihu dan ciro kuɗi.

Dubu goma ya miƙa mata, “Ga wannan ko wani abunne ku dinga siyarwa, yadda take godiya kai ka ce ya bata duniya ne ji ya yi da ace yanada wanda yafi haka da tabbas sai ya daɗa masu sai dai bashi dasu.

Alhaji ubale ba wani babba bane, zamu iya cewa matashi ne, dan ba zai gaza shekara arba’in da biyu ba, yana zaune garin Kaduna yana aiki, shida iyalinsa gidansu Ummu Hani gidansa ne da ya ci gado, inda duk shekara yake zuwa garin kano dan karɓar kuɗi gurin masu hayarsa, gida uku ne ɗaya nasa biyu na ƴan uwansa mata, wanda duk shi yake kula dasu.

Daɗi biyu ne ya cika Ummu Hani ga kuɗin da bata ya kuma tunatar da ita zafata iya sana’a, ga kuma alƙawarin kawo musu wata akalla zasu samu raguwar tsoro aransu.

Koda su Aisha suka dawo bayan sunci abinci kasantuwar alhamis ba islamiya suna gida, ummu taga ga damar yi musu maganar sana’ar.

Yawwa Daman Ɗazu Alhaji ubale yazo, me innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, yaushe? me ya ce? su biyun suka faɗa atare zaton su ko ya ce subar gidan.

Murmushi Ummu Hani tai, gami da ciro kuɗin da ya bata, shi ya bani ajiyar zuciya sukai Aisha ta ce to me ya ce?

Bayanin yadda akai komai sannan ta ce to yanzu wa ce sana’a kuke ganin ya da ce muyi? Wadda ba tallah cikin ta.

Duk shiru suka yi, kamin Sajida ta ce “yaya tunda muna da shinkafa ki dinga dafawa, kinga muna ci muna saidawa kuɗin sai ki siyo su kayan miya, sauran ki adana sabida irin siyan su magani.”

Murmushi Ummu tai Sajida akwai tunani duk da ba wani shekaru ne da ita ba.

“Aikam yaya wannan shawarar ta yi wallahi, kuma kinga babu mai shinkafa nan kusa anjima sai mu je mu farfaɗawa jama’a” Inji Aisha.

“Tam shikenan ina ganin innaje siyo kayan miyar har fulawa zan siyo sai mudinga fanke da safe” Inji Ummu “Hakan ma ya yi” Duk suka faɗa.

Duk ihun da su Hasana suke, ƙin tafiya da su Ummu Hani ta yi, dan tasan kaya ne zasu mata yawa, shima Muhammad da kamar ta barshi, ganin su Aisha za su fita farfaɗawa jama’a yasa ta goyashi tai kasuwar rimi.

Aisha ce ta kulle gidan tana riƙe da Hasana inda Sajida ke riƙe da Usaina Khairiyya a gefe, gidan da ke kallonsu suka fara shiga suka bada ajiyar makulli sannan suka faɗamata za su fara saida shinkafa da fanke sannan su ka yi waje.

Gida gida suka dinga bi, gami da gun masu shaguna, duk matashin da suka gani suna faɗa masa, dan sun san kowa kuma kowa yasansu su kan ce ya tayasu talla.

Sai yanma liss Ummu Hani ta dawo Aisha da sauran suka gyara kayan miya dan kaiwa markaɗe na miyar gobe.

Zuwa isha Ummu Hani ta gama soya tattasan ta, ta sa kanwa miya kawai yake jira a haɗa da shi, saukewa ta yi ta raba biyu ta barshi dan shan iska kamin ta rufe da abin ta ce shinkafa.

Tuni ta tafasa naman ta shima ta so ye abin ta, haka ma kifin ta ta soya shi.

Sai da ta tabbatar ta gama komai, sannan ta zuba wa ƙannenta abinci, ba komai ba ne face dafadikan shinkafa, cikin naman da ta siyo dan abincin siyarwar ta sanya musu, mutun ɗaya biyu, naman yasa su Hasana suka kasa bacci tun da ta kawo suke murna zasu ci nama.

Sunaci yaran suna nishaɗi, yara ne ba masu rainuwa ba, duk da cewar rabi rabi ta basu yadda suke cikin farin ciki, ka ce ta ciccika musu kwano ne.

Kamar ko yaushe ita kaɗan ta zuba ta ci, danma tana gudun mitar Aisha ne da itakam bazata ci ba.

Ummu Hani na ɗaya daga cikin mutanen da basa son cin abinci sai kayan kwalama.

Kamar yadda ta saba sai da ta kulle gidan, sannan tai ɗaki dan kwantawa sabida tashin da Muhd ke kamata yasa dole take baccin wuri.

A tsakar gida ta bar su Aisha nata hira Kasancewa da wuta, bawai sakata take sawa ba a’a kwaɗone tun ummansu nada rai tasa me walda ya musu yadda za’a iya sanya kwado ta ciki, hakan yasa ummu hani batajin komai take kwanciyar ta ko ƙannen nata basu kwanta ba, dan tasan bazasu iya buɗe gidan ba bare su fice.

Kamar yadda ya saba, yauma kukansa ne wato muhd ya tashe ta, bata da nauyin bacci tanajinsa ta farka.

mama ta fara bashi sannan ta saɓa shi a kafaɗa yai gyatsa kamin ta goyashi yai luf abaya.

Agogon da ta kalla taga uku saura yasa ta fasa komawa bacci, ta ɗauko kayan fanken data siyo ta hau kwaɓi.

Ba me yawa ta kwaɓa ba, Gwangwani biyar ta kwaɓa dan tasan ko bai ƙare ba su da kansu zasu iya cinye shi a yini guda.

Sai da ta gama ta tabbatar ta rufe yadda zai tashi kamin safiya sannan ta koma ɗaki ta ajiye gefenta sannan ta sauko da Muhd ta kwantar itama ta kwanta.

Da sassafe ta tashi sai da ta tabbatar ta haɗawa ƙananan ta abinda zasu ci ta soya musu fanken su, sannan ta ɗi bi kayan suyar ta ta yi soro dan anan take son yi, bata son ta ce cikin gida maza su dinga anfani da haka suna shigar musu gida.

Tai mamaki sosai yadda duk da kasancewar da wuri ta fara, anma ta fara samun masu fitowa siya, tana zuba wa mutun na farko da yazo siyan na ɗari tana zuba wa tana murmushi har ranta take jin daɗi, dan batai zaton zata samu masu siya ba a yau.

Zuwa bakwai da wani abin, ƙulli kaɗan ya rage, bata tashi ba su Aisha suka fito yaya mu zamu tafi.

Tom sai kun dawo Allah ya bada sa’a, suka ce amin ta ciro ɗari ta basu gashi ku raba.

Aisha ce ta zaro ido, “Yaya ɗari ta yi yawa.” Murmushi Ummu Hani ta yi, “ku dai kuje ai ku uku ne ina ɗari zatai muku yawa.”

To kawai A’isha ta ce, ta amsa suka yi waje a hanya ta samu canji ta bawa biyun ashirin ashirin ta ce wannan zamu ajiye sabida wataran kunsan yaya tunda ta bada, in na tsaya musu yanzu za tai fishi.

Hakan ya yi suma suka ce dan goyon bayan Aisha.

Kan takwas Ummu ta gama suyar ta tas, ta kwashi kayanta tai cikin gida sai da ta wanke komai sannan ta haɗa ruwan wankan muhd ta kai ɗaki.

Sai da ta masa wanka sannan ta tashi su Hasana suma ta musu, ta basu abincin su, ta ce su kula da muhd ta haɗa ruwa, me dumi ta shiga wanka yadda take jin jikin ta na ciwo dole tasan sai tai wanka da ruwan zafi zata samu sa’ida.

Koda ta fito karyawa ta yi ta ce kar su hasana suyi hayaniya ta kulle gida tai kwanciyarta kamin wasu mintina bacci yai gaba da ita.

Bata farka ba sai wurin goma, su Hasana nata wasa da Muhd ta miƙe ta ɗora  shinkafa kamar wadda zasu iya ci har dare, ta ɗora yadda tasan ko ba masu siye zasu ci abar su.

Zuwa sha biyu ta gama komai, har miya tana juye wa a kular da ta aro a maƙota ne, su A’isha suka dawo kasancewar juma’a ce yau da wuri aka taso su.

Aisha tai mamakin yadda yayar ta su tai sauri haka, tun a period ɗin karshe take burin ata shi suzo su taya ta aiki sai dai har ma ta gama.

Yaya mai zai hana ki huta ki kawo in siyar inji Aisha

“Ce miki na yi na gaji, kije ki zuba muku abinci in kunci ku kwashe kayan ɗakinku ku dawo dasu ɗakin mu, ku gyara shi kar muje matar tazo bamu gyara ba ummu hani ta bawa A’isha amsa.

Tom shikenan Aisha ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukan kula guda, bara mukai miki soron sajida tai saurin ɗaukan ɗayar sukai waje.

Yauma yaran cikin farin ciki suke dan Ummu tasa musu kifi, gashi kuma da miya.

Aisha da Sajida ne suka hau gyaran ɗaki inda Khairiyya ta goya Muhd su Hasana su ka yi soro gurin Ummansu kamar yadda yanzu suke kiran yayar tasu, bayan sun gama cin abincin nasu.

*****

Motoci ne da suka amsa sunansu na mota, ƙirar sabuwar ya yi, a jere suke tafiya, kai tsaye airport suka nufa wato Muhd Murtala da ke nan garin kano.

Tawagar gidan Alhaji Lukman kenan, Hamshaƙin ɗan kasuwa, kan hanyarsu ta tarɓo autan gidansa, kuma namiji tilo da Allah ya bashi cikin yaransa shida, wato Ayatullah.

Basu da ɗe da isa ba jirgin su Ayatullah ya sauka, sun isa da wuri ne dan baya son jira.
A nitse ya ke sakkowa daga girgin kai ka ce baya son sakkowa, sai dai ba haka bane ɗabi’ar sa ce haka, komai nasa a nitse yake abinsa.

Koda ya ƙaraso, dai dai inda masu tarar matafiya suke tsayawa ya yi tsayi yana bin gurin da ido dan gano mataryansa.

Ya Fatima ya fara hanga, gurin ya nufa yana murmushi da saurinsa.

Ta baya ya rungumeta, “I missed you so much yaya, ji yo dashi ta yi bari kawai My boi nafi missing ɗin ka.”

Dady dake gefe ya ce “Eyye wato yar uwarka kawai kai missing, mu ko oho ko.” Mami ta ce, “Kyale shi Dadin zainab zo mu tafi.”

Da sauri Ayatullah ya ƙarasa inda suke, “Habawa kuma kunsan nai missing ɗinku sosai daga ku sai yaya da kowa da kowa kawai ita na fara gani ne.” Ya faɗa yana langaɓe kai.

“Eh mana ai dole ita zaka fara gani, tunda ita ce aranka.” Mami ta faɗa tana masa hararar wasa.

Duk su biyun ya haɗa yasanya ajikinsa, yana faɗin “Haba sai yanzu na ji sanyi a raina, rashin iyaye kusa ai ba daɗi.” Gabaki ɗaya suka sa dariya.

Kaga malam sakar min iya ye Zainab ta faɗa da salon tsokana.

Juyowa ya yi “Ke kuma wa ce, na sanki?” Harararsa ta yi.

“Oh na tuno ke ce wadda su Dady suka tsinto ko?” Ta kai masa duka ya kauce yana dariya.

Haka ya bi sauran ƴan uwan nasa su kai yaushe gamo, Zainab ce ta ƙarshe ahankula ya raɗa mata a kunne, nifa ban missing ɗinki ba, ture shi tai kaɗan alamar wasa, to ni ce maka akai na damu ka dawo ne, ni intani ne kama bar ƙasar ka dena dawowa, masa mu sarari, cikin wasa duk take faɗin haka.

Kyaji dashi ni karki cika ni da abinda ba har zuciyarki yake ba, nasani ji kike tamkar kije ki jawoni.

Turo baki tai, ni kaga yan zuma ka koma, baka ji ke ɗazu me mami ta ce ba Dadin Zainab, meaning ba wanda yai missing ɗinka Dadinma anbarmin.

Yatsina fuska ya yi, ya yi rau rau da idanunsa, ya matsa jikin yayar su Yayata kinganta ko.

Ya Fatima ce ta kai mata duka, Allah zainab ki kiyaye mu, duk aka sa dariya sukai gurin motacinsu.

Dady da mami sun shiga tasu motar, Mami ta ce ka shigo nan kawai mu tafi, Zainab tai saurin cewa ai gwanda dai ya shiga ɗin, danni wannan sabuwar ni ce a cikinta, ba me hanani shanawa.

Aiko kanta rufe bakin ta ya shige motar itama kuwa ta shige kinge, malama wallahi bazai yiwu ni inshiga tsohuwa ba, sai dai mu shiga wannan ɗin tare, tagumi ta yi, da sigar wasa Baba Habu muje ta ce da driver ɗin.

Ayatullah kenan Matashi ɗan gata gaba da baya ta gun iyaye da ƴan uwa.

Ya Fatima ita ce Babba, sun shaƙu sosai dashi, kusan ita tai rainonsa hakan yasa kamin ma ya ambaci mamin su sau ɗaya, sunan yaya ya fito daga bakinsa sau goma.

Zainab ita ce daga ita sai shi, sai dai ta bashi shekara bakwai, dan har su mami sunyi zaton ita ce auta, Allah ya kawo Ayatullah sai dai tazarar shekarun su bai sa ya be zama kamar sakonta ba.

Yadda suke rayuwa kai kace baifi shekara biyu ko ɗaya ta bashi ba, wato sako da sako suyi faɗa su shirya tun yarinta, yanzu da aka girma babu faɗan sai dai sukan gwada sakuntar.

*****

Ummu Hani ce zaune a zauren gidansu inda kulolin abincin ke daga ƙofar gida, kamar ɗazu da safe, ta yi mamakin yadda ake ta siya daɗi da farin ciki ya cikata.

Zuwa huɗu saura ta siyar tas, tasa Usaina ta kira su Sajida suka shigar da kulolin.

Tana gida sai aikowa ake siyan shinkafa, tana cewa ta ƙare sai gobe, dan duk wanda ya siya musamman matasa sai ya faɗawa abokinsa dan kuwa Ummu Hani ta iya girki.

Rainon ummansu kenan, tun yaranta suna ƙanana take sanyasu aika ce aika ce hakan yasa Ummu ta horo ta ko ina.

Zaune suke a tsakar gida, A’isha na wanke wanke Muhd na hannun Sajida inda Ummu Hani ke lissafa kuɗi.

“Kunga cinikin da albarka wallahi inaga indai zamu ɗore ahaka koda abincin mu ƙare zamu iya rayuwa.”

Aisha ce ta ce “Gaskiya kam, nima fa yaya nayi mamakin yadda daga farawa har an waye damu.”

“Nima dai gaskiya.” inji Sadija.

“Ina ga ko dan jiyan mun yawata da yawa mun farfaɗa in wasu sun mance wasu zasu tuna.” Kairiyya ta faɗa.

Yawwa na ce ba, “Ya kuke ganin zamuyi da ribar da muke samu.” Ummu Hani ta tambaya.

Inaga kawai banki zamu samu mu tara kinga kamar yadda kika faɗa ɗazu in abincin sadakar can ya ƙare mu kuma already mun tara na siyan wani buhun shinkafar, A’isha ta ce tana ƙokarin dire kwandon data kife kwanuka.

“Bari to in wanka sai innaje rimin siyo kayan miya in ta wo da banki insha Allah.” Ummu Hani faɗa gami da ɗaukar Muhd daga cinyar Sajida.

“Yau tunda kuna gida agunku zan barshi sabida naga gajiya yake a bayan, ga iska jiya sai da na shafeshi da rab da daddare sabida yadda hancinsa ya toshe, ina ga yau ma sai na siyo man shanu in saka kasa a hancin sa girjinsa.” Ummu Hani take faɗawa ƙannen nata.

“Tom shi kenan” Su ka ce.

Mama ta bashi sai da ta tabbatar ya ƙoshi ya yi gyatsa ta miƙawa Aisha shi, tana faɗin “Sauran a mai mugunta,” gaba ki ɗaya suka sa dariya dan sun san da Aisha ta ke, ita ce gwanar yima yara mugunta, dan haka ne basa shiri sa su Usai.

Sai da Ummu Hani tai wanka ta shirya tsaf duk da ba wata kwalliya ta yi ba mai kawai da kwalli ta shafa ta goge fuskarta da tsumma anman hakan baisa kyanta ya ƙi fitowa ba.

Har ta ce musu ta fita, ta dawo. “Ku maida wa da momin walid kulolinta tunda sana’a ba yar ƙare ba ce, zan siyo mana bokitai masu murfi muga zuwa musamu wani abin sai muma musayi ta mu.”

Khairiyya ce ta miƙe da sauri tana faɗin “bari in miƙa mata.”

“To uwar yawo zauna.” Sajida ki miƙa mata kuma wallahi na dawo aka ce kun fi ce zan gamu da yaro, ta faɗa tana shafa kan Muhd ji take tamkar karta barshi sai dai ta na gudan masa mura, ta yi waje ita da Sajida inda ita Sajida ta shiga maƙota Ummu tai titi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 5Ummu Hani 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×