Skip to content
Part 7 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Koda Sajida ta kaiwa Momin Walid kulolin cewa tayi su aje agunsu kawai ita daman ba anfani take dasu ba, inma ta aje mutuwa zasuyi akawai, in yaso daga baya in sun samu kuɗi sosai sa biya ta.

Koda Ummu Hani ta dawo suka faɗa mata da kanta ta shiga taima Momin Walid godiya, dan daman botiki guda ta iya samu ta siyo kuɗin sun yanke mata, dan ta biya ta ƴan gwanjo kowa cikin ƙannen nata ta siyo masa riga guda ta sanyi, duk da zafi ake ganin anata bonanza naira ɗari yasa taga bara ta siyo tasan in sanyi yazo zasu kai ɗari biyar biyar.

Kamar jiya adaren Ummu Hani ta soya komai cikin dare ta kwaɓa fanken ta kamin ta koma bacci.

Da asussuba ta tashi ta soya na ƙannen ta, ta ɗora ruwan koko da ruwan wankansu a ƙatuwar tukunya sannan ta ɗebi kayan suyar ta ta kai soro.

Gida ta dawo ta gyara ko ina sannan ta koma ɗaki tana jiran ruwan kokon ya yi ta dama.

Kusan shida saura minti biyar ta kammala komai ta tashi su Aisha dan su shirya zuwa makaranta kamar kullum ɗaya cikin su ce ta shiga wanka inda biyu Ummu ta zuba musu karin su suna ci.

Shida da rabi Ummu ta buɗe gida ta ɗora manta akasko dan suya.Kamar jiya Bashir me shago ne ya fara zuwa gaishe shi ta fara yi, kamin ta ta ce dan Allah ko zaka ɗan jira yanzu na ɗora kasko ba komai ya ce sai dai bana jurai tsaiwa.

Murmushi ta yi ta tashi daga kujerar da take ta ce ga wannan ba in ɗauko wata, to kawai ya ce yaja ya zauna.

Tana shiga taga Muhd ya tashi yana kuka da sauri ta amsheshi ta hau rarrashi sai da ta bashi mama ta goya shi jikin filo ta jingine a bango tuni yai luf duk da bai bacci ba. Sai a lokacin ta tuna tafa ɗora kaskon mai da sauri tai waje riƙe da kujera.

Turus ta tsaya ganin Bashir na jefa mata cikin mai har ya yi kasko ɗaya da alamu ma an siya.

Da sauri ta ƙara tana faɗin “dan Allah ka yi haƙuri wallahi jaririnmu ne ya tashi shine na manta na ɗora mai.”

Juyowa ya yi ya sakar mata murmushi, “Karki damu na iya aikin gida ai.” Itama murmushin ta yi eh duk da haka ka yi haƙuri.

“No ni nasa kaina Aisha ta zo zata soya ba ce ta je ta yi shirin makarantar ta, kinga anyi ma ɗari da hamsin” “Tom mun gode” Ta ce.

Kujerarsa yaja gefe ita kuma ta aje tata tana suyar yana kallon ta, tausayin yaran yake ji tun lokacin ma iyayansu nada rai bare yanzu da suke rayuwa su kaɗai lokacin da Ummansu ta rasu tinaninsa ya zasu rayu sai dai kasan cewarsa namiji bakuma su taɓa magana ba yasa yake ta tsoron zuwa yaji ya suke dan gudun kar su yaran da jama’a suyi tsammanin yanason ya yi amfani da rashin iyayansu ya cutar dasu.

Lokacin da su Aisha suka faɗa masa zasu fara sana’a daɗi yaji aransa sai yaji yana son ko yaya ne ya taka rawa a cikin masu yi masu ciniki.

A kaskon da ta juye ta zuba masa harda ƙari yana kallo amsa ya yi ya maida ƙarin “Kinga ni wannan ma da badan akwai Bala ba yamin yawa, karki damu banyi dan ki biya ba” Ya faɗa gami da in waje murmushi kawai ta yi bata taɓa sanin cewar Bashir nada kirki ba sai yau dan ko dariya baya yi.

Aisha da sauran ƙannen ta ne suka fito “Yaya mu mun tafi.” Ta ce “Tom Allah ya bada sa’a.” Suka ce “amin.” Ta basu kuɗin makarantar su suka wu ce.

Ta kusa tashi Kursum Babbar ƙawarta ta zo sanye ta ke da uniform murmushi suka hau yiwa juna.

Ummu hani ta ce “Malama ki ta fi makaranta, kin kusa makara.” Kursum ta ce “Zuwa nai in kuma jin ra’ayin ki dan Allah Ummu Ki daure ki komo makaranta, mutuwa bayana nufin ƙarshen rayuwar mu ba.”

“Uhum Kursum na rasa yadda za’ai ki gane, inna koma makaranta inyi yaya da Muhd da ƴan biyu.”

“Kai Ummu sau nawa kike son in faɗa miki ki kawowa ummanmu su in aka tashi sai ki ɗauke so.”

“Tom yanzu sa ace na kai mata su inna dawo me zan basu, su dasu Aisha ita ma Umma nema take, ku goma sha uku ne a gabanta, sannan a ce na ɗora mata nauyin mutun bakwai.”

“Karki damu a ƙalla nayi hizifi talatin da wani abin, na hadda ce nayi primary na yi jss ss dinma na fara, na iya karantawa in rubuta ya isheni rayuwa wallahi har raina ina gode ma Allah, wasu basu iya yadda na yi ba, inda rabona wataran zan koma duk daɗewa shi girma baya haha neman illimi.”

“Shi kenan Ummu ba in wu ce inna dawo zanzo ganin ɗanmu,” su ka yi murmushi baki ɗaya Kursum ta yi waje inda Ummu Hani ta bita da kallo kanta ta ɗaga sama dan shanye hawayen da suka biyo mata  dan ita yanzu tasa ma ranta babu abinda zaisa tai hawaye, indai kan kula da ƙannenta ne, tasan karatu nada anfani ada shine babban burin ta anman yanzu yadda ƙannenta zasu rayu rayuwa me kyau cikin tarbiyya ingantacciya shi ne babban burinta.

Koda ta koma gida su Hasana ta tasa ta yi musu wanka ta basu koko da fankensu sannan ta yi nata wankan kamin ta zo taima Muhd.

Zaune take tana ma Muhd wasa yan biyu zagaye da ita sunata sheƙa dariyarsu tuni ta nemi damuwar ɗazu ta rasa itama biye musu tai suke ta shirmensu.

Yau batajin bacci hakan yasa ta ɗora miya da wuri kan goma ma ta kammala ta bari sai sha ɗaya ta ɗora shinkafar.

*****

Koda su Ayatullah suka isa gida a parking space suka aje motocin su, kamin daga bisani su ƙarasa cikin gida gabaki ɗayan su a main parlour suka jibge, inda Ayatullah ya yi ciki dan yadda yakejin jikinsa in be wanka ba bazaiji sa’ida ba.

Sanye yake da Short da singlet lokacin. Da ya fito daga wanka ko da ya fito daga ɗakinsa tsayawa ya yi daga bakin ƙofa yaɗan kalli inda zai sada shi da inda mutan ke zaune ya kalli hanyar dining area shafa cikinsa ya gun cin abincin ya nufa dan yahajin yunwa in yaje hira za’ayi ta yi.

Abinci ne iri iri jere kan table ɗin, food flask ɗin farko da ya buɗe ne yasa wani farin ciki ya ziyar ce, shi gefe soyayyiyar doya ce sai gefe yam ball, kusan second best food ɗinsa kenan, saving kansa ya yi ya zuba lemon abarba me sanyi ya hau ci.

Tabbas ba abinda ya fi gida daɗi inba a gidanba shi baya taɓajin daɗin girki koda anyi irin wanda yake so ɗin kuwa.

Sosai ya ci duk da ba wani ci ne dashi ba, har ya miƙe ya dawo ya hau bubbuɗe abincin, aransa yanajin daɗi yasan duk dan shi akai inda ace bai zo shi kaɗai ci ba, da haka yan uwan nasa zasuyi ta mita sai ya ci wanda ko wacce tayi.

Flask ɗin ƙarshe da ya buɗe ne yasa ya koma ya zauna, wow kamshin miyar kukar da ya daki hancinsa, best food ɗinsa daga tuwo sai doya inda yasan da tuwon nan raba cikinsa  biyu zai yi, but still in ya tafi baici ba yasan bama zai iya magana ba sai tunanin miyar nan me daɗin ƙamshi.

Kaɗan ya zuba ya ci dan mai da yawun sa, sannan ya maida komai ya rife yana ƙoƙarin tashi yaji muryar Zainab na faɗin “Eyye sannu wato nan kazo kana kwashe mana abinci mu ko oho.”

Dariya ya yi “Kinga ni yanzu a koshe nake, in kinajin rigima ki bari zuwa gobe in inajin yunwa”. Ya bar gun.

Main falo ya nufa, kusa da Ya Fatima ya zauna yana faɗin “Kai Alhamdulillah yau na ci abincin gida.”

“Gashi can na rage muku kuje ku ci, Zainab da ke ƙokarin zama ta ce, ce maka akai mu almajirai ne.”

Ya Basira ta ce, “What, wai ka ci abincin kake nufi, murmushi ya yi kaina bisa wuya na.”

“To baka isa ba” inji kadija dole ka ci abinda na kawo bazan wuyar banza ba, to shi kenan Karki damu ai indai naku ne zanci nasu oh oh ne ko ɗanɗano, Zainab ta ce to daman an ce ma ni zan ɓata lokaci ne in wani maka girki.

Banza ya yi da ita dan ya bata haushi, ya dubi Mami ya ce “Mami gaskiya tuwon da kikamin ya yi daɗi sosai.” Ya dubi yah Fatima, “Nasan ke ki kai dangin doya ko?”

“Miyar in tayi ragowa asamin a firgi sai in ɗumama gobe.”

Dariya kowa yasa, Mamin ta ce, “To ni ce maka akai ni na ma tuwon, yayar ka ce ta yi, komai kagani akan table ɗin su sukayi ba hannuna.”

“Wow shi yasa nake sonki yaya.” Ya faɗa yana ɗora kansa bisa kafaɗar yaya Fatima.

“Ni Bani nai tuwo ba, Zainab ce ta yi.”  “what ya faɗa da zare idon wasa, haba no wonder wannan abinci ko taste babu, yanzu haka amai ke tasomin” Ya faɗa yana barin gurin, da sauri Zainab ta sa dariya tabi bayansa.

*****

Da rana ma sai da Bashir me kanti ya zo siyan shinkafa basu wani yi magana ba ya dai yiwa ƴan biyu da ke ta gefenta wasa ta zuba masa ya tafi.

Tana nan zaune ta kusa tashi ma motar da ke ɗauke da kayan Hajiya Balaraba ta tsaya a ƙofar gidan, matar ce ta fara saukowa ta karaso inda Ummu ke wato cikin soronsu.

Cikin mutunci da girmamawa Ummu Hani ta gaida matar dattijuwa ce da baza ta gaza shekara hansin da biyar ba.

“Ke ce Ummu Hani ko?” Ummu tai murmushi, “Eh ni ce.”

Itama matar murmushi ta yi, “Sunana Balaraba ni ce wadda Alhaji Ummaru ya muku bayani zamu zauna tare.”

Faɗaɗa murmushin ta Ummu Hani ta yi “Ayya sannu da zuwa, munata saka ran zuwan  ki sai yau Allah ya nifa” Inji ummu Hani.

“Eh wallahi wasu uzururruka suka tsaidani.”

Khairiyya Ummu ta kwalawa kira itama da ƙarfi ta amsa gami da fitowa tayo waje.

“Ku shiga ki nuna mata ɗakin ita ce wadda na yi muku bayani “Kara gaida ta Kairiyya ta yi.” Ta amshi jakarta su ka yi ciki.

Ɗakin ya yi matar ta faɗa duk da ta ci alwashin ko baiba haka zata zauna bare yanzu da ta kuma ganin yaran sai ta kuma tausaya musu, duk da cewar itama abin tausayi ce anman ba kamar su ba.

Sajida na wanke wanke Aisha na wasa da Muhd ta same su sai ta ji duk zuciyarta ta yi rauni.

Yaran data zo dasu ne suka shigo da kayan ba wasu tarkace ne da ita ba katifa ce da kayan sawarta da na girki da ƴan kwanuka.

Tana zaune riƙe da Muhd su A’isha suka shimfiɗa mata leda suka jera mata komai.

Ji take kamar ta yi kuka, inama ace yaranta ne da farin cikinta sai yafi haka, da take riƙe da Muhd tausayinsa da na ta ya cika ta.

Bata taɓa haihuwa ba, sun rayu da mijinta kusan shekara arba’in da ɗoriya, tun auren ƙuruciya sai dai Allah bai basu haihuwa ba.

Ya auri mataye duk sun gudu sun barshi sabida baya haihuwa, itama iyayanta sun sha raba auren har aure ta yi sau biyu, sai dai Allah bai bata haihuwa ba haka yasa da ta fito a auren ta na uku iyayanta suka haƙura suka kyaleta ta cigaba da zama da mijin ta.

Lokacin da yake jinya haka tai shekara biyar tana wahala dashi komai nasu ya kare ƴan uwansa duk suka gujeshi.  Allah gatansa ita ce gatansa, kullum cikin ci mata albarka ya ke dalin rashin lafiyarsa sai ritaya ta yi da fanshonsa da nata suke rayuwa.

Itama danginta ba wani ta tata suke ba kowa kansa da yaransa ya sani.

Lokacin da mijinta ya rasu lokacin ne ƴan uwansa suka fito su ala dole ga masu ɗan uwa kuma magada.

Ko arba’in ba’ai ba suka saida gidansa suka bata tuminin takabar ta, ta yi kuka iya kuka dan gidan ita dashi su ka yi wahalarsa kasancewar ba sheda dole ta haƙura da shi tanaji tana gani tabar gidan.

Gidan su ta koma wanda ya ke yanzu fal da ƴan uwa kasancewar tun rasuwar iyayansu ba’a raba gado ba yasa ba wanda ya kore ta, dan tana da gado agidan sai dai kuma kowa baya baya yake da ita, dan gani suke tamkar zata ɗora musu nauyi.

Alokacin ta kuma kokawa rashin haihuwa, gashi dai ƴan uwanta ne uwa ɗaya uba ɗaya, anman gudunta suke sabida karta zame musu lalura yanzu da ace tana da yaranta kome take ciki haka zasu kula da ita…

Hajiya Balaraba ba ta jima da zuwa ba Ummu ta saida abincin ta koma cikin gida ita da y’an biyu.

A tsakar gida ta samu Hajiyan har lokacin tana riƙe da Muhd sauran na zazzaune suna hira kaɗan kaɗan.

Itama Ummu Hani zaman ta yi suka ci gaba da hirar tare.

Da daddare Hajiya ta ce, ko su Hasana ne Ummu ta bata su kwana tare Ummu ta yi murmushi. “Aikam dai waɗannan hanaki bacci zasu yi,” “ba kiga tun ɗazu suke raɓe raɓe ba dan kar ki ce zaki tafi dasu.”

Dariya Hajiya ta yi “To shikenan Khairiyya da Sadija ko Aisha sai mu dinga kwana tare.”

“Tam shi kenan A’isha ku ɗauki kayan shinfiɗar ku” ‘To suka ce.”

Cikin dare kasa bacci Ummu Hani ta yi yadda jikin Usaina ya yi zafi zau, alamar zazzaɓi, fanadal ta bata ta sanya tsumma da ruwan sanyi ta shafe ta dashi, sai dai har lokacin jikin babu daɗi.

Suna a haka Muhd ya tashi shimfiɗe Usaina ɗin ta yi ta Ɗaukeshi mama ta ba shi.

Shima ɗin da alamu bayajin daɗi dan sai kuka yake da kyar ta samu ya yi bacci ta goya shi.

Ko fanken safe bata samu ta kwaɓa ba, sabida yadda jiƙin Usaina ya yi zafi ga yarinyar da dauriya ko kuka bata yi ta yi shiru da alamu tanajin jiki.

Kwana Ummu Hani tai ba ta yi bacci ba, sai asuba jikin Usaina ya yi dama dama mai makon Ummu Hani ta kwanta bacci fita tai dan sama musu me za su ci.

Sai da ta kammala komai ta tashi Usaina, ta bata shayi mai zafi duk son tea na yaran nan kasa sha tai.

Hakan yasa Ummu Hani ta tashi su Aisha ta ce in sun shirya su faɗawa Hajiya bata son tashin ta ne zata kai Usaina Asibiti.

Muhammad na baya Usaina na kafaɗar ta, ko nauyi bata ji Hasana na biye da ita haka suka fi ce.

A hanya ta gamu da Bashir a nitse ta gaida shi, ya amsa. “A’a ina zuwa haka kinsan kuwa gidan naku na nufa siyan fanke.”

Murmushin ƙarfin hali ta yi “Ai yau nama manta wallahi da batun fanke, tun dare Usaina ba lafiya zan kaita asibiti.”

“Ayya kawo in rike miki ita” “A’a kabar ta zan iya wallahi.”

“Eh ai bance bazaki iya ba, tunda ma yanzun a hannunki take kawai hanyar zanyi ne gurin Maman Bola na siyi ƙosai tinda ba fanken.”

“Oh” Ta ce ta miƙa masa ita, sun kai asibitin primary health care dake nan gaba dasu.

A asibiti an basu magani suka koma gida Bashir ɗinne dai ya kawo mata Usaina ɗin, Har gida, ta yi ta godiya dan ta yi tayi ya barshi ya ƙi, ya ce sai ya ƙarasa ladansa.

Su A’isha sun tafi makarantar Ummu Hani ta dawo, aiko Hajita tai ta faɗa, danme bazata faɗa mata ba ita so take su maida ita uwa Ummu tai ta bata haƙuri.

Hajiyam ce ta kula mata da Muhd, ita kuma ta kula da Usaina tare su kai girkin rana ba siyarwa Ummu Hani ta fita dasu.

Daren yau duk dauriya irinta Ummu Hani kuka tasa, gashi ta kasa tashin kowa yadda duk ukun zazzaɓi ya rufesu Hasana uwar rigima kuka kawai take Muhd ma haka, ga Usaina kwance shinfiɗe ta ta yi, ta goya Muhd ta rungume Hasana tana rarrashinta gashi dai jikin Usaina ya fi zafi alamun zazzaɓin ya kamata sosai, sai dai Hasana tafi tsorata Ummu Hani yadda taga duk wasu abubuwa sun firfito mata a jiki.

Sai wajen uku ta samu biyu su kai bacci Muhd yama ki kama maman duk son sa da shi, abinda ya kuma tsorata ta kenan.

Kamar jiya yadda taga dare haka ta ga rana, da asussuba ta tashi su Hajiya hankalin hajiya ya tashi ganin jikin yaran towo gaskiya ina ganin Hasiya Bayero za’a kaisu, ni zan goya Hasana inyaso ke ki goya Usaina Khairiyya ta goya muhd ku su Aisha ku zauna a gida.

Tare suka fi ce, Bashir na ganinsu zasu wu ce ta bakin shagonsa ya tawo lafiya dai, nan suka masa bayani subhanallahi ya faɗa ba inzo muje zaifi kyau da namiji.

Da sauri Ummu Hani ta ce shagonfa  karki daku yanzu Bala zai ƙaraso, “Tom” Ta ce kawai su ka yi gaba.

Shine ya tsarar musu adaidai ta, inda su kai asibitin hankalin Ummu Hani ba’a kwance yake ba yadda takejin ɗimin jikin Usaina a bayanta yana tsoratata haka mintina kaɗan kaɗan takan taɓa na sauran.

Kasancewar sunje da wuri basu samu layi da yawa ba, duk da wasu sun rigasu sosai.

Likitan ya yi ƙoƙarinsa inda ya dubasu ƙarshe ya basu gwaje gwaje. Gyanda ce inda aka bawa Hasana magani dan ita tata ta fito, wato da sauƙi, su ta su Usaina ta kume  a ciki, kwantar da Usaina da Muhd a kai anman duk da haka agunta tabar Hasanan dan kuwa tasan inma am tafi da ita gida kuka kawai zata ishe su dashi.

Sai yanma Ummu Hani ta ce da Hajiya gwanda su tafi in yaso ta bar mata Kairiyya kar abarsu A’isha su kaɗai su kwana.

Hajiya ta so ta zauna Ummu ta koma gida ta huta, sai dai kuma yadda taga yaran basu waye da ita ba yasa ta koma gida.

Shima Bashir da ya tabbatar an basu kwanciya komawa shago ya yi, sai da rana yaje ya amso abinci ya kawo musu hakama da mangari ba, shi ya rako su Aisha bayan Hajiya ta koma gida.

Wajen takwas suma su Aisha suka tafi suka bar Ummu Hani da Khairiyya dan jinyar.

<< Ummu Hani 6Ummu Hani 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×