Skip to content
Part 8 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Sai dare mazajen yayyen Ayatullah ɗin suka zo ɗaukan su, ya so ya bi yaya Fatima, Mami ta ce be isa ba, ba inda zai je.

Hannun Abbakar mijin Zainab Ayatullah ya riƙo, yay ce pls yaya na karka bari matar ka ta dawo gobe, anman dai kasa ta dafa min tuwo sai ka kawon, gabaki ɗaya kowa yasa dariya Abubakar ya ce kar kaji komai nawan, kamar bata dawo ba.

Washe gari Ayatullah na bacci sai jin an bigeshi ya yi, da hanzari ya farka inda yaran suka sa dariya, tsuke fuska ya yi, wato sai yau kuka zo ko, ya faɗa, we are sorry uncle jiya akwai school suka haɗa baki.

Tom shikenan muje parlour su kayi waje baki ɗaya cike da farin ciki. Kamar jiya yauma ƴan uwan nasa sun hallara, nan akai breakfast ko dining area basu je ba, suka hau hirar yaushe gamo.

Ayatullah yana son yan uwansa sosai tare da yaran su. Yau kam Mami da Dady sunfi kowa farin ciki, ganin yadda gidan ya cika da zurriyar su, Balƙisa ce kawai bata nan, wato babbar jikar gidan, suna exam ne ita, suna sa ran anjima zata iso in ta kammala.

Ayatullah ya dawo daga masallaci sai ji ya yi an rungume shi ana ihu, ture ta ya yi kaɗan, ke nifa ba ruwa na da ke, sai yau kikaga damar zuwa dubanin, tai murmushi, kai uncle kaima kasan daba dan exam ba ni zan tuƙoka zuwa gida, ya lakuce mata hanci, kajimin yarinya, ta ina zaki tuƙoni zuwa gidan.

“Kai lallaima Uncle, am 15 fa, and kana cemin yarinya,” “to sannu gwaggo ina wuni” ya faɗa yana rissinawa.

Dariya tasa “lafiya ƙalau ɗannan,” “Eyye yarinyar nan kin rainani.” Ta yi ciki da gudu ya bita yana ɗan sauri.

Balƙisa kenan ɗiya ga ya Fatima ita ce jikar farko a gidan Alhaji Lukman, wanda duk da cewar Ayatullah ya bata wajen 11 yrs, anman suna mu’amalarsu tamkar sa’ani, may be shaƙuwar dake tsakanin Ayatullah da ummanta ce ta shafeta.

Balƙisa na shiga ɗakinsa ta shiga, ta hau bincike yana ganin bata falon yasan sauran zancen, da sauri ya ƙarasa ɗakin nasa.

Ita da Yaya zainab ya gani suna dube dube.

“Kai lallaima mutanen nan, sata ido biyu” Da sauri Balƙisa ta ƙarasa ta riƙe masa hannu, “Uncle wai ina ka aje jakun kunan ka ne, tun jiya nake addu’a Allah yasa baka buɗe ba, a buɗe agabana.”

   Anti Zee ta ce “Baka buɗe, shi ne muka zo nema don ɗaukan namu tsarabar.”

Rike ƙugu ya yi tamkar mace abinka da Tanko na mata na mata, “Eyye wato ma kuɗauka ba in baku ba.”

Dariya suka yi, “eh mana, suna ina jakun kunan,”  “Sai ku danne ni ku kwata.”

Wayar sa da tai ƙara ce tasa duk su kai shiru, dan ya ɗauka.

“Assalamu alaikum,” kamar yadda ɗaɓi’arsa ta ke ya faɗa.

“Please ina magana da Ayatu ne?” Aka tambaya a ɗayan ɓangaren, “eh” ya ce muryar sa na nuna alamun be gane me magana ba.

Ajiyar zuciya akai daga ɗaya ɓangaren, “Kana magana da Nasir Ɗahir Galadanci.” Murmushin fuskar Ayatullah ne ya ƙaru, “Ah Nasir ashe kana da contact ɗina har yanzu.”

“Eh,” kawai wanda ya kira kan nasa da Nasir ɗin ya ce, kamin ya ce, “Dan Allah taimako zaka min, wallahi ina cikin wani hali, kawai Allah ya tuno min da kai ina bugo number ɗinka kuma ta shiga.”

“Subhanallahi kana ina yanzun, me ya faru yimin kwatance gani nan zuwa.”
Ayatullah ya faɗa atare.

Kashe wayar yayi bayan yaji kwatancen, ya dubi su Zainab jakunkunan basu ƙaraso ba, may be jibi ni na fice suja bishi da kallo kawai.

Afalo yama su Mami bayani yai waje Mota ya ɗauka da sauri ya shilla titi.

*****

Maƙota nata zuwa Dubiya, yau satin su Ummu Hani guda a asibiti, likita ma ya ce mata maybe gobe ko jibi ya sallame su dan jiki ya yi kyau, duk da ita bata yadda ba yadda take ganin duk ƙyanda tayi caɓa caɓa jikin yaran, sai dai yanzu yan biyu har wasan su suke suna kuma iya cin abinci.

Yauma kamar kullum ɗakin nasu cike yake da ƴan dubiya nasu Ummu Hani da na sauran abokan jinyar su.

Zaune take ita da Kursum sunata hira ta aminai, Malam islamiyyarsu da ɗalibai suka zo nan suka ma su Muhd Addu’a suka bata abinda suka haɗa na taimako, suka fi ce, suna fita Bashir ya shigo riƙe da madara dan su Hasana sunfi amsar Shayi, wanda kusan shi ya ɗauki nauyin hakan, dan yawancin kuɗin Ummu sun ƙare gurin magani, ga kuɗin gado har na mutun biyu, dan daba dan masu zuwa dubiya na bata me hamsin me ɗari ba da tuni ta gaza.

Wani zubin in yan dubiya sukazo sai taji tamkar tai kuka, ganin cewar duk ciki fa masu jelen nan babu wanda yake jininsu na kusa ko na nesa, kawai abokanan arziƙi ne na unguwa.

Su Hasana na hango Bashir suka yi gunsa da gudu suna murna, bai damu da yanayin jikinsu ba ya sanyasu ajikinsa, yanason yaran akwai shiga rai.

Yaɗan jima a ɗakin kamin ya tashi ya ce shi ya wu ce sai da safe, Ummu Hani da kursun sukai ta yi masa godiya.

Sai isha sannan Kursum ta miƙe dan tafiya, dan kullum sai tazo da yanma bata tafiya sai isha’i ɗin.

Kamar koyaushe Khairiyya Ummu tasa ta kula dasu Muhd, ta tashi dan raka Kursum suna tafe suna hira haka suke ka rasa ke suke tattaunawa, zasu jima suna hira sannan in an tashi rabuwa ajima a bakin hanya ana hirar dai, kamin Kursum ta samu mota.

Da sauri ya fito yana ƙoƙarin kiran waya, karon da suka ci yasa wayar ta faɗi sun kuyawa ta yi ta ɗauki wayar  tai saurin miƙa masa, tana faɗin, “Dan Allah yi haƙuri ban kula ba.”

Khairiyya data fito da gudu tana faɗin yaya Muhd, yasa ta kamo hannunsa ta danƙa masa wayar ta yi ɗakin da gudu Kursum ta rufa mata baya.

Kuka Ummu tasa ta yi waje dan kiran likita, ganin Muhd na suma kamin likita yazo yaro ya sassanƙame.

Shiko Ayatullah kasa motsi ya yi, yabi inda yaran sukai da kallo tun da yake bai taɓa ganin inda bugun zuciyarsa ya ƙaru daga ɗora idanunsa kan mace ba sai yau.

Wayarsa da tai ƙara ne yasa ya ɗauka yana faɗin kana ina gani a Hasiya Bayeron.

Girgiza kai kawai ya yi gami da murmushi kamin ya bar gun, ya nufi inda Nasir ya kwatan ta masa

Yaron Nasir ɗin ne ba lafiya, ga ba kuɗi sabida malamin private ne, hutun corona da a kai ya sanya basa samun albashi kullun sai buga buga, shi ne leburanci shine dako.

Tare suka yi islamiyya da Ayatullah nan zubairiyya da ke Galadanci lokacin su Ayatullah suna cikin gari, kamin su koma GRA.

Duk wani taimako Ayatullah ya bada, shi ya ɗauki Nasir da yaron da matar Nasir zuwa Aminu Kano, sabida an mai da su can.

Ita kuwa Ummu Hani dakin likita ta yi, da gudu suka dawo a tare likitan ne ya juyo ya ce da wata nurse ta fitar da Ummu Hani, daga ɗakin yadda take kuka kai ka ce ya ce mata Muhd ya mutu ne.

Jijjiga ce irin ta maleria ga ƙyanda abinka da jariri jiki bai kwari,  dole ciwo ya wahalar da shi.

Da taimakon Allah likitan nan ya shawo kan lammarin ya na fitowa Ummu ta yi gunsa da sauri, murmushi ya mata hakan yasa ta saki ajiyar zuciya.

Ki je ki kula dashi insha Allah babu komai anman zai kyau ki nema masa gidan sauro gaskiya, koma in ce dukan su dan asibitin nan akwai sauro.

Godiya ta yi ta yima likitan, inda ya yi office ɗinsa ita kuma ta yi ciki.

Muhammad na bacci ta zuba masa ido, ayyanawa take aranta in ya mutu ya zataji, sai da Kursum taga hankalin aminiyar tata ya kwanta sannan ta mata sallama ta fice, Ummu kasa raka ta tai dan gani take kamar in ta kuma barin Muhd wani abun zai same shi.

Shi ko Ayatullah daga Aminu Kano gida ya wu ce, bayan ya ci abinci ya yi wanka ya motsa jiki, kamar yadda al’adar sa take gami da nafila ya faɗa gado dan kwanciya.

Sai dai me kasa bacci ya yi idanunsa yarinyar ɗazu kawai ke hango masa, yayin da kunnuwansa  ke tuno masa da sa’adda take bashi haƙuri cikin sanyin murya.

Fulo yasanya ya danne kansa, wai duk ko ya samu yai bacci anma ina shi har mamaki yake daga ganin mutun for few seconds ace kana tunaninsa haka.

Tashi yai dan duba agogo ƙarfe sha ɗaya da wani abun, a hankula ya sauka daga gadon ya fito daga ɗakinsa yana sanɗa.

Yasan yanzu a tsarin gidansu duk da shi namiji ne dare yayi ya fita, amma yana jin bazai iya bacci ba, in ba zuwa ya yi ya tambayi yarinyar nan me yasa ta tsays masa a rai ba.

Bai ɗauki mota ba dan yasan dole Dady zai ji shi, tunda iyanzu yana falon da bai da nisa da bakin gate yana kallon labarai,  dan Mami da wuri take barci dan kar ya tashe ta sai yazo nan ya zauna zuwa 12 ya koma.

Ɗakin mai gadi ya nufa aransa yana Addu’a Allah yasa bai tafi boys quarters ba, inda ya ke shi da iyalinsa.

Ya yi sa’a yana zaune yana jin radio.

“Ah Ayatu lafiya dai ko, “eh daman zan ɗan fita ne shi ne na ce kar a saka sakata, kawai a kulle da key.”

“Anman baka ganin dare yayi kasan dai dokar da Alhaji yasa kar in bari kowa ya fita after 9 ko.”

Murmushi Ayatullah yayi “karka damu ka ce baka ganni ba, bare ma bama za’a kaiga nemana ba insha Allah.”

Shiru Baba ya yi Ayatullah ya yi ta roƙonsa, kamin ya ce tom shi kenan dan Allah karka ka daɗe, to ya ce ya fi ce da sauri danma kar Baba ya canja ra’ayi

Yana fitowa tsoro ya kamashi duk da hasken da ya galmaye unguwar ya saba baya fitar dare a inda ya ke karatu kuma duk dare sai kaga wasu a waje.

Daurewa ya yi ya yi gidan ya Fatima dan basu da nisa, yana tafe yana juyawa bakajin komai sai bugawar iska karar bishiya na tashi, sai lokaci lokaci karnukan na ɗan kuka.

Da sauri ya ƙarasa hango Ya Abbakar na ƙoƙarin shiga da mota, tsayawa Abbakar ɗin yai ganin Ayatullah ɗin dan hasken da ke unguwar yasa ya ganeshi.

“A’a sarkin na ci wato sai da ka biyo ta,” Dariya Ayatullah yayi ya gai dashi kamin ya ce, “a’a ba gun ta nazo ba daman gunka na zo.”

“To ni kuma Ayatu,” “Eh Abba,” Sunan da yaransa ke ke faɗa masa shi Ayatullah ke faɗa masa.

“Ok tom mu shiga daga ciki ko,” da sauri Ayatullah ya ce, “No nan zaifi daman niyata insa mai gadi ya kiramin kai.” To Ya Abbakar ya ce ya fito daga motar.

Daman frnd ɗina ne ya kirani yaronsa ba lpy, Ayatullah ya masa bayanin ɗazu kamin ya ce shi ne nake son ka aran mota mami da Dady baza su bari in je ba, cewa zasu yi sai da safe kuma yana buƙatar kuɗi.”

Shiru Abbakar ya yi kamin Ayatullah ya riƙo hannunsa Please Abba, shi kenan Karka jima ya miƙa masa key ɗin motar, gami da zaro kuɗi ungo ka daɗa masa.

Sanin Halin Abbakar in yaƙi amsa masifa zai masa, yasa ya amsa yana godiya ya ja mota yabar gun.

Kai tsaye asibitin Hasiya Bayero ya nufa inda yaga yarinyar ɗazu ta yi nan shima ya yi, so kawai ya ke ya tambaye ta me yasa ta tsaya masa a rai.

Gado gado yake bi yana kalla ko zai ganta.

Kasan cewar dare yayi su Ummu Hani basa saka rai da zuwan kowa dubiya, yasa ta aje hijab ɗinta a gefe Muhd na cinyar ta tana bashi mama, yayin da suke hira da maƙociyar ta, wadda itama matashiya ce za tai shekara 19 tana jinyar ƴar ta tafari ne, sun saba sosai da Ummu Hani.

Kallon gaban sa da zai ne, suka haɗa ido da Ummu, da sauri Ummu Hani ta ja hijabinta ta lulluɓe jikin ta, shi kuma ya yi saurin juyawa baya..,

Kamar dazu girgiza kai kawai Ayatullah ya yi yabar dakin.  Murmushi ya yi bayan ya fita gami da dan bugun goshin sa yabar asibitin, Gida ya wu ce dan yasan yanzu gidan Ya Fatima sunyi bacci.

Ya yi sa’a Dady ya kwanta ya Parker mota ya yi dakin sa.

Kamar dazun kasa bacci ya yi, tashi ya yi ya ɗauki computer ɗinsa ya hau online, duk a ƙokarinsa na kore tunanin matar mutane, tsoron sa daya kar ya samu alhakin tunanin matar wani, wanda ya rasa me yasa ya ke tunanin ta, me yasa da ya tuna bugun zuciysrsa ke ƙaruwa.

Ita kuwa Ummu Hani tsaki kawai ta yi, inba wulaƙanci ba kawai cikin daren nan kai ba jami’in asibiti ba ka banko dakin mutane.

Hirar su suka ci gaba da Zainab inda ta kwantar da Muhd.

*****

Bashir ne zaune yana cin tuwo, Ummansu ta fito daga Madafa ta kalle shi ta girgiza kai, kamin ta ce kai yanzu dan Allah bakajin kunya a ce kullum ƙaton ka dakai sai dai ka shigo gida abaka ɗimame.

Murmushi ya yi kamin ya ce karki Damu Umma, insha Allah na kusa huta wannan gorin, kedai ki cigaba da mun addu’a very soon zan nemo matar aure.

Kaji ka baka shirya auren bane, anman inba haka ba ko Bushira da take masifar sonka ai da ka duba.

Da sauri ya miƙe ya wanke hannu, ni na fita ya ce yai waje.  Girgiza kai Umma ta yi ita kam zata so taga ranar da Bashir zai yadda ya kalli Bushira a matsayin mace.

Daga gida shagonsa ya wu ce ya ɗebi kayan da yasan Su Ummu zasu buƙata ya yi asibiti.

Ga mamakin sa an sallame su ta haɗa kayan su Muhd, shi kawai take jira tana ganinsa ta saki fuska gami da gaida shi cike da jin daɗi ya amsa.

Shi ya ɗauki Usaina dan har lokacin jikinta bai kwari ba, yayin da yake riƙe da sauran kayan da yazo dasu inda Sajida ta goya Muhd, Ummu Hani ta riƙe kayansu da Hasana.

Duk wani cike cike da cikon da ake buƙata Bashir ne ya yi, dan Ummu Hani kaf kuɗin ta ya ƙare Hajiya ce ma kwanaki ta bada itama abinda ba’a rasa ba.

Har ƙofar gida mai adaiadaita ya kai su, Bashir ya miƙawa Ummu Hani kayan da yazo dashi ta ce ina wallahi Ya Bashir mun gode bazan karɓa ba wanda kayi ma ya isa.

Yai yai ta amsa taƙi, ya ce tom shikenan alamar ya ji haushi, itakam Ummu haƙuri kawai ta bashi ta yi cikin gida, taƙi amsa ne sabida tasan ba wani ƙarfin jari ne dashi ba, ɗawainiyar da yayi da su tayi yawa in ta nuna zata dinga amsar kuɗinsa da cutarwa.

Cinikin su Ummu ya tsaya sabida babu kuɗin kayan miya fulawa da mai, shinkafar ma wataran gaya sukeci dan itama Hajiya ta ƙarar da kuɗinta.
Rayuwa ba daɗi sai dai aƙalla Ummu takanji sa’ida aranta inta tuna komai tsanani yana da sauƙi.

Bashir bai san me yasa har yanzu Ummu bata dawo da Abincin ba, yana son ya tambaya baya son taga yana musu shisshigi, ya yi tsanmanin ko so take jikin yaran ya yi kyau sosai sai dai kuma yanzu gashi ƴan biyu har yawonsu suke, bata dawo dashi ba.

Yaukam ya yi ƙundunbala bayan ya shiga sun gaisa da Hajiya, sun fito shida Ummu Hani ya ɗan kalleta kinsan kuwa nayi missing abincin ki, yau she za’a dawo mana dashi ne.

Murmushi tayi kamin ta ce bari kawai Yaya kuɗi sukai tsiya, shine Hajiya ta ce in bari a musu Fansho sai ta bani.

Shiru kawai ya yi ta dube shi ganin yayi shiru lafiya dai.

Yanzu Ummu daman baki ɗauken komai ba, dan dai kuɗin kayan miya da fulawa ba kya tambaya ta.

Murmushi ta yi bawai, “ban ɗaukeka komai bane, banason in ɗorama damuwar da ba taka ba, sannan naga kaima da kanka kai hidima a kwanciyar mu a asibiti shi yasa.”

“To naji in kin ɗauken mahinmanci yanzu nawa kuke buƙata?” “Eh to kamar dubu ɗaya da ɗari biyar, anma kusa fanshon ai karka damu.”

“Ban tambaye ki ko ankusa ko ba’a kusa ba muje ki amsa.”

 “Anma, kinga malama biyoni ya katseta yayin da yai gaba.”

  Murmushi kawai ta yi ta bi bayansa.

A ƙofar shagon ta tsaya ya auna mata fulawa da siga ya lissafo kuɗi dubu biyu ya bata.

Zare ido tai, kai ai sunyi yawa kinga in bakyaso ki zubar amsa tai tana murmushi, shikenan na amsa amma gaskiya Ba shi ne, yanzu ka ɗauko littafin Ba shin ka ka rubuta a gabana in gani.

Girgiza kai ya yi Ummu Hani akwai pride, shi yasa take kuma burge shi, duk da tana buƙatar taimako but still tana yin iya yinta dan mutunta kanta.

*****

Abun duniya ya ishi Ayatullah ko yaya ya ke ɓe shi kaɗai tunanin matar mutanen da be san me yasa ya ke yi ba, sai ya mamayeshi, fuskarta muryarta sune suke masa yawo a ka.

Ada ya tsara wata ɗaya zai yi a Nigeria, ba shiri ya samu ya kammala shirye shiryensa ya koma makaranta dan gani yake watakil in yama bar ƙasar zuciyarsa zata dena kawo masa unreasonable abubuwa.

Babu yadda gida basu yi ba ya zauna yaƙi, ya nuna wani abu ne ya taso masa mai mahimmanci dole haka suka haƙura suka ƙyale shi sukai masa rakiya koma.

*****

Cinikin Ummu Hani ya kankama kusan kamar da kullum cikin ɗauwainiya take na ƙanne dana abincin siyarwar ta.

Tun kwana biyar da dawo da cinikin ta haɗa kuɗin Bashir ta kaima sa da kyar ya amsa anmafa tasha mita.

Umman Bushira ce wadda ta kasance ƙanwa ga Umman Bashir ta shigo gidan su Bashir da alamu hankalinta ba’a kwance yake ba yadda yanayinta ya nuna.

Lafiya dai Bushira me ya faru haka, naganki duk a hargitse.

“Ai bari kawai Yaya matsalar ba tawa ba ce ni kaɗai ada na so in shiru na ga dai da cutuwa gwanda aima tufkar hanci.”

“To Lafiya me ya faru” Umma ta tambaya tana maida hankalinta ga Umman Bushira.

“Eh daman wannan yaron Bashir ne naga yana ƙoƙarin jawowa kansa jangwan.”

Ware ido Umma ta yi “Me yayi na shiga uku ni Hasiya.”

Kwantar da hankalin ki bai jawo ba tukun cewa nai yana ƙoƙarin jawowa kansa.”

Ƙishin-ƙishin najin yana soyayya da wata yarinya ko ince uwar mata, a shekaru ƙarama ce, anman ta maida kanta uwar mata tunda har shayarwa take.”

“To bazawara ce ko kuwa shegene da ita?” inji Umma.

“Ba ɗaya ƙanin ta ne kinsan bama shayarwar ce abin ji ba, a’a duk wanda zai aure ta na tabbata nauyi ya ɗorawa kansa, tunda ƙannenta shida a ƙarƙashin ta suke banda wata tsohuwa.”

“To” umma tasa dariya, kema dai Baraba da shiriri ta kike, ina Bashir zai je ya ɗaukowa kansa wannan wahalar, bacin da yasan kansa ma da kyar yake iya riƙeshi.

“Allah yaya ni nagani da idona yadda yake musu wahala inda zakije shagon nasa sai kinga ya faɗa.”

“Wai ke tsaya wasa ki ke ko kuwa?” Umma ta nutsu.

Wallahi yaya ba wasa nake ba na ce miki ni ganau ce.”

“Ina da sake, zai zo ya samen, dolema ya canja, mace gudama ya aka iya bare ga garke.”

“Yawwa gwanda dai ayima tifkar hanci wallahi in ba haka ba kuma kin haifawa wasu ne, tunda nasan a yanzu haka moran da su kai masa baki masa ba.”

“Ina fa na yi masa ni kullun ina tausayinsa ashe shi ya je ya ƙare a gun wata to da sake…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 7Ummu Hani 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×