Skip to content
Part 9 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Bashir yana shigowa Ummansa ta rifeshi da masifa, shiru kawai yayi bai ce koma ba, sai da ta gama sannan ya ce “wallahi Umma kome aka faɗa miki kan wai ina ɗawai niya da yaran nan Allah sharri ne, ki je ki gani su suke wahala da kansu Hasalima da na basu abashi suka amsa, daga baya suka biyani.”

“To naji inason wallahi ka fita sab garsu dan in yanzu in sun ɗauki nauyin kansu da an kwana biyu sun fuskanci kanasan ɗaya daga cikinsu shi kenan zasu dena nema su ɗora ma nauyi.”

Murmushi ya yi “kaji Umma ni kuma sai ka ce bansan me nake ba, zan yadda su ɗoran nauyi.” Daɗi ya cika Umma “ah to ashe kasan me kake.”

“Karki damu abincin ma aikawa zan adinga siyon da badan babu me abinci kusa ba sai Ɗanwake ai da bama zan dinga zuwa ba.”

Da haka Bashir ya kwantar da hankalin ummansa suka koma wata hirar.

Washe gari da sassafe Bashir ya shirya dan kwana yai yanason ya ɗora idanunsa kan kyakkyawar Fuskar Ummu Hani, aikam wanka kawai yayi baima tsaya kari ba yai shago.

Shida da rabi ya bar shago yayo gidan su Ummu Hani, kamar kullun da ya saba dan siyan fanke.

Kasan cewar angane fanken nasu, yasa tun sassafe da costomomi hakan yasa kawai gaisawa sukai tai shiru, dan ita ba mutun ba ce me sakin fuska duk da ta sakarwa Bashir fuska amma agun sana’arta bata wasa.

Da yawa matasan unguwar kanzo dan ko zasu samu su saba sai dai babu fuska.

Tana ƙoƙarin sallamarsa ya ce a’a ta sallami yara wanda makaranta zasu, yayi haka ne dan kawai bai gaji da kallon ta ba, guri ya ka ma ya samu zauna kawai.

Yana nan zaune Bushira tazo siyan Fanke yana ganinta ya tsuke fuska sama sama ya amsa gaisuwar ta, haushi ya cika ta ko fanken bata amsa ba tai gida.

Umman ta na zaune tana zuba dumamen yara ta dubi Bushira towo lele ba sallama, Bushira tai shiru “Lafiya dai me ya faru?”

Kuka Bushira tasa, “Ba yaya Bashir bane na ganshi gurin Ummu Hani sai fara’a yake mata yana gani na ya haɗe rai awani wulaƙan ce ma fa ya amsa gaisuwa ta.”

“Eyye lallaima yaron nan ki barni dashi, zan maganinsa wallahi Ibrahim jeka ka amso mata fanken ki tafi makarantar ki karki damu yau zai rabu da yarinyar nan.” Bushira ta sa murmushi “Aikam da na ji daɗi.”

*****

Ummu Hani na zaune tana zuba miya ga wani matashi da ya zo siyan shinkafa hango Kursum da ta yi ne yasa ta saki fuska suka sakarwa juna murmushi.

Sai da Matashin ya cinye ya fita sannan Ummu Hani ta dubi Kursum “Hajiya lafiya ina makarantar yanzu dai bai ci an tashi ba.”

Murmushin takaici Kursum ta yi “Bari kawai, Bana faɗa miki naci 8 credit a qualifying ba babu math.”

Eh haka ne munyi maganar lokacin muna asibiti.

“To duk yadda zamuyi ni da Umma mu haɗa kuɗin WAEC ɗina mun kasa tunda gov. bazata biyamin ba, shine umma ta ce kawai in haƙura in maimaita ssc 2 ɗin shine yasa yau baƙin ciki banje ba.”

Hararar ta Ummu Hani ta yi, “Eyye wato ke daɗi ne ya miki yawa ni yanzu da Ummanmu zata dawo ace in fadi in ta maimaitawa ko sau nawa ne wallahi bazan damu ba.”

Kina da dama kiyin anfani da abarki rayuwa dole da akwai faɗuwa.

Nisawa kaɗan Kursum ta yi kamin ta ce “Eh haka anman ni mutun ce dole akwai damuwa.”

“Haka ne yanzu nawa ne kuɗin exam ɗinne” Ummu Hani ta tambaya.

“Bari kawai 17k shiru” Ummu Hani ta yi na wasu mintina kamin ta ce, “To nawa kuka samu” “Eh mun samu 9k.”

“Oh bama yawa cikon ina zuwa,” ta shi ga gida yayin da Kursum ta miƙe itama dan zubawa Bala abinci.

Kuɗin da Ummu ke adanawa ta je ta ɗebo dubu goma ne takwas ta ɗebo tabar biyu.

“Kinga ungo wannan a cika,” a ɗan razame Kursum ta kalle ta kai “Ummu ke da kuke ajewa yanzu da bakwa ajewa ai da lokacin da Muhd su ka yi rashin lafiya bamusan ya za’ayi ba.”

Murmushi Ummu Hani ta yi karki damu akwai wasu.

“Ni kinga Allah har raina na haƙura zan maimaita ba zan amshe kuɗinki ba.”

“Tom shikenan na ji ba kyauta ba bashi ki faɗawa Umma duk sanda ta samu sai ta dinga ragewa.”

Daɗi ne ya cika Kursum ta rungume Ummu Hani cike da annashuwa.

*****

Ita kuwa Umman Bushira sai da ta gama komai sannan ta shirya ta yi gidan yayarta wato Umman Bashir.

Kamar rannan zuga Umman Bashir ɗin ta yi Umman kuwa ta hau tai fam, musanman jin cewar Bashir ɗin da ya ce zai dena zuwa bai dai na ba.

“Kinsan me yaya gidan zamu ki yima yarinyar warning shine hanya kawai da zaki rabata dashi.”

“Shikenan hakan za’ayi, ina zuwa” Umma ta miƙe ta shiga ɗaki dan ɗauko hijabinta.

Ummu Hani na zaune ita da Kursum suna hira, lokaci lokaci Bala nasa musu baki, wanda yazo cin abinci kasan cewar sun saba da Kursum yasa yake ɗan saka bakin.

Suna nan zaune Umman Bashir suka shigo, Bala kasan cewar yasan su ya yi saurin gaida su, yayin da ita kuma Ummu Hani kamar da Umma ta yi da Bashir yasa ta saki fuska sosai, tana faɗin “Umma sannu da zuwa ku shiga.”

“Ke dakata ba zama muka zo yi ba, bari ma dakata gidan uban waye kika sanni?” Duk Umman Bashir ke faɗe cikin fishi.

“Kema dai yaya da wani abu kike ba dole tasan ki ba tunda tana morar ɗanki” Umman Bushira ta faɗa.

Murmushi Ummu Hani ta kuma yi, tamkar bata ji ko fahimci ba mutunci ne ya kawo su ba, ta kuma cewa “Dan Allah ku shiga ta faɗa tana ƙoƙarin shiga ciki.”

“Ke dakata baki ji na ce miki ba zama muka zo yi ba, ku baku da gurin da zan shiga in zauna, nazo in miki tsakani da ɗa na ne, ki fita sabgarsa.”

“Anman Umma…” “Ke bansan bariki, ki sauraren dan daɗin bakinki da kini bibin ki duk nasan irinsa bazaimin tasiri ba.” Umma ta dakatar da ita.

Sum sum  Bala ya tashi ya fi ce, kai tsaye shago ya wuce Bashir na zaune yaba tilawa Bala ya zayyana masa komai da hanzari ya miƙe ya yi waje.

Inda ita kuma kursum haushi ya rufeta ta miƙe.  “Haba bayin Allah tayaya zaku zo ku rufe baiwar Allah da masifa, ita ba ita ce ta ke jawo Bashir ba, inta ita ne ma kar yazo, Shi ya kawo kansa kamata ya yi kuje can shi ku masa, ku ce karya kuma zuwa.”

Kursum ta faɗa azafafe dan ita ba gwanar haƙuri ba ce.

“Kai! Ke ni zakima rashin kunya, me kike nufi wato ban isa da yaro na ba kome?” Umman Bashir ta faɗa a zuciye.

“Kinga yaya aike kika kyale ta kamata ya yi ki wanke yarinya da mari inta kawo miki raini wallahi, kinsan yara irin waɗannan ba tarbiya suke da ita ba.”

“Wa? Ta mare ni, tab! da wallahi bata kuma ba, sannan ai ba rashin kunya nai mata ba gaskiya na faɗa, maganar rashin tarbiya kuma kowa yasan waye mara tarbiya a unguwar nan.” Kursum ta faɗa yayin da Ummu Hani ta daka mata tsawa, kai kace ba sa’ar ta ba ce.

“Kursum” Ummu ta faɗa cikin fishi, “Me yasa baki da kunya ne, ki shiga gida ba gunki suka zo ba.” Ummu Hani ta faɗa murya a kausashe.

Sim sim Kursum ta shige ba tare da ta kuma cewa komai ba, yayin da Ummu ta jiyo ga su Umma tana basu haƙuri.

“Umma dan Allah kuyi haƙuri, indai yaya Bashir ne zan yi ƙoƙari ya dena zuwa, kuma indai ni ce nima zan fita sabgarsa.”

“Ke munafika kina wani sin sin da kai na munafurci, nasani yadda waccan take jin tashen balaga haka kike ji, to na dai faɗa miki dan wallahi zuwa na, na gaba ba zai miki daɗi ba, ki fita sabgar sa dan ni ban shirya surukuta da mai zaman kanta ba…”

“Haba Umma mene haka, ina ni ne kike son in daina zuwa, to mene kuma zaki zo ki dinga ci mata mutunci, ni nake kawo kaina ba ita take jawo ni ba.” Bashir da ya shigo ya faɗa.

A fusace Umma ta juya “Eyye sannu isasshe wato da gasken ne baka dena zuwa ba, yanzu uban me kazo yi?”

Hannunta ya riƙe “Muje,” fizgewa ta yi “Ba inda zani inaso ka sani itama ta sani ni uwarka dana haife ka nama katanga da yarinyar nan, da mutan gidan nan in wallahi na kuma jin ko da abayan idona ka zo ko ka shiga sabgar ta ban yafe ba.” Fuuu ta fita.

Juyawa ya yi ya kalli inda ta yi, ya juyo ya kalli Ummu Hani, ya ce “Ummu dan Allah ki yi haƙuri bansan…”

Hannu Ummu ta ɗaga masa “Karka damu ka tafi, kar fushin mahaifiya ya hauka karka damu uwa tafi komai kana ji tace karka kuma shiga sabgarmu.” Ta yi ciki da gudu.

Baƙin cikin Ummu Hani ɗaya kiranta me zaman kanta da Umma ta yi, wato haka ake musu kallo, ita ba kanta take ji ba, yanzu in mutane suka farawa ƙannenta kallon masu zaman kansu ya zata rayu.

Allah ka gani ba yanda zamu yi ne, bawai zaman mu kaɗai muka zaɓa ba.

Dafata Kursum tai “Mene ki ke kuka haba Ummu, koda son Bashir kike ba wai mutunci kuke ba ya ci abinda mahaifiyarsa ta miki kiji farat ɗaya ya fitar miki a rai, ki taso ki koma gun sana’ar ki, u are strong, u can endure it, karki bari abu kaɗan yasa ki bar hanyar da zaki nemawa ƙannenki rayuwa mai kyau.”

Share hawayenta ta yi, tunawa da ta yi ko mene akwai wasu a ƙarkashinta, miƙewa ta yi ta fito, su Aisha duk sunyi carko carko suna kuka.

Murmushi Ummu ta yi, “Ku kuma mene haka jibeku dan Allah,” ta faɗa tana murmushi ta amshi Muhd suka yi soro.

Bana ganin comment ɗin ku da voting ɗinku fa ko dai labarin bai yi bane a fasa.

Tun ina yin rubutun ina son rubutawa har na fara ƙosawa ina ga aje shi zanyi kawai sai inna samu faraga na dunga rubutawa tunda ba masu karantawa.

Share and follow pls

<< Ummu Hani 8Ummu Hani 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×