Skip to content
Part 19 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Washegari bayan Ummu Hani ta siyar da fanke ta dawo gida, miya ta ɗora ta abincin gida na rana da kuma na siyarwar da take.

Tana zaune tana yanka kabeji suna hira da Hajiya Ummu ɗin ta ce dana sauke abincin nan shiryawa zan yi in zo in tafi gidan kawu kan sha biyu tayi masu siyan abinci su fara zuwa.

Anya zaki iya gamawa kan sha biyun nan kuwa, har kije ki dawo yanzu fa tara ta wu ce ga waken ma ban gama tsinta ba, Hajiya ta faɗa lokacin da ta buɗe labulen ɗakin ta dan ganin ƙarfe nawa.

Yau inaga haƙura za’ai da waken kawai in ji Ummu Hani. Kusan sha ɗaya Ummu Hani ta kammala shinkafa da miyar ta zuba a kulolin da suke zubawa, kan ta shiga wanka.

Ummu na wanka Hajiya na yiwa Muhammad dan in dai Ummu zata fita bazai zauna ba ko ina yana ɗafe da ita.

Sai wurin sha biyu sauran kaɗan Ummu ta kammala shirwa Hajiya ta dubeta anya kuwa bazaki jira su Hasana su dawo ba kin san Halin Usaina in ta dawo taga bakyanan zatayi ta nunƙufurcin nata ne da ɗacin rai.

Leƙawa ɗaki Ummu ta yi kai har sha biyun ta yi bari kawai ma in kai abincin in Aisha ta dawo na je.

Hakan ma zai fi dan na tabbatar yanzu inma kinje da wuya ki samu ɗaya cikin kawunnan naki se ma dai ki jira ko ki bada saƙo.

Aikam se da yanma ma kawai zan tafi Ummu ta faɗa lokacin da ta ɗauki botikin da ta yanka salak a ciki.

Da hanzari Muhammad yabi bayanta Hajiya ta zo ba inda zata yayi burus da ita, sai da yaga ummun ta zauna a tebur ta suna maga da Ado wanda zai fito mata da abincin sannan ya koma cikin gida.

Hajiya tasa dariya lallai Muhammad wato se ka tabbatar ba inda zatan ko yayi dariya irin tasu ta yara kan ya zauna ya hau wasan sa.

Sai wurin biyu da wani abin su A’isha suka dawo abinci kawai Aishan ta ci ta can ja kaya ta fito dan amsar yayar tata.

Itama Ummun abinci ta ci bayan ta shiga wanka ta shirya Usaina dan bata yawo da Hasana, ita bata damu ta ce sai ta bita ba.

Duk da kasancewar Husaina tafi hankali bata da hayani sai dai akwai ta da kwalaficin Ummu Hani, ada kan Umman su ta rasu ko yaushe yarin yar na jikin Umman daga baya kuma da ta rasu ta dawo mannewa yayar ta su.

Sai wurin huɗu suka tafi, aiko har ƙofar gida Hasana ta biyo su tana faɗin wallahi Hus saina faɗawa Malam Umar lafiyar ki kalau kika ƙi zuwa islamiyya.

Hararar da Husainar ta watsawa Hasanan gami da faɗin kiji da makarar da kika yi, yasa Hasanan cewa Umma adawo lafiya, ta ɗakawa Muhammad da ke baya duka, kafin ta koma gida, tsoron Husainar take sosai dan ko a makaranta Hasana baki ne kawai da ita da tsokana, anma yara sun raina ta in tayo tsokanar ma sai dai ta zo bayan Husaina ta buya, duk da cewar kamar su daya ba’a gane su anma hali yasa tuni yara suke gane wace Hasana wace kuma Husaina.

Kusan yayyen su ma kai Har hajiya ba da kama suke gane su ba da haline, Ummu Hani ce kawai ko suna bacci kuma ko daga bacci ta tashi zata nuna wace Hasana wace Husaina.

Shiga iri ɗaya Ummu Hani sukayi da Husaina material ne wanda Faruk ne ya ɗinka musu dukan su, dark blue ne da adon pink yayi kyau sosai duk da kasan cewar Ummu Hani baƙa ya mata kyau. Ba wata kwalliyar fuska ta yi ba dan kullun mitar Faruk shine ta dena kwalliya in zata fita, wannan yasa mai kawai ta shafa ta goge fuskar ta da tsuma, sai dai duk da hakan ta yi kyau sosai, dan kwana biyun nan ta kuma yin wani fresh har wani haske ta ɗan kuma.

Goya Muhammad da ta yi take kuma riƙe da hannun Husaina shi zai sa kawai wasu su kasa tsaida ida dan zato za kai sabuwar amarya ce mai yara biyu.

Ummu Hani ta yi sa’a tana zuwa gidan Kawun nasu ya dawo kusan dawowar sa kenan.

Ba kamar da ba ya na zaune a kan tabarma yana ganin su ya sake fuska yana murmushi, a’a su Ummu ne a gidan namu ya faɗa da fara’a.

Ita ma Murmushin ta yi kan ta durkusa ta hau gaida shi, lafiya kalau Alhamdulillah, ya yan uwan na ki ya tambaya. Lafiya kalau wallahi ta bashi amsa.

“Tabawa!!” Ya kwalawa matar sa kira ta fito daga madafa, itama Murmushin ta saki kan ta ce ah yau su Hani ke tafe murmushi Ummu Hani ta yi kan ta ce inna ina wuni.

Miƙo musu tabarma inji kawu, ajiye mabirgin da ke hannunta ta yi kafin ta shiga ɗaki tana kuma faɗin lale maraba.

Bayan sun zauna ne inna ta ce Ummun ta kwanto da Muhammad. Miƙo mata shi Ummu Hani ta yi bayan ta sauke shi yako makale alamar ba zai zo ba kawu ya ce kaga sulaiman sarkin ƙiwa.

Murmushi Ummu Hani ta yi kafin ta ce Muhammadu ne, kunya ce ta rufe kawu dan shi a zatonsa Ummu Hani ɗin sunan Baban su zata sawa yaron.

Shirun da ya ɗan ratsa ne yasa Ummu Hani nisawa kaɗan kafin ta ce,

“Daman Kawu zuwa nayi in faɗa ma gidan su Faruk sun na ce suna son in tare su anasu lissafin ma sati uku suka ce na ce su dai bari abin da kuka yanke shi za’ayi banason a muku tutsu.”

Tsuke fuska kawu ya yi jin batun tarewa yasan yanzu za’a fara batun kayan gado.

Kallon ta ya yi rai a ɓace kan ya ce, “To in ce dai kunyi kayan gado, ko suma mijin zai miki dan in zan tuna kamar sun ce basai munyi komai ba ko.”

A nutse Ummu Hani ta kalli kawun nata duk da ran ta ya ɓaci daurewa ta yi ba tare da ta nuna ba ta ce “Eh haka suka ce ba sai anyi komai ba, anma…”

Bata ƙarasa ba Kawun ya ce “Anma me ai tunda sun ce ba sai anyi ɗin ba kawai basai kin wahalar damu ba, ki ce musu in sati ukun ta yi zamu kawo ki.”

Kasa maga Ummu Hani ta yi ranta ya ɓaci sosai, Inna ce da ke gefe ta ce, “Ah haba malam ai ba haka ake ba, ki ce musu kawunnan naki sunce nanda wata guda insha Allahu.”

Sannan in sun bugo kati ki kawo sai a rarrabawa dangi.

To kawai Ummu Hani ta iya cewa kan ta miƙe mu zamu mu tafi. Inna ta ce towo tun yanzu ku tsaya ku ci abinci kawu ya watsawa inna harara alamar dan me zata ce su tsaya su ci abinci.

“A’a wallahi a koshe muke inji Ummu Hanin ta fada kafin ta sa kai ta fita rike da hannun Husaina.

Tana fita inna ta dubi kawu cikin faɗa take faɗin “wallahi Malam kana jika mana gari, ai ba haka ake ba kana dai kallon yaron da yarin yar nan zata aura yanzu kanajin duk kudin sa bamu jasu ajiki ba zata bari mu dan gwali arziki ne?”

Dafe kai kawu yayi, ya ilahi meke damu na kin san Allah ban kawo haka araina ba anma yanzu ya kike gani.

Kaima dai kasan halin yarin yar nan kana kallon rashin mutun cin da ta mana akan shinkafa tun bata kai haka ba in muka ce zafi zamu bita baza ta bari mu more ta ba.

Kinga ni tun ɗazu kike mai maita zance mafita zaki faɗamin, malam ya faɗa a hasale.

“Tunda mijin ya ce zai riƙe mata ƙannen nata, ka ce ta baka karamin da ƴan biyun ka ce zaka riƙe…”
“Mtsss Malam ya ja tsaki wannan ai gurguwar shawara ki ke bani ke kin san ko ada bazan iya ciyar da yaran nan ba bare yanzu kina kallon yadda yaron yake dumur mur alamar daɗi yake ci kike min maganar in ɗauko shi in riƙe kuma kina batun harda wasu ƴan biyu yara uku kenan fa.”

Uhum Malan kenan daɗi na da kai gajen haƙuri baka tsaya kaji ƙarshen zance na ba.

Takai ci ya kuma kama Malam kafin ya ce inajin ki keda soki buru tsun naki.

Murmushi ta yi kafin ta ce “kaga yadda suka shaƙu da yaran musan man na goyon in ka ce ta baka bazata baka ba, anma akalla dai zataji aranta ai ka nuna kana son rike ƙannen ta in ta ƙi baka sai ka nuna shikenan ko hutu ne dai ya kamata su dinga zuwa, ni kuma in ta tare sai inje in ce tabani yayen yaron kaga in na tawo dashi zasu haɗoni da abinda yaro zai ci, sannan kuma Zata dinga sa mijin yana zuwa yana duba mata ɗan yaye.”

“Kinga kuma babu ta yadda za’ai ya zo ba tare da wani abin ba” kawu ya faɗa fuskar sa fal murmushi.

Itama inna murmun ta yi sannan ta ce to da ni dai kaji tunani na. “Ah ai wannan shawar nai kyau ce zan je in faɗawa ummun ɗin.”

Ita kuwa Ummu Hani suna fita gidan Yar Umman ta suka yi tunda tasan Kawu zai faɗawa sauran ƙannen sa wato yayyen baban ta batun zuwan nata wannan yasa bata biya sauran gidajen ba ta yi gidan Gwaggon ta su.

Tana zaune tana kaɗa miya ummun ta shiga yanma tayi lokacin sosai dan da ɗan nisa tsakanin gidan Gwaggon da kawu ba kuma su hau mota ba.

“A’a su Hani a gidan namu” Inji Gwaggo ta faɗa cike da kulawa, murmushi Ummun ta yi kan ta samu guri ta zauna tana faɗin “wash wallahi na gani.”

“Kinga kafin ki zauna ga ruwa me sanyi a tulun can ɗebo ki jiƙa maƙoshin ki, ba dole ki gaji ba kin sun kuma gardin ɗa baya.”

Ba musu Ummu ta miƙe ta ɗebo ruwan aiko taji da ɗin sa Husaina ta ragewa bayan ta sha kafin ta ɗebo na botiki ta bawa Muhammad dan na tulun ya masa sanyi.

Badai maganar tarewar ba ce inji Gwaggo ta tambaya tun kan Ummun ta mata bayani.

Kunya ce ta kama Ummun ta ce eh kanta aƙasa.

Murmushi inna ta yi kingani ɗazun nan na gama batun zanzo inji yaushe ne tariyar ta faɗa lokacin da ta ke dire tukunyar da ta sauke a ƙasa.

Eh daman jiya ne yake ce min mahaifan sa sun takura shi ne na ce sai na muku bayani to daga gidan Kawu Musa na ke, ya ce min in ce musu nan da wata guda, ummun ta faɗa duk kan ta a ƙasa.

Masifa Gwaggo ta fara wata ɗaya kuma, sai ka ce yar tsana yana sane da a wata guda ba iya miki kayan ɗaki zasuyi ba, kar lokaci yayi yasa azo aji kunya.

Ran Ummu tun ɗazu sai yanzu ta ɗanji sanyi aranta, eh daman dan su Faruk ɗin sun ce basai an kai komi ba.

Tsaki Gwaggo ta yi wane irin basai an kai komi ba ai ko sun siya sai dai su fidda nasu mu zuba namu daga baya sa dawo dashi haka kawai ai ba siyar ki mukai ba.

Mikewa ta yi ta shiga ɗaki minti kaɗan sai gata da kaya cikin kwali ta dire sannan ta koma ciki.

Ummu!! Ta kwalowa ummu hanin kira da hanzari ta bita ciki.

Kaya tasa ta fito dasu tsakar gidan.

Bayan sun zauna ne ta ce waɗannan kayan girki ne tunda aka ɗaura auren nake ɗan siye, gobe ko anjima in Malam ya dawo zan tambaye shi zanje in samu su Musan dole ne su miki kayan ɗaki.

Ummu zatai magana gwaggon ta katseta tunda kun huta tuƙan tuwon nan ba in sallah ban la’asar ba.

Ummu na tuka tuwon tana murmushi sosai taji daɗi aranta tasani duk da cewar su Gwaggo suma sun watsar dasu sai dai a koda yaushe ko yaya suka samu dama suna kyautata musu ta kuma sani sunfi son su akan dangin mahaifin su.

Aranta ta ce ko me yasa dangin uba suka fi nuna ko in kula oho.

Tana kwashe tuwon Muhammad da Husaina na gefe suna cin wanda ta zuba musu Gwaggo ta fito, kinga seda ina Sallah na tuna. Ummu ta kalle ta dan jin me ta tuna.

Maganin da na bawa Ummi ta kawo miki kin gane kuwa yadda za’ai dashi kunya ta cika ummu ta kasa magana.

Shikenan dai zan zo in samu Hajiyar tunda tariyar tazo in yaso sai in kawo mata tunda kina sana’ar ki acan ga yara bana ce ki tawo nan ba inna samu lokaci sai in dinga zuwa ingani.

Ita dai Ummu bata ce komai ba sai tuwon da ta zubawa kanta kawai ta fara ci.

Sai bayan Mangariba tukun nan Ummu ta baro gidan Gwaggon. Tare suka fito da gwaggon inda ta sauka a gidan Kawu Musan su kuma su Ummu suka wuce gida….

<< Ummu Hani 18Ummu Hani 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×