Shopping Cart

Close

No products in the cart.

Ummu Hani by Fadimafayau

Ummu Hani | Babi Na Talatin Da Biyar

<< Previous

Ran Ayatullah ba daɗi ya ce, ‘au ashe kana gida Kawu Barka da yanma.’ Kawu ne ya ce to shan kunun na mene badai dan na ce kaje gunta ba ran Ayatullah ya kuma ɓaci sai dai kan ya ce wani abu Umma ta ce Malam gaidaka fa ya ke sai a lokacin ya ce lafiya kalau maza ku je. Gida ne Babba sosai kusan duk area din babu ya shi duda cewa ba wani na masu kuɗi bane anma kasancewar sa cikin gine ginen talakawa sai ya fita zakka a ƙofar gidan Ayatullah ya parker Tijjani ya shiga. A’isha suna farfajiyar gidan sun kure waka gami da kafa ring light a gaba suna rawar wakar da take trending a Tiktok kwana biyu wato ashe daga zaune ma ana Tijjani ya kusa minti uku sannan suka katse Aisha ta haushi da masifa, “bana ce kar wanda ya biyoni ba ni wallahi na tsani damu.” Tijjani bai damu ba ya ce to ai Baba ne yace in rako Ayatullah wai zakuyi maganar aure.

Dariya Balkisa ta sa “Hajiya su Pops fa da gaske suke aurar da mu zasuyi nima dazun Ib yazo wai Boos dinmu ne ya turo shi.” Tsaki Aisha taja aiko wallahi ni ban shirya aure yanzu ba” “Jeka kace ya shigo.” Inji Balkisa Tijjani na fita suka kuma kunna wata wakar da take trending ta Warr Aisha ta cika kaya a ciki da mazaunan ta rike da hoda yayin da Balkisa ke acting tamkar namijn Ayatullah tuni ya kufula kan Tijjani ya fito kawai baya son batawa Abban sa rai anma da tuni ya tafi wallahi.

A ciki sa suka shiga sai da suka gama rawar su sannan Balkisa ta matsa gefe ta hau editing don so suke suyi posting yau dan suma su samu su shiga challenge din kar viewers dinsu suga basuyi ba yayin da Aisha ta zare kayan da ta zira a jikin nata ta matsa kusa tana goge fuska. Sannu ko ta faɗa bai iya amsawa ba dan yasan yana buɗar baki zai iya zaginta.

Bata damu ba ta ce yanzu “Tjee ke faɗan kazo batin aure to gaskiya ni ban shirya aure ba kaje ka faɗa musu though u are my type but yanzu dai am not ready in zaka jirani to no i mean u have to wait for me,” tsaki ya ja lallai ma yarinyar nan ta rainashi cikin fishi ya ce sabida me zan jiraki, dariya ta yi sabida ina sonka mana kai lallai bata da hankali ya kuma fade a ransa, “yes ina sonka kawai ban shirya aure ba anma in kaga zaka barni inyi Tiktok dina it’s ok am good to go.”

Balkisa da ke gefe ta ce Film din fa Aisha ta ce ai shi kinga dayan nan kawai nai niyar yi Bama sai ansa shi cikin sharadi ba, what film fa are u mad u mean ni zan auri yar film ya kuma faɗa da ɗan karfi, dariya tasa to ya zakayi kwafa kawai ya yi bai ce komai ba. To ya zaka barni in Tiktok din ta faɗa bayan shirun da ya ratsa.

A fusace ya ce “baki da hankali ne ni wallahi matata bazatai Tiktok ba.” Fu ya fi ce taɓe baki ta yi taja tsaki Balkisa ce tace “ke baki da hankali ki samu wannan guy din in ya kufce miki to wallahi ko irin su Mai baranda baki samu shi yasa nake lallaɓa Ib in akai auren na haihu duk wani rashin mutunci zan fito da shi fili lokacin ko beso darajar yaranmu ya zauna dani.”

Shiru Aisha ta yi, ‘’Eh kuma fa hakane ni kaina nasan inna rasa Ayatu nayi asara ga kyau bana filter ba ga nutsuwa ga illimi banji ko shiga Tiktok fa yanayi,” “To kin gani kawai ki basar ayi komai in an daura kun haihu bazai sake kiba koda ba ɗan uwanki bane bare jinin ki ne doke darajar yara da iyaye ya kyaleki.”

Koda Ayatullah yaje gida Hajiyar su ya lamintawa komai ta tsani Tiktok da yan film ta yi ta faɗa da kyar ta shawo kan Alhaji yace shikenan zai samu kanin nasa, ilai kuwa ta same shi ya ce indai Aisha zata cigaba da Tiktok to gaskiya shi bazai yadda ayi auren ba.

Koda Kawu ya dawo gida ya yi tama Aisha faɗa umman su ta haushi da faɗa danme zai dungawa Aisha faɗa mene aibun Tiktok bayan a gida suje video din bawai yawo suke zuwa ba A’isha ce ta ce ‘Umma kyale Baba badai Tiktok bane na daina ai aure yafi komai murmushi Umma yasa yawwa yar albarka ai gwanda da kika watsa masa aniyarsa kika dena nima nafiso kiyi auren ki, yawwa ko kefa yar kelen Baban ta yanzu taso muje mu samu yayan tunkan ya maganar fasa auren ta yi nisa kawu ya faɗa.

A gidan su Ayatullah Alhajin su Ayatullah ya dube shi ya ce to kaji dai ta dena sai ku shirya dama sati guda ya rage, ran Ayatullah ya ɓaci dan dai kawai baya son mahaifin sa yayi danasanin haihuwar ɗa namiji tunda shi kaɗai ya haifa cikin yan uwansa mata takwas da wallahi guduwa ma zai yi kawai baya son ya zamewa Abban nasu abinda ake cewa da haihuwar namiji birarre gwanda haihuwar mata ɗari anma in ba haka ba shikam iya cuta an cuce shida yaran da zasu haifa shida Aisha din dan ba’a zaɓa musu uwa ta gari ba sam.

Kwana uku ya rage bikin an gama komai yau take dinner sam ango baya cikin farin ciki ko gayya bai yi ba Aminsa ɗaya keta kai komo a bikin yanzunma shi yazo tafiya dashi gun dinner din duda baya cikin farin ciki ya yi kyau sosai duda ba walwala a fuskarsa dole zaima kyau a ido dan shidin akwai kwarjini da cika ido.

A gun dinner tun takwas har goma ba amarya Umman su Aisha ce ta ce ango ne da laifi baije dauko amarya kamar kowa ba doke haka ya taso shida abokin sa suka tagi gurin mai make up din, ita take sanar musu ai amarya tun da tazo ko make up ba’ai ba aka kirata a waya wai an dawo da shooting din film din yau ta tafi. Shiru kawai Ayatullah ya yi suka koma gun biki akaita kiran wayar Aisha shiru.

Sati daya biyu kai har wata guda ba’asan inda Amarya ta ke ba ran Alhajin su Ayatullah ya ɓaci cikin fushi ya ce shikam wallahi bada dansa ba sai dai kome kawu zai ce ya ce anma bada dan sa ba tunda ta zaɓi karuwanci to taje.

Ita ko Aisha a gun film din ne yadda akai ta zugata ai ita din expert ce Film uku ko huɗu in tayi nan da nan zatai kuɗi tayi suna duk nan  taji tama fasa auren duda tana son Ayatullah anma tana son shahara tasan in ta aure shi kuɗi ba matsala bane anma shahara ba’a siyan ta, ta yanke in tayi Film biyar ko shida kowa yasan ta zata dawo kuma dole sai ya aure ta wannan shine abinda ta yanke dan shi ɗin yafi karfin rabin ranta sai dai zuciyar ta da ke harba jini bisa sassan jikin ta in babu shi babu ita. Shiko Ayatullah yafi kowa farin ciki da jin daɗi na guduwar tata in mutane suka zo musu jaje haushi ma suke bashi maimakon su zo masa murna.

*****

Koda Ahmad ya koma gida kuka yasawa hajiyar su shi an cuce shi ba’a kyauta masa ba ansan Ummu ita ce farin cikin sa Hajiya fada ta haushi dashi wai baida hankali mai zaiyi da bazawara kuma mai yan shegu cikin fishi ya ce ko ita ce shugabar karuwan Nigeria yana son ta a haka fadan da Hajiya tasa yasa ya bar dakin ya ci gaba da kunkuni. Kalid ne kanin sa ya biyo shi ɗaki ya ce kasan Hajiya da Kawu da son kuɗi ka tara su faɗa musu yarinyar nan fa Hajiya tafi family din mu kuɗi a iya binciken dana yi taji gado mai mugun yawa kawai mantawa tayi da gadon kuma inajin zafin mutuwar mijin ta ne yasa anma in aka jima zaka sha mamaki.

Shiru Ahmad ya yi kasan Allah Kalid ni ban taɓa son abin ta ba ita nake so banma san tana da komai ba shiru Kalid ya yi kan ya ce eh ita kake so anma in kana sonta baka aure ta ba aikin banza ne wannan ita ce kawai hanyar auren ta, kawun sa ya kira a waya wanda shi ke iya juya Hajiyar su ya kuma zugata yanzun ma shi ya zugata ta tubure kan auren..

Zaune suke Kalid ya hau musu bayanin dukiyar Ummu duk suka ruɗe Kawu ya haushi da faɗa dan me bai faɗa musu ba tun da Hajiya ta ce ni bacin raina ma ɗazun na tura shashun can sunje sun mata tijara no wonder ta ce zata kulle su ashe tasan me ta taka tana dashi. Kawu ne ya ce ai yanzun ma ba matsala bane shi Ahmadun shi zaije ya shawo kanta tunda suna son juna zata amince gyaɗa kai Hajiya tayi to kaji dai kaje ka tabbatar ta hakura nima zanje sai naji sauki zan tisa su gaba muje su bata hakuri ya zama tamkar kawai aikin su ne banma san anyi ba.
Ahmad ya ji daɗi sai dai bai so cewar wai sai dan wani dalili daban zai auri Ummu ba shi har ransa san yarinyar yake kuma tausayi take bashi.

Kusan kullum sai Ahmad yazo anma Ummu bata sauraron sa dan ta riga ta rantse ma ranta ko me za’ai bazata aure shi ba kai koma waye a duniya ta fasa aure wannan yasa Ta ce Mahmud mai son Aisha kanwar ta ya turo dama ya jima yana son ya turo ɗin Aisha ɗin taki lokaci guda aka sa auren Aisha dana Salma wata huɗu ne ba yawa dan duk mazajen a shirye suke suma su kawu sun ce asa shekara Ummu tace ba komai insha Allahu ba abinda zai gagara.

Tana zaune tana ma Muhammad wanka Umman su Salma na shafawa Hasana da Usaina mai yayin da Umar da Faruk ɗin Ummu ke shimfiɗe kusa da Hajiya Umar ba Bacci Faruk nata wutsil wutsil Hajiyan su Ahmad ta yi Sallama ita da Kannen Ahmad ɗin, Ummu ta gane su cikin sauri ta miƙe mai kuma ya kawo ku ba Ahmad bane ba riga na faɗa muku ni bazan aure shi ku kwantar da hankaljn ku.

Hajiyan su Ahmad din ce ta yi murmushi haba yarinya ai kya saurare mu Umman su Salma ce ta ce ku shigo ganin da tayi kamar da salama sika zo haƙuri sosai Hajiyan Ahmad ta bawa Ummu sai dai Ummu akwai kafiya da zuciya karki damu Hajiya ni ban kullace su dagaske lefinane danayi tunanin auren saurayi ina budurwa ya wuce komai anma wallahi bazan aure shi ku faɗa masa ya dena zuwa gidan nan tun kan in haɗa shi da hukuma. Jiki ba kwari Hajiya suka tafi sai da suka tafi Umman su Salma sukai ta mata faɗa ita dai ta yi shiru kawai.

Sannu a hankali ayayin da agogo ke juyawa a hankula cikin daƙiƙu kan mu ankara sai dai muga lokaci yaje kusan haka yake ga rayuwar Ummu anyi bikin Aisha da Salma wanda duk Ummu ce ta ɗauki nauyi abinda suke samu a shago dashi tayi komai Salma ta gode mata tamata addu’a dan kam abotar su da Ummu ba abinda bata mata ba kusan kawai saidai ta ce eh mahaifin ta ya rasu anma gata da uba kewa diyar sa ta samu daga kawar tata, ita kuwa Aisha godiyar ta ga yar uwar tata ba adadi dan tasan cewa ta musu sadaukarwar da bama ko wanne uba kewa yaran sa ba, kullum cikin yi ma Ummu addu’a take kan tayi wa kan ta da mijin nata ta yiwa Ummu sau goma.

Umar da Faruk sunyi wayo watan su goma sha tara yawo suke ko ina Umar yafi faran faran dan har bakin sa ya buɗe yayin da Faruk da da kiwa baya yadda da kowa sai Ummu da kairi ko Kursum baya yadda da ita kullum cikin faɗa suke shida Muhammad dan Muhammad kishi ne dashi da yaga Faruk a cinya zaizo ya janye shi shi kuma Faruk din yasa kuka.

Zaune suke Kursum ta dawo daga makaranta dan ta samu direct level 2 a Buk Ummu na zaune Muhammad da Faruk sun gama faɗa kan kowa shi zai zauna a cinya Ummu ta ce to kowa ya zauna kusan kan wanda zai jingina a kirjin ta ma sai da akai faɗan dakyar tashawo kan Muhammad kan ai shi yaya ne sannan ya hakura Faruk ya jingina shi kuma ya zuna kusa dashi, Kursum da ta shigo ne ta ce eyye lallaima yaran nan ku tashi so kuke ku kassara babar taku yara sai binbinin uwa kamar me.

Umar ne dake wasa da su Hasana da Usaina ya tawo Anti tunsumu Mai tira wawo min ashi ya fada cikin muryar sa ta yara, dariya ta yi da ɗaga shi kaga na waje ne to rufe idon ka ta ciro alawa ta danga masa ta sauke shi ya yi gun Umman su Salma yana murna ya mika mata dan ta buɗe masa, Su Hasana ma tasowa sukai ta miƙa musu Faruk da Muhammad na kallon ta sun kusa sakan sittin suna nazari kafin su miƙe su karasa suma ta basu daga ɗan nesa Faruk ya tsaya yana jiran ta miƙo masa sai da ta harare su sannan ta ce kaga kwadayyun mutane ai na ɗauka bazaku amsa ba duk mai so ya mazo.

Kusa suka matsa caraf ta ɗaga Faruk abinda yake gudu kenan karta ɗauke shi aiko ya tsanyara kuka dariya kowa yasa Hajiya ta ce kema dai wallahi Kursun da neman rigima kike kinsan halinsa da rikici dariya Ummu tasa ai ita ta yo wallahi yanzu har mamaki nake da take shiga jami’a Umman mu fa kan ta rasu haka zatai ta mata tsiya wai ko Baban mu bata yadda ya taba ta dan kiwa.
Dire shi Kursum ta yi ta mika masa alamar ya karasa gun Ummu da gudu ya hau janye Muhammad Kursum ta ce tab ni bani yayo Baban sa yayo shima ai kawai da wanda ya saba yake hira suka sa dariya, murmushi Ummu ta yi rayuwa kenan wai yau ita ce in an anbaci Faruk take dariya ba kuka ba tabbas duniya zancen banza ce.

Kusan yau shekarar su Faruk biyu a duniya har an kawo kuɗin Kursum duk yadda Kannen Ummu sukai da ita kan ta yi aure taki yadda take sa musu kuka in sun dame ta da batun yasa suka rage mata maganar suka bari su bata lokaci. Tsaf ta shirya kasuwa zata dan siyayyar kayan abinci da wasu kayan bikin Kursum dan bikin ya matso sam bata yi niyar tafiya da yaro ba wannan yasa sai da Faruk yayi bacci ta fara shirin ta, sai da ta shirya ta cewa su Hajiya ta tafi kan ta kai soro ta jiyo kukan Faruk dafe kai ta yi ta koma ta goyo shi aiko Muhammad ma da suka shigo yanzu shida Usaina ya bita da Gudu yana kukan shima rike hannun sa kawai ta yi suka fi ce tayin da Umar da su Hasana ke mata bye bye.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.