Ya tsaya yin magana da su na zame hannuna da nufin tafiya ya ƙara riƙe hannun tilas na tsaya suka gama maganarsu muka shige.
Washegari hospital na je sun tabbatar mini na kusa haihuwa ƙafafuwana da hannuwana duk sun kumbura ba tare da Lema muka je ba ni da Amina ne shi ya fita harkokinsa.
A falon da na saba zama na zauna ban ko shiga ɗaki ba na miƙe ƙafa kan Carpet, Dina ta faɗa mini za su gidan ƙawar Mamansu ganin ban ga kowa ba na yi tunanin su dukkan su suka tafi ashe Amal ba ta je ba.
Ruwa Amina ta yi saurin shiga kitchen ta kawo mini ta koma hado mini lemon kwakwa na buɗe jakata na ciro maganin da aka ba ni a asibiti na haɗa su na sha ina ajiye kofin muka yi ido huɗu da Abakar ya fito daga ƙofar da za ta kai ka ɗakin Khalil, sanye yake cikin riga da wando wandon guntu iya gwiwa riga mara hannu miƙa yake da ta sa damatsansa ƙara buɗewa.
Na yi saurin kawar da kaina ya iso ya zauna kusa da ni na yi kamar ban ga abin da ya yi ba “Barka da tashi Ummuna.”
Ban yi niyyar kula shi ba amma Ummunsa da ya kira ni ta sa ni saurin duban sa ka ji tsoron Allah Abakar za ka so a yi maka abin da kake yi?
Ya kwantar da murya “Ya zan yi da zuciyata da ke azalzala ta?
Na buɗe baki zan yi magana Amina ta taho shiru na yi har ta ƙaraso ta ajiye mini tray da ke ɗauke da jug da cup ta gaishe da Abakar ta juya caraf ya ɗauki cup din ya tsiyaya ya kai baki na ce idan kana son aure ka zo na ba ka Amina Abakar, ta zamar mini kamar yar’uwa yarinya ce mai hankali da tarbiya za ka ji daɗin zama da ita wani mugun tsaki ya ja “Na ce miki ina neman a yi mini hanya ne?
Fitowar Amal ta sa ya yi shiru ta iso ta zauna kusa da shi tana mashi shagwaɓa jiya ta ce za su yi hira shi ne Khalil ya ce mata ya yi barci.
Na fara ƙoƙarin tashi marata ta murɗa na miƙe da ƙyar na kama hanyar barin wurin ina jin mummunan tsakin da Amal ta ja.
Na isa ɗaki na kwanta mara ta ce ba ta san wani abu wai shi barci da nake so na yi, na yi ta juyi jin abu na ta gaba na sauka gadon na daɗe durƙushe ina ta fama da ciwo sai da ya lafa na miƙe jakata da mayafina na mayar na fita ɗakin.
Ba su Amal a falon na wuce dakin Amina na ce ta zo mu je hospital, take ta shiga ruɗu tana tambayar ba ni da lafiya?
Kai kawai na ɗaga mata ita ta koma ta ɗauko kayan haihuwar da na haɗa ta faɗo ma Iliya za mu fita.
Su Dina da suka shigo muna fita ta ce in shiga motarta Suhaima da suka shigo tare ta shiga ciki, muka shiga motar Dina ni da Amina.
Kafin mu kai ciwon ya tsananta a gare ni ko Lema da ya kira sai Dina ce ta ɗauka, sun karɓe ni na ci gaba da cin kwakwa ciwon da na ji a duniya tun da nake ban taɓa jin irin sa ba sai bayan magrib na haihu na samu ɗa namiji sai da aka gyara mu aka fito da ni, Lema da Dina da Amina suna nan har lokacin, an dai ce Khalil ya zo ya tafi.
Suna ta gaishe ni murmushi kawai nake bin su da shi don na wahala.
Bashir Lema da ke riƙe da Babyn ya zo ya kango mini shi, Nurse ɗin da ta jagoranci karɓar haihuwar cikin girmamawa ta ce mishi yaron nan shi ne sak. Ta nuna Dina ta ceita da Babyn sun biyo shi.
Murmushi kawai yake, Dina ta zo ta karɓi Babyn ta yi musu hoto su uku har da papinsu ta kuma yi musu su biyu ita da Babyn, ni dai ina ta kallon su.
Amina suka bari ta kwana da ni da safe Aunty Larai ta iso sai ta koma gida.
Ƙa’idar asibitin mace ta haihu sai ta kwana biyu suke sallamar ta da na yi kwana biyun suka sallame ni muka koma gida.
Ko da na ga su Amal da Suhaima ba su tanka mini ba Khalil dai ya je hospital ɗin shi da Abakar ban yarda na gan su ba rufe ido na yi na juya baya har suka tafi.
Ba da son Bashir Lema ba sai don alkawarin da ya yi mini muka tattara kayan mu muka bi jirgi zuwa Kaduna, da Amina muka tafi da Dina da ta ce za ta, shi kwana ɗaya ya yi ya koma Abuja.
Na ga tsantsar murna daga ahalin Lema na wannan haihuwa, sai nake ta jin ina son ganin wannan Farida da wannan dangin miji ba sa so sai Mama Zulai ita da ta zo sai da ta ce ma Dina zuwan me ta yi? Da yake miskila ce komai ba ta ce ba.
Kwana huɗu da haihuwar sai ga Tajuddin ɗin Dina ya zo barka, daki ta shige ta bar ni da shi a falon ƙasa muka gaisa ya yi mini barka, mun ɗan yi shiru na wani lokaci ya fara magana kan Dina shi har yanzu yana son ta ko da ya bar ta ya bar ta ne don sa ma ma rayuwarsa maslaha.
Bayan rabuwar su ya gan ta sau biyu ya ji daɗin yadda saka suturarta ya canza har malamin da ke koya mata karatu ya bibiya.
Yanzu ya dawo amma ta ƙi in taya shi shawo kanta.
Na ce kar ya damu in sha Allah komai zai daidaita a tsakanin su.
Kuɗi masu nauyi ya ɗora kan showel din Babyn ya kwantar da shi ya fita kuma sai ga ledoji cike-cike ya ba da su an kawo mini masu ɗauke da kayan Baby da nawa.
Ta waya na kira Dina na ce ta fito ya tafi sai ga ta na nuna mata abin da ya kawo da ban haƙurin da yake ta taɓe baki ta ce sai na rama, yadda ya wahalar da ni na yi murmushi na ce “Uhmm a dai rama a kaɗan kar a ji zaren da tsawo ya tsinke.”
Ta ce “Ba ta gane hausar ba in faɗa mata da turanci.
Aunty Larai ta ce in zo in yi wanka, na miƙe na ɗauki kayan da aka kawo tana jinjina kayan da aka zubo masu tsada na haura sama ta biyo ni ta yi mini wanka, sai da na shirya tana can tana yi ma Baby Dina ta shigo nan muka yi maganar Taj na ba ta shawara sosai, da muka ɗauki lokaci muna maganar.
Ana gobe suna Bashir Lema ya dawo shagalin suna aka sha sosai yaro ya amsa sunan mahaifin Bashir Lema Ahmad ni kuma na laƙaba mishi Aman.
An sanya auren Suhaima sati biyu bayan haihuwata, mahaifiyarsu ta diro ana saura sati guda biki.
Magabatan Tajuddin sun zo da ban haƙuri tare da roƙon a haɗa auren da na Suhaima sai da Haj ta yi da gaske Bashir Lema ya yarda don ya ji zafin yadda aka wulaƙanta mashi ‘ya, ta sha wahala kan ciwon so.
Ni ma na lallaɓa shi da gwada mishi har yau Dina tana son Taj.
Ranar da mahaifiyar su Amal ta zo yana gidana ina ƙasa wurin Vicky ina faɗa mata yadda za ta yi mana abinci ya kira wayata na bar ta na tafi saman, yana kwance bisa gado Aman na gefen sa ya ajiye wayar da ke hannunsa na zauna saitin ƙafafunsa ya sanya mini ido na ɓata fuska sai na sanya tafukan hannayena na rufe fuskata na ce “Kallon fa?
Murmushi mai sauti ya yi ya ce “Kin yi kyau ne babyna, kullum ƙara kyau kike.
Gidan Haj za ki zo mu je Farida ta iso.”
Wani ragaga na ji gabana ya yanke ya faɗi da ambaton Maman su Dina ta zo.
Na miƙe na isa gaban mirror na zazzaga hoda na fara shafawa ina kallon kayan jikina tsaf nake tun wankan safe da na. yi amma na raina kwalliyar na sanya wet lips sai na tuɓe rigata, wardrobe na isa na buɗe na ji shi yana maganar me ya sa na tuɓe kayan nan na mishi kyau a cikin su, ban ba shi amsa ba na ciro less cikin waɗanda ya yi mini na haihuwa mai tsada ne ƙwarai ko ruɗewa na yi sai ga ni na ɗauko turarukan da aka hado mini na musamman irin namu da aka ba ni tabbacin kar na yi amfani da shi sai ina kusa da mijina don namiji ya shaƙa ba zaman lafiya na adana su sai na yi arba’in.
Na sassanya a sassan jikina na sanya doguwar rigar less ɗin ɗankwali hula aka yi mini na ɗora na dubi kaina zan iya cewa na haɗu ƙarshe na sanya agogo da sarka da yan kunne na zura takalmi na waiwaya inda yake ya zuba mini ido na ɓata fuska ya yi murmushi sai ya sauka gadon kaya ya sauya zuwa farar shadda da ke ta sheƙin da ke nuna tsadar ta ya murza hula ya ɗaura agogo zan ɗauki Aman ya riga ni ya sanya shi a kafaɗarsa sai da na yi ma Aunty Larai sallama da faɗa mata dalilin fitar ta yi yar mitar ta ita ba za ta zo ta yi miki barka ba zai kwashe ki da jegonki.”
Na dai yi shiru ta ce “Ki je sai kun dawo.”
Na fita na same shi a mota na ɗauki Aman da ya kwantar gefensa na zauna kujerar, kallon da yake mini yana rage ido ya sa na tuna kunun da na dama na sanya turarukan nan, yana tuƙin yana waiwayowa ya dube ni.
Part ɗin Hajiya muka fara shiga tana tare da mutane hakan ya sa bai zauna ba ya tafi part ɗinsa na gidan da matarsa ta sauka.
Na zauna tare da Haj Aman na hannunta tun da na shigo.
Wayata ya kira ya ce na same shi can, bed room ɗin Haj na shige na kwanta ji na shiru ta shigo ta ce Baban Dina ya kira wayarta ya ce ta turo ni ya kira wayata ya ce na same shi can ban zo ba .
Shiru na yi ta gane ban son zuwa ta ce tashi ki je ba komai ai ke ce ƙarama.
Na miƙe na kama hanyar barin ɗakin.
Tun kafin in shiga na fahimci akwai mutane fal lon, sai da na shiga na ga ya’yanta ne su Amal, wata yar mata yar firit na gani mai tsananin kama da Amal ba ta da tsawo ba kuma ƙiba ko kaɗan sanye cikin riga da wando sai baƙin gyale ta yi rolling idonta da farin Glass ita da ya’yanta suka yi mini wani duba sai Dina ce ina Aman na ce yana wurin Haj ta tashi ta tafi ɗauko shi don ina yin suna ta tafi Abuja.
Cikin kujera ɗaya suke zaune ita da Bashir Lema, Suhaima da Amal na zaune wuri ɗaya na nemi wata kujerar na zauna na gaishe ta, ba ta amsa ba sai shi ta duba ta ce “Ita ce Amaryar? Ya ɗaga mata kai har yana ƙarawa da maman Aman, sai na ga ta ƙara tsuke fuska ina ta zama suna ta maganganunsu zaman duk ya gundure ni na miƙe na ce mata sai anjima ina tunanin zai taso mu tafi sai ce mini ya yi ina za ni na ce wurin Haj.
Ina shiga wurin Hajiyar kuma na yi masa text zan koma gida saboda wanka.
Ok kawai ya turo mini na cika tam mai aikin Haj na tura ta karɓo mini Aman suka dawo tare da Dina muka fita tare da ita Iliya ba ya nan keyn motar wani ƙanen babansu ta karɓo ta mayar da ni.