Har ƙarfe takwas bai dawo ba tunanina ma can zai kwana sai ga shi ina kwance a gado, rufe idanuwana na yi a zuwan na yi barci amma ya zauna yana girgiza ni yana mini magana a kunne dole na buɗe ido “Taso mu je mu ci abinci.”
Ya faɗi mini na girgiza kai na ce na ci.
“Ai za ki ƙara tare da ni.”
Na ce a’a ya lallaɓa ni har na sauka gadon muka fita yana cin abincinsa ina kallonsa da ya kammala muka koma ɗaki sai ga Mutum ya birkice yana son haƙƙinsa na ce abun bai ɗauke ba jikina na rawa, ya gama yamutsa ni har ya gamsu sannan ya tafi bayan ya ɗauki kaya kala ɗaya da fitar sa na yi saurin gyara smhimfiɗar gadon da muka yamutsa Inna ta shigo da shirin kwanciya sai mita take “Tun da matarsa ta dawo da ya koma can sai kin yi arba’in ni ba na son wannan fitinar.”
Na yi mata shiru amma a raina ina jinjina ya tafi har sai na yi arba’in, gaskiya mata na haƙuri shi ya sa idan aka samu waɗanda ba sa iya sarrafa kishinsu komai suke yi ciki har da kisa.
Baiwar Allah kusan shekara ba ta tare da mijinta yau ɗaya da ya tafi ya bar ni ya tafi wurin ta na ji ba daɗi, da ƙyar na lallashi kaina, na faɗa ma zuciyata da ke tafasa ba laifi ya yi ba ko ni na dawo tafiya ba zan so ya bar ni ya tafi wurin wata ba to imanin ɗayan ku baya cika har sai ka so wa ɗan’uwanka abin da kake so wa kanka.
Da asuba ina barci na ji ana kiran wayata ban buɗe ido ba saboda barcin nake ji sosai Aman ya ɗan taɓa hirar dare ya tashi ya ƙi barci dole muka zauna inna da ke bisa sallaya ta riƙa kiran sunana na buɗe ido a hankali ta ce “Wayarki ake ta kira.”
Na miƙa hannu na ɗauko ta idona bishi-bishi na ga sunan da na sanya ma Bashir Lema a raina na ce lafiya? Wayar ta ƙara ɗaukar ƙara na ɗauka ina kanga ta kunnena “Ki zo ɗakina.” Abin da ya ce mini kenan ya katse kiran na miƙe ina ɗaura igiyar barcina Aunty Larai na bi na da kallo na fita ɗakin.
Zaune na same shi a gefen gadonsa kafin in zauna ya kamo ni muka kwanta ina duban fuskarsa ” Lafiya ka dawo yanzu? Na faɗi ina duban agogon da ke kafe a ɗakin.
Bai yi magana ba sai ajiyar zuciya da yake fiddawa na hakikance ransa a ɓace yake don haka ya yi ta fama lokacin da Dina ke jinyar ciwon so.
Hannu ya miƙa ya rage hasken ɗakin ni dai na yi lamo a jikinsa amma ina tuna Inna da Aman, bai bar ni na fita ba sai da aka fara knocking na zare jikina na tafi na buɗe Amina ce, ta shaida mini Inna ta ce Aman ya tashi bin ta na yi muka tafi na same shi a kafaɗarta tana jijjiga shi na sa hannu na karɓe shi ina gaishe ta ta amsa tare da tambayar inda na tafi cikin tsoron faɗan da za ta yi na ce Abban Aman ne ya zo ba ta yi faɗan ba sai mamaki da ta shiga na abin da ya kawo shi ni dai na yi amfani da hakan na gama shayar da shi na shiga wanka, na iya yadda aka koya mini na yi na fito na shirya kaina lokacin ta kammala ma Aman.
Amina ta shigo da tray na abin kari na ce ta ajiye ma Inna ni ta kai mini ƙasa tare da na Abban Aman .
Inna ta riƙe baki “Ke da za ki karya kina jego ki sha magani.”
Na ɓata fuska na gaji da shan saƙe-saƙin da take ba ni ta sanya mini turare na turara gabana sai na fita na same shi ya yi wanka har ya sanya kaya yana ɗaura links na tsaya gabansa ina gaishe shi ya kama hannayena sai ya ba ni feck a kumatu na yi murmushi sai na shaida mishi abinci ya kammala ya dubi agogon da ke ɗaure hannunsa wayarsa da ke bisa gado ta yi ƙara na isa na ɗauko na miƙa mishi sunan Haj na gani sai da ya gaishe ta na ji yana faɗin ni ba mu yi da ita za ta tafi ba ta dai ce ba za ta bikin su Dina a Family hause ba, ni kuma na ce ta yi haƙuri zan saya mata gida amma sai bayan bikin .
Ya yi shiru cikin saurare sannan ya ce ‘Ga ni nan zuwa.”
Ya tayar da kaina a kafaɗarsa ya ce in kawo mishi Aman ya gan shi gidan Haj za shi .
Na ce karyawar fa?
Ya ce sai ya dawo.
Muka fita ya gaishe da Inna ya ga Aman din ya tafi.
Har rana bai dawo ba sai da Su’ada ta zo da yake kullum sai sun zo gidansu saboda shirye-shiryen bikin, ita take ba ni labari Maman su Dina ta bar gidan ta kama haya kafin ta sayi nata ta ce ba za ta yi bikin ya’yanta a Family hause ba.
Wannan matsalar da aka samu ita ta kawo cikas a bikin, yaranta sun bi ta su kuma dangin uban sun ce matuƙar ba su dawo ba sai dai ta aurar da su ita kaɗai Bashir Lema ya so a ƙyale ta Haj ta ce idan har yaran ba su dawo ba har shi ta zare hannunta a kansa.
Ya tafi gidan da ta kama da bai taɓa zuwa ba ya zo da su Dina.
Hakanan aka yi bikin ana ta yada magana da aka kai Dina ma sai da aka yi faɗa tsakanin yan’uwansa da ƙawayenta cikin daren ta zo gidan Haj suka kwashe ta ba daɗi da yan’uwan Lema ranar da na je wuni a gabana Haj ke fadi “Shi ya sa sai a ce an ƙi mutum ba son shi ne ba a yi ba sai dai a ƙi halinsa, tun asali Farida fitinanniya ce ba ta so a zauna lafiya matuƙar tana ƙasar nan ba za a yi kiɗa da waƙa ba, ga shi yanzu ya ce matuƙar ta koma London a bakin aurenta haka za mu yi ta fama tana tayar mana da hawan jini.
An dai gama biki dukkan su Kaduna aka ajiye su na je gidan Dina sai dai ban zauna ba don ban yi arba’in ba har lokacin.
Lema ya koma Abuja yana tafiya kuma aka ce mini Maman su Amal ta bi shi, da na tuna zaman da za mu yi da ita sai gabana ya buga in cika da fargaba.
Rashin zuwan sa kuma tun da ya tafi na kan danganta shi da komawar ta sai in ce shi kenan ta ƙwace mijinta an bar ni nan, na dage da addu’a har azumin litinin da Alhamis na so farawa Inna ta hana ni ta ce in bari tukun ɗana ya yi ƙwari, ina yawan sadaka saboda ita sadaka maganin masifa ce.
Ga gyaran da na mayar da kai Inna na mini shi dai uzurin aiki yake ba ni na wata kwangila da ya samu na yi arba’in na je gidanmu da na sauran dangi Haj dama kullum sai an kawo ta ta duba mu.
Shirin komawa aka fara yi mini Aunty Larai da Lubna da Aunty Ya gana suka yi mini rakiya Hassana ta so zuwa yarinyarta ba ta da lafiya.
Idan na ce ban tsure ba cikin fargaba nake mai yawa kan komawa ta in tarar da Maman su Dina na yi ƙarya, addu’a nake ta yi a zuciyata ko hirar da suke yi a hanyar mu ban sanya baki ba.
Mun isa sha biyu na rana, Amina na gaba Aunty Larai na biye da ita sai ni.
Ba kowa a falon sai TV da ke ta aiki muka wuce ɗakin saukar baƙi, Amina ba ta zauna ba kitchen ta faɗa nan na zauna tare da su muka yi sallah kamar ba ta gaji ba sai ga abinci ta haɗa ta kawo kowa ya ci aka kishingiɗa sai na yi amfani da damar na tafi ɗakina na buɗe gyare yake tsaf sai na sa turarukan wuta da na zo da su ɗakin ya ɗauki ƙamshi Abban Aman ya kira ni muka yi magana na shaida mishi mun iso ya ce na gaishe da su Aunty Larai sai ya dawo.
Na rufe ɗakin na fito na wuce dakin da suke nan muka zauna har magrib da Abban Dina ya dawo ya gaishe da masu rakiyata ya ɗauki Aman ya tafi da shi na yi musu sai da safe na tafi na shiga ɗakin ba daɗewa ya shigo Aman ya miƙo mini ya fita ina sauya mishi kaya ya shigo na miƙa mishi shi na yi shirin barci zuciyata cike da son tambayarsa ina su Amal da Mamanta.
Sai da ya yi wanka muka kwanta daren ya zame mini daga cikin dararen da ba za su gogu ba a rayuwata da Bashir Lema ko da ya dawo sallar asuba nan ya dawo ya kwanta duk da gajiyar da nake ciki na yi wanka na gyara kaina na fita wurin su Lubna da na samu har sun karya anan na zauna ni ma Amina ta kawo mini abin karyawa ina ta mata sannu da ɗawainiya.
Karfe sha ɗaya sun gama shiri mai gidan ya yi musu kyauta mai nauyi direban Haj da ya kawo su ya juya da su sai na ji duk ba daɗi, don shi ma mai gidan ya fice ɗaki na koma muka kwanta da Aman, abinci ma ban fito ba anan Amina ta kawo mini sai na ji duk na takura da zaman ɗakin fita na yi na zauna a falon da na saba zama ina nan Amal da Mamanta suka shigo trollyn da direba ya shigo musu da ita na gane tafiya suka yi na yi mata sannu da zuwa ta ɗaga mini hannu sai ni ma na kama kaina. Sai da ya dawo da yamma na ji ashe bikin ɗiyar ƙawarta suka je a Kano. Kwana na biyu da dawowa Sai ga Abakar ya dawo gidan shi ma duk na takura da zaman gidan bayan Mamansu Amal da Amal ɗin ga shi shi ma da yake son takura mini da son yi mini magana ba na cin abinci tare da su sai dai idan ni ke da girki na kan yi da kaina in gabatar masa da shi su kuma su ci na Peter.
Ya mallaka mini mota wata fara tas mai kyau na yi murna ƙwarai da godiya na kira duk wasu na kusa da ni na faɗa musu suka taya ni murna matsalar dai ban gwanance a tuƙin ba.
Wani yammaci mun dawo daga sallon na ga Amal cikin kwalliya za su fita da Abakar a motarsa suka fita, kallo ɗaya na yi musu na wuce Amina na biye da ni.
Lulluɓina da jaka kaɗai na ciro na dawo falon da na fi mu’amala da shi na mayar nawa na zauna Amina ta kawo mini apple da na ce ta wanke mini ina ci Abban Dina da matarsa suka fito ya zo inda nake ya ɗauki Aman da na ɗora kan gadonsa yana kwance yana ta wutsil-wutsil ya ce na dawo?
Na amsa mishi ya koma kusa da matarsa suka zauna. Shuɗewar awa guda Amal ta shigo da wani irin ihu da gunji da ba iyayen kaɗai suka shiga kiɗima mai tsanani ba ni kaina ta razana ni.
A tare suka yi kanta cikin su har na kasa gane wanda ya fi shiga ruɗu ni dai na miƙe tsaye na tsaya a inda nake ina jin cikin gunji tana faɗin yau ta faɗa ma Abakar irin ƙaunar da take masa amma ya tabbatar mata ba zai aure ta ba yana da wadda yake so rarrashi suke tana botsarewa abin har ya ba ni takaici na tattara na yi dakina kamar wasa haka suka yi ta fama da ita ta ƙi haƙura har uban ya kira Abakar ya iso a wani yammaci sun marabce shi da abin ci da na sha da suke tarbar bakinsu masu muhimmanci kafin suka zauna Abban Dina ya bijiro mishi da son auren Amal don ta ce shi take so, uwar ta karɓe da cewa idan ya karɓi auren Amal akwai kuɗaɗe da za su ba shi ya yi jari ta ɗora bundle na dolar Amurka har biyu a kan tebur ɗin gaban su za kuma su sai mishi muhallin zama a birnin Abuja.
Godiya ya yi musu kan wannan kyauta ya ce su saurare shi ya tashi ya tafi.
Amal ta shiga walwala da murna kafin ta gano Abakar zare kansa kawai ya yi.