Tsiya ta yi ta yayyafawa ba za ta yarda dukan da na yi ma yarta ba, ranar dai ya ɗan taɓuka ya ce marina ta yi don na ɓarar mata da jus ya nemi ta fita ta ƙi ta ce saboda wannan abar ita zai duba ya yi ma haka? Ya ce Yes yadda ya sanya sadaki ya auro ta ni ma haka ya yi ta yi ta nuna kanta tana faɗin ita yake haɗawa da wannan sai ta nuna ni.
Ya ce “E. Ta jinjina kai ta fice ya je ya rufe ƙofar ya dawo jakar da ya yi tafiya ya ɗauko sai da ya fitar da duk abin da ke ciki tsakiyar wasu kaya da ke tsakiya ya ciro manyan banguls suna sheƙi ya ce “Ga gift da ya bari sai ranar da za mu cika shekaru huɗu da aure ya ba ni. Kallo ɗaya na yi musu na kawar da kaina hawaye na zubar mini ta gefen ido.
Aka fara knocking ya tambaya Amina ce sai ya tashi ya buɗe ta miƙo Aman ya karɓo shi ya zo ya ba ni na ƙi karɓa sai shi ya ciro ya manna mishi a baki.
Wunin ranar bai shawo kaina ba dare ya yi hannuna ya hana ni barci da zugi da sassafe Dr da ya kira ya zo ya duba hannun magunguna ya ba ni ya yi mini allura.
Sai da muka kwana uku ya ga ba ni da alamar haƙura don ba na magana da shi ko Aman din ko oho nake da shi idan yana nan abin da ya fi ci mishi tuwo a ƙwarya kenan ya kira Baba Isah ya kai ƙarata don mun samu sabani da yarinyarsa nake fushi da shi ba tare da sauraren ta bakina ba baban ya yi mini tatas da ba ni umarnin na ba shi haƙuri,na ja shesshekar kuka na ɗauke idona daga kallon wayar da ya sa a hands free ya fita ya ja mini kofar, ya dawo ɗauke da Aman da ke zallon in ɗauke shi ya tsaya da shi a kaina na kai hannu na goge hawayena sannan na miƙa mai lafiyar na karɓe shi annuri ya mamaye fuskar Bashir Lema ya zauna kusa da ni yana kallon mu yana ganin ya saki nonon ya karɓe shi ya fita da shi bai jima ba ya dawo inda ya tashi ya zauna ya lallaɓe ni in je in yi wanka faɗan Baba Isah ya sa na miƙe na tafi, na fito ɗaure da towel na gan shi kwance bisa gado daga shi sai guntun wando na zauna a kujerar madubi na fara murza mai na sanya hoda da turare ya sauko gadon ya taso ya iso ya ɓalle gorar madara mai sanyi da ke hannunsa ya miƙo mini na karɓa na sha don hakika akwai yunwa tare da ni a kwanakin nan ba na iya cin abinci mai yawa kaɗan nake ci daga wanda Amina ke kawo mini in ji cikina ya cushe sai da na ji cikina ya taso na ajiye gorar saman mirror ya miƙo hannu zai kwance towel ɗina na riƙe sai ya sa duka hannayensa ya tashe ni ban yi yunƙurin kokowa da shi ba har muka kai gado hasken ɗakin ya kashe ya juyo gare ni al’amari mai girma ya samu a wannan haɗuwa ta mu da ta sa bayan lafawar komai ya yi ta sakin zantuka masu nauyi akan sha’anina tarin ƙaunar da yake faɗi yana yi mini ta zubar da kaso mai yawa na ɓacin ran da nake ciki duk yadda na kai da ƙi sai da ya sa muka yi wanka tare na sake wani sabon shirin, duk da idanuwana da suka kumbura don tsakanin kukan da na yi a kwanakin nan ba ƙaramin kyau na yi ba cikin riga da skirt na English wear bakake da ratsin fari wata hula da na sa ta tsari a wurin Mufida na saye ta na ɗora na koma tsakiyar gadona ina kallonsa yana nashi shirin wata dakakkiyar shadda ce da ta ji ɗinkin da ya zauna a jikinsa ga hula ta tsaya a sha tara agogo da Links din wuya da hannu iri daya takalmi Cover ne ya yi kyau ƙarshe da na samu zuciyata na narkewa ina ƙara dulmiya kan ƙaunarsa, cikas ɗina da shi matarsa da yarsa Amal.
Ya miƙo mini hannunsa na kama ya ja ni na sauko “Zo mu fita ki zauna a falo ki daina zama ke kaɗai a ɗaki kina tunani.” Kai na ɗaga mishi ba don ina son ganin Amal ko uwarta ba muka fita su ɗin na fara gani uwar tana zaune kan wani ɗan Bar da aka yi don shan drinks, Amal na kwance da ear piece a kunne uwar ya dube mu sai ta fara sakin magana da za ka san tsabar kishi ne ke ragargazar ranta wai an dai yi abin kunya mutum ya auro sa’ar ya’yan cikinsa.
Bai ce mata komai ba sai da ya raka ni na zauna ya koma inda take ya dafa teburin gabanta ban san me ya ce mata ba ta fara ihu da sakin maganganu, kusa da Amal ya zauna bai tanka ta ba wayarsa da aka kira ya sa ya ce in koma ɗaki na san yana gudun ya tafi ya bar mu tare na ce na kusa kammalawa idan na gama zan tafi ya kaɗa kai ya fice.
Khalil da Abakar suka shigo, kwana biyu ban gan su gidan ba na ƙara duƙar da kai kan abin da nake zaune kasan Carpet ina ci.
Khalil ya ƙwala ma Amina kira ta iso cikin sauri ya karɓi Aman yana ɗaga shi sama yaron na bangale baki shigowar su na ga Maman su Amal ta bar wurin Amal ta dawo kusa da Abakar na miƙe tsam don komawa ɗaki ca! Da suka yi mini da ido ya sa na rasa ina zan tsoma raina da ƙyar na ja ƙafafuna na tafi ɗakina.
Zuwa lokacin na fara jin ba daɗi da zaman Amina ba aure, ina yawan roƙon Allah ya kawo mata miji na ƙwarai don dai ta yi girman da ya kamata ita ma ta tafi ɗakinta don na san idan ba ta girme ni ba ba zan girme ta ba.
Amal sam ta kasa haƙura da Abakar, wani irin mugun so take masa.
Wani babban mutum mai muƙami na siyasa ya fito neman aurenta amma ta ƙi fafur ta ce sai Abakar.
Iyayen sam ba su da kwanciyar hankali ta kai ta kawo bin sa take duk inda yake babban tashin hankalin da ta fara shaye-shaye duk yadda iyayen suka so tsare ta a gida abin ya faskara ba a yi mata tarbiyyar bin umarni ba sai yadda take so idan ta fita sai ta raba dare.
Wani yammaci ina gyara kayan Aman wayata ta yi ƙara na dubi inda take ina jin ƙyuyar tashi in ɗauko har ta katse ta kuma ɗaukar ƙara na miƙe na isa gare ta baƙuwar lamba ce na yi picking muryar Abakar na ji zan katse kiran na ji ya fara haɗa ni da girman Allah in tsaya in saurare shi, sanin nan ɗin ba hurumin da za a haɗa ka da girman Allah ka yi abu ba ne na datse kiran na cilla wayar bisa gado na koma kan aikina shigowar saƙo na ji ban duba ba har sai da Amina ta miƙo mini Aman, na zauna tsakiyar gado ina ba shi nono na ɗauki wayar text ɗin na fara buɗewa daga Abakar ne roƙona ya yi kan in ɗauki wayarsa kan maganar da na taɓa yi masa ne na aure ina za mu haɗu mu yi magana yana son yarinyar tawa.
Wayar na sauke ina ɗaukar zancen na shi a shewar dila wai ni zai yi ma dabara take na fara neman tsarin Allah daga faɗawa tarkon sheɗan.
Tun daga ranar Abakar ya sarƙafe ni da turo saƙonni na son in ba shi dama da gaske yake har na aminta da ba shi damar ya ce mu haɗu a wurin shakatawa na Drumstick.
Da yammacin wata lahadi na shirya cikin hijab dogo har ƙasa fuskata da tafukan hannayena kawai ke bayyane na bar Aman wurin Amina na ce mata zan je na dawo sai da na yi Bismillah da addu’o’i na tashi motar gabana na harbawa ina jin ban yi daidai ba abin da na yi .
Na isa ƙarfe biyar daidai da na duba agogon jikin motar, jiki a mace na sauka na jingina da motar ina ƙare ma wurin kallo a waya yar runfa na hango Abakar na taka na isa wurin kallo ɗaya ya yi mini ya sunkuyar da kansa ya ture mini kujera na zauna muka gaisa a sanyaye ya tambayi me za a kawo mini na ce ba zan ci komai ba kai tsaye ya tafi kan abin da ya sa ya neme ni.
Amina da son jin labarinta ya tambaye ni na shaida mishi iyakar abin da na sani kanta ya ce in shaida mata idan ta amince sai na tura mishi lambarta, na yi mishi sallama har zan miƙe ya ce “Zan yi aure don kare kaina daga faɗawa halaka amma ba don so ba mutum ɗaya… Amal da ta diro kanmu kamar an jefo ta ta katse shi daga zancen da ya fara wani irin kallo take mana mai cike da tarin mamaki kafin ta buɗe baki ta ce wani abu na tashi na yi tafiyata.
Ina kan hanya ina jin faɗuwar gaba addu’a na yi ta yi har na isa gida.
Kasantuwar ni ke da girki sallah na yi sai na yi wanka na fito.
An zauna cin abinci Aman mai son a sake shi ya yi ta’adi bai bar ni na ci na kirki ba uban ya karɓe shi don in samu in ci, Amal da ba ta halarci zaman cin abincin ba ta fito daga ɗakinta gaban teburin ta zo ta tsaya tana fuskantar uban sai da ta yi mini wani kallo da ya haifar mini da kaɗawar ciki sannan ta taɓe baki ta ce Papi ɗinta ya bincike ni ta gan ni da Abakar.
Wani kallo ya yi mata mai nuna son tabbatar da cikin hankalinta take ta ƙara jefa mini wani kallo ta ce idan bai yarda ba ta yi mana vedio hantar cikina ta kaɗa na dinga ji kamar na tashi na zura da gudu.
Bai ce komai ba bayan kallon video da ya yi na miƙe na tafi ɗakina ina kiran sunayen Allah sai lokacin nake jin nadamar amsa kiran Abakar na lulluɓe ni don wani zullumi ke rufe ni kar ya san alaƙata da Abakar.
Bai tsaya kallon labarun da ya saba ba ya shigo ya kuma zaunar da ni don tabbatar da gaskiyar abin da ya gani, ba wata-wata na ce na shiga wurin ne muka haɗu ya ce yana son magana da ni Amina yake so.
Bai ce mini komai ba miƙewa ya yi ya yi shirin kwanciya ya kwanta ya rufe rabin jikinsa idanuwansa a buɗe suna kallon sama na gama abin da nake na kwantar da Aman tsakiyar mu na kwanta har safiya bai ce mini komai ba ni dai sai addu’o’i nake ta ja.
Da wuri ya fita sai da na kammala abin da zan yi na samu Amina a ɗakinta na yi mata bayanin sakon Abakar, idan tana son sa sai in ba shi nombarta.
Hawaye ta fara zubarwa tare da zuwa ta kama ƙafata tana yi mini godiya bisa alherina a gare ta murmushi kawai na yi na ce mene ne abin kuka kuma? Ta goge idonta na ce in ba shi? Murmushi kawai ta yi sai ta miƙe ta tafi ta hau katifarta ta juya baya.
Ni ma na juya na ja mata ƙofar.
Text na yi masa na tura mishi nombar Amina da bayanin amincewar ta, sun fara waya ba daɗewa ya ce zai turo iyayensa na samu Bashir Lema na yi masa bayanin, kallona ya yi ta yi ya daɗe bai yi magana ba har na tsargu.