Skip to content
Part 15 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Da safe ina kwance saboda sanyi mai ratsa jiki da ke shiga ta duk da tattakewar da na yi.

Hassana suna ta hayaniya da ƙawayenta suna tsara yadda za su gudanar da shagalinsu, ina sauraren su sai murmushi nake har na ji fitar su na gyara kwanciya sai na ji shigowar baƙi da ba zan iya shaida muryoyinsu ba ina kwance Mama ta shigo ta ce “Taso Ummu, baƙinki ne.”

Na gwalo ido daga kwancen “Ni kuma? Ta ce “Ki taso.”

Na miƙe laffaya na naɗe jikina sai na fita mata ne su uku Su’ada da na shaida a cikin su ya sa ni gane daga inda suke.

Na zauna kusa da Su’ada na gaishe su, biyun manyan mata ne Su’ada ta kama hannuna ta sanya cikin nata “Na ji daɗi ƙwarai da za ki zama matar yayana.” Ɗan murmushi na yi, ɗaya matar ma ta yaba ni ɗaya ce dai ba ta ce komai ba. Su’ada ta gabatar mini da su a matsayin yan’uwan Bashir Lema uwa ɗaya uba ɗaya wadda ba ta ce komai ba ita ke bi mishi suna kiran ta Mama Zulai, a hayin Rigasa take aure.

Sai mai bi mata Aunty Fatahiyya a Malali take aure.

Suka ɗan sha lemon da Husaini ya shigo masu da shi suka ce mini za su tafi Su’ada da ɗaya matar da ta yaba ni Aunty Fatahiyya kenan suka ajiye mini leda kowacce da ta ta. Na yi musu godiya na bi su don rakiya suna gaba ni da Su’ada muna baya har lokacin tana riƙe da hannuna “Ina fata za ki gyara kanki da kyau da kula da mijinki sosai saboda wata za ki je ki samu Ummu, mahaifiyarmu na son ki ta ce na gaishe ki.” Ta faɗi cikin rage murya.

Na ce “In sha Allah zan kula Mama kuma ki ce ina amsawa na kuma gode.”

A mota suka zo har kuma gaban ta na raka su Su’ada ta ce na raka ta wurin Nabila ba mu jima ba don cewar da suka yi mata kar ta daɗe.

Aunty Fatahiyya ita ta ja motar na ƙara musu godiya suka tafi.

Na koma gida ina ma Mama bayanin su ina fitar da abin da suka ba ni ledar Su’ada Set ne na mayuka masu asalin kyau da tsada sai na Aunty Fatahiyya rigunan barci ne masu kyau da suka yi matuƙar burge ni sai takalma ƙafa ɗaya.

Na ji dadin kyautar na ƙara gode musu a raina na tashi na adana su a kayana.

Da ya bar wurin Ummu Radiyya wurin mai nuna masa gidan da aka samu ya nufa ya duba gidan ya sa a ka yi masa vedio ya tura ma yaransa suka kukkushe wannan ta ce ba wannan wannan ta ce abu kaza bai mata ba.

Dina da ba ta ce komai ba ta ce “Ka yi mana sabon building Papi.”

Shiru ya yi da ta faɗi haka zai so yi musu yadda suke so amma ina zai sa Ummu Radiyya, part ɗinsa na gidansu babu inda zai ajiye ta dole dai sayen ginannen ya kama shi.

Ya bar wannan gidan daga ba sa so ya ce a nemo wani sai ya nufi gida.

Ɗaki ya bi kowaccen su ya duba ta ya janyo su zuwa parlor Amal ta ce mishi gobe za su koma fa kansa ya shafa ya ce zai zo daga baya su za su fara tafiya.

Dukkan su tambayoyi suke zubo mishi me zai tsaya yi?

Ya dai kasa faɗa musu aure zai yi, ya bar su ya tafi wurin Hajiyarsa,  magana suke kan iyayen Ummu da ita kanta Ummun, sai da aka kira azahar ya fita.

Washegari shi ya tafi raka yaran nasa zuwa Abuja suka hau Flight na U.S.A

Kwana ɗaya ya yi ya dawo Kaduna ya ci gaba da shirin aurensa duk da Baba Isah ya ce mishi ya ɗan saurara ko da ya yi sati rabon sa da ita Baba Isah ya ce mishi an ba shi an kuma amince da buƙatarsa ta haɗa na su auren da na  Hassana.

Ya yi farin ciki amma kamar ma Hajiyarsa ta fi shi farin ciki sai hamdala take ta so a haɗa akwatunan lefe amma babbar yar ta mace mai bi ma Bashir Lema Mama Zulai kamar yadda duk Family ɗinsu ke kiran ta ta hana tana ta ƙarfafa mata kawai a ba su kuɗi daga ta taɓa aure.

Ta biye zancen yar ta ta amma duk da haka sai da ta zaɓar ma Ummu Radiyya atamfa Super wax guda uku da less biyu wurin Fatahiyya, Su’ada na wurin ta ce “Ni fa Hajiyarmu? Harara ta ba ta ta ce “Surukata na saya ma wa.”

Suka sa dariya Su’ada da Fatahiyya Mama Zulai ta kasa ko murmushi don ita ba ta maraba da auren da ɗan’uwan nasu zai ƙara ita kaɗai ke shiri da matarsa Farida.

Sauri-sauri take ta bar gidan don ta samu ta isa gida ta tsegunta ma Farida da take tunanin ba wanda ya faɗa ma ta za a yi mata kishiya da wannan figigiyar yarinyar yar cikinsa.

Tana ta fatar ya zamanto ita ce ta farko da za ta fara kai mata labarin.

Nan ta bar Fatahiyya da Su’ada Hajiyarsu ta haɗa mata yan kayan masarufi da take ba ta duk cikin su ita ce take auren ma ra shi a Naira road take aure .

Ta shiga gida ana sallar la’asar,sai da yaranta suka fita zuwa makarantar islamiyya ta janyo wayarta da ta sanya ma kati musamman don kiran, ba ta da manyan yara saboda mutuwa da na farkon suka yi .

Bugu daya kiran ya shiga sai dai har ta ƙaraci ɓurarinta ta katse ba a ɗaga ba

Sanin halin matar yayan nata akwai ginshira ba lallai ko ta kallon kiran ta ɗaga ba don ba ta son a dame ta duk da ƙosawar da ta yi ta isar da tsegumin da ke tsungulin ta haƙura ta yi ta fita tsakar gida ta kama harkokin gidanta har sai dare tana tare da Maigidanta sai ga kiran ta kallon sa ta yi don ba ta so ya fahimci da wa za ta yi wayar, yana yawan jan kunnenta kan zantukan da take kwashewa na family ɗinsu tana ba ta , ita kuma tana haka ne saboda kwance na ta da na ƴaƴanta da take aiko mata ta kan kuma yi sayayya ta turo mata ta ce ta sayar .

Fuska ta yi ta mike sai ta bar wurin can ɗakinta ta shige ta soma amsa kiran.

Bayan gaisuwa sai ta tambaye ta yaushe za ta zo? Sai an yi biki ko kafin a yi ?

Da rashin fahimta ta tambaye ta bikin wa za a yi ? Cike da jin dadin ba ta sani ba ta gyara zama “Baban Dina mana da zai yi aure ashe bai faɗa miki ba ?

Daga ɓangaren Farida wani nauyi ta ji kanta ya yi da jin zancen kamar almara sai dai sanin babu wasa irin wannan tsakanin ta da mai ba ta wannan mummunan labarin ballantana ta ce wasa take mata.

Kin san me kike faɗa mini Mama Zulai?

Kai ta fara ɗagawa kamar tana ganin ta  “To ki tambaye shi daga ba ki sani ba amma tabbas haka maganar take.”

Ci gaba ta yi da magana sai da ta kula ita kaɗai ke zubar ta tuni ta daɗe da kashewa ya sa ta juyawa sai suka yi ido huɗu da mijinta Malam Adamu, wani dibi -dibi ta yi tana mai addu’ar Allah ya sa bai ji ba sai dai addu’arta ba ta ci ba don lafazin da ya furta mata

“Wannan ba hali ba ne mai kyau Zulai, amma kin kasa gane kin girma. Mene ne amfanin kunna fitina?

 Shiru ta yi ta raɓe shi ta ɗauki buta ta tafi banɗaki ta kuma ƙi fitowa so take sai ya kwanta ta fito.

Duk borin Farida da barazanar ta kan auren da zai kara bai ji ko gezau ba shirin sa kawai yake baƙin cikinsa ɗaya har bikin ya taho daf bai samu gida irin wanda yaransa ke so ba har sai ana saura kwana uku ya samu wani gida anan kusa da gidansu na Unguwar Sarki layi biyu ya raba su shi ma bai yi yadda yaran ke so ba bene ne hawa ɗaya sun ce ya yi musu sai dai ba wadataccen  space harabar gidan ina za su shaƙata ko wacce ina za ta ajiye motarta akwai rumfar adana motoci da bai fi ta ci mota uku ba don a abubuwan da suka tsara mishi zai saya ma kowaccen su mota za a zubo su a jirgi gefe guda kuma Hajiyarsa ta nuna fushinta kan rashin sayen gidan har lokacin dole ya biya kudin gidan kusan sabo ne fenti kawai za a yi da yan gyare-gyaren da ba a rasa ba hakan ya sa har ranar ɗaurin aure ba a kammala ba ga furnitures ya yi magana da wani kamfani masu shirya gida, abin ya haɗe mishi ga London da zai koma ya taho da yaransa ya dubo matarsa da kwana biyu ba ta da lafiya ya yi magana da iyayen Ummu tarewar ta har sai ya dawo.

Ana ta shirin biki, Aunty Ya gana da Lubna kullum sai sun zo saura sati guda ya rage Aunty Larai ta zo ta tafi da ni kamar yadda ta ce “Aunty Ya gana ta ce ba su gane ba Hassana fa?

Harara Aunty Larai ta ba ta”Ku ba ta shirya Hassana kuke ba don Ummu ta taɓa aure? Ni ma zan je na shirya ta.”

Dariya suka yi Ya gana da Lubna.

 yamma muka tafi don ba da wuri ta zo ba.

A gidan Aunty Larai wurin gyara na musamman ta kai ni, kullum Baba Isah ke fita da ni ya ajiye ni gidan da ba nisa da nasu can nake wuni shi take roƙo kuma ya ɗauko ni gyara nake sha ba na wasa ba ni kaina sai na yi ta kallon kaina da zarar na samu na keɓe, na yi kyan da tsayawa faɗi ɓata baki ne santsin fata da ƙamshi  ko angon Aunty Larai ta hana shi gani na ni ɗin ma hankalina na gidanmu da aka ce tuni hidimar biki ta yi nisa baƙi sun zo daga Borno Gwoggo Mamu ma ta iso da zuri’arta daga Zaria, an kawo akwatin Hassana.

Labarin komai sai dai na ji a bakin Nabila da ta ƙi zuwa saboda Aunty Larai don na ce mata ta sani.

Sai ana gobe daurin aure muka koma gidanmu kowa ya gan ni sai faɗin ma sha Allah amarya ta fito a yi ta rangaɗa mini gudar da ke sa kaina sarawa.

Su Hassana sun gabatar da walima ni kam muna ɗakinsu Nabila da ƙawayena na kusa .

Sai da yamma na koma gida na so zuwa kai Hassana aka ce sai na tambayi nawa mijin.

WhatsApp na shiga na ajiye mishi saƙo ban jira ganin amsar shi ba na kashe datar da wayar duka.

Muka kai amarya gidanta da ke Asikolaye, ana dawowa na nemi makwanci na yada hakarƙarina.

Da asuba na idar da sallar asuba ina zaune a inda na idar da sallar Fa’iza ta shigo, ta tsallake duk jama’ar da ke ɗakin ta iso inda nake, wayar Baba Ali ta miƙo mini “Babanmu ya ce na kawo miki za a kira ki.”

Cike da mamaki na karɓa ina tunanin wanda zai kira ni ta wayar Baba.

Ta juya kenan wayar ta ɗauki ƙara sai na ga ta tsaya tsaye na miƙe saboda msunan da na gani jikin wayar na wuce ta sai na yi waje kusa da bayi na tsaya na karɓa kiran da ya kusa tsinkewa gaishe shi na yi ya amsa da wata irin murya daban da wadda na saba ji daga gare shi, wani iri na dinga ji a jikina da ya sa na ƙagara mu gama wayar ya shaida mini zai zo da daddare mu yi sallama gobe zai tafi ya zo da yaransa. Muka yi sallama na koma ɗaki ina tunanin yadda zan ga ya’yan nasa da aka ce duk mata ne su ukun, hakanan sai yammatan da na gan shi da su a wayar Nabila suka faɗo mini a rai ina saƙa ko su ɗin ya yake da su don a cikin su na ga mai kama da shi.

<< Ummu Radiyya 14Ummu Radiyya 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×