Skip to content
Part 18 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Gaban mirrow na isa na gyara ɗaurin ɗankwalina da ya kwance na fita, gabana na ci gaba da harbawa na sauka ƙasa ‘yammata na hango tun kafin na gama sauka ɗaya na tsaye ta juya baya waya kafe a kunnenta daya na zaune riƙe da remote ta mayar da hankali a canza tasha, ta ƙarshen kallo ɗaya na yi mata kamar ta isa ita da Bashir Lema komai nata na shi ne, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya idonta na kan wayarta.

Da fara’a da na ɗora kan fuskata na ce “Assalamu alaikum.” Cikina cike da mamakin kasantuwar waɗannan zabga-zabgan yammatan ya’yansa to ta yaushe ya aure su na lissafa shekarun auren Baba Isah da yake sa’an shi 15.

Gabaɗaya suka kalli inda nake wadda ke tsaye tana waya ta kafe ni da ido, mai kama da Bashir Lema da na yi imani ita ce babbarsu ta ce mini “Sannu.”

Mai remote ta ɗaga mini hannu, na nemi wuri cikin sanyin jiki da  gaɓoɓi na zauna ina faɗin “Sannunku da zuwa.”

Ba wadda ta amsa sai mai riƙe da remote ta ce “Ina Amaryar Papi?

Ɗan sansarai na yi sai kuma na ce “Ni ce.” Dukkan su na ga wani maɗaukakin mamaki a fuskarsu mai riƙe da remote ta fashe da dariya, mai yin waya ta kashe wayar ta dube ta ta ja wani ɗan banzan tsaki babbar su da na haƙƙaƙe ita ce Dina don ya faɗa mini sunan yaransa Dina ita ce babba sai Amal Suhaima ita ce ƙarama, wayar ta ci gaba da dannawa.

Ƙaramar su Suhaima ta ce “Ba zan yi dariya ba sis Amal? Wannan yarinyar da ba ta fi kamar ni ba papi zai  auro?

Ta faɗi cikin harshen turanci.

“To me ya dame ki? Ta ba ta amsa har na ji ɗan sanyi jin ba ta goyi bayanta ba sai na ji ta ce “Na kira papi yana faɗa mini ɗakunanmu a ƙasa suke, ita wannan da ya kwaso da ko kaya ba ta iya sanyawa ba ita ce tare da shi a sama. Kin ga abin da na guda tun da aka ce zai yi aure, na nuna masa ɗakin da nake so a sama kin ga ya ba ta.

Mun faɗa mishi ba ma son gidan nan ya saya ya ce saboda ita tana zaune gidansu.

Suhaima ta noƙe kafaɗa “Ni ba ni da matsala da ita, kar dai ta shiga hanya ta daga ganin ta kuma yar ƙauye ce.”

Ajiyar zuciya na fitar ina duban yan yatsun hannuna wani abu na nutsewa a cikin ƙirjina su waɗannan ba su yi tunanin ina jin turancin ba? Ƙarfin hali na yi na miƙe na ce su shiga ɗakunan su su kintsa su fito ga abinci.

Dina ta ɗaga mini kai ta miƙe cikin harshen hausa ta ce Papi ɗinsu ya ce keys na ƙofofinsu na hannuna, na ce mata E, ina zuwa.

Saman na koma jikina na ba ni ni suke kallo ni kuma tunani ya sarƙe mini ƙwaƙwalwa yadda aka yi ya haifi wadannan manyan yammata da kuma maganganunsu a kaina na tsaya gaban mirrow ina kallon kaina da neman inda ƙauyanci ya samu matsuguni a suffata, ta su shigar na yawo a idona

abaya ce jikinsu dukkan su.

Na haɗiyi wani yawu na miƙa hannu cikin kasala na dauko keys din na fita.

Kowacce tana nan a yadda na bar ta Dina da na fahimci ta fi su sassauci ita na miƙa ma wa ta karɓa tare da furta ta gode ta wuce Amal ta taɓe baki ta bi ta Suhaima ƙaramar su da nake kyautata zaton za mu zo tsara ta bi su a ƙarshe.

Ina daga tsaye ina shawarta in yi tafiyata ɗakina ko in zauna? Zuciyata mai ba ni shawarar zaman ta ƙarfafe ni kar na share su saboda mahaifinsu, na zauna na zuba ma TV ido ba dan ina gane abin da ake nunawa ba.

Motsi da na ji ya sa ni dawowa daga tunanin da na lula Dina ce da Suhaima sun canza shiga Dina riga ce doguwa ba ta kai ƙasa ba hannunta na best ne ta kama gashin kanta da ya sha gyara a  tsakiya.

Suhaima kuma riga da wando ne na wani  yadi mai taushi sun kama jikinta ita ma kanta ba ɗankwali.

“Bismillah ga abinci.” Na faɗi ina nufar inda aka shirya abincin “Suhaima ta ce “Babu house girl ne a gidan?

Na ce akwai, Dina ta tashi ta biyo ni ta zauna Suhaima ta ce “Pls ɗan kira mini ita.”

Wani dum na ji aike kuma? Sai dai na yi mata uzurin baƙunta na wuce dakin Basira can idan an fita  na kira ta tare muka dawo na nuna mata mai kiran ta da na tsinkayi tana bubbude kwanonin abincin fuska yamutse tana faɗin “Ni fa ba Nigeria ba irin wannan dishes din nasu.”

Basira ta isa gaban su cikin ladabi ta fara gaishe su Dina ta ɗaga mata hannu Suhaima ta ce ta shiga ɗakinta ta wanke mata bathroom basirar ta tafi ta bar ni da tunanin ko ya za ta yi ta gane wanne ne ɗakin?

Amal ta fito, ita ma wata yar riga ce jikinta da har ta fi ta sauran rashin kirki kai tsaye dinning ta nufa amma ita ganin abin da suke ci girgiza kai ta yi ta ce ba za ta iya ci ba ta dawo kan sopa ta zauna tana faɗa musu papi ya dawo ya ba ta key ɗin sabuwar motarta ta fita ta nemi abin da za ta ci.

Suhaima ta ce idan kin fita kuma sai kin taka zuwa gidan Haj. Kuma papi ɗinsu ya ce zai bar ma matarsa keys na motocin ta karɓa mana.”

Tsaki ta ja ba ta yi magana ba sai na gane ita ban ma ishe ta kallo ba, ikon Allah mai tsayar da wando ba zariya na faɗi a raina.

Tunanin kama kaina ya ɗarsu a raina na miƙe kenan kiran shi ya shigo wayata na ɗauka ya tambayi sun iso na ce E muna tare ya ce ga shi nan zuwa in jira shi kaɗan.

Komawa na yi in da na tashi ina jin duk na takura da zaman, ba abin da nake so irin na gan ni a ɗakina in rabu da waɗannan yan rainin hankalin.

Wayata na yi ta dannawa har na tsinkayi buɗe Gate ban motsa daga inda nake zaune ba har ya shigo Amal ta tashi da gudu ta maƙale shi kanta yake shafawa har Dina da Suhaima suka isa Amal ta matsa ya kama hannuwansu cikin shagwaɓa Amal ke faɗa mishi ita yunwa take ji.

Ya ce ba an yi musu abinci ba? Auntynsu tun safe take kitchen ta yi musu girki.

Waiwayowa ta yi ta dube ni sai ta ce ita ba za ta iya cin abincin da ta gani ba.

Key ya ciro ya miƙa mata haɗe da kuɗi ya ce ta fita ta ci abinci bai son zama da yunwa, ina kallon ikon mai sama a haka za ta fita sai ga Basira ita ta aika ta ɗauko mata wani siririn mayafi ta rufe kanta ta fice.

Ajiyar zuciya ta ƙwace mini ganin wannan lamari da ya sanyaya mini yatsu, sam ni kam ban ma ƙaddara ya ga wanzuwa ta a wurin ba hankalinsa na ga ya’yansa tambayoyi yake musu don ya tabbatar ba su cikin kowacce matsala, da kansa ya raka su har dinning ya kuma lallashe su suka ci abincin kamar wasu yan shekaru biyu sannan ya juyo gare ni yana mini murmushin da ya saba yi mini hannu ya miƙo mini yana kira na, na miƙa mishi nawa hannun ya sa a nashi muka nufi sama yana tambaya ta na ga su Dina na ce na gan su.

Shigar mu daki kaya ya sauya muka zauna bakin gado rabin jikina na jikinsa labari yake ba ni kan inda ya je na ce abinci fa ya ce ba yanzu ba, ni ma ɗin ba na jin yunwa hakan ya sa muka ci gaba da wanzuwa a ɗakin har muka tsinkayi knocking shi ya bayar da iznin shigowa ni kuma na raba jikina da na shi Amal ce ta shigo, cikin fara’a ya tambayi har ta dawo? Ta faɗa mishi inda ta je kuma ta yo mishi take away ya zo su ci.

Haka ya mike bai ko waiwaye ni ba suka fita.

Tagumi na zabga ina hango yadda rayuwa za ta cigaba a haka ni dai ban saba ganin wannan abin mamaki ba wai ango ya kwana da ƙunzugu.

Kwanciya na yi na dunƙule jikina ina jin wani sanyi na lulluɓe ni fiye da wanda nake ji. Allah ka sa na iya, Allah ka ba ni juriya nake faɗi iya laɓɓana don ina hango al’amarin,  Abakar ya faɗo mini shi ya sa na ci burin ɗorewar zaman aurena da shi saurayi da za mu gina rayuwarmu, to yanzu wannan ko ba kishiya  waɗannan ya’yan nata sun ishe ni kishi ƙila ma har gara kishiyar da su.

Cikin sati guda da na yi da shi ya tarairaye ni ya nuna mini zallar ƙauna da ta sa zuciyata fara doka masa, dawowar su in dai haka rayuwar za ta ci gaba ba za su bar ni da shi ba akwai matsala, ina son kulawar da ya fara ba ni ina nishaɗantuwa da lokacinsa da yake sadaukarwa ya tarairaye ni.

Na daɗe kwance jin shirun shi ya faye yawa ya sa na tashi na leƙa window tare na hango su shi da su, su duka suna cikin annashuwa na koma na zauna bakin gado ina neman abin da zan yi ya ɗauke mini tunanin su cikina ya fara ƙugi na dubi lokaci ƙarfe huɗu saura kunnena kuma ya tsinkayo kiran sallah, na miƙe na shiga toilet alwala na ɗauro na zo na ba da farali.

Kasa daure kiran ciromar da cikina ke yi na yi na zare hijab ɗin jikina na sauka ƙasa, suna zaune a falon mahaifinsu na sallah na dubi inda yake ina tabbatar ma kaina cikin biyu dole a samu ɗaya, ko dai akwai ƙarancin rashin sani a tare da shi ko kuma ƙarfin zamansa a Turai ya rinjayar da shi.

Na wuce su zuwa kitchen lemo na ɗauko na fito na isa dinning na ɗebi abinci daidai yadda zan iya ci na juyo daidai da idarwar shi, ba zan iya zama a wurin ba saman na koma ita ina ci muna waya da Nabila da na kira mun daɗe muna hira ganin biyar ta yi na sauka ƙasa don faɗa ma Basira abin da za ta dafa ban same su a falo ba sai hango su na yi ta window bisa wasu kujeru a waje su duka huɗun, bakina na taɓe na shiga kitchen ɗin, Basirar da na samu cikin aiki ya sa ni yin turus ta ɗan rusunar da kai ta yi mini barka da yammaci, na amsa sai na tambaye ta abin da take girkawa ta lissafa mini abin da Dina da Suhaima suka sanya ta, abin da Amal ta sanya ta ne ba ta iya ba ta nemi taimakona ni ɗin ma ko sunan abin  ban taɓa ji ba.

Baki na taɓe na ce “Ki faɗa mata ba ki iya ba.”

Alamun razana ƙarara suka bayyana a fuskarta da alama ta shiga halin ni ‘ya su “Ban san ya zan yi ba Haj, wadda ta yi mini hanyar aikin nan ta ce ɗorewa ta a aikin nan rashin saɓa ma yaran nan, ni kuma ban san ya zan yi ba.” Ta ƙarashe faɗi kamar za ta ɗora hannu a ka.

Rasa me zan ce mata na yi na ƙara cewa “Ki tambaye ta.” Sai na juya, don ban ga ta inda har za ta gama nasu abincin ta yi mana wani ba, kamar na tsaya na yi mana sai kuma na yi tunanin ba lallai ko na yi su bar shi ya ci ba.

Sama na koma na shiga ɗakina har aka yi magrib aka yi isha’i na yi wanka na sake kwalliya cikin wasu riga da zane,  ina gyara ɗaurin ɗankwalina ya shigo, bayana ya tsaya ya kwantar da kansa saman wuyana ya zuba hannayensa a jikina “Kin yi kyau babyna.”

Ya kama hannuna zuwa gado muka zauna sai sannan na kula da manyan hotuna da muka ɗauka ni da shi da ya shigo da su na ɗauke su ina kallo fuskata da murmushi don sun yi kyau ni da shi guda biyu sai ni kaɗai guda ɗaya. Na ce mishi na gode. Ya shafi fuskata “Za mu je gida ki gaishe da Haj.” Kai na ɗaga mishi na miƙe neman mayafi na sanya takalmi muka fita ina mamaki da bai yi zancen abinci ba.

Suna kwance dukkan su a falo, shi ya ce musu su zo mu je gidan Haj duk kai suka girgiza, ni dai na wuce na riga shi fita har sai da na shiga motar ya fito ya shiga ya ja mai gadi ya buɗe Gate muka bar gidan.

<< Ummu Radiyya 17Ummu Radiyya 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×