Da daddare mun gama cin abinci ya zauna a falon suna kallon TV shi da ‘ya’yansa, ni ban zauna ba sama na wuce na yi wanka na gyara kaina da mai da hoda da haɗin turarukanmu masu sanyin ƙamshi.
Wata rigar barci da na samu kyautar ta daga Aunty Fatahiyya kalarta ja ce mai guntun hannu da ta yi mini kyau ba kaɗan ba na sanya, ban rufe kaina ba na zura takalmina na sauka ƙasa.
Gabaɗaya suka juyo suka dube ni, jikin hannun kujerarsa na tsuguna na ɗora hannayena kan hannun kujerar na kwantar da kaina a kai, ya bar kallon TV ya juyo gare ni na kwantar da murya na faɗa mishi roƙon Basira, ya jinjina kai “Kuma su Amal sun riga sun sanya ƙawar Mamansu ta samo masu aiki. Amma za a duba.
Karaf Suhaima ta ce “A’a Papi mu ba za mu da Hausa girl ɗin nan ba.”
Na dubi inda take kafin na dawo da saurare na gare shi”Ki ba ta haƙuri kawai Baby.”
Wani yawun da ba shiri na haɗiya jin ya bi maganar ‘yarsa na miƙe na koma sama gado na hau na rufe jikina na shiga barci, cikin barcin na ji ya naɗe ni cikin jikinsa.
Da safe na samu Basira har ɗakinta bayan kuɗin da ya ba ta na ƙara dubu ashirin na ce ta yi haƙuri yaransa sun ce ba za su da bahaushiya ba.”
Ta fashe da kuka”Duk wahalar da nake da su abin da za su yi mini kenan? Na ajiye mata kuɗin gefen ta na ce “Ki yi haƙuri.”
Na fita na shiga kitchen maimakon kwanciya da na yi niyyar yi girki na ɗora adadin flate ɗaya na haɗa abin sha na shirya a tray na fito muka yi kaciɓis da Basira ɗauke da jaka na ce “Lafiya Basira? Ta ce “Zan tafi ne, na gode ƙwarai da karamcinki.”
Na ce “To Basira Allah ya sa da mu da alheri.”
Sai na ji duk ba daɗi don mun saba, ta juya su Suhaima da ke zaune a falo ta ce “Idan kika tafi wa zai gyara mana ɗaki wa za mu aika kafin mu tafi?
Basira dai ba ta juyo ba.
Na fasa isa dinning na ƙarasa tsakiyar falon na zauna ina cin abincina da ƙamshinsa ya cika wurin kallona duka suka yi suka koma kallon tv, na gama na koma kitchen na dauraye abun da na yi amfani da su na haye sama, ta window na hango mutanena sun shiga motar Dina sun bar gidan.
Zuwan Su’ada da Aunty Fatahiyya ya sauko da ni, muna ta hira da su, Aunty Fatahiyya ta nuna mini kayan da take sayarwa da suka iso ba wasu kuɗi a hannunta hakan ya sa na ce mata sai wani lokaci ta matsa mini tana nuna mini muhimmancin sayen Su’ada na taya ta na zaɓi wani less na 30k Su’ada ta ce “Wallahi ba za a kawo shi ba na fi karfinsa me ya sa nake mayar da kaina baya? Na rasa yadda zan yi wani na “50k ta zaɓar mini ta ce ita za ta karɓi kuɗin a wurin sa
Sai da su Suhaima suka dawo na ga kayan da suka yi ta jida ashe abinci suka fita ci kamar yadda na yi zargi Su’ada na ta nuna mini da ido to kin ga yadda ake yi dogayen riguna masu daraja suka zaba da za su tafi suna ce mini “Allah ya kiyaye hanya Amal ta dube su baki buɗe “Har da ita ne Aunty? Aunty Fatahiyya ta ce “Wane irin zance ne kuma ban da ita to da wa za ku zauna?
Ta ce “Da Mama Zulai.”
Wata yar dariya Aunty Fatahiyyar ta yi “Ita Mama Zulan ta ce muku za ta bar gidanta ta bi ku can ta zauna ?
Suhaima ta karɓe “Yes sun yi waya da Mommynmu.”
Kai kawai Aunty Fatahiyya ta kaɗa Su’ada ta yi yar dariya suka fita na raka su ina masu godiya.
Washegari ina shiri zan tafi gidan Haj yi mata sallama don gobe za mu tafi Nabila amarya ta zo yi mini bankwana mun ɗan taɓa hira na ce mu je gidan Hajiyar, muka fita muka tafi mutanena tun da babansu zai fita suka ce mishi Basira ta tafi kuma yunwa suke ji tare suka fita da shi na rufe ƙofa muka bar gidan.
A can muka wuni Haj ma ta yi mini tsarabar kayan amfani sosai da ta ce ba lallai in samu a can ba.
Tare muka wuni da Nabila sai yamma na yi mata rakiya ta tafi ni kuma na jira sai da ya zo da daddare muka tafi.
Muna shiga falon Amal ce kaɗai ta yi saurin isowa ta kama hannunsa tana tambayar shi “Wai da gaske har ni za su tafi? Sai da ya zauna ta zauna kusa da shi ya ce “Har da ita ɗiyata Amal.”
A cikin harshen nasara suke maganar sai na gwada kamar ban san me suke cewa ba na wuce sama na bar ta tana dire-diren ita mominsu da Mama Zulai ta ce za su.
Har na gama kwanciyata na kwanta tunanin irin rayuwar da zan yi da waɗannan bayin Allah a Abuja na damfare a cikin kaina.
Da safe ya ce mini ƙarfe goma za mu tafi na riga na haɗa suturuna waɗanda su kaɗai ne abin da ya ce zan tafi da su, Suhaima da Amal na ta yi ma akwatunana da Hassana da Lubna suka janyo don tun tara suka iso ganin tafiyata wani kallo, har wani suna suke faɗi suna dariya.
Hassana ta ce “Ya kamata Aunty Ummu ki sake akwatunan nan ki sayi na masu kuɗi waɗannan yan rainin hankalin ya’yan mijin naki su suke ma dariya.”
Na ƙara kallon akwatunan tun na aurena da Abakar ne da har yau ba abin da suka yi, Lubna sai huci take don duk cikin mu ita ce ta gado zuciyar bare-bari.
Ta ce “Ni ke zaune da yaran nan karairaya abin banza zan yi na watsar.”
Na yi murmushin takaici “Ita rayuwa duk inda ta kai mutum akwai irin haƙurin da za ki ga dole sai ya yi shi Maman Sayyid.”
Ta ja mummunan tsaki ta yi gaba, muka bi ta.
Su suka sanya mini kayana a Boot, Bashir Lema ya jima da tafiya gidan Haj, ganin yadda suka baje suna cin abincin da aka sawo musu na ce mu koma sama .
Ɗakina muka shiga muka zauna muna hira goma saura minti biyar sai ga knocking ɗinsa na buɗe ya ce in fito mu tafi, kuɗi na cire na ba kowaccen su har Aunty Ya gana da ba ta samu zuwa ba na ba Lubna ta ba ta muka sauka ƙasa ina riƙe da ‘yar Hassana, jikin motarsa da za mu yi tafiyar a ciki muka tsaya hawaye na ji suna sulalowa daga ƙoramar tozalina Hassana ta kai hannu tana share mini ita ma nata idon na zuba, Lubna ta karɓi yarinyar tana ƙoƙarin hana mu ga nata ruwan hawayen “Allah ya kare ki ya tsare ki Ummu Radiyya ya kai ku lafiya.”
Na gyaɗa kai “Amin Maman Sayyid.”
Su Amal suka zo suka wuce mu zuwa motar Dina da za su tafi a cikin ta ta Amal da Suhaima an wuce da su tun jiya “Allah ya ƙara maki haƙuri Aunty.”
Hassana ta faɗi tana share hawayenta na ce “Amin Hassanata.”
Bashir Lema ya iso yana murmushi “Kuka ta sanya ku gaba tana yi muku ko?
Lubna ta yi murmushi ta ce “Allah ya tsare ya kai ku lafiya.”
Ya ce “Amin na gode.”
Ya ciro kuɗi ya miƙa ma Hassana “Ku shiga mota Hassana mun gode kwarai, ba samu Driver ba a gida ya kai ku.”
Hassana ta noƙe tana jin kunya na miƙa hannu na karɓa zai buɗe motar Amal ta iso kai ta langaɓe cikin shagwaɓa da harshen turanci ta ce Papi tare da kai zan tafi.
Fasa buɗe gaba da ya yi niyya ya yi ya buɗe mata gaba sai da ta kumbura fuska kamar za ta yi magana sai kuma ta dubi su Lubna ta shiga, ya buɗe motar ya ce mini in zo in shiga na saki hannun Lubna da ke cikin nawa na sanya mata kuɗin da ya ba su sai na shige ya mara mini baya ya rufe ƙofar, ban iya waiwayawa ba don rawar da zuciyata ke yi hawaye sababbi suka ɓalle mini tattausan hannunsa na ji akan fuskata ya taɓo hawayen da ke zuba sai kuma ya sanya ɗayan da ke riƙe da hankacif ya goge mini ya janyo ni jikinsa hancina na shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke fita a jikinsa.
Daidai kunnena yake raɗa mini kukan me kike? Ban amsa shi ba illa ƙara nutsuwa da na yi a jikinsa.
Wayarsa ya ciro ya yi kira tun ina jin shi har barci ya yi awon gaba da ni da ma jiya ban samu yin barci da wuri ba, da safe kuma da na yi sallah ban samu na yi barcin ya ishe ni baSosai na yi barci har sai da aka kusa shiga Abuja, zaune na tashi ina kallon hanya ya tambaye ni na tashi na yi murmushi, ruwa ya buɗe ya miƙo mini na karɓa na sha kaɗan na miƙa mishi gorar, kafaɗarsa na mayar da kaina ya sa hannu ya tallafe ni.
Hira suke da Amal da ke gaba har muka shiga birnin tarayya, idanuwana na bude sosai ina kallon babban birnin, tsarin garin da gine-ginen na yin awon gaba da tunanina.
Wani katafaren Gate na ɗaya daga cikin tamfatsa -tamfatsan gidajen da ke cikin wata hamshakiyar unguwa Direban su Dina da ke gaba ya matsa horn. Wani dogon matashi inyamuri ya wangale Gate motocin suka sulala ciki.
Na miƙa na kukana kawai ina ta kallon haɗuwa da tsarin gidan, a rumfar adana motoci suka Parker su muka firfito Tirƙashi! Na faɗi a ma’adanar sirrina dole su Amal su raina gidanmu na Kaduna, ko kusa ko alama yaro da ganin birni ya san ya fi garin su, harabar gidan kawai a bar kallo ce da ban sha’awa.
Matashin da ya buɗe Gate mai sanye da riga fara da baƙin wando ya zanzare ƙafarsa farin combat ne wuyansa ya sha ɗauri necktie.
Ya ƙaraso yana miƙo gaisuwa wasu matasa namiji da mace su ma suka iso macen mai matsakaicin tsawo ce da jiki fara ce sanye da riga da skirt kala daya da na matashin mai gadin.
Matashin da take tare da shi shi ma dogo ne siriri ya fi wancan hasken fata shi ma shigar sa iri daya da su hakan ya ba ni damar gane uniform ne .
Jerawa suka yi suna miƙo gaisuwa Bashir lema ne ya tsaya yana magana da su ya ce in shige kamar yadda su Suhaima ba su tsaya ba suka wuce.
Aljannar duniya! Ita ce kalmar da ta suɓuce daga fatar bakina yayin da na tsoma ƙafata a wani irin falo da ban san yadda zan fasalta shi ba, abin da dai zan iya cewa ƙaton gaske ne an shirya shi shiri irin na turawa ba hayaniya ba hayaniya ba wasu tarkace, komai an ajiye shi a kintse a kammale ban san iya adadin kujerun da ya laƙume ba na dai hango wani labulai na alfarma da ya raba wannan falon da wani ga wasu irin fitilu da suka ƙara ƙawata wurin, motsin da na ji ya dawo da ni nutsuwa ta ma’aikatan nan ne suka ajiye kayanmu, sai sannan na ankara da ni kaɗai ce na dubi kowace kusurwa ban ga inda su Madam Amal suka shiga ba kusa da akwatina na na koma na tsaya rashin sanin abin yi.
Takun takalman da na ji ya sa ni ƙara waiwayawa Bashir lema ne “Ya kika tsaya nan? Na turo baki “To ina na san inda za ni.”
Akwatina daya ya ɗauka ya kama hannuna muka yi yamma wasu step guda hudu muka taka muka yi yar tafiya sai ga wata kofa ya murɗa handle din muka shiga dogon corridor ne ya wuce wata kofa ta farko sai can kusan karshe muka tarar da wata kofar ya buɗe muka shiga wani falon ne hamshaƙi, marabarsa da na farko girma da wancan ya fi wannan amma shi ma kam ya haɗu ya ja ni muka shiga bedroom da nan take na ji na ƙosa na ɗana tsalelen gadon da na gani.
A bakin gadon ya zaunar da ni ya koma ya zo da sauran akwatinana ya ce “Ki yi wanka ki yi sallah za a kawo miki abinci.
Ina fata za ki fi jin daɗin zama a gidan nan? Na ƙara kallon dakin a raina na ce “Har ma abin tambaya ne, an ce da wani zai ci tsire?
“Idan kika kammala zan kai ki nawa wurin, gobe kuma sai mu zagaya ki ga gidan naki.”
Na yi saurin kallon sa jin gidana da ya ambata “Je ki yi wankan.” Ya ba ni umarni tsaye na miƙe sai da ya fita ya ja ƙofar na saki ajiyar zuciya na tuɓe kayan jikina na zube su bisa gado sannan na taka gaban akwatunana wanda na zuba kayan kwalliyata na ɗauka na bude na ciro kayan kwalliyar na jera su saman mirror.
Na shiga bathroom din da sai da na tsaya na wasu sakanni ina ƙare mishi kallo sai ka ce ba za a mutu ba, komai na ciki fari ne ƙal, an zuba kayan wanka har da towel.
Na haɗa turarukan wanka ina ji na cikin wani irin nishaɗi Mamanmu kawai na ƙosa in gama wankan in kira in ba ta labarin gidan da Allah ya kawo ni kamar a mafarki wai gidana ne.
Cikin nishaɗin na kammala wankan na ɗaura alwala na daura towel na sanya wani a kaina na fito, me zan gani ni Ummu Radiyya! Amal ce da Suhaima tsaye suna girgiza jiki ba alamar rahma a fuskokinsu.