Skip to content
Part 31 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

A falon da na fi zama muka zauna su kuma ba kowa a wanda suke zama. Vicky ta yi ta karakainar jera mana abincin, Nabila da ta yi tsit tana kwasar gitki sai da ta cinye na gaban ta ta ajiye cokalin ta dube ni “Ke haka yarinyar nan ke ba mijinki abinci?

Na ce “Mene ne? Ta ce  “Ta gwanance, kina zaune yana cin abincin wata?

Na narke fuska “Kin san uwar kasalar da nake ji? Allah wanka ma da ƙyar nake yi.”

Ta jinjina kai “Kodayake burgewar auren manya kenan ka yi ta zuba shagwaɓarka ana tarairayar ka, amma matashi za ka ajiye ma wannan budurwar ga girki ka ƙware fargaba ba ta kusa kashe ka ba? Ke kin ga ko ruwa ba ki ɗauko mishi amma yana lelenki ba mu ba masu auren yan bana bakwai komai sai kin yi musu kina nan kina tarairayar su gudun su kyallo wata a waje.”

Na yi yar dariya na ce “Shi ba ma ya cin abincinta, na Peter yake ci Khalil ne dai muddin yana gidan bai yarda da cin na Peter ba ko’ina take sai ya nemo ta ta yi masa.

Ni aka dauko ma ita saboda laulayin da nake.

Ta ce “To ki kula kar ya cutar da yar mutane.

Na ce  “Da fa shekarunta don idan ba ta girme ni ba ban girmat ta, tana da hankalinta in kin ga ya yaudare ta dama ita ma tana da ra’ayin abin.”

Rufe bakina sai ga shi ya fito cikin fararen riga da wando na shan iska na turawa rigar mara hannu wandon iya gwiwa.

Wurin mu ya yo yana ƙwala kiran sunan Vicky ta fito daga kitchen ya ce ta kawo mishi abinci wuri na ya juyo yana mini magana sai da ya fara cin abincin na kama hannun Nabila muka koma ɗakina ta ce  “Amma dai zaman wannan ƙaton baligin bai dace tare da ke ba.”

 Na taɓa baki “To ya zan yi? Yayarsa ke da gidan.”

Ta ce “Kamar ya ya ? Na ce  “Haka Mama Zulai na ji tana sakin magana. Ita ke da gida saboda ita ce mai ya’ya.” Nabila ta dubi nawa cikin  “Ai ke ma ga shi nan Allah ya ba ki idan ya so ma sai ya ba ki biyu a lokaci daya.”

Na yi yar dariya “A ina za a haifo biyun kina ga ko girma ya ƙi yi kullum sai na duba shi a madubi.”

Ta yi dariyar ita ma “Me kike ci na baka na zuba zai yi har sai ya ishe ki. Amma ita Mama Zulan nan ba ta zama nata dakin mijin sai ta baro ta zo nan tana shiga rayuwarki.”

Zan yi magana wayata ta ɗauki ƙara sai da na miƙe na isa gado na ɗauke ta Bashir Lema ne  da jin dadi a muryata na fara amsa kiran ina tambayar shi yaushe zai dawo don kwana biyu kenan da tafiyarsa Sokoto ya yi ma abokinsa ɗan majalisa rakiya.

Ya ce sai jibi na ɓata fuska na ce Nabila ta zo za mu fita na yi ma babynta sayayya.

Ya ce har ta haihu ne  na ce a’a idan ta haihu.

Ya ce to zai yi ma Iliya magana zai kuma sanya mini kuɗi in yi sayayyar da kyau,

na yi godiya na ajiye wayar.

Fuska muka gyara sannan muka fita na leƙa Vicky da ba ta barin ƙofarta a buɗe sai da na buga ta zo ta buɗe na shaida mata zan fita ta yi mini fatan dawowa lafiya.

Har mun bar wurin na ji ta bayan mu da harshen hausa da tun da na gano tana ji idan dai ni da ita ne muke magana ta ce “Kin rufe ɗakinki Madam? Na ce “Ai kam na manta ban zare keyn ba.”

Ta juya da sassarfa ta ce bari na kawo.

Ba jimawa ta dawo da shi ta ba ni na sa a jaka, Nabila cike da ƙullewar kai ta yi mini tambayar dalilinta na tambayar na rufe ƙofa?

Na ce ni ma ban sani ba sai na ba ta labarin satar da ake yi na kuɗin mai gidan don ba a daukar nawa da ajiyewar da nake don gwada Vicky.

Ta ja ajiyar zuciya “Duk yadda aka yi ta san wani abu, da za ki  matse ta za ki ji.”

Na ce  “Zan gwada.”

Muka shiga mota Iliya ya ja wani shopping Mall ya kai mu ya kai mu muka yada zango wani wurin kayan yara komai na saya masu matukar kyau da tsada Nabila tun tana kallona har ta hana ni ta ce kuɗin sun yi yawa na ce kar ta damu ina da shi ne ta ce  “Shi kenan yanzu kin hutar da kuɗina da honey ya ba ni ya ce zai cika mini in yi mana sayayyar ni da Baby.”

Na yi  murmushi na ce  “Sai ki adana abin ki.” Ta ce  Ai da zai ji kin saya karɓe kuɗaɗensa zai yi, zan dai faɗa masa kin saya bayan na saya.

Mun fito suka kwashe suka zuba a mota.

Wani wurin zannuwa muka shiga wasu atamfofi masu kyau na zaɓa na ce “Ban da cika miki kaya Nabila da na ba ki kin kai wa su Mama.”

Ta ce “Haba sai ka ce a kaina zan ɗauka? A fa motarsa za mu koma.”

Mama biyu na saya mata, Lubna daya Aunty Ya gana ma haka sai Hassana Aunty Larai da na sani maabociyar less na sai mata shi sai Maman Nabila ita ma atamfa.

Baba da Baba Isah yadika masu kyau kowa yadi biyar biyar.

Nabila ta kama baki daga inda take tsaye kamar an kafe ta “Lallai kin zama Haj ta wajena, irin wannan ci ma naira mutunci Allah ya ƙara danƙon soyayya ya tsare ki daga sharrin maƙiya da mahassada.”

Na daki kafaɗarta “Wai ke ya batun neman aikinki?

Ta kada kai “Ana ta yi, bai samu ba ne har yanzu.

Na yi mata addu’ar Allah ya sa a dace.

Muka nufi mota har estate ɗin da mijinta yake muka kai ta na yi ta duban wurin na ce “Ai wannan ya ishe ki zama Nabila kyau ki tattaro ki dawo gabaɗaya.”

Ta ce mahaifiyarsa har yanzu ba ta yarda ba wai idan ya ɗauke matarsa za ta daɗe kafin ta dinga ganin shi.

Na ce “Allah ya kyauta.

Ban daɗe sosai ba na tafi, na samu mutanen gidan duk sun dawo.

Tun da ya tafi ban daɗewa nake barci yau ma da wuri na kwanta da na tashi da safe na tashi da karfin jiki har na ji mamaki.

Na fita na samu Vicky a kitchen na ce ba na ce da safe ta dinga hutawa ba?

Ta rausayar da kai ta ce  “Idan ban yi miki girkin ba me zan miki Madam? Daga gyaran ɗaki da wankin toilet sai girkin, gyaran dakin kwana biyu sai ki ce mini za ki yi.”

Na yi ɗan murmushi “Na ji sauƙi ne Vicky, dama saboda ban iya komai aka samo mini ke.”

Hawaye na ga ta fara sharewa na ce “Subhanallah lafiya?

Ta share ido  “Ina tsoron a sallame ni ne Madam, daga kin ce saboda ba ki iyawa aka ɗauko ni.”

Na ce “Kar ki damu, ba zan tauye miki hanyar abincinki ba. Yanzu ma dambu nake sha’awa kuma na san ba lallai kin  iya ba?

Ta sunkuyar da kai “Ban iya ba.”

Na ce “To ki je abin ki.

Barzazzar shinkafa da na yi ma Mama magana ta ba Nabila ta kawo mini na ɗauko na fara aikina Vicky na tsaye tana kallona muryar Amal ta ƙwala mata kira ta fita, ta window na hango fitar su su duka, har mota na ga Vicky ta bi Amal sai da ta shiga ta juyo, Amal mota daya da Mama Zulai Suhaima da Dina.

Na ɗora kamar an ce mini kalli saitin window ido huɗu muka yi da wasu tiƙa-tiƙan ƙadangaru sun buɗe baki bi-biyu na fara gani sai na ga sun yo kaina na daka tsalle na fasa salati da ya karaɗe kitchen ɗin na juya ƙafata da niyyar rugawa in bar kitchen ɗin gabana na wata irin dokawa na ji kamar an yi mini dabaibayi na harɗe sai na ji kamar an yi sama da ni na faɗi ƙasa rikica! Na ƙwallara ƙara idanuwana na rantse ina ganin ƙadangarun nan sun yo kaina muryar Vicky na ji ta riƙe ni tana kuka kafin na ji ta sake ni numfashi nake ta ja da nake jin yana ƙoƙarin barin jikina na dai ji muryar Easter da Khalil daga nan ban sake sanin a inda nake ba na farka na gan ni a wani kyakkyawan ɗaki a saman gado gadon ya tabbatar mini asibiti ne.

Komai da ya faru ya fara dawo mini hoton ƙadangarun nan ya fara mini yawo na fashe da kuka Bashir Lema da ban kula da shi ba ya iso da sauri ya rungume ni yana jijjiga ni yana faɗin ya isa Vicky ya ba umarnin ta kira Dr suka dawo tare  Dr ya yi mini tambayoyi kan yadda nake ji da abin da ke damu na yanzu na rufe idanuna hawaye na bin gefen fuskata na faɗi ƙadangarun da na gani da ganin da nake masu yanzu kalaman rarrashi ya yi ta karanta mini da kwantar da hankali ba komai .

Ya juya ga Bashir Lema da ke tambayar sa cikin fa ba wata matsala?

Ya ba shi tabbacin jini ne kaɗan ya zuba sun kuma samu nasarar tsayar da shi ya ce zai kara yi mini scanning don tabbatar da cikin na lafiya.

Ya yi mini ya bayar da magunguna ya sallame ni ina riƙe a jikinsa muka fito a harabar asibitin na fahimci dare ne Khalil na gani muka shiga motarsa Vicky na gaba muna baya har lokacin ban bar hawaye ba yana faɗa mini ba wasu ƙadangaru gobe za a duba gidan idan akwai ma za a fitar da su.

Yana riƙe da ni magungunan na hannun Khalil muka shiga gidan gabana na dokawa ina jin kamar zan ƙara ganin ƙadangarun, suna zaune a falon, shi suka yi ma oyoyo sai na gane daga tafiyar da ya dawo bai dawo gida ba asibiti ya zarce saboda saƙon da ya samu ina asibiti.

Mama Zulai kaɗai ta ce mini ya jiki, ban shige ba jiran sa na yi ya gama magana da su muka tafi ɗaki wanka na yi na yi salloli ya fita ya sa a ka shigo da abincin da Peter ya yi  har na sanya rigar barci na hau gado ya ce in sauko in ci, na sauka a hankali na isa wurin abincin na zauna ya zo ya zauna gabana ya buɗe flate din da ke rufe aka buga ƙofa, muka kai duban mu ga kofar a tare shi ya amsa ya tambayi waye cikin mamaki muryar Vicky ta bayyana ta ce ita ce.

Ya tafi ya buɗe tray ne a hannunta ta ce abinci ta kawo mini, da mamaki a muryarsa ya ce “Abinci kuma ba ga shi Peter ya kawo ba?

Ta ce “Ni na ce mata ina son indomie.”

Daga inda nake mamaki ya rufe ni na Vicky ban dai yi magana ba don na fahimci akwai abin da ta sani da ni ban sani ba.

Ya ba ta hanya ta shigo ta ƙara yi mini sannu ta ajiye ta fice.

Indomien  na ci na koma gado, Easter ya kira a waya ta zo ta kwashe kayan.

Ya shiga bathroom ina ta danna wayata har ya fito ya goge kansa ya shafa mai da turare ya sanya riga da wando na barci ya hau gadon ya sanya ni jikinsa, yadda nake ji yake tambaya ta na ce ban jin komai, barcin da ya zo mini na rufe ido bakina ɗauke da addu’o’i.

Da safe na tashi da sauƙi na kuma kara jin ƙarfin jikina ni na gyara ɗakina bayan mun karya da abin karin da Vicky ta kawo na yi wanka.

Bai fita ba zama ya yi a  gida sai yamma y fita da ni na shaƙata na ga gari ya ce zai sanya ni driving school na koyi tuƙi idan na iya ya saya mini mota kafaɗa na noƙe na ɓata fuska na ce ni shi nake so ya koya mini murmushinsa mai tsada ya yi ya ce shi kenan idan ya samu lokaci zai dinga koya mini.

Washegari ma ya ƙara fita da ni har ya fara nuna mini tuƙin kwanansa uku da dawowa da safe muna kwance wayarsa ta yi ƙara ya kai hannu ya ɗaga na buɗe ido jin yana tambayar me ya faru Zulai? Ya ɗan saurara sai ya kashe wayar, ya faɗa mini Haj ta zo ido na ware na fara ƙoƙarin barin jikinsa riga ya sanya ni ma na sa muka fita.

<< Ummu Radiyya 30Ummu Radiya 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.