Skip to content
Part 11 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Tun komawa ta gida na manta da batun, sai shirin tafiya suna Katsina nake, matar yayana ce ta haihu sosai yayan nawa yaso in je in zauna har sai tayi arba’in, karatuna da kuma koyarwar da nake ta hana ni tafiya. Na samu dai daga makaranta an bar ni in yi sati, ranar sunan muka tafi, can yan sunan suka baro ni, sai da nayi sati na dawo.Washegari Lahadi na koma makaranta, da aka tashi ina ta sauri in wuce gida,dan ko gidan Hafsa ban yi niyyar shiga ba, a gajiye nake kwarai, dan tun da na je gidan jegon ban zauna ba.Wani dalibi ke kirana “Malama na tsinkayi kiran, ya karaso inda nake “Malam ya ce ki zo””Wane malam? na tambaye shi da mamaki. Shiru ya yi wanda ya bani tabbacin bai san sunan malamin ba, “Yana ina? na kuma tambayar sa “Office din malam Mas’ud” ya faɗi yana nuna min da hannunsa.Na juya zuwa can da tunanin shi ke kirana da sallama na tura ƙofar, tsaye yake ya juya baya fitinannen ƙamshin turarensa da a kullum ya shiga zai fita ya bar mu da shakar daddaɗan ƙamshin nasa, ya fallasa min gane waye, gaba ɗaya ya waiwayo bakon malaminmu ne, sanye yake cikin fara kal din jallabiya idonsa sanye cikin farin glass, wanda tun soma ganina da shi ban taba ganin shi babu shi ba, sumar kanshi ya shafa idanuwansa na kaina, sauri nayi na soma gaishe shi, ya amsa a hankali, yana nuna min wurin zama da hannunsa, na ɗosana mazaunaina kan daya daga cikin kujerun Office din. Kafe ni ya yi da idanuwansa da suka yi matuƙar tasiri a jikina, dole na sare na sunkuyar da kaina. “Me ya hana ki zuwa makaranta tsawon sati guda?

Muryar sa ta ratsa dodon kunnena, mamaki ya kama ni jin tambayar ta sa ya aka yi yasan sati daya ban zo makaranta ba? shi da yake zuwa karshen mako kaɗai.Na dai daure na ce “Haihuwa aka yi mana a Katsina” “Shi ne sai a tafi har tsawon sati? Shiru nayi cike da mamakinsa.Na daɗe zaune ba tare da ya bani umarnin tashi ba, sai ni nayi ƙarfin halin tambayarsa izinin tafiya, shiru ya min sai da aka kara wasu mintunan ya sallame ni, na fito cike da takaicinsa.Da daddare muna shirin kwanciya Umma ta ke ce min malam Mas’ud ya yo ma wasu dattawa jagora sun zo neman iznin fara neman aurenki.” wani banbarakwai na ji ina bazawara wai sai an tambayi neman aurena, taɓe baki nayi, ganin na ki cewa komai yasa ta tambaya ta na ce “Matansa fa biyu me ya ja min faɗa wa mata har biyu? Kabli da ba’adi tayi ta kawo min, ni dai nayi mata shiru har barci ya kwashe ni. Ranar da malam ya ce Abokinsa zai zo ina koyarwa a aji yasa aka kirani, na fita na same shi ya ce “Ya kika zo makaranta ummulkhairi? Nayi zaton za ki zauna a gida dan yin kwalliyar taron baƙon naki.”

Murmushin da yake zaton zan yi ban yi ba, cewa nayi “Ina ganin har mun tashi malam”Ya ce “A’a yana hanya, ki je gida kawai zan sanya a riƙe miki ajin.” Na ce “To” gidan na wuce bayan ya bani wata leda me ɗauke da gororin ruwan faro da su maltina da Hollandia, ya ce in ba baƙon. Ina shiga gida Umma ta ce “Ya aka dawo tun lokacin tashin bai yi ba?Turo baki nayi “Wai yau bakon da Malam ya ce, zai zo” faɗa ta rufe ni da shi na kin faɗa mata ranar zuwan na shi da nayi.Da kanta ta ta je ta share dakin yayana da nake bi mawa da kanena me bi min, ta gyara ta saka turaren wuta, ni dai sai dubanta nake ta gama ta zo ta ce “Ba za ki yi wanka ki ɗan gyagygyara ba? na ce “Nayi wanka kafin in fita” ta ɓata rai “To na ce ki ƙara”Na ce “Wai ke Umma ko sanin mutum ba ki yi ba amma duk kin tashi hankalinki da zuwan sa.” Hararata tayi “Meye abin tashin hankalin duk wanda kika ga kafin ya zo neman aure ya fara da neman izini, kin san na kirki ne. Kuma malam Mas’ud ya yi yabon halayensa.”

Shiru nayi sanin halinta in ta tsaya kan tana son abu, mafi a’ala ka barta kawai.Girki ma na ga ta ɗora, hada kazarta ta sa aka yanka, gwoggo ta ce min Baƙona za ta yi wa miya.Kan ba yanda zan yi na sake sabon wanka nayi kwalliya, ina sa kaya na ji muryar malam Mas’ud suna gaisawa da su ummarmu, da sauri na zura hijab.Yaron yayata da ake riƙo cikin gidan mu ya shigo ya ce in zo ana kirana, gabana na ji yana faduwa.

Na isa ɗakin cikin sanyin jiki, kaina a kasa malam ne ya amsa sallamar da nayi, gaisuwar da nayi musu ma shi ɗin ne ya amsa, ya ƙara da “Alhamdulillahi yau ga Ummulkhairi ga Tahir ƙanƙara.” gabana na ji ya tsananta bugu dama tun shigowata na shaƙi ƙamshin turaren nake zargin kar dai a ce shi ne? Ina fata za ku fahimci juna?

Muryar malam ta dawo da ni nutsuwata, miƙewa ya yi suka yi musabaha ya fice. Shiru ne ya biyo baya kafin ya yi gyaran murya, “Da farko sunana Tahir Abdurrahman ƙanƙara, ana kirana Sodangi a gidan mu, ai kin san dalilin da ke sa ake sanya wa yaro suna Sodangi ko?

Kai na yi saurin daga mishi, ya cigaba “Abokaina na kirana kankara, ku kuma kuna kirana da bakon malami, ko ba haka kuke cewa ba? Shiru nayi ya cigaba “Ni haifaffen ƙaramar hukumar kankara ne ta nan jihar Katsina, amma a Kaduna na tashi, na dai dawo gida nayi auren farko, maaikaci ne ni, ina kuma taba kasuwanci, matana biyu. Tunda ya fara magana nake satar kallonsa dan mamaki da ya lullube ni, kwata kwatan shi ba zai wuce shekaru talatin da biyar zuwa da bakwai, amma ya ajiye mata har biyu yana hankoron tarkato ta uku. Ba shi irin tsawon nan duk kuwa da cewa shi ɗin ba gajere bane, irin masu ginannen jikin nan ne, dan haka ba shi da ƙiba kuma bai cikin ramammu, fatar jikinsa da alama baka ce, amma tsananin gogewa da hutun da ya bayyana a jikinsa ya mayar da shi chaculate color. Ba wani matsanancin kyau yake da shi ba, sai dai yana da matuƙar kwarjini da wasu irin fararen idanuwa masu ɗaukar hankalin mata ga kyakykyawar sumar kai da ta kara sa shi ya haɗu ya zama irin namijin da kowace mace za ta yi ma kanta sha’awar a ce shi ɗin nata ne.

Sai so nake in ji ya yi magana game da maluntarsa sai dai naji shiru bai yi ba. Ban san na shagala ina dubansa ba sai da na ji yana kiran sunana, kunya kuma ta lullube ni na sunkuyar da kaina, sai na amsa a hankali, magiya ya yi ta min in dube shi, da kyar na tada kai na kuma kallonsa, fararan idanuwansa da ke cikin glass ya kafe ni da su, maida kaina ƙasa nayi dan wani abu da naji yana yawo a cikina.

Mun jima har Ummata ta aiko da shiryayyen girkin da tayi mishi, zama sosai ya yi kan yar chanese carpet din da aka shinfida dan shi ya ci abincin, da na nemi in ba shi wuri hanani ya yi sai tsiya yake min wai daga jin wannan abincin girkin manya ne ba ni nayi ba.Ni dai zaune kawai nake mamakinsa ya kusa kashe ni, ko kadan bai nemi jin ta bakina ba, ina son sa koko? A’a sai kokarin da yake na kiran sunana, wanda muryarsa take matukar tasiri a jikina, kuma ya ce sai na dube shi.Idanuwan nasa ma ba sauki bane kallon su, ni kaɗai na san me nake ji da ya kammala ya ce in mishi iso zai shiga ya gaida su Umma.”

Na wuce yana biye da ni har ɗakinmu, na bar shi da ita suka gaisa, ya bata tarihinsa kamar yanda ya faɗa min, kuɗaɗe ya ajiye mata, wanda tayi ta fadin ya dauki kudinsa.Miƙewa kawai ya yi na kai shi ɗakin gwoggo, ita ma kuɗaɗen ya ajiye mata ya fito.Ganin na tsaya ya waiwayo ya yafito ni, sai da muka je zaure ya ce “Ba ki raka ni ba? ya rungume hannayensa a ƙirji, yana kallona “Ba ki ce in gaida iyalina ba? dan jim nayi ba tare da na ɗago ba na ce “Afuwan ka gaishe su”.Ya ce “Ki bani nombar mama” na kira mishi ya sa, nayi mamakin bai nemi tawa ba, sai ta Ummata. Taɓe baki nayi shi dai ya sani, na dai samu ya tafi.

Da daddare mun yi shirin kwanciya Ummata ta dube ni da murmushi a fuskarta, “Da alama mijin aure ya zo Ummuna”. Na ce “Kai Umma?Ta ce “Allah kuwa na yaba ƙwarai da shi, ai ni tunda ya biyo ta hannun malam na ji ya yi min. Za a je har kankarar a yi bincike, Alh ma me mutane a can. Riƙe haba nayi “Kai Ummata, daga ganin mutum, ni gaskiya ban ma ji zan iya auren sa ba”.”Saboda me? ta ce min cikin gatse, “Ni da ganin shi zai yi son mata duk ya bi ya kafe ni da ido”.Umma ta fara hasala, “Ya yi miki maganar banza ne?Na girgiza kai “To wallahi kika kuskura kika kore shi yanda kika saba yi wa masu zuwa, kowa da matsalar da za ki karanto mishi, ni da ke ne a gidan nan. Banda kina shashasha, mutuwar auren ki shekaru biyu kenan, har ƴan zannuwan da kika fito da su sun soma sanyi, kina raɓe komai sai an ba ki?

Ƴan’uwanki kowacce tana ɗakinta, ba za ki yi fatan kema ki tafi naki ɗakin ba” Tura baki nayi “Amma fa Umma matansa biyu”Tsaki ta ja “To sai me? ni uwarki mu nawa muka zauna banda mutuwa da ta maida mu mu biyu. Halin mutum ai jarinsa, da halinki za ki zauna.”

Ganin ko ta ina na ɓullo ma Umma ba nasara yasa nayi shiru cikin tunani.Gari na wayewa sai ga kiran sa, ya gaishe da Umma, ita kuma ta bada wayar aka kawo min.Haka ya yi tayi kullum safiya sai ya kira Umma har yasa da an kira wayarta sai ta ce a duba mata, in shi ne sai ta ce a kawo min,a rana sai ya kira sau biyar, dabarar tashi kuwa sosai ta ci, dan sai faɗa Ummana take min na samu me sona zan wulaƙanta. Ranar wata juma’a na kai wa ƙanwata Hauwa’u ziyara, ubanmu daya.Sai fira muke yaro ya yi sallama, ya ce “Ana sallama da ummulkhairi”duban juna muka yi da Hauwa’u kafin na dubi agogo, “Amma waye wannan da rana gatse gatse?Ta ce “Ki je ne Aunty sai ki gani.” Ban ƙi ba hijab na sa sai na fito, a raina ina ta saƙa Allah yasa in samu wanda nake so, kafin Umma ta sa ni auren me mata biyu. Kalle kalle nake dan samun nasarar gano me kirana, jikin wata bishiya na hango shi, shi ɗin ne dai Tahir Sodangi cikin shigarsa ta jallabiya, da farin glass ɗinsa manne a idonsa.

Karasawa nayi inda yake cikin mutuwar jiki, sallama nayi masa kafin na gaishe shi, ya ce “Daga kankara nake, na ga ba zan iya komawa kaduna ban gan ki ba.” Yake nayi Na ce “Za mu ƙarasa gida ne? Kai ya girgiza “No daga nan zan gan ki in wuce, da me mashin suka haɗo ni, ya kawo ni nan.” Na ce Uhmm ya ce “Na gan ki zan wuce, me zan samu?Nayi turus kafin na yi ƙarfin halin cewa “Me to kake so? Murmushinsa me tsada ya yi “Da wasa nake, ba yanzu ba”Ledar da ke hannunsa ya miƙo min, na ɗora hannuwana saman hancina.”

Haba dai ya za ka ɗora wa kanka ɗawainiya? Idanuwansa ya watso min, ba shiri na miƙa hannu na karɓa, sallama muka yi nayi mishi fatan sauka lafiya. Da shiga ta Hauwa’u ta karbi ledar tana fadin, “Aunty tayo samu”.Sai ta buɗe, set ne na mai da sabulu da turare masu tsada.Hauwa’u sai yaba kyautar da aka yi min take cikin murna da zumudi, musamman da ta fidda dalleliyar waya samfurin Samsung S10, ni kam tunani na faɗa cikin nazari anya kuwa mutumin nan me mata har biyu, ina ya samu wa’annan uban kuɗaɗen da ya yi min wannan sayayyar dan ya burge ni? ni fa ba irin wadannan matan ba ne, duk da jikinsa na nuna akwai hutawa da kwanciyar hankali a tare da shi.

Muryar Hauwa’u ta dawo da ni daga tunanin, “Kai Aunty wannan babba ne, irin wannan babbar waya haka? ta kunna ta sai ta kawo “An riga an yi charging ta hada layi Aunty” ban samu abun ce mata ba sako ya shigo miƙo min tayi, “Ga waya a kira kowa, amma banda rival ɗina. Abinda sakon ya ƙunsa kenan, Hauwa’u ta matso “Duba account balance ɗin, na san ba zai rasa zuba miki kuɗaɗe ba”Maimakon dubawar wayar na miƙa mata, da murnarta ta ce “Wallahi five thousand Aunty”Na fidda ido ita kuma ta kama dariya “Kawai daddaɗan text message za ki tura mishi yanda za ki ƙara sace zuciyarsa”harararta nayi “Ba ki da hankali Hauwa’u, matansa biyu fa mutumin, ta hannun malam Mas’ud ya biyo malamin mu ne, duk da cewar da aka yi yana aiki kuma yana kasuwanci, ina tsoron ya tarkato rigima ya riƙa kawo min dan ya samu shiga wajena, in zo in aure shi yan bashi su taso mana mu shiga uku.” Duk da jikinta ya yi sanyi sai cewa tayi “In sha Allahu ma ba haka ba ne Aunty, mutumin kirki za ki aura wannan karon wanda zai riƙe ki har mutuwa.”Na ce “Allahu ya sha”Ledar kayan na tura mata gabanta “Haɗa su ki adana, har wayar ba amfani zan yi da ita ba”.Marairaicewa tayi “Saboda me Aunty?nan dai tayi ta min magiya har ta samu na yarda zan riƙe wayar,Su turare da mayukan da sabulun nan na barta da su, duk yadda ta kwaɗaita min kyan su za su gyara min skin, na ce ta ajiye min.Yamma sosai na bar gidanta na nufi gida. Bayan magrib mazan gidan mu duk sun shigo ana cin tuwo, kanena Nura ya ce “Wallahi Ummu tayi babban kamu, kun ga ƙatuwar wayar da me son ta ya kawo mata? wal…….”Dalla ko ba wani ustaz da ta yayibo ba.” Yaya Mustapha ne ya katse shi, sai kuma ya juyo kaina “Wawuya ke kuma da ba ki san kanki ba, haka auren farko kika yayibo wanda ya kasa riƙe ki, yanzu ma daga wannan garan ya zo sai wancan saunan. Yanzu kuma kin kwaso ustaz zai yaudare ki da ƙatuwar waya.

Tsawar da Umma ta daka mishi ta sa shi yin shiru, dan daga cikin mu ba wanda ya ga zuwanta. Ni dama tuni na fara hawaye, faɗa ta shiga yi mishi kan idan ba zai mini fatan alheri ba kar ta kuma jin bakinsa.Kwanon tuwon da nake ci na ɗauke sai na kai kitchen, ɗaki na wuce na kwanta sai share hawaye nake, wayar ta shiga ƙara ,na miƙa hannu sai na dauko ta, ina ɗagawa muryarsa ta daki dodon kunnena.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 10Wa Gari Ya Waya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×