Ba dai har kin soma barci ba?
ban ba shi amsa ba illa gaishe shi da na shiga yi,
“Ki kunna datarki muyi fira” na amsa da to sai ya kashe wayar.
Daurewa kawai na riƙa yi wurin ba shi amsar maganganun da yake min, dan har dalilin mutuwar aurena ya tambaye ni, ni ma nayi ƙarfin halin yi mishi complain kan kyautar da ya yi min tayi yawa, shi me iyali da yawa kar ya shiga hakkinsu.
Amsar da ya bani ita ce “Kin sa ni dariya sosai Ummuna, a takaice dai kina min nasiha da kar in ciyo bashin jama’a in riƙa kawo miki, dan son samun haɗin kanki, ganin ƙarfina bai kai na yin kyautar ba.”
Mamaki ne ya rufe ni ya aka yi ya gane nufina? duk da fahimtar da nayi shi ɗin mutum ne me wayau.
Yan kame kame na shiga yi mishi na ni ba haka nake nufi ba, ya ce “To ya ji ya gode da nasiha, yana kuma cike da alfaharin samun mace mai hankali, tare da jimamawa tsohon mijina asarar da ya tafka.
Mun fi awa kafin na samu ya bar ni, ina ta mitar yanzu haka matarsa wadda ke da girki na nan zaune gefensa, ya shanyata yana shan firarsa da wata.
Na kwanta sai dai barci ya gaza ɗaukata, firar da muka yi take ta mini yawo a kai,
Anan nake tuna rayuwata ta baya.
Alh sule me kwano shi ne mahaifina, haifaffen ƙaramar hukumar Dutsinma ne ta jihar Katsina, matansa na aure uku ne kafin Allah ya yi wa matarsa ta uku gwoggo Jamila rasuwa.
Mahaifiyata Bilkisu ita ce uwargida, yaranta shida biyar maza sai ni mace tilo a cikin su,
ni ce ta biyar sai kanena Nura shi ne auta.
Kasancewa ta ya mace guda da Ummarmu ta mallaka yasa na tashi kamar tsoka ɗaya a miya wurin Ummana.
Sai mai bi mata gwoggo Rabi yaranta bakwai, su kuma duka mata ne, tayi maza uku duk sun rasu, gwoggo Jamila yaranta huɗu duka maza, ta rasa ranta a wurin haihuwar ɗanta na hudun, Ummarmu ke rikon yaran da ta bari.
Sana’ar mahaifina sai da kwano na rufin sama, yana da rufin asiri.
An sa ni makarantar boko da islamiya kamar yanda aka sa ƴan’uwana, gidan mu suna kallon juna da na su Hafsa wadda aka ce kwana talatin ta bani a haihuwa, ajin mu daya a boko da islamiya, barci kawai ke raba mu.
Muna kuma kare karatun sakandare aka yi mana aure, Hafsa ta auri malam Mas’ud ni kuma na auri telan mu da ke mana ɗinki Abubakar, matashi ne shi kuma kaɗai mahaifansa suka haifa, mahaifinsa ya rasu, da yawan ƴan’uwana ba su so aurena da shi ba, su na cewa ɗan mace ne, ni kuma na tsaya kai da fata sai shi.
An yi auren mu an miƙa ni gidansa, tare muke da mahaifiyarsa, sai dai an kebe mini wurina, muna ta zuba amarci, daɗin amarci ya debi Abakar sam baya fita yini da kwana muna tare yana ɗaka kwance, ko abinci mahaifiyarsa ke yi ta miƙo mana, da daɗin duniya ya ishe shi sai ya kwashe rabin abincin garar ya sayar ya saka kuɗaɗen aljihu muka yi ta cin daɗin mu.
Idan mutanen da suka ba shi ɗinki suka zo, sai mahaifiyarsa ta ce “Ba ya nan.”
A kwana a tashi gara ta ƙare, kayan kitchen ɗina da ba a bude ba ya yi ta zara yana sayarwa muna cin abinci har suka ƙare, dole ya koma dinkinsa, wanda ba kasafai ya cika samu ba daga ya gama kore costomers ɗinsa.
Gidan mu nake tafiya in gaya wa Ummata matsalata, haka za ta yo min hade haden kayan abinci da ƴan kuɗi in koma, ƴan’uwana duk wanda ya bata abu ni za ta adana mawa idan na zo ta ba ni.
A haka na samu shekara lokacin kuma ciki ya bullo jikina me azabar laulayi, Abakar kuma ya tasa ni da bala’i idan ya kai ƙarata wurin mahaifiyarsa kiri kiri ta ke bani rashin gaskiya ta rika rarrashin ɗanta.
In ya sa kai ya fita tun safe sai dare zai shigo, bai fi ya ajiye min dari ba ko dari da hamsin, mahaifiyarsa ban ma ga fuska ba ballantana in saka rai za ta sam mini dan wani abu da zan saka a baki.
A haka wata rana yayyena Wasila da Habiba suka kawo min ziyara, sun same ni ba yadda nake, waya suka yi gida aka zo aka ɗauke ni sai asibiti, ɓari nayi wanda na sha matukar wahala, sai da aka yi min ƙarin jini.
Ƴan’uwana sun ɗauki zafi da al’amarin, suka ce ba zan koma ba, mahaifina dattijo yasa aka shirya ni.
Bayan na murmure aka mayar wa Abakar.
Watana biyu kacal da komawa na kwanta wani ciwon, nan ma ƴan’uwana suka kai ni asibiti, likita ya yi ta fadan ulser da ta kama ni saboda rashin kula.
Ƴan’uwana sun sha alwashin wannan karon ba zan koma ba, dan haka da abokan Babanmu suka yi ta kamun ƙafa, su roke shi ya yi hakuri a raba auren,
Dan aure ba zai yuwu babu abinci ba.
Da aka nemi Abakar ya bani takarda tsayawa ya yi kai da fata shi fa yana son matarsa.
An sha fama da shi kafin babban yayana na ɗakinmu Yaya Sani da duk ya fi ɗaukar zafi da halin da nake ciki ya ce “To zai yanko mishi sammaci, daga baya so a rabu lafiya, mahaifiyarsa ta lallaɓa shi wai ya yi saki ɗaya idan an kwana biyu suka huce sai ya dawo da matarsa.
Da haka na samu muka rabu, Yayana Sani da ke zaune a Katsina ya tasa ni ya tafi da ni gidansa, farkon abin da na fara yi da na koma can faɗawa wata islamiyya na jona karatuna na addini, dan dama nayi mutawassiɗ, sai na fara sanawiyya.
Matsala ta farko da na fara fuskanta a gidan dan’uwan nawa me matuƙar so na, ita ce kishina da matarsa ke yi Aunty Rahma,
dan duk ƴan’uwana suna taya Ummarmu so na.
Da ya shigo ni ce mutum ta farko da zai fara nema, yana cin abinci ina gabansa sai na kula sun fara samun matsala a zamansu, har ta kai ga yin yaji ta bar mana ƴaƴanta, ni kuma ina samu aka yo bikonta, sai na tattara kayana sai gidan ubana.
Ko da ya zo yana faɗan me yasa na taho? Rahma bata isa hana ni zaman gidansa ba, sai dai ita ta bar min gidan, ban yarda na bi shi ba, karshe Ummanmu ta ce ya tafi kawai ya bar ni.
Haka ya tafi ba dan yaso ba, mafarin dawowata gidan mu kenan.
Ranar Asabar da na je makaranta malaminmu na ainihi me mana matanir risala shi ne ya shigo.
Ai kam yana fita ajin ya dauki hayaniya ana tambayar juna ina sabon malami?
dan ba karamin cinye ƴanmatan ajin mu yake bakowacce na fatan ya taya.
Wasa wasa sai ga shi Tahir ya dage zuwa wajena a duk Lahadin duniya, makaranta kuwa tun daga ranar da ya kira ni a office din malam Mas’ud bai ƙara zuwa ba.
Ya samu babanmu ya ce yana so ya turo magabatansa, Dattijai sun zo sun nema mishi ni kuma bayan tafiyar su ya zaunar da ni ya ce sai in yi shawarar lokacin da nake gani zan kammala shirina, sai ya sa musu rana, dan ya ce su kawo sadaki, kuma yasa an mishi binciken gidan su a ƙanƙara, gidan su babban gida ne shi ma an yabi halayensa.
Ya sallame ni na tashi na tafi, da zamana a ɗaki sai na samu kaina ina hawaye, Ummata da ke ninkin kaya ta harare ni “Shashasha wadda bata san inda ke mata ciwo ba”.
gwoggo ta shigo suka haɗu suka yi ta mini faɗa.
Nan na ji Gwoggon tana tambayar Umma yau matar da aka sa tayo binciken gidan su Tahir a ƙanƙara za ta zo?
Umma ta ce tana nan zuwa amma bata faɗa mata ranar ba.
Ranar da matar ta zo tare suka zo da wata da ta ce cikin matan yayyen Tahir akwai ƴar’uwarta amma ita matar nan Dutsinma take aure, ita tayi ta basu labarin gidan su Tahir, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro sai mahaifiyarsa, ta dube ni inda nake tsaye ina shirin makaranta,
“Ƴar nan shiga gidan Tahir sai kin yi shiri, matan nan nasa gogaggu ne, haka za ki ga sun zo suna yauƙi duk da uwargidansa yar ƙanƙara ce, makota suke gidan su da na su Tahir ɗin.
An ce duk aikin gwamnati suke.
Matar da suka zo tare ta ce “Ai maganin sammu kawai za a samo ki yi ta sha kina wanka.”
Ban ce uffan ba sai barin dakin da nayi, dakin Gwoggo na shiga na kwance nikab din da na ɗaura, kwanciya kawai nayi bisa gadonta maganganun matar suna min yawo a kai, duk na shiga rudu in a da ina fargaban auren Tahir saboda shi kansa, to yanzu ga labarin matansa da na samu na san suna nan kamar ka taba su jini ya fito dan gogewar fata, na dubi hannuwana da duk sauron ɗakin Ummata ya gama cijewa, shawarar wa zan nema dan samun mayukan da za su gyara min fata?
Ban kai ga samun mafita ba na tuna an ce matan nasa ma’aikata ne, ni kuma ko turancin ban gama gwanancewa ba, wa zan samu ya koya min turanci? Abin ya mini yawa.
Miƙewa nayi na shiga makotanmu gidan su Hafsa wurin matar yayanta Aunty Zahra ƴar gayu ce, ita na tambaya mayukan da zan saya da za su gyara min skin, za na min sunayen su ta shiga yi da kuɗaɗen su, sunan ɗaya na ɗauka na ce zan saya, na ɗan jima kafin na tashi na koma gida, inda na samu magabatan Tahir sun zo sun kawo sadaki dubu Tamanin babanmu kuma ya sanya rana kwana arba’in.
Ummanmu ta kira duka yayyena a waya za su yi shawara kan yadda za a yi min kayan ɗaki, dan wadancan kayan nawa saida su aka yi bayan fitowata, aka ba yaya Sani kudin.
Yamma sosai yaya Sani ya iso, da daddare ya kira ni yana dakin Gwoggo yana cin tuwo, dan nesa da shi na zauna na ce “Ga ni yaya Sani”
loma ya kai baki “Malama Ummu ashe aure ya zo?
Dan murmushi nayi ban yi magana ba,
“Ai na ga mijin, wancan satin ya je har Katsina ya gaishe ni.”
Gane ba zan yi magana ba yasa ya cigaba “In kina da zaɓin kayan da kike so sai ki gaya wa Gwoggo ko Umma”
Na ce “To” ya gama ja na da wasa ya sallame ni.
Da safe duka suka haɗu a ɗakinmu Yaya Sani, yaya Isuhu, sai yaya Jamilu, sai Mustapha wanda nake bi mawa, Umma na zaune ni kuma ina gyara kayana.
Yaya Sani ya ce “Kowa ya faɗi abinda zai bayar gwargwadon samun sa.”
Kowa ya faɗi, yaya Sani ya ce ” Zan haɗa da kuɗaɗen ta na kayan ɗakinta, da gudunmuwar ku da tawa, in saya mata komai na kayan ɗaki.”
Umma ta miƙo sadakin
“Ga sadakinta nan tun jiya Alh ya bayar da su, ya ce a bata.”
To bata Umma sai tayi yan nata saye sayen na kayan kitchen.”
Miƙo min tayi na karɓa na saka a jakata sai na fito dakin, wanka nayi sa’adda na koma duk sun tashi sai yaya Sani ke musu bankwana zai koma.
Uwardaka na shige na shirya na fito yana miƙewa “Sai ina Ummun Ummanta?
dan murmushi nayi “Gidan Yaya Wasila za ni in dubo ɗanta da aka yi wa shayi”.
To mu je in sauke ki”
Ya faɗi yana yin gaba.
Washegari Lahadi Tahir bai zo ba Gwoggo sai magana take ko lafiya yaron nan yau bai zo ba? bai kuwa taɓa fashi ba tun da ya soma zuwa”.
Ni dai ina jinta nayi mata shiru.
Ƙarfe takwas na dare ina kwance aka aiko kirana cike da mamaki nake duban yaron “Ko dai ba ni aka ce ba?
Dan akwai yammata biyu kannena a dakin Gwoggo, su ma an sanya ranar bikin su bayan an yi nawa za a yi nasu.
Gwoggo ta ce in dai leƙa in gani, daga yaron na makota ne ya san ni sarai, dogon hijabina na saka dan an soma sanyi sai na zura silifas, a zaurenmu na ga mutane biyu zaune ta hasken wayar da ke hannun ɗaya daga cikin su na gane mace ne da namiji, dan zauren akwai duhu bamu da wutar lantarki, gaba ɗaya aka haske ni da torch din wayar, wata faɗuwar gaba na ji.
Tahir ne da wata tsaleliyar mace kyakykyawa ajin farko, cikin matukar kwalliya take, karfin hali nayi na yi masu sallama kan wani benci da Kodayaushe za ka same shi a zauren suke zaune,
Ita ta amsa sallamar jin muryarta kadai ya kara kidimani dan muryar tata me matukar dadi ce,
Gefensa ya nuna min “Zauna man”
na zauna amma daga nesa da shi sabanin ita da har jikinsu na gogar na juna, shi na fara gaidawa kafin ita
ya ce “Wannan ita ce Basma matata ta biyu, Basma ga Amaryata ummulkhairi”
“Nayi murnar haduwa da ke amaryarmu”
ta fadi tana mishi wani duba da kashe ido,
wani mugun yawu na hadiya gaba daya duk na muzanta.
Ya ce “Ta kawo min ziyara daga abuja shiyasa ba ki gan ni da wuri ba, kamar in fasa zuwa sai wani week din to ina son ganinki kawai sai muka taho tare.”
ni dai “Uhm kawai na ce, ya ce “Ku shiga ciki ta gaishe da su Mama, ku kuma kara gaisawa haka nan na mike na wuce gaba kamar kazar da ƙwai ya fashe mawa, ɗakin Gwoggo na fara kai ta sannan namu, babanmu ya kwanta.
Mun fito muka sake zama goma ta gota ya ce min za su tafi masauki da safe za su wuce.
Sai da ya ga ta fita ya dawo gabana ya tsaya, a kuma daidai lokacin nefa suka maido wuta fitinannen kallon sa yake jifana da shi,
“Kike wani kakkama jiki ko duk sanyin ne?
Kai na girgiza. Wani kallon ya kuma watso min
“Ba ki da matsala bana ai yarinya,
ba ruwanki da jin sanyi kina da bargo.”
Ƙara sunkuyar da kaina nayi,
“Wai yau saura kwana nawa ne?
Saurin ɗago kai nayi muka haɗa ido sai nayi saurin mai da kan,
“Me tambayar ai ya fi wanda ya tambaya sani”.
Murmushi me sauti ya saki “Kuma fa haka ne, Allah dai ya nuna min ranar.
tare muka fito na ƙara yi musu sallama, ina kallo suka miƙe titin gidan mu.
Dana kwanta kasa barci nayi, ina tunanin al’amarin da ke daɗa kusanto ni, to yau fa na ga zahiri irin matan Tahir
ɗin, wani tunani da nayi yasa nayi saurin janyo wata jaka tawa da nake ajiye ajiyena, ledojin kayan kwalliyar da Tahir yake siyo min na shiga fiddawa, ban taba gwada amfani da su ba.
Da safe na shiga wajen Zahra na nuna mata, tayi ta mamakin dama ina da mayuka da sabulai masu matuƙar kyau da tsada amma nake neman saye?
Dibar mata nayi na fito zuwa dakin Innarmu maman Hafsa kenan kamar yanda muke ce mata, yayanta Umar na zaune, sai tsiya yake min ban tanka shi ba. Gadonta na haye ina gaishe ta, kallon Umar tayi “Ba ka gama ba ne?
ya zaro ido “A Innarmu ya da kora kuma?
ta ce “E idan ka kammala yi tafiyar ka” ya ce “Da fira za muyi da yar ƙanwata amarya”
ta girgiza kai “Ka same ta can ku yi” ya mike ya fita yana mitar Innarmu ta kore shi.
Sai da ta gyara labulai sannan ta dauko wata leda, su zumar mata, hakin daka gumba su tabaje da tsimi ta fiffiddo
ta haɗa ta dama sai ta miƙo min, “Maza shanye ummulkhairi” dafe cikina nayi duka wannan Innarmu?
Ɓata fuska tayi “Kin ga duk abin da ke cikin ledar nan sai kin shanye su, shashanci kenan za ki shiga cikin kishiyoyi ba za ki gyara kanki ba?
Musamman na sa yar Sokoto tayi min hadin su masu matuƙar kyau ne”
Na karba ina sha ina ɓata rai. “Kullum ki zo ki rika sha ummulkhairi” kai na daga mata nasiha take ta min ina saurarenta na daɗe sosai kafin na fito na koma gida, Yayyena na samu yan dakin Gwoggo su dukan su sun zo wuni, wurin su na shiga muka yi ta shan fira, kafin babbar yayar mu a dakin nasu Aunty Habiba ta ciro kuɗaɗe sai ta miƙo mini, “Dubu 25 ne ummulkhairi mu dukan mu kowacce dubu biyar, sai kuma wasu kudin da muka haɗa za mu yi miki kazar amare da cicciɓi, wata leda ta miƙo min me ɗauke da garin magani. “Maganin sanyi ne, jikawa za ki rika yi kisa yar tsamiya kina sha sau uku a rana.”
Na karba tare da godiya sosai a gare su kafin na miƙe zuwa ɗakinmu.
Very interested