Ajiyar zuciya na fidda na faɗi na ga ta kaina yau, hannuna da ya sha ƙunshin amare na ɗora bisa goshina, sai hannunsa na ji ya dora saman nawa yana murzawa, gabana ya tsananta bugawa, "Wai duk ina ƴan gidan mu? A rasa me jinyata sai shi."
Cikin kunkuni nayi maganar, ban ƙaddara ya ji ba. Sai da na ji yana bani amsa, "Saboda ni na fi kowa iko da ke a yanzu shiyasa." Shiru nayi can na ce" Zan yi sallah" ya ce "Bismillah" sauka nayi a hankali na shiga bathroom din cikin dakin, alwala nayi na zo. . .
Allah yasaka da Alkhairi