Skip to content
Part 14 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ajiyar zuciya na fidda na faɗi na ga ta kaina yau, hannuna da ya sha ƙunshin amare na ɗora bisa goshina, sai hannunsa na ji ya dora saman nawa yana murzawa, gabana ya tsananta bugawa, “Wai duk ina ƴan gidan mu? A rasa me jinyata sai shi.”

Cikin kunkuni nayi maganar, ban ƙaddara ya ji ba. Sai da na ji yana bani amsa, “Saboda ni na fi kowa iko da ke a yanzu shiyasa.” Shiru nayi can na ce” Zan yi sallah” ya ce “Bismillah” sauka nayi a hankali na shiga bathroom din cikin dakin, alwala nayi na zo na rama sallolin da ban yi ba.

Nayi zaune kan sallayar na ki tashi tun yana min magana har sai da ya ce zai zo ya ɗauke ni idan ban tashi na zo na kwanta ba.Tashin nayi ina hayewa gadon na rufe idona da karfi a fatan da nake barci ya ɗauke ni, na kuwa samu nasarar hakan.Ban farka ba sai ana sallar asuba, ban gan shi ba cikin dakin, miƙewa nayi nayo alwala na kabbara Sallah, ina azkar ya shigo na gaishe shi ya tambaye ni jiki, na ce “Na ji sauƙi.”

Ya tambaye ni zan yi wanka? Na ce “A’a sai na je gida.” Tea ya kuma haɗa min na sha. Sai tara likitan ya zo ya sallame ni, kannena yan mata da suka kawo abin karyawa su suka dauki yan kayayyakin mu da ke dakin, ina tafiya a hankali yana biye da ni a baya, a raina ina cewa ko mashin zamu hau ko adaidaita sahu oho!

Mun iso harabar asibitin sai ya yi gaba na koma bin sa a baya, wata dalleliyar mota samfurin Corolla Camry baka da ke ta sheƙin ɗauke ido cikin hasken ranar da ya soma bullowa ya buɗe tun kan ya gama karasawa inda take, umarni ya ban in shiga gaba na shiga na zauna cikin tunanin ko motar wa ya aro tare da yi ma kaina addu’a Allah yasa ba dan karya na aura ba.

Ya zauna mazaunin direba kannena suka shiga baya. Ko da muka isa gidan mu tare da shi muka shiga ina gaba yana biye da ni har dakin Ummata, kwanciya kawai nayi suka leƙo ita da Gwoggo ya gaishe su, suka yi mishi godiyar ɗawainiya. Suna fita ya dawo kujerar da ke kusa da wadda nake kwance, “Daga kin warware ki tashi mu wuce ƙanƙara, gobe mu dawo.

Idan na dawo da ke sai in wuce Kaduna.” Hannuna na sa na dafe goshina. “Ina rokon ka dan Allah ka rufa min asiri, me kake tunani zuriar ku za su tuna a kaina idan suka gan ni na bi ka ba tare da na tare ba?”

Ya rage nasu kome za su tuna, tun da ba sabon Allah aka yi ba, kwanciyar ki nan fa ganin dama ta ne idan ban so ba zan ce ki tashi mu wuce Kaduna. Dan haka sai ki zaba.” Miƙewa ya yi sai ya bar ɗakin, Na bi shi da kallo cikin saƙe saƙe. Ba a jima ba aka soma shigo da akwatuna set ne guda shida, yaron yayata ya duƙo saitin kunnena “Ga kayan lefenki nan, ya ce ki zabi wadanda za ki yi tafiyar da su, yana waje yana jiran ki.” Kuka na fasa wanda ya yi sanadin shigowar su Ummata suna tambayar dalili, ina kukan nake faɗa musu, Yayana Jamilu da suka shigo tare mummunan tsaki ya ja ya ce,

“Wallahi duk Umma ta sangarta yarinyar nan.” Su kuwa tafa hannu suke ita da Gwoggo kafin suka rufe ni da faɗa, kan dole na share hawaye. Ruwa me zafi na samu nayi wanka ina fitowa samu nayi sun yi ma kayan akwatin ɗaiɗai sai ma sha Allah Gwoggo ke fadi, ni kuma da ke kwalliya ina satar kallon kayan tsoro ne fal ya cika min ciki, anya ba wani boyayyen al’amari game da Tahir Sodangi?

Da ganin waɗannan kaya ta’adi me yawa aka yi wa Naira kafin a mallake su, kaya ne masu matuƙar kyau da tsada, wani akwati da suka buɗe abayoyi ne na isassun mata wadanda na fi ganin ana tallar su a social media. In ta burin mallakar ko da ɗaya ce, duk da yake yaya Sani ya taɓa saya min sau ɗaya.

Gwoggo sai mita take, “Kin samu yaro mai kaunar ki ummulkhairi, iyayensa masu mutunci, sai godiya suke na basu ke da aka yi, zai kai ki cikin su su san ki ki san su, meye abin daga hankali? Ni dai ina jin ta, ga ƙannena A’isha da Aimana da ke ta kara zuga ta ta hanyar faɗa mata uban tsadar zannuwan da suke fitarwa.

Harara na galla musu yayin da na miƙe dan saka kaya, less din da nayi kwalliya ranar daurin aure shi na mayar, ina fesa turare Gwoggo ta ce “Ki zo ki zabi kayan da za ki yi tafiyar da su”.Baki na tura “Kwana fa ɗaya ya ce Gwoggo ni kala guda zan ɗauka”ta ce “An ji zo ki ɗauki dayan” sai ta fice su Aimana suka bi bayanta da sauri dan sun san sauran aka bar su da ni, Abaya na dauka wata da na ga ta bani sha’awa. Cikin wata madaidaiciyar jaka na saka duk wani abin da na san zan yi amfani da shi, na zura takalmi sai na fito tsakar gida Umma nake tambaya inda ta ajiye min hijab di na wanda na dinka mahadin less din, kafin ta fito daga kitchen din sai ganin Tahir nayi ya fito daga dakin su Nura da yaya Mustapha yana share baki da hanki, da sauri na juya zan koma daki muryarsa na ji yana cewa “Zo ki kwashe kwanonin nan.”

Nan na gane girki Ummata ta yi mishi, kan ba yadda zan yi na dawo yana tsaye inda yake yana aikin kallona, magulmatan ƙannena Aimana da A’isha suna kallon mu suna murmushi ƙasa ƙasa, dan mu kadai ne a tsakar gidan.

Na kwaso na kai kitchen sai na koma daki sai ga shi ya shigo, sallama ta ban girma tare da kyautar da suke ta faɗin tayi yawa ya yi musu, jakar da na zuba kayana ya dauka sai ya bar dakin, Ummata ta sa aka fitar da cincin da dubulan da alkaki da aka yi min, ta ce “In kai wa Mahaifiyar Tahir idan na tashi tarewa sai ayi min wani.

Ni dai kunya ke ɗawainiya da ni, su Aimana suka raka ni har gaban motar, na ji yana jaddada musu zuwa azahar motar kai kaya za ta iso duk me zuwa sai ya shirya, suna amsa mishi da “To”Yana yi ma motar key ribas ya yi sai muka bar layin.Yana tuƙin yana duba na har dai ya ƙare ya ce “Wai jikin ne ko kuma gidan na mu ne ba ki san zuwa? Sauke tagumin da na rafka nayi “Kin duba kayan sun yi? Ya kuma tambayata “Sun yi Allah ya kara budi na alheri.”

Na fada a hankali “Ban sa bra ba sai mun je Kaduna sai ki zabi size ɗinki.” Idonsa na kan titi ya yi maganar, ni kuma na ji kamar in nutse, amma haka nan nayi dauriyar cewa “Ba na sa wa.”

Ta fakaice ya dube ni “Saboda me?” Ciwon kirji take sa ni.” na ba shi amsa Duk waɗannan abubuwan da nake gani ta hijabi suna tsokale min ido, ba a tare su da komai? To an kusa zuwa wajen.”

Na faɗi a zuciyata ina kuma jin kamar kasa ta buɗe in shiga, duƙewa nayi na sanya kaina tsakiyar cinyoyina, duk maganganun da yake min ba su sa na ɗago ba, har sai da ya ce “Ai sai ki tashi mun iso”.Sai kallon inda muka zo ɗin nake, daidai wani gida ginin bulo da bulo muka tsaya kafin ka ce me yara sun cika wurin suna ta mishi barka da isowa “Mu je ko” ya ce da ni ban yi alamar fitowa ba na juyar da kaina daga kallo na da yake na ce,

“Saboda Allah haka zan zo musu hannu bi biyu?Ya ce “Idan za ki kuma zuwa kya yi musu tsarabar” daga haka ya fice na bi shi a baya. Gida ne na yawa me sasa daban daban, mata ne suke ta bullowa daga sasansu suna mishi murna tare da fadin ango ka sha ƙamshi, har da masu mishi guɗa rafar dari biyu ya lika wa wacce ta fi su baki.Wani babban falo muka shiga, kujeru ne masu tsada na zamani a ciki amma rashin goge su dattin su duk ya fito, akwai kayan kallo amma su ma duk sun yi kura, kasa carpet ne me tsada, amma da gani yau bai samu shara ba. Dattijuwa ce farar bafulatana kyakykyawa duk da shekarunta take mana lale lale, kasa na zauna ina gaishe ta, ta ce In tashi kar in bata kayana yau jikokinta da ke mata shara ba su yi mata ba.

Tana ta sa ma aurenmu albarka, ta tashi ta kawo min abinci sai ta fita Tahir da ke ta danna wayarsu na ce mawa “In zuba maka ne?kai ya girgiza wadannan matan me suka iya zan fita in nemi abinci”.Ba zan iya ci gaban sa ba, dan haka sai da ya fita sallar Azhar sai na zuba kadan, ina idar da sallah matan gidan suka yi ta shigowa muna gaisawa, sai da suka lafa na zare hijab dina na soma sharar falon da na gama na kwashe wata yarinya da ke ta leƙena ta madubi na yafito, ruwa na ce ta kawo min da tsumma da omo sai da nayi mopping din falon sai na goge kayan kallon da tsumma me kyau da na sa ta ta kawo min, na goge kujerun na kunna fanka, suka fito fes ina goge ta karshen suka shigo shi da mahaifiyar tasa, hannu ta shiga tafawa.”

Daga zuwa yar nan kin ta da kanki tsaye? Shi kuma sai kallona yake ta cikin glass din idonsa, fuskarsa kuma a haɗe ya ce kuma haj daga asibiti aka sallamo ta.”

Ido ta fidda “Asibiti kuma? Ya ce “Wallahi jiya jiri ya kwashe ta tana da ulser sai ta zauna da yunwa, ina isa na samu za a kai ta Hospital.” Ta ce “Allah sarki sannu kin ji wuce ciki ki kwanta” Na wuce na bari yana cewa a kira mishi yaran gidan ya ji dalilin kin gyara wa mahaifiyar tasa wuri. Cikin ma yana bukatar gyara dan haka gyaran na shiga yi, motsina ya shigo da ita ta koma tana faɗa mishi shigowa ya yi ya ce “Ba kya ji ko? Na ce “To wai idan bamu yi mata ba wa zai mata?”

Ya ce “Haka ne”Sai ya fita ganin ya fita na ce mata ba wasu labulayen ta ce Akwai ta nuna min inda suke na ciro na cire na jiki na canza da wa’annan, carpet ne ba zan iya cirewa ba jikokinta majiya karfi ta kira bayan ta fita suka cire sharar wurin ce ta hanani suka share aka malala wata. Kudade na bayar na ce a wanke labulayen da carpet har turaren wuta na kunna cikin irin wadanda Hafsa ta hado ni da su nan da nan wurin ya yi ras, sai shi min albarka take. Sai magrib ya shigo ina cin tuwo ya ce,

“Tun da kin gyara dakin tsohuwa saura na mijinki, zo mu je ki gyara min tawa shimfidar.”

Shiru na mishi ko da ya maimaita ban motsa ba, a kunnena ya rada min bayan ya rankwafo “Wa ya ce miki amarya na cin tuwo? Sai ga Haj ta shigo ya yi saurin matsawa.

“Ki sa baki Haj mu je sashina ni ma ta yi min sharar.” ta ce “Maza kammala ummulkhairi.” Na miƙe dan dama na gama na wanko hannuna da bakina sai na shige su gadonta na haye nayi kwanciyata, jin shiru sai ta leƙo “Mijinki na jiranki ta shi ki je kin ji?Ta fada cikin sigar lallashi kunya na ji ta dabaibaye ni “Ni mama ke na zo wa baƙunta.”

Ta ce “Na sani, yi hakuri ƴata.” Na miƙe sai na fito yana zaune yana danna wayarsa, miƙewa ya yi sai na bi shi a baya Sasan da muka nufa duk gidan ba me kyan sa, ƙanƙararren gini ne na zamani, ciki ma ya hadu har ba magana a gyare yake fes ba batun wani gyara, kitchen ne farko sai ka ƙara gaba ka taras da lafiyayyen falo wanda ya ji kayan alatu kofofi uku ne kowace da inda ta kalla, a farkon falon na ga bokitan su alkakin da na zo da su, a raina na ce nan aka kawo su kenan.

Kujera na samu na haye shi kuma ya buɗe daya daga cikin kofofin wadda take a kusurwa ya shiga, can an ɗan jima ya fito daga shi sai guntun farin wando lafiyayyen kirjinsa me cike da kwantaccen gashi a waje sunkuyar da kaina nayi ya ce”Ki cire lillibin nan ki shiga kitchen ki dafa min ruwan lifton” da hannu ya nuna min kitchen din, ba tare da na cire lillibin ba kamar yadda ya ce sai da na ƙare ma kitchen din kallo kitchen ne na zamani da na kare mishi nazari sai na kunna gas na tafasa ruwan na juyo na kawo mishi.

“Ya ce “In za ki kwanta ki shiga ciki na ce zan kewaya kofar da ya shiga ya nuna min, na buɗe na shiga daki ne me ɗauke da makadeden gado na zamani sai dressing mirror a gefe da wardrobe da sauran tarkacen da za su fahimtar da kai cewa me wurin namiji ne. Wata kofa da na gani ita ta sa ni tunanin nan ne makewayin, da na shiga sai da na murza key wanka nayi da na fito na same shi a inda na bar shi, na ce “Zan koma wurin mama.” Wani kallo ya jefa min “Mama na dauko wa ke ko kaina?Jakarki tana ciki, in kina son canza kaya akwai wata jakar ma ki yi amfani da kayan ciki.”

Ba ni da zaɓi dan haka cikin na koma tawa jakar na ɗauko na ciro kayan kwalliya nayi kwalliya, na saka turare, wata nineties ɗina na saka na koma karshen gado na makure bayan na tattake da hijab ɗina ina sauraren bugawar da ƙirjina ke yi.Tara da kwata na ji ya kashe komai sai ga shi ya shigo bathroom ya wuce ya fito yana duban inda nake lemar jikinsa ta bani tabbacin wanka ya yi.

“Yo Alwala ki zo mu yi sallah.” ya ba ni umarni. Mun idar da sallar ya dafa goshina addu’ar da Manzon rahma ya ce ayi idan an yi sabon aure ita ya yi min, kafin ya yi ta kwararo addu’o’i yana nema mana albarkar aure. Shi ya fara tashi ya tsaya gaban madubi yana saka turare, sai satar kallon sa nake, ba sanannen ciki ya waiwayo ya kama ni ina kallonsa saurin kauda fuskata nayi, ya ce “Gulma, wata gulmar kunyata da ake ji, wata rana ke da kanki ban kira ki ba za ki zo ki haye nan” yana fadi yana shafa kirjinsa.

Sauri nayi na tashi na haye gadon na kwanta a inda na tashi na rufe idona ruf. Ban san ya iso inda nake ba sai hannunsa da na ji kan ƙirjina yana lalube, “Kullun na ga ababen nan cikin hijab ba ƙaramin daga min hankali suke ba, dan duk boye sun da ake cikin hijab bai hana su bayyana ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 13Wa Gari Ya Waya 15 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×