Wani yammaci ban yin komai sai na kai wa Mmn Ummi fira. Cikin firar nake ce mata ban taɓa jin labarin Kawun nan me sunan Tahir ba, har sai da ya zo.Ta ce "Kuma shi ya riki mijinki, an ce tun ƙare primary ɗinsa, ya ɗauke shi. Halima kuma matarsa ta farko, tun primary school suke tare, saboda yawan shakuwar su, ake ce musu mata da miji, tun nan yake sonta take sonsa. Lokacin da suka gama secondary School, aka nemi ta fitar da miji ta ce ita fa bata son kowa sai Tahir.
Iyayenta suka kaɗa. . .
Thank you