Skip to content
Part 18 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Wani yammaci ban yin komai sai na kai wa Mmn Ummi fira. Cikin firar nake ce mata ban taɓa jin labarin Kawun nan me sunan Tahir ba, har sai da ya zo.Ta ce “Kuma shi ya riki mijinki, an ce tun ƙare primary ɗinsa, ya ɗauke shi. Halima kuma matarsa ta farko, tun primary school suke tare, saboda yawan shakuwar su, ake ce musu mata da miji, tun nan yake sonta take sonsa. Lokacin da suka gama secondary School, aka nemi ta fitar da miji ta ce ita fa bata son kowa sai Tahir.

Iyayenta suka kaɗa suka raya, amma ta dage, shi ne suka aiko gidan nan, nan ɗin kuma suka ce kwata kwata Tahir ɗin guda nawa yake? da har za a yi mishi aure, dan shekarun su ɗaya. Makarantar aikin jinya ta samu, har ta kammala ta fara aiki, suka ƙara aikowa Halima fa na jiran Tahir, akwai makotaka da zaman tare dan haka yan’uwan Tahir suka zaunar da shi, da lallashinsa kan ya yi hakuri ayi auren nan. Lokacin ko aiki bai samu ba yana dai zuwa kasuwa wurin harkokin marikinsa, wanda yake babban malami ne, har makarantu yake da su na islamiya a Kaduna da Lagos, ana yin auren Kawun ya buɗe mishi shago, na sayar da sarƙa da ƴan kunnaye. Kasuwancin ya cigaba da yi, har ya samu aiki a mamatar man fetur da ke Kaduna.Gidan Kawu Attahiru ya fara zama da ita, kafin ya saya mishi gida su koma.” Jin tayi shiru na ce “Ta biyun fa? ya aka yi ya aureta? Wani kallo ta min “Ni uwar surutu ko? to ki tambayi mijinki.”

Marairaicewa nayi “Dan Allah ki faɗa min, da zai gaya min da bai gaya min ba” Ta ce “Ita ƙanwar abokinsa ce, a Abuja suke zaune, mahaifinta me arziki ne. Ya kai wa abokin nasa ziyara ta gan shi, shi kuma Tahir na yabawa da ita ya ce “Ƙanwarka kyakykyawa, ya ce “Na ba ka ita. Shi ya ɗauki maganar wasa sai ga shi yana dawowa yayan nata ya kira shi kan maganar, shi ne ya zo yana fadi wa yan’uwansa, ke har mahaifinta sai da ya kira shi kan batun daga ta tayar musu ita fa tana san sa gata yar gata wurin mahaifinta wanda su biyu kawai ya haifa ita da wanta, mahaifiyarta kuma Allah ya yi mata rasuwa.

Tahir dai ya amince aka sha biki, wanda aka sha daru da Halima, jin Basma na aiki ita ma ta ce sai ya nemo mata aikin, a asibitin kawo take aiki yanzu haka. Basma a Abuja take zaune, sai dai ya je mata hutun karshen mako, to yanzu ma na ji an maida ta aiki kadunan, Basma tayi ta yin bari har waje mahaifinta ya fitar da ita, Halima ce dai ban tunanin ta taɓa ko batan wata ba.” shiru nayi ina nazarin labarin da ta babba ni, duk da na dan san wasu ban san wasu ba. Aikowar da Haj tayi kirana ya katse mana firar, na tashi. Washegari ina barci sai na ji saukar duka akan cinyata.Na tashi a firgice tare da mamakin waye zai min wannan aikin, Hafsa na gani, take na wartsake cikin matukar mamakin ganin ta “Yar duniya daga tafiyar kwana ɗaya, sai muka ji ki shiru, kina nan har wasu mazaunai kika ajiye, ke miji daɗi.”

Harararta nayi “Shi ne hada dukana, ke da waye? Ina Ramla? ta ce “Ni da ƴan kai amarya”Na ce “Amarya kuma? wace Amaryar? ƴar dariya tayi “Ke amaryar mana, mun biyo ki ne.” Na fiddo ido “Haba? dan Allah da gaske? ta ce “”Kar ki raina min hankali Malama.” na kwantar da kai, “Ki yarda wallahi ba ni da masaniyar komai.” Nan ta bani labari ai Tahir ne ya tura ya ce a dauko masu raka ni a kaini Kadunana jinjina lamarin dan bai faɗa min ba.

Na ce “Ina sauran?ta ce “Su na sasan Haj, ni kaɗai na zaro jiki na tambayi inda kike”.Hure mata ido nayi “Wai sai kallona kike meye? ta ce “Na ga amaryar ne har an cika mata aiki, ana a’a a’a ga shi nan soyayya tayi daɗi jikin ma ya nuna kina karɓar sakon yan…. toshe mata baki nayi na faɗi “Na shiga uku, kin bani kina matar malam kina maganganun banza.” ta ce “Ko ba maganganun banza ba.” na ce “Sharrinki dai ke zai kashe.” ta cigaba da min tsiya, ni kuma ina ta ware ido in ga ta inda waɗanda suka zo tare za su ɓullo.

Matar Yayansa Rabi ta yo musu jagora, Yayyena mata su biyu, sai ƙanwata Hauwa’u, sai ƙanwar Ummata, Inna magajiya, sai Gwoggo. Rufe fuskata nayi, da kyar na samu na gaishe su. Da na nemi Hafsa da Hauwa’u su zo mu shiga kitchen in musu girki, Hafsa ce min tayi “Ai da alama ke ce kaɗai ba ki san da zuwan mu ba, amma am mana abinci da abin sha waɗanda suka gwada an san da zuwan mu.Tare muka kwana da ƴan’uwana da Hafsa, su Gwoggo suka kwana wurin Haj.Sai da aka karya kumallo da safe, aka yi wanka kowa ya kintsa. Nayi sallama da mutanen gidan, da Haj wadda ke ta matse ido.

Amma da Usaina dai har yau ba wadda ta dawo duk yanda aka kai ga roƙon mazan nasu, ba a sha kansu ba, sun ce sai sun gane muhimmancin mahaifiyarsu ko da za su dawo.Hada Uwargidan Yaya Babba muka tafi da ta yaya Magaji.Ni da Hauwa’u da Hafsa wuri guda muka zauna, bayan motar da Tahir ya turo yaya Babba ma sai da ya dauko wata. Ƙarfe biyu na rana muka shiga garin Kaduna.A unguwar NDC nan gidan Tahir Sodangi yake, muna ta wuce tamfatsa tamfatsan gine ginen da suka mamaye unguwar. Mai motar farko ya yi horn gaban wani tangamemen get, ba ɓata lokaci aka hangame get din, motar ta sulala ciki, me bi mata ta mara mata baya.Harabar gidan yana da matuƙar girma, ga shuke shuke da suka ƙara ƙayata shi.

Kowa ya fito muka nufi ainihin inda ginin gidan yake, wani katafaren falo muka shiga, inda wasu mata su uku suka tare mu, sai da muka yi sallah suka gabatar mana da abinci sai sannan na gane gidan Kawu Attahiru ne. Matan biyu matansa ne, ɗayar kuma da ta fi su kuruciya Uwargidansa ce ta riƙe ta.Kafin dare an yi matukar sabo da amaryarsa me suna Aunty Kulu, a lurar da nayi ita ɗin shuwa ce, dan kamanninta, da kuma yanayin shigar ta. Ko su Uwargidan Yaya Babba Maman saddiƙa, ba su santa ba, wai auren kwata kwata shekararsa uku, kuma wannan shi ne karo na farko da ta fara zuwa Arewa, a Lagos ya ajiye ta, sai dai ba yarinya ba ce za ta yi shekaru talatin da bakwai. Uwargidan shiru shiru take, sam bata magana. Su ukun suka je suka gyara min daki. Sai dare bayan Kawun ya dawo an gaggaisa, Aunty Kulu da Uwargidanta, su ka ce za su mika ni ɗakina. Hauwa’u da Hafsa ma suka ce za su sai ƙanwar Innata Inna magajiya. Tsakanin su ba nisa, shi ma tafkeken Gate ne, ginin gidan upstairs ne hawa ɗaya, akwai wadataccen fili wanda ya sha adon furanni, sai rumfar adana motoci, akwai bukka ta shan iska irin ta turawa.Inna magajiya ta ruko ni a kunnena take raɗa min, “Ki yi ta jan duk wata addu’a da kika sani har mu shiga ciki.”Ban ki ta tata ba addu’o’in nayi tayi, wata kofa suka tura muka shiga ta sadamu da main falo na gidan, wawakeken falo ne wanda aka yi matuƙar kayatawa da kayan more rayuwa.Ba kowa ciki sai sanyin AC da ke ratsa duk wanda ya shigo, mun ratsa tattausan kilishin da ke barazanar shanye ƙafafuwan wanda duk ya taka.Kofofi huɗu muka gani, biyu suna kallon juna, biyun ma suna kallon juna, Aunty Kulu ta sa key ta buɗe wata da ke kallon yamma, muka shiga falon nawa, ya yi kyau ƙwarai, an shirya shi da kujeru da labulaye, sai kayan Electronics wanda ko ɗar ban yi ba, na san Tahir ne ya sanya min, muka wuce ciki inda tankamemen gadona yake, me haɗe da mirror da wardrobe an shirya akwatuna sai ƙaramin fridge wanda na san shi ma Tahir ne ya sanya min.Gadon na haye na yaye rufar da nayi dan in sha iska, wayar Aunty Kulu ta shiga ƙara, ta fita falo dan amsawa sai da ta ƙare sai ga ta ta shigo,suka mimmike dan komawa gidan Kawu Attahiru Aunty Kulu ta ce “Hauwa’u da Hafsa su zauna su taya ni kwana.Sun tafi suka bar mu, Hauwa’u ta shiga toilet Hafsa ta miƙe tana leka window, ta juyo ta yafito ni, sai na isa kusa da ita, kallonta nayi sai na dubi inda take nuna min, Tahir na gani zaune a rumfar shan iska da ke a harabar gidan, dan harabar tar take da haske kamar rana. Sanye yake cikin kananan kaya, wadanda suka yi matuƙar amsarsa, farin Glass ɗinsa manne a idonsa.

Farin teburin da ke gabansa wani glass cup ne yana shan abin da ke ciki, suna fuskantar juna shi da wani. Zura mishi ido nayi, dan ba kaɗan ya yi min kyau ba, wata kaunarsa na ji tana ƙara fizgata, shagala nayi na lula cikin tunanin lokutan da suka shuɗe abubuwan da suka gudana a tsakanin mu. Girgiza min kafaɗa da Hafsa take yasa na waiwayo cikin wani yanayi na ce “Meye? Wani kallo ta min soyayya manya yarinya.” Na galla mata harara Me nayi? tayi ƴar dariya ba ki yi komai ba.Cikin sanyin jiki na koma bakin gado, ina cigaba da tunanin da ya ƙara daure min kai tun shigowar mu gidan, wai wannan tamfatsetsen gidan na Tahir ne, dan ba kaɗan ya ruɗa ni ba. Hauwa’u ta fito, ta zauna muka ji ana magana daga falo Hauwa’un ta tashi ta leƙa, Tahir ne ya aiko mana da gasassun kaji da kayan tande tande, ci muka yi muna fira har muka kwanta.

Da safe da baƙin rai na tashi. Wanda suka danganta shi da tafiyar da za su yi su bar ni, ni kuma abin da ya ɓata min rai tun zuwana Tahir bai neme ni ba, sai txt kadai da ya yo mini yana min ya hanya. Dan ko da ya shigo gidan Kawu Attahiru na dai ji muryarsa yana gaishe su, amma ban gan shi ba.Sai hantsi ƴan rakiyata suka baro gidan Kawu suka iso wurina, ina jin su sai shawara suke a kai ni wurin kishiyoyina wasu su na cewa a ƙyale ni, dan daga cikin su ba wacce aka ga idonta.Ni dai ina riƙe da kofin kunun gyaɗa wanda aka kawo mana daga gidan Kawu Attahiru ina kurɓa a hankali, sallama muka ji wadda bata ko sa na ɗaga kaina ba, cikin girmamawa ya gaishe su, ya kuma yi musu sallama ta ban girma.Sai da na ga sun zauna a mota kafin na fara share ido. Ina tsaye har motocinsu suka fice harabar gidan, na koma ciki na zauna gefen gado nayi zuru.Na idar da sallar azahar, ina tsaye gaban mirror ina dan ƙara gyara fuskata,na soma shaƙar ƙamshin turaren Tahir, waiwayawa nayi shi ɗin ne, yau ma cikin shigar kananun kaya yake, hannuwansa zube cikin aljihunsa yana kallona kwarjininsa yasa na kasa cigaba da kallonsa sai na sunkuyar da kaina, ya tako zuwa inda nake “Ranki ya daɗe Amarya.” Ya fadi yana zama bakin gadon, hannunsa ya miƙo ya kamo ni ya zaunar da ni kan cinyarsa, ya zagaya hannuwansa kan cikina, sai ya rungume ni ya dora kansa bisa wuyana, wai kuma sai ya ke ce min “Ko tausayi ma abin, kin danne ni da wadannan manyan abubuwan naki” ya ƙarasa fadi yana duka bombom ɗina, mutsu mutsu na kama yi zan sauka ya matse ni maganganun da yake gaya min suka sa ni rufe ido.Jin na ƙi magana yasa ya ce “To tashi mu je ki ci abinci, akwai baƙi kuma da na kawo miki”.Saurin miƙewa nayi.

“Baƙi? kuma ka bar su zaune”. cikin hanzari na fita zuwa falon, yara ne mata su biyu, wanda kamanninsu suka gwada alamar su ɗin yan biyu ne, Shekarun su ba za su haura shida ba. Na kamo su na zauna tsakiyar su ina tambayar su sunayen su, kamar yanda na za ta suka ce Hassana da Hussaina. Muka haɗa ido da Tahir ya ɗora ƙafa daya kan daya, murmushi nayi “Ƴan biyun waye masu ban sha’awa? Mahaifinsu babban yaron Babana ne ( Kawu Attahiru) Baban shi ya yi mishi aure, cikin gidansa suka zauna da matarsa bata samu haihuwa da wuri ba sai kan yaran nan, tana kuma haihuwar su, Allah ya karɓi ranta. Ni kuma mahaifiyar tasu farkon kawo ni garin nan ita ke min komai.Marairaice fuska nayi cikin nuna jimami, kamar yanda na ga shi ma ya shiga jimamin, nayi mata addu’ar samun Rahma.Ya ce Dawo nan ki ci abinci” Flate na tashi na dauko na dawo na zauna, na juye abincin na janyo yaran mu ci, suka ce sun koshi.Sai na basu ice cream din da na gani a wata ledar daban suna ta tsotsa, ni kuma ina cin abincina, Tahir na caccanza channel da remote control din da ke hannunsa. Sai da na kammala ya ce min zai fita. Ganin kan yaran a tsefe, ga su kuma masu gashi ne yasa na ce “Wa ke so in mishi kitso”.Kowacce ta ce ita, na zauna na yarfa musu kitso me kyau.Sai yamma likis, wata da nake zaton me aiki ce ta shigo sai da ta gaishe ni kafin ta ce “Alh ya ce su Hassana su zo.” Ban so ba, ta fita da yaran dan samun su a tare da ni ya ɗebe min kewar kadaicin da nake ciki.Wanka kawai na shige, da na fito na ɗaura alwala, zane na daura da dogon hijab na kabbara Sallar isha’i, sai da na idar, sannan nayi kwalliya, akwatunana na sauke ina shi ma Hafsa albarka a raina, dan kafin a taho da kayana ta je ta dauki wasu daga cikin kayan akwatina ta dinko min, Atamfa na ɗauko wadda ta sha dinkin da ya zauna min, na koma gaban mirror ina yaba kyan kitson da Hafsa ta yarfa min da safe.Two step ne kanana ban daura dankwali ba, turare na fesa sai na dawo falo na kishingida rashin sanin abin yi, ban wani daɗe ba aka buga ƙofar sai aka shigo, Basma ce, mun kalli juna ni da ita, kafin na miƙa mata gaisuwa da fara’a kan fuskata, ga mamakina ita tata fuskar ba walwala. “Sweety na kiranki” abin da ta ce min kenan sai ta juya, na yunkura na shiga ciki hijab na ɗauko na sanya kafin na fito sai sake sake nake a raina, ita kuma wannan me ya canza ta? wani barayi na zuciyata ya bani amsa da kishi mana, ke kishi wasa ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 17Wa Gari Ya Waya 19 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×