Skip to content
Part 2 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Da auren Tahir a kaina ba zan iya ba wani kaina ba, tunda na ɗandana zumar Tahir kowane namiji fanko na ke kallonsa, ba zan iya haɗa jiki da kowa ba. Muje kasuwa in zabo katifar, wuyarta dai in samu shiga gidan. Shi yasa na zaɓi ƙarar da duk abinda na mallaka in kaiwa malamai dan su samo min kan Tahir.

Taɓe baki Fadila ta yi, “Gayen nan dai ba karamin tafiya ya yi da imaninki ba, mu dai in dai kana da masu gida a rana magana ta ƙare. Kin sanar wa su mama ko?” Girgiza kai ta yi.

“Tashin hankalin da na shiga ya mantar da ni muje in faɗa mata.” Tare suka mike dan gayowa mahaifiyar Latifa batun tarewarta a yau wadda suke ga daki ga daki.

Ina shiga ɗakina bathroom na shiga wanka na yi dan tun wankan safe ban kuma ba, gamawata na fito ɗaure da tawul a ƙirjina, zama na yi gaban dressing mirror ina mulka mai ta jikin mudubin na zura ma cikina ido wanda yake a shafe ba alamar akwai wata halitta kwance a ciki, tunanin yin shiru da maganar cikin kar in gaya wa Tahir har sai ya bayyana kanshi na yawo a ƙwaƙwalwata. Turo ƙofar da akayi yasa ni saurin jan tawul ɗin dan suturce jikina da yake waje, tare da jin takaicin wanda ya yi min wannan aikin.

Tsaye yake idonshi fes bisa kaina, “Ina jiranki.” Kalmomin da ya furta min kenan sai ya juya. Ban ko samu bin shi da kallo ba dan wani takaici da naji tagumi na rafka da hannu bibbiyu.

“Me mutumin nan ya mayar da ni, shashasha ko sakarai?”

“Ba ko ɗaya illa hakan shi ne auren.”

Zuciyar ɗazu ta dawo ta kwaɓe ni daga zugar da ɗayar ta fara min.

Biyayya ga miji ai wajibi ne ga duk macen da ke so ta tsira, ba ki faɗi ba, ke ce a ƙasan shi, fito na fito da miji da miji ba inda zai kaiki face halaka.

Har na gama shirina tsaf zuciyar nan tawa tana ta jero min da kalmomin haƙuri da biyayya, har na miƙa wuya na zaɓi kai kaina ga Tahir. Duk da nake tunanin bai cancanci hakan ba, ganin irin tarbar wulaƙancin da na samu daga gare shi, wani ƙarin wulaƙancin ma bai tashi sanin amaryar shi za ta tare ba aure wajen watanni nawa har sai da na dawo.

Na gama zura rigar barcina zan ɗora hijabi kiran Aunty Laila ya shigo wayata. Sai da na zauna bakin gado sai na amsa kiran, da murmushi a fuskata, “Amarya ba kya laifi.” Ta faɗi da sigar zolaya, wani malalacin murmushi na saki,

“Ki dai gyara kalamanki ka da amaryar gaskiyar ta ji ki.”

Dariya ta yi ta ce, “Kina raina duk wunin yau, sai yanzu na samu na kira ki.”

Muka shiga fira tana bani labarin yanda suka kasance bayan rabuwata da su. Kiran Tahir da ke shigowa yana yankewa yasa hankalina rabuwa biyu, har ta fahimci ban tare da ita sosai, ta ce “Ko na shiga lokacin ogan ne?”

Murmushin ya ƙe nayi “Me kika gani?

“Babu komai, mu kwana lafiya.” Ta katse kiran.

Murmushi na yi na kashe wayar gaba ɗaya, na ajiye ta, sai na zura hijab ɗin, rufe ƙofata na yi, na ratsa falon har lokacin matan biyu suna zaune wanda na ƙaddara zaman nasu a gulma dan nasan sun riga ni wucewa to me kuma ya dawo da su?

sun bi ni da wani Irin kallo kafin kowacce ta miƙe zuwa ɗakinta cikin matsanancin kishi.

Taɓe baki na yi tabbatar da zargina, dama abinda ya zaunar da su kenan. Ban same shi falo ba sai na wuce bedroom, ɗakin ba wadataccen haske, sai dai ya ɗauki sanyi ƙwarai

ina ƙoƙarin zare hijabina. Na jiyo sautin sa cikin wata galabaitacciyar murya, “Ki bani ruwa Please.” Jin muryar ya bani tsoro, dan haka sai na ƙarasa na kunna fitilar ɗakin,

take ya gauraye da haske, dafe yake da mararsa, ruwan na yi saurin ɗaukowa na ƙarasa gabansa na miƙa masa ina tambayarsa abinda ya same shi, mararshi ya nuna min,

maganin da na gani a hannunsa ya sha ya bi da ruwan ya koma ya kwanta, na maida ruwan na dawo na zauna ina jera mishi sannu, mun ɗauki wani lokaci a haka kafin barci ya kwashe shi. Tagumi na yi na zura masa ido har na soma gyangyaɗi, gyarawa nayi na ɗan kishingiɗa barci ya yi awon gaba da ni. Cikin barcin na riƙa jin nishin shi, tashi nayi da sauri ina ta ma shi sannu ya ce in yi masa addu’a a ruwa nayi na ba shi ya sha, to ba laifi ya samu sauƙi har muka yi barci, fara kiraye kirayen sallar asuba ya farkar damu.

Alwala ya ɗauro ya shiga ibada, rashin samun isasshen barci ya sa na kasa tashi,

sai da aka tada sallah na farka na ga yana haramar fita, daurewa nayi na miƙe na ɗauro alwalar na bada farali. Ina azkar ya shigo na gaishe shi tare da tambayar shi jiki

ya ce, “Alhamdulillahi”

Na tambaye shi abinda zai ci ya ce bai sha’awar komai zai dai ɗan kwanta zuwa takwas da rabi zai shiga makaranta. Na ce “Asibiti ya kamata ka fara zuwa ya ce

“Kar ki damu idan na fito makarantar zan shiga Hospital ɗin.”

Da ya kwanta zama nayi na tasa shi, har ya tashi ya yi wanka ya shirya, ya yi min kyau ƙwarai cikin shigar ƙananan kaya ga farin glass ɗin shi na rai da rai ya manna, wurin motarshi na jira shi da ya shiga wurin matansa, sai da ya shiga ya zauna na zagaya na ajiye masa jakar laptop ɗinsa, cikin ido ya dube ni

“Ki gyara min ɗakina pls Ummuna.”

Saukar da idona nayi nayi masa a dawo lafiya sai na koma ciki.

Dakinsa na koma na shiga gyarawa ina mita a zuciyata zai tare da amarya ni zai sa in gyara masu wuri, ban sa ganda ba ko ganin ƙyashi na gyara ko’ina fes na sanya ƙamshi, har bathroom na gyaro na wanke boxers ɗinsa na shanya, na so shiga gidan kawu Attahiru mariƙin Tahir sai dai na ce bari in bari sai gobe yau in yi masa danbun nama, ɗakina na koma na gyara jikina da ɗakin, sai da Halima ta gama girkinta ta fita sai na shiga, ina aikin danbun naman ina girkin rana na ji ana knocking gane ba kowa kusa yasa na fito na buɗe.

Mata biyu na gani suna kitimillin shigo da katifa sai namiji ɗaya da ke taimaka musu. Sannu na yi masu suka ce sun zo shirya ma Latifa ɗaki ne, duk da faɗuwar gaban da na ji sai na basu hanya tare da yi masu izinin shigowa na nuna masu ɗakin,

ajikinsu suka fito da key suka buɗe suka shiga.

Na koma kan aikina, na fito shirya dinning na samu Halima jikin fridge tana shan ruwa kusa da dinning, taɓe baki ta yi idanuwanta na kan ɗakin amarya, tsaki me ƙarfi naji ta ja,

“Aikin banza ai indai sana’ar mutum kwashe kwashe ba abinda ba zai jajibo ba,

yau kuma me zuwa daga ita sai katifa ya kwaso, gayyar na ayya.”

Ta kuma jan wani mummunan tsaki. Ni dai ban ɗago ba ballantana har in gwada na ji abinda ta ce. Har na gama abinda nake na wuce ta tana ci gaba da maganganunta.

Yamma liƙis amarya ta iso da yan rakiyarta, kamar yanda lokacin da aka kawo ni ba wadda ta ce mana mu ci kanmu haka suma ba wadda ta yi masu maraba, har suka ƙare arerewarsu suka tafi.

Waya ya yi min ya ce in taimake shi inyi girkin dare, ban ƙi yi ba nayi, sai dai abinda ya ban mamaki ana fara zaman cin abinci waya kawai ya yi mata sai ga amarya tsagal ta fito idanuwanta fes kan kowa, ta zauna aka ci abinci da ita.

Wata doguwar mace fara mara jiki, sai dai tsawo kamar daren sallah.

A raina nake faɗin wani aiki sai namiji, itama ba yarinya ba ce, kamar yadda Halima take tsararsa, na yi imani wannan ma ba wata tazara me yawa ce a tsakaninsu ba.

Da muka kammala ya zaunar damu ya yi mana nasihar zaman lafiya, lokacin tashina na yi masu sai da safe na wuce ɗakina. Washegari ban shiga gidan kawu Attahiru ba

dan rashin ganin Tahir wanda ya yi sammakon fita makaranta da ya dawo ma wani shirin ya sake yi ya fita, ya buɗe motarsa zai shiga kenan wani mutum da maigadi ya buɗe wa gate ya ƙaraso wurinshi yana masa sallama, musabaha suka yi ya ciro takarda a aljihunsa ya miƙa wa Tahir, tambayar shi va yi ta mece ce

“Sammaci ne yallabai.”

Bai ko tsaya sauraren ƙarin bayani ba ya buɗe takardar, ya shiga karantawa, ƙarar Halima aka shigar ana bin ta bashin wasu maƙudan kuɗaɗe. Zufa yaji tana keto masa,

ya sallami mutumin ya rufe ƙofar motar sai ya koma cikin gidan, amarya Latifa kawai ya samu a falon, ya wuce ta zuwa ɗakin Halima, daga bayansa take cewa,

“Bata nan.”

juyowa ya yi, ya faɗa kan ɗaya daga cikin kujerun falon, ya dafe fuskar shi da hannayensa, Latifa da ke tsaye kansa ta gama kisisinarta dan taji damuwarsa amma ya yi mata banza, wata kujerar ta zauna dan tayi ma kanta alƙawarin sai taji tushen

matsalar.

Shigowar Halima yasa shi ɗagowa,

“Daga ina kike?

Ya tambayeta cikin fushi,

yamutsa fuska ta yi

“Unguwa na je.”

Ƙwafa ya yi

“Yayi kyau, da izinin wa?”

Shiru ta yi ya jefo mata takardar ta faɗa kan jikinta, ta ɗauka tana dubawa

gabanta ya faɗi, ta kalli inda Latifa ta zubo mata ido. Wuce ta ya yi zuwa saman shi,

ta mara masa baya, Latifa ta bisu da kallo har suka shige, sai ta mara musu baya,

laɓewa ta yi tana sauraren yanda Halima ke kuka da magiya kan Tahir ya rufa mata asiri.

Shi kuma yana bambamin ya gaji da halinta na cin bashi, yau har ta kai ga a kawo mishi sammaci. Ta ina ya rage ta da har za ta jefa kanta a masifar ciwo bashi. Ina take kai abinda yake bata? Sai da Latifa ta gama saurarensu sai ta bar wurin tana taɓe baki

ita kuma ta ta masifar kenan ta cin bashi. Allah shi kyauta an kuwa tafka asara.

Ɗaki ta koma tana tir da wannan bala’i da Halima ta tarkato a ranar kwananta,

kamar yanda ta zata tunda suka gama da Halima ya fito ya bar gidan, bai kuma shigowa ba sai da kowa ya nabba’a a makwancinsa.

Tana ta kai kawo a ɗakinta da taji motsi ta leƙa window, sai sha daya ya shigo ta ba shi wasu mintoci kafin ta kare shirinta na zuwa turaka. Kwance ta same shi

fuskarshi na duban sama ya yi matashin kai da hannayensa, idanuwansa a rufe suke amma ta san ba barci yake ba, haka yake idan ransa ya ɓaci.

A hankali ta hau gadon gabanta na faɗuwa, sai tsine wa Halima take a zuciyarta

ita ta taɓo zuciyar mazan tun jiya take banka ma cikinta magunguna a matse take ƙwarai amma wannan ƴar sherin ta lalata mata daren.

Ta daɗe amma barci ya gagara daukar ta a buƙace take, ganin ya juya sai ta mirgina ta haɗe jikinta da nashi, duk da ya ji abin a matsayinsa na lafiyayyen namiji, sai ya ture ta, ƙara matsawa ta yi ta manne masa. Tsaki ya yi ya fara magana cikin fushi

“Look Latifa ki bar ni please” Ya ƙara ture ta,

“Ba burinku kullun ku ganni cikin damuwa ba? Ta fashe da kuka tana faɗin ita meye laifinta me tayi masa? Shiru ya yi yana sauraren ta, a ransa yana jin bai yi mata adalci ba, laifin wani bai shafar wani, a hankali ya kai hannu ya ja ta ta lafe jikinsa. Sai dai abinda take son bai samu ba.

har sai da ya dawo sallar asuba, ta ja hankalin sa har ya shafa’a da fita duba sauran matansa.

Har na yi wanka na shirya ban ji Tahir ya shigo ba, na duba agogo ƙarfe goma.

Na zauna ina duba wayata sai ga shi, muna gama gaisawa ya fita. Har na yi mamakin fitar shi daga shigowa, ina son tambayarsa zan shiga gidan kawu Attahiru,

Lilliɓina na zura na ɗauko mazubin da na zubo dambun naman da na yi na fito na rufo ƙofata, na tako cikin falon, can jikin ƙofar da za ta fitar da kai cikin falon

idona ya gano mini abinda ya sanya ni juyawa zan koma inda na fito.

“Ina za ki kuma?”

Muryar Tahir wanda ke tsaye Latifa na gaban shi kamar za ta faɗa jikinshi, a kallon da na yi masu sanda na riske su cikin shauƙi suke abinda yasa na yi mamakin yanda aka yi har ma ya gan ni, ƙafata kamar ba za ta ɗauke ni ba, ƙirjina na mini wani zafi saboda kishi. Na isa inda suke,

“Ina za ki?

Ya tambaye ni yana ƙare ma yanayina kallo,

Dama na fito ne in tambayeka zan shiga gidan kawu in gaishe shi.” Wani kallo me kama da harara ya min da idanuwansa masu rikita ni,

“Haka dama ake tambayar unguwa sai an fito?

<< Wa Gari Ya Waya? 1Wa Gari Ya Waya? 3 >>

16 thoughts on “Wa Gari Ya Waya? 2”

  1. Na karanta was gari ya waya wlh ya ilimantar ya Kuma fadakar, Maryam litti Allah ya qara baseera da zaqin hannu

  2. Slm.masha Allah novel yayi Allah ya Kara basira da daukaka kina fadakarda mu sosai Allah ya Kara lpy da kwarin Ido.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×