Keke napep na kuma hawa, muna tafe barcin na dibata. Har ƙofar gida ya sauke ni, na wuce me wanki yana min sannu, ina shiga ɗakina gado kawai na faɗa, duk kuma yanda nake ji bai hanani janyo wayata ba, missed call din Tahir na samu rututu. Ummarmu na soma kira na faɗa mata abin da ya same ni, sosai ta shiga damuwa jin na kuma bari a karo na biyu, da muka gama sai na kira Tahir.
"Me ya same ki? da ɗaukar sa abin da ya fara ce min kenan kafin kuma in yi yunkurin amsawa. . .
Zato