Skip to content
Part 22 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Keke napep na kuma hawa, muna tafe barcin na dibata. Har ƙofar gida ya sauke ni, na wuce me wanki yana min sannu, ina shiga ɗakina gado kawai na faɗa, duk kuma yanda nake ji bai hanani janyo wayata ba, missed call din Tahir na samu rututu. Ummarmu na soma kira na faɗa mata abin da ya same ni, sosai ta shiga damuwa jin na kuma bari a karo na biyu, da muka gama sai na kira Tahir.

“Me ya same ki? da ɗaukar sa abin da ya fara ce min kenan kafin kuma in yi yunkurin amsawa ya kuma cewa “Ina kika bar wayarki, nake kira tun safe? Sai na rasa wace tambayar zan soma amsawa na dai yi ƙarfin halin cewa Miscarriage na samu, shi ne a ka yi min wankin ciki.”

Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun ya yi ta maimaitawa da wata irin murya da duk tausayin kaina da nake sai da na ji shi ma ya bani tausayi. “Ke da wa kuka je Hospital din?” Ni kadai na je.” “Haba Ummulkhairi, ke ma da nake zaton zan samu nutsuwa ta bangarenki kema din haka za ki yi min? hankalina na ji ya tashi da jin zancansa a kaina, da sauri na ce “Me nayi maka? “Saboda Allah ga ƴan’uwanki a gida sai ki fita ke kaɗai, cikin halin rashin lafiya? A garin da ba ki san kowa ba, yanzu idan iyayenki suka ji ya za su kalle ni?

Da sauri na soma rantsuwa jin zargin da yake min “Wallahi duk kan su na buga kofar su da zan wuce” kashe wayar na ji ya yi ni ma na ajiye tawa, na maida kaina kan pillow na kwantar cikin tunani. Awa biyu aka ƙara da yin wayar mu sai ga Hajiyar tudun wada da Malam. Wani dan matashi da ba zai wuce tsarar kanena Nura ba ya kawo su, su Malam sun dan jima sai suka wuce, Haj suka bari wajena. Basma da Halima sun shigo sun gaishe ni a tsaitsaye.

Washegari malam ya dawo da su ƴan biyu, kwanaki uku Haj tayi da ni, har ƴan’uwana da suka zo daga gida Aunty Maimuna da Aunty Habiba nan suka zo suka same ni tare da ita. Har ƴan kankara sun zo cikin su hada Hajiyar Tahir, su kwana suka yi da kansu kuma suka shiga kitchen abin da yasa takaici ya ishi Halima, ganin yanda suka sake sabanin da da in sun zo suke a raɓe. Ranar Asabar maigidan ya iso, shigowar asuba ya yi, dan haka bai nemi kowa ba, saman shi ya haye.

Da safe na fito zan shiga kitchen neman abin da zan karya da shi, muka yi ido huɗu, a cikin tafiyar da nake yi kamar me sanɗa dan tun zubar jinin da nayi jikina ba karfi lallabawa kawai nake, na karaso na gaishe shi sai kallona yake ganin yanda na lalace cikin yan kwanaki kaɗan. Kitchen din na wuce Ade na ciki tana aikinta, gaishe ni tayi tare da tambaya ta jiki, na amsa na kama nawa aikin, na kammala ina shiryawa a tray Basma ta shigo, “Ki zo yana kiranki.”

Abin da ta ce min kenan sai ta juya, na sunkuci tray na bi bayanta. Zaune na same su, Tahir shi da matansa, ina zama ya fara magana wadda ta shafi irin zaman da ake yi mishi a gida ba wadda ke shiga sabgar wata, tare da daura laifin kacokan kan Halima dan ya ce ita ce babba, dole ta ja kowa a jikinta.

Kan dole ta ba shi haƙuri, ni ma hakurin na ba shi, na miƙe ɗauke da tray na zuwa ɗaki.Ina zama karyawa na soma a hankali, sai ga shi ya shigo hannayensa kawai ya harɗe a kan kirjinsa yana kallona, kallo ɗaya na mishi na maida kaina ƙasa, takunsa na ji zuwa in da nake ya ɗago ni yasa ni jikinsa, kyakykyawar runguma ya min “Ki yafe min, Ummulkhairi.”

Me ka min? Na tambaye shi “Na tafi na bar ki kina ta shan wahala, rabon da Allah ya bamu ya zube bana kusa, ballantana in rarrashe ki.” Wasu hawaye na ji sun ziraro min, ɗago ni ya yi ya zura min ido “To ba gani ba, meye na kukan? ba zan kara barin ki ba, zan tafi da ke in kula da ke” jin tsayuwa na neman gagarar mu ya koma kan kujera zama ya yi ina jikinsa, hankacif ɗinsa yasa yana share min fuska.”

Ki fara shirya kayanki, sammako za mu yi idan Allah ya kaimu.” kai na gyaɗa mishi sai ya zame jikinsa ya mike “Zauna ki ƙarasa cin abincinki.”

A hankali na ce “To kai fa? Kai ya girgiza “Akwai abubuwan da zan aiwatar yinin yau, kar ki damu. Fita ma zan yi.” yasa kai ya fice.

Maimakon cin abincin, bedroom ɗina na wuce ina kwanciya hawaye na cigaba da yi ina godiya ga Allah bisa canjin da ya yi min dan abin da ke ta sa ni kuka tuna sanda nayi bari a gidan tsohon mijina, ranar da aka dawo da ni ba wani nuna jin tausayi ko wata kauna, burinsa kawai ya biya buƙatar sha’awarsa, abin da ya takura shi kenan da ba ni.

Dama kukan mu matan hausawa kenan, a kullum, rashin nuna kulawa daga mazajenmu. Mace na so a rarrashe ta a nuna an damu da ita, ko da ba a bata komai ba, ki yi abin kirki a yabe ki, a’a ba mazan yanzu ba, sai ki daɗe kina wa miji abin kirki, ba zai taɓa nuna ya ma san kina yi ba, sai randa kika saɓa mishi za ki ji kwandon Ala tsine.Mata masu fama da irin wadannan matsalolin. ban san iyakar su ba.Yana gama musu ganin dakin da ya shiga yasa duk kan su suka bi shi da kallo, kowacce da abin da take sakawa a ranta.

Halima ta ja dogon tsaki ta miƙe tayi ɗakinta, Basma ta bari zaune tana share zufar da ta ji tana tsatstsafo mata. Ba irin ta ta dace da zama da kishiyoyi ba, kishiyoyin ma har biyu ringis, ban da jarabtar da aka yi wa zuciyarta na masifar son Tahir Sodangi da ta haƙura da shi.Ta dubi Halima da ke tafiya kamar kububuwa dan fushi “Gara ke da ni”ta faɗi cikin siririyar murya.

Ita ma miƙewar tayi ta nufi na ta dakin cikin sanyin jiki. Halima na shiga na ta dakin gado ta fada ta shiga zabga kuka wiwi na bakin kishin wadannan mata da Tahir ya dauko mata, duk yadda ta so ta kori Basma ta bar mata gidan ta zauna ita kadai, abin ya faskara, sai ma wata da ya ƙara dankaro mata. Har sai yaushe Tahir zai bar zuciyarta ta huta? tuna rayuwarta a farko tayi tana ita kadai sai yanda tayi komai na shi ita yake miƙa mawa, yanzu kam dan karshen wulaƙanci sai ya tara su kamar awaki sannan zai ba su duk abin da zai basu, kuma iri ɗaya. Girgiza kai ta shiga yi hawayen na daɗa ambaliya kan kuncinta.

Amma da gani wannan yarinyar ta samu amsuwa a zuciyarsa yanda yake kaffa kaffa da ita, sam baya wasa da lamarinta. Ko Basma ɗiyar masu da shi, kyakykyawa ajin farko kyankyasar inji, da ta sha fargaban idan ta shigo Tahir zai juya mata baya sai ya bata mamaki, sai shafe wata bai tafi wurinta ba tana Abuja, lokuta da dama ma sai Basman ta dame shi da waya ko kuma ta dauki excuse wurin aikinta ta zo Kaduna.

Kwafa tayi tuna amarcin wannan yarinyar sai ya shafe sati biyu a kankara, abin haushin ma wai bazawara, sanda tana kankaran kuma duk weekend baya daga kafa sai ya je. Ko a muamalarsu ta auratayya suna su biyu duk girkinta ya dinga takura mata kenan da bukatarsa, amma tun zuwan yarinyar nan idan ta gama aiki ita kuma ta amsa baya damunta, kishin hakan hana ta barci yake, tunanin abin da ya yi a wancan dakin ya taru ya kulle mata zuciya.

Aiki ne ja a gabanta, yarinyar nan ga ta da kuruciya daga zuwa har ta fara ciki. Ƙwafa ta kuma yi “Mu zuba yarinya da ni kike wasan.Tun fitar Ogan bai shigo ba sai dare. Ko da ya shigo kuma bai sauka kasa ba sama ya yi zamansa.Halima me girki ita ta bi shi kafin daga bisani ta sauko kiran mu, bisa umurnin Ogan.

Ni ce karshen zuwa dan sa’ar da ta shigo na fito wanka ina kwalliya, simple make up nayi sai na zura wata jallabiya maroon colour na rufe kaina da gyalen rigar, takalmi flat na saka. A kujerar kusa da ƙofar na zauna Ogan na gaida kafin nayi musu Sannu, da alama wanka ya yi cikin jallabiya yake me guntun hannu sai annuri ke fita a fuskar shi, musamman idanuwansa masu haske, ga ƙamshin turarensa da ya cika wurin. Glass cup ne a hannunsa yana shan abin da ke ciki.

Ajiye cup din ya yi sai ya yi gyaran murya “Dalilin da ya sa na tara ku, gobe idan Allah ya kaimu zan yi sammako in koma wurin aikina, sun bani wurin zama ina da mata har uku, ba zan tafi in zauna ni daya ba, dan haka na tara ku in ji da wa zan tafi? ni dai na yanke zan tafi da guda, bayan wata kuma sai in dawo in tafi da wata.”

Basma ta lumshe idonta ta kwantar da kanta jikin kujera, ban da matsalar ta da a shirye take ta ajiye aikinta dan ta kasance da mijinta. Kuɗi ne mahaifinta ya tara musu, mijinta na da su, account ɗinta cike yake da kudi duk wata za ta ji alert. Halima ce tayi magana “Amma Tahir aikin mu.” Wani kallo ya jefa mata “Aiki da auren wanne ne a gaba? shiru tayi “Dan haka gobe da ke za mu tafi.”

Wata zabura tayi “Ni kuma Tahir? Idan na tafi zan samu matsala” kallon dazu ya kuma jefa mata “To meye nufinki, ba za ki ba? shiru tayi alamar hakan ne, duk da kishin da ke cin ranta na wadda za ta tafi ta kasance tare da ogan koma bayanta. Duk da shi ma aikin kishi ne ke sa ta yinsa.

Ya juya wurin Basma wadda har sai da na tabo ta dan yadda yake ta magana bata ko motsa ba.

Ta sauke kyawawan idanuwanta a kansa ya gane karin bayani take nema ya maimaita mata ta ce ita ma za ta tsaya saboda aikinta.”To tafiya kan amarya ta faɗa.” Halima wadda ke jin kamar ta kai wa bakinsa duka idan ya ambaci kalmar amarya ta aika mishi da harara a fakaice, cikin kunkuni ta ce.

“Dama haka ka shirya” dubanta ya yi “Magana kike? saurin girgiza kanta hada hannayenta tayi kafin ta taɓe baki “Kuma a haka da jikin nan za ka kwashe ta? ta fakaice ya dube ta bai yi magana ba “Kamar yanda na ce muku, ba zan iya shigowa duk sati ba ko sati biyu, sai dai karshen wata, dan wani sati biyun zan je ƙanƙara ne in gano Hajiyata. Ya sallame mu na koma ɗakina. Ban kwanta ba sai da na sauke akwatunana dan zaben wadanda zan yi tafiyar da su.

Ƙarshe na yanke in tafi da abu na duka dan in na bar su har sai yaushe zan dinka su? dan anan dogayen riguna nake amfani da su sai tsirarun kayana, na kwanta cikin tunani, shi kenan yanzu ba rabon in halarci bikin kannena su Aimana, na dubi agogo lokaci ya yi nisa sai da safe zan kira Ummata da Babana da sauran ƴan’uwana in yi musu sallama.

Bayan dawowarsa daga sallar asuba zaune yake gefen gado, damuwa kwance saman fuskarsa. Uwargida sarautar mata na gefensa. “To yanzu me kike nufi? idanu ta dan kada “Ka san dai ba wadda ta yi maka sanin da nayi maka, in duk su sun yarda ni kasan na san ka sarai dama ka shirya tafiyarka da Amarya, ka ɓullo mana ta haka.”

Ƙara daure fuska ya yi “Amma na ba kowacce hakkinta, in ma hakan shi ne nufina.” Ita ma ɗaure tata fuskar tayi “Saboda ta fi mu ko? wani ɓacin rai ya ji ya taso mishi kamar ya biye mata sai kuma dalilin da ke sa yake kasa biye mata ya bijiro mishi, kome za ta mishi da ya tuna ta fara son sa tun a shi din take so, ta aure shi bai da komai sai ya kasa ci mata fuska. “Tsaye ya miƙe “Babu macen da ta fi ki a wurina halima, kina da daraja ta musamman, sai dai idan kin zubar da ita da kanki, shi yasa kullum nake nuna miki abubuwa kin kasa fahimtata.”

Kanta ta ji ya fasu “To amma me ya sa ka zaɓe ta cikin mu? Ba zaɓen ta na yi ba ki shirya mu tafi.

<< Wa Gari Ya Waya 21Wa Gari Ya Waya 23 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×