Skip to content
Part 23 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Cikin salon yaudara ta ɗa namiji ya ce “Ba zabenta nayi ba ke ce babba ki shirya mu tafi.” Girgiza kai ta shiga yi, ya matsa kusa da ita janyota ya yi jikinsa suka faɗa tsakiyar gadon. Sai dai tun kafin abu ya yi nisa ta soma bijiro mishi da zancen kudaden da take so ya bata, zuciyarsa ce tayi bakikkirin ya tsani wannan bakar dabi’a tata, in har zai yi kwanciyar aure da ita sai ta roke shi.Ji ya yi shaukin abin ya sake shi, miƙewa kawai ya yi ya faɗa bathroom. Cikin shigar kananun kaya ya sauko, dakin Basma ya fara shiga suka yi sallama kafin ya shigo wurina ya samu na gama shiryawa ina saka dan-kunne.

Akwatunana ya soma fitarwa kafin ya dawo “Kin kintsa? na ce mishi “E” Kin karya? nan ma “E” ɗin na kuma cewa “Fito mu je” ya bani umurni na rataya jakata mahadin takalmin da ke ƙafata. Tare da sauran matan muka rankaya har inda motar da za mu yi tafiyar a cikin ta take, wata dankareriyar Jeep ce sabuwa dal tana sheƙi, a tafiyar sa ta farko ya fara hawanta, baka ce wuluk. Mutumin da ya tuka shi a tafiyar sa ta farkon yau ma shi ne riƙe da sitiyarin.Tafiya me karfi muka yi, saboda nisan inda muka nufa. Tun ina zaune kan mazaunaina, har na sulale na kishingida, Tahir ya janyo ni ya nade ni da jikinsa, dan haka barci sosai nayi. ƙarfe shida na yamma muka shiga garin na Lagos. Amma yawan cinkoso da go slow na ababan hawa yasa, bamu isa unguwar da za mu ba sai da muka shafe sama da awa guda. Da ganin yanayin unguwar da muka shiga gidajen cikin ta na ma’aikata ne, gaban wani flat house ya Parker motar sai muka firfito hasken wutar lantarki ya haskaka wurin, flat hudu ne a rukunin,.waya waya ce kowacce waya flat huɗu ne. Wanda ya yi driving ya sallama bayan ya fito mana da kayan mu, Tahir ya buɗe kofa falo ne babba sai ɗakunan barci guda biyu, sai kitchen. Kan daya daga cikin kujerun da suka yi wa falon ƙawanya na nitse, Tahir na gama shigo da kayan datse ƙofar ya yi ya dawo gabana ya tsaya “Ya ya dai Madam, gajiya ko? Murmushi nayi “Taso muje ki yi wanka” bin bayansa nayi, a cikin bed room din akwai bathroom manne da shi. Ni na fara yin wankan, ruwa me zafi nayi amfani da shi, wai ko zan samu sauƙin gajiyar da nake tare da ita.

Dama ga jikin ba karfi, da kyar nayi sallah, ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi Tahir wanda idar da sallar sa kenan ya miƙe sai ya tafi ya buɗe, hannu ya ba me kwankwasawsar sannan ya mishi tayin shigowa, muryar mutumin na ji ya ce “Dawowata yanzu kenan, Madam ke ce min ta ji dawowarka, shi ne na ce bari to in kawo maka abinci”.Godiya Tahir ya shiga yi mishi ya ce “Yanzu dama zan fita in samo mana abin da zamu ci, ka san ni ma na ɗauko Madam” Ƴar dariya mutumin ya yi “A lallai ka temaki kanka” “Ummulkhairi” Tahir ya shiga kiran sunana.

Na fito da hijab din da na idar da sallah a jikina na gaishe da mutumin me fara’a Tahir ya ce “Neighbour dinmu ne” na ce “Allah sarki” mutumin ya juya “Sai safe laila za ta shigo ku gaisa” na faɗi “Allah ya kaimu”Ciki na koma na yi shirin kwanciya, na zura rigar barci, Tahir ya shigo “Fito mu ci abinci”.Sai ya juya na fito da hannu ya nuna min wata kofa ya ce “Ɗauko mana spoon da flate”. Sai da na gama ma kitchen din kallon nazari ba abin da ba’a sa ba na nau’in kayan girki, haka nau’in kayan abinci.Tare muka ci sai muka kwanta, wai Tahir ya dage tausa yake min, dan in huce gajiyar da ya ja min ga shi bani da lafiya. Sai dai daga tausar bai yi min komai ba muka shiga barci.

Da Asuba sallah kawai na tashi na gabatar na koma na kwanta, dan gajiyar da nake ji. Sai dai na ji ana taɓa ni, na bude idona a hankali suka sauka kan Tahir, da ke tsaye kaina ya sha wanka yana fitar da sansanyar ƙamshi. “Zan fita wurin aiki, Ummulkhairi”. Sauri na yi na tashi zaune “Za ka tafi ban baka abin break ba” “Kar ki damu, idan na fita zan karya, ki yi kokari ki dafa ko indomie ne, kar ki ce za ki yi abinci, zan taho mana da abinci.Ki huta, har ki samu ki warware” kai na gyaɗa mishi, nayi addu’a ya fita ya ja min ƙofar .Sai da na sha barcina na, karfe sha daya na tashi wanka na soma yi, nayi kwalliya da riga da zane na Atamfa, sannan na shiga kitchen ba kamar yanda ya ce ko indomie in dafa in ci ba, tea na haɗa na komo falo ina kurɓa a hankali. Knocking na ji ana yi, abin da ya bani mamaki, amma dai na tashi na buɗe, wata matashiyar mace na gani, wadda za ta tasamma shekara 28 amma idan an gaya maka, in kuwa ba ka sani ba, za ka ce bata wuce Ashirin da hudu ko da biyar, dan hutun da ya ratsa ta.Fara ce, doguwa mara jiki, sanye take cikin bakin material ɗinkin doguwar riga, ta yane kanta da siririn mayafi.Kwando ne riƙe a hannunta, tana min murmushi, ni ma sannu da zuwa na shiga yi mata cikin murmushin muka shiga ciki, mun gaisa ta turo kwandon gabana, “Ga abinci nan na kawo miki” na yi mata godiya “Sunana Laila, ni ce Neighbour ɗinki, ta wancan flat din, da yake kallon naku.”

Na yi murmushi sai ni ma na gabatar mata da kaina, sunanta da ta fadi na gane matar mutumin jiya ce. Kasa na sauka ina cin abin da ta kawo min, muna ɗan taɓa hira “Na ji dadin dawowarki, kasancewarki musulma kuma Bahaushiya, sauran flat ɗin guda biyu mazaunan su, basu da mata.” Na ce “Allah sarki, ni ma na ji dadin haɗuwa da ke, me kirki da ke.”

Muka yi dariya tare, da ta tashi za ta tafi, na ce zan bi ta in ga wurin nasu. Tare muka fito, sai yanzu na ga wurin da kyau, akwai shukoki masu ban sha’awa da suka zagaye wurin. Mun shiga wurin nata ina zaune tana girkinta, dan ta ki yarda in taya ta wai in bari in huta gajiya. Ƙarfe ɗaya nayi mata sallama, na ce zan je in yi sallah. Ina idar da sallah,. sai ga ta ta kawo min abinci, dan haka da Tahir ya kira ni sai na ce ba sai ya sawo abinci ba. Ya dawo muna cin abinci , yake ce min sunan mijin Laila, Ahmad, mutumin kirki ne, na san shi tun Kaduna State University ( KASU) sai kuma yanzu Allah ya kuma hada su anan.

Tun daga ranar Laila bata taɓa fashin kawo min abinci ba, wai mijinta ya gaya mata na samu miscarriage, ban gama warwarewa ba muka taho. Aikina shi ne wanka sai in yi Sallah, in gyara wurina, sai ko shiga wurin Laila, kamar yanda ita ma take shigo min.Mace ce me tsananin kirki, iyayenta mutanen Kano ne, a Kano aka haife ta, kasantuwar mahaifinta maaikacin gwamnati ne garuruwa daban daban suka zauna , sai a ƙarshe aka turo shi Lagos. Bai jima da yin ritaya ba, yanzu haka suna America tun yin ritayar tasa, yaransu uku, Laila ce babba, sai mai bi mata namiji sai autar su, wannan kenan zamana da laila tun da ta fahimci ina da ilimin addini sai muke zama ina koya mata, ni ma sai nayi amfani da wannan damar na fada mata ina son ilimin zamani, iyakar karatuna sakandare kuma ina so in gwanance a Turanci, sosai take koya min abubuwan da suka shige min duhu, ƙarshe ta bani shawarar shiga wata makaranta Adult education, da ke kusa da mu.

Da na tambayi Tahir bai hanani ba, shi ya karbo min foam, ina jin dadin makarantar, a gida kuma ina da Aunty laila.Ya kai ni gidan Kawu Attahiru da ke agege, gida ne babba har ya fi gidansa na Kaduna, akwai jama’a sosai, duk wani bahaushe da ke ta wurin gidan Kawun ya mayar gidansu. Sannan Aunty Kulu tana gyaran Amare wanda ta amsu sosai a garin, wuni mata suke shigowa, har da masu taya ta aiki ta ɗauka.Wuni zungur nayi a gidan, sai yamma ya zo muka koma gida, na samu an yi min kitso, hada turaren jiki da na daki ta bani, Kawu Attahiru ya bani kudi. Dana dawo na raba mana turaren ni da Aunty Laila.

Dawowata da kwana biyu na soma ciwo, wanda zuwan mu asibiti binciken farko likita ya ce ciki ne, ba abin da nake iya yi ma kaina, Tahir na kula da ni yanda ya kamata, wata biyu shi ma kamar wancan nayi mafarki jini na bi na, shi ma haka ya bare, sai dai wannan da sauƙi ƙwarai, dan da gani sai Laila muka yi bidirin mu. Wasa wasa sai mafarkin jini ya aure ni, da nayi kuma zan tashi cikin jini, gaba ɗaya rayuwata ta canza, da dare ya yi jikina zai gashe kamar wuta, gari na wayewa sai in warware, abin da na lura da shi indai Tahir zai zo da bukatar shi to jikina zai ɗauki mugun zafi, mun je Asibiti, duk magungunan da suke faman rubuto min ba abin da ya canza, tun Tahir na kula da ni har na lura ya canza, yanzu da ya dawo wurin aiki zai yi barci, zuwa la’asar zai fesa wanka ya fita ba zan kuma ganin shi ba sai dare sosai, yana da yawan buƙata, amma an wayi gari baya nema na kwata kwata, sai dai randa rabo ya zo, yana yi kuma yana complain din zafin jikina, sai dai ya yi ta kalallame ni, da tausaya min yake bani da lafiya, shiyasa yake nesa da ni, kuma idan ya zauna kusa da ni ba zai iya riƙe kansa ba.Kamar na yarda da maganarsa, sai ranar da muna zaune aka kira wayarsa, gaba ɗaya sai na ga ya canza, ya kashe wayar aka kuma kira ya kara kashewa, ana karshen sai ya kashe ta gaba daya, take sai na tsargu, zargi kala kala ya shiga zuciyata.Bari nayi sai da ya yi barci na sato wayar, kitchen na shiga dama na rike time ɗin da aka kira shi, sunan da na duba Latifa na gani a rubuce, WhatsApp na shiga sunanta na bi na duba chart ɗinsu, ai ina karanta sakonnin da suka gudana a tsakanin su, wanda ko ni matarsa ba zan taba iya zagewa in rubuta mishi wadannan kalaman fitsarar ba. Ba kunya kwata kwata ba ɗa’a, hotunan sassan jikinta da ta turo mishi ba dadin kallo, sai dai ba fuskarta iya gangar jiki ne.Zuwa lokacin zuciyata ta gama tsinkewa, na gaza cigaba da ganin abin da nake ganin, hawaye ne ke shatata kan fuskata kamar sakarai ya kunna famfoTake wani post da na gani yana yawo a kafafen sa da zumunta ya fado min, wai wata tsohuwa ce ke cewa “Kashedin ku da wayar miji, domin ita ɗin kamar albasa take kina bare ta kina hawaye.

Na goge wayar dan na jike ta da hawaye, na lallaɓa jiki ba kwari, na mayar da ita inda na ɗauko ta.Sai ya zamto tun daga ranar da ya yi barci zan saci wayarsa, abin da kuma zan gani ya hanani kwanciyar hankali, da da ban binciki komai ba, idan lokacin barcina ya yi Tahir bai dawo ba kwanciyata nake in kuma yi barci na, amma yanzu ban iyawa, zuciyata ta din ga sakawa da warwarewa inda yake da kuma abin da yake yi, sa’a ta ɗaya cikin da na samu a wannan karon ya tsaya har ya soma girma. Wani dare da na gaza barci iya daɗewar sa ya kai sha daya, amma ranar sai sha biyu ya shigo, pretending din da na saba yi idan ya shigo yau zaune ya same ni ina kuka, abin da ya sa shi ya rude yana tambayata jikin ne?ganin ya ma raina min hankali yasa na ƙi magana, sai cewa ya yi wai meeting ne ya rike shi. A zafafe na ɗago halan da aljanu kake meeting din, cikin mamaki yake duba na dan bai taba ganin nayi mishi tsiwa irin haka ba.”Me kike nufi da kalamanki?Wayarsa da ya ajiye nayi maza na suro na buɗe na shiga WhatsApp na lalubo acc din Latifa sai na miƙa masa. Tun kan ya karba ya fahimci komai.

<< Wa Gari Ya Waya 22Wa Gari Ya Waya 24 >>

2 thoughts on “Wa Gari Ya Waya 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×