Haƙuri nake ba shi bai ce komai ba, har ya sauya kayan jikinsa, ya zauna falo bai min magana ba. Haƙuri na ƙara ba shi sai na shiga ba shi labarin shawarar da muka yanke ta buɗe shagon ɗinki. Amsa min da ya yi yasa na gane ya haƙura, wayarsa ya miƙo min.
"Ga Hajiyar tudun wada, ta kira ni wai in haɗa ta da ke, dan kin kirata bata ji, na amsa sai da muka gama gaisawa da ita da Malam sai na ce ta bai wa su ƴan biyu, suka yi ta. . .