Skip to content
Part 3 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Marairaicewa na yi na ba shi haƙuri, “Sai kin dawo” ya faɗi yana harɗe hannayensa a ƙirji, gifta su nayi na wuce har kuma na isa gidan raina a ɓace yake,

Haj Hajara uwargidan kawu Attahiru ta tarbe ni ta kaini wajenta muka gaisa na bata dambun naman da jallabiya da darduma da turare da nayo ma kawun tsaraba na ce a ba Kawu,Ita kuma doguwar riga da darduma.

Ta ce in zo muje in gaishe da kawun, Sallar alha ya idar na gaishe shi cikin nutsuwa, ya amsa yana ta sa mini albarka ya ajiye kayan ya buɗe cooler ya yi arba da danbun naman, ya maida ya rufe ya ce “Adana min naman nan da kyau Haj” tana ƙoƙarin ɗauka Tahir ya shigo ya ce “Na gani zan ci Baba dama na rabu da ganin ka da shi.

Ya ce “Dama saboda irinku nake cewa a adana min, daga me kawo min bata nan ina za ka gan shi, iyalinka ta kawo min kuma mu cinye tare da kai.”

Kallon mamaki Tahir ya juyo yana min, dan har ga Allah bai taɓa sanin ni ke kawo wa baban nashi dambun nama ba. Kawun yana nuna mishi tsarabar da na kawo masa ni kuma sai na miƙe na koma sasan Haj, duk da zaman kuramen da muke na gwammace in zauna wurinta da in koma gida.

Sai yamma sosai na koma shima Tahir ne ya kira ni ya ce ba zan dawo ba hala can zan kwana.

Sai da amarya ta kammala kwanakinta wanda har aka so ayi fitina dan Uwargida Halima dagewa tayi da ba wasu kwanakin da amarya Latifa za ta yi a cewar ta auren da aka ɗaura wata da watanni shi ne sai tayi wasu kwanaki tun yaushe suka tare.

Halima ta karɓi girkin sai Basma da ya zo kaina sai na kaima Tahir tsarabar da nayo masa, Jallabiyoyi da agogo sai turaren da yake sawa, gyara sosai nayi wa ɗakin dan abinda na lura da shi yanzu babu me gyarawa. Na wanke boxers dinsa a laundry na sake zanen gado na saka ƙamshi.

Muna kwance dare ya soma nisa wasanninmu muke yi yana gab da cimma burinsa sautin wata ƙara ta ya shiga kunnuwanmu, Tahir wanda ya kasa barin abinda yake

na raɗa masa “Ba ka ji anyi ƙara ba?

Ƙyaleni ya yi ya cigaba da abinda yake har zuwa lokacin da aka kuma ƙwalla wata,

ba shiri ya raba jikina da na shi ya sauka gadon jallabiya ya lalubo ya zura da sauri sai ya bar ɗakin.

Cikin kasala nima na sauko kayan barcina na mayar tare da hijab sai na bi bayansa,

saukata kasa na fahimci daga dakin basma karan ke fitowa mun kalli juna da Latifa wadda ta fito ita ma a lokacin, tare muka shiga ɗakina dakin barcinta muka same ta Tahir na riƙe da ita tana fizgewa, idanuwanta a rufe da dafe hannunta a kanta tana fadin “Kaina”

Matsawa nayi kusa da su ina addu’a ina tofa mata, ganin ihun nata ya soma sauki shima ya fara addu’ar yana shafa mata. Da hannu ya yafito Latifa wadda tun shigowarmu ta maƙale a jikin kofa ya ce ta zo ta riƙe masa ƙafafuwanta hannuwanta da kanta gaba daya ta karkada ta ce ba za ta iya ba tsoro take ji.

Bai ce komai ba umarni ya bani inje saman shi in kawo mishi zamzam, da azama na fita na dauko sai da na biya kitchen na ɗauko kofi cikin kofin na juye mishi ina riƙe da kofin yana addu’a a zamzam din.

Ya kafa mata kofin da karfin tsiya ya dura mata ba laifi ta sha, za kuma a dauki wani lokaci ba ta bingire a jikinsa, saukar numfashinta ya bamu tabbacin ta samu barci, sai dai ko ya ya Tahir ya motsa za ta kankame shi.

Latifa ta taɓe baki daga inda take tsaye sai kawai ta juya ta bar ɗakin, maimakon ɗakinta ɗakin Halima ta wuce tana ranƙwashin kofar taji daga ciki tana tanbayar waye

“Ni ce Latifa”

Ta bata amsa a ƙagauce, “Shigo” ta bata izni zaune ta same ta kan kujera, “Hala ba ki ji meke faruwa a gidan ba? a yatsine ta dube ta “Me kika gani?

“Na ga ba ki fito ba.”

Baki ta taɓe

“Me zan fito yi musu su ƙarata can” ita ma bakin ta taɓe “Kin hutar da kanki ganin kayan takaici” kallon da Halima tayi mata ya bata tabbacin ƙarin bayani take nema,

dan haka sai ta gyara zama ta bata labarin ilinbon da Basma tayi dan san kasancewa da Tahir,

anan suka dau lokaci suna la’antar Basma tare da jin dadin bata ma ummulkhairi wannan daren, kafin Latifa ta fito tayi ɗakinta. A wannan daren zan iya cewa sam bamu rintsa ba ni da Tahir muna tare da Basma ina taimaka masa.

Asubar farko ya nemi temakon megidan da ke makotaka da mu muka wuce da ita Hospital, Asibiti ce me zaman kanta. ƙwararrun likitoci suka rufu kanta karshe sun tura mu wurin likitan ƙwaƙwalwa dan dama shi ke dubata dan tana fama da wani ciwon kai me tsanani sai dai yana jimawa bai tashi ba.

a gwaje gwajen da likitoci suka yi sun gano ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta wadda suka ce a guji abinda duk zai bata mata rai dan shi zai tayar da ciwon.

Ni da Haj Hajara muke wurinta idan na wuni ita kuma sai ta kwana, tun ina saka ran ganin yan’uwanta har na cire sai ranar nan naji Tahir na waya ƙarshe na gane yayan Basma ne abokinsa, anan na fahimci basu gari shi da mahaifinta da matar mahaifin nata dan mahaifiyarta bata raye.

Sai a ranar su Latifa suka shigo Hospital din, tunanina gaishe da Basma suka zo ashe wai ganin likita Latifa za tayi, sai da suka gaishe da Basma Latifa ta fita ganin likita,

fitarta ne Halima ke fadin wai ciwon ido Latifa ta ce tana yi shi ne za ta ga likita,da alama akwai tsegumi me yawa a bada labarin nata. Kafin Latifa ta gama ta zo har ta ƙosa da zaman ta sallame mu ta tafi,

sai da Latifar ta gama sai ga ta jin Halima ta wuce yasa ta canza fuska daga ƴar fara’ar da ta shigo da ita. bata ɓata lokaci ba Ita ma ta wuce. Wucewarsu Tahir ya shigo ƴan kwanakin nan har tausayi yake bani dan yanda yake a tsaye da ɗawainiya me yawa akan ciwon Basma,

kunun gyada me kyau wanda na daure da shinkafa na tsiyayo masa yana tururi, ban jima da dawowa daga gida ba, nayo mana girkin sai na damo kunun,

na miƙa masa idan sa na kan Haj Hajara da ta miƙe za ta fita yana ƙara mata godiya kan dawainiyarta, ya maido dubansa kaina bayan fitar ta dan murmushi yake min

hannunsa ɗaya kan sumarshi yana shafawa

“Anya kuwa Ummulkhairi zan iya saka wani abu a bakina? kalaman ban hakuri nayi tayi masa har ya yarda ya karɓa ya kurɓa a hankali yake kurɓa muna fira wadda duk akan ciwon na Basma ne, shigowar likita yasa na ƙara gyara lilliɓina sun yi musabaha da Tahir sai na gaishe shi

Sabon bill na makudan kuɗaɗe ya miƙo masa dan gaskiya a yan kwanakin nan da Basma take kwance ba ƙananan kuɗaɗe ake cajinshi ba. Na dube shi cikin tausayawa yayinda yake jifana da murmushi Mug din ya miƙo min ya ɗauki mukullan motarsa

“Bari inje in sauke Haj a gida ta samu ta ɗan huta, daga nan ina musu transfer kuɗin.”

gyaɗa masa kai nayi na kuma bi shi a baya har wurin motarsa sai da ya ja motar suka bar wurin sai na koma ciki wurin Basma wadda kodayaushe cikin barci take. Zamana ba daɗewa aka turo kofar.

wata hamshakiyar mata ce ta shigo biye da ita wani attajirin dattijo ne sai wani matashi da ba zai wuce tsarar Tahir ba biye da su. Ba tare da sun kula da sannun da nake yi masu ba suka rufe gadon da take kwance,

hankalin mazan tashe yake kwarai, cikin mintocin da banyi zaton Tahir zai je gida ya dawo ba sai ga shi ya dawo ban raba ɗaya biyu ya samu labarin zuwansu ko kuma dama yasan da zuwan nasu, a take kuma na fahimci su ɗin ko su waye

Mahaifin Basma ne da matar mahaifinta sai yayanta abokin Tahir. Cikin matuƙar girmamawa Tahir ya shiga gaishe su, mahaifinta ya shiga faɗin rashin jin dadinsa da aka bar masa ƴar sa anan kwance tun soma ciwon ba a yi ƙoƙarin fita da ita da ita waje ba, dan haka ya ce su je ya ga likitan da ke dubata in ta kama ya ɗauke ƴar sa.

Fitarsu aka bar ni daga ni sai matar sai Basma wadda bata ma san sun zo ba,

ganin kamar zamana ba shi da amfani yasa na miƙe na wa matar sallama wadda ke matuƙar ji da kanta. ta amsa da ƙyar, na fito asibitin na tari me daidaita sahu zuwa gida. mun kusa isa kiran Tahir ya shigo wayata, tanbayata ya yi inda na shiga na ce “Na tafi gida”

Ya ce Amma ame na tafi kuma me yasa na tafi ban sanar masa ba. na ba shi hakuri sannan na ce keke napep na hau. Faɗa ya fara me yasa ban jira direba ba wani haƙurin na kuma ba shi ya ce me zan yi a gida bayan ban daɗe da dawowa ba, na ce na ga yan’uwanta sun zo

ya ce “Haka ne”

Sai ya kashe wayar. nima na mayar da tawa jaka. Bayan na sallami dan adaidaitan kwandon da na kwaso kwanonina na ɗauka zuwa ciki. na wuce ina amsa gaisuwar megadi da direban da dawowar nan tawa na samu ya ajiye yana kai matansa unguwa,

na zo shiga ƙofar da za ta shigar da kai main falo muryar Halima da maganar da naji tana yi yasa ni tsayawa haɗe da saurarawa

“Ai in faɗa miki ƙawata wai hidimar da yake da waccan ta kwance a asibitin itama Latifa ta ƙirƙiri ganin likita a asibitin saboda tana fama da ƙaiƙayin ido, maimakon ta nufi Eye centre a’a wai ita ma can za ta dan asibitin tsada ce da shi ta fitar hankali”

Muryar ƙawar naji ta ce “Musamman da aka ce abin ya haɗa da ƙwaƙwalwa dole za a ji naira, to wai shi dama mahaukaciya ya kwaso? Wata dariyar mugunta Halima ta saki

“Oho masa tana can dai kwance ana illata aljihunsa, ita kuma Latifa ta nemi a yanka mata Glass duk da gaya mata da aka yi ciwon idonta bai kai tayi amfani da Glass ba”

“To ke kuma fa?

ko zama za ki yi ki zuba ido sun zo bayanki suna cin arziki ke an bar ki ƴar kallo”

Haliman ta amsa da “Kin san kuwa waccan matsiyaciyar har ta samu ta sawo labulaye

cikin muryar mamaki waccan ta ce “Wai kina nufin ko labulai bata zo da shi ba?

Haliman ta ce

“E mana, amma fa ni ki bar ƴan wahala ni ba ta hanyar ciwo zan karbi nawa ba, kai tsaye zan fito mishi ya bani rabona” Shewa ƙawar ta saki

“Hakan ya yi ta wajena”

Jin kamar suna tahowa ya sa ni shiga da sallama, kawar ce ta amsa suka raka ni da ido

Sannun ku na ce musu na wuce ciki.

Na daɗe kwance a ɗaki ina juya zancen Halima da kawarta game da ciwon idon Latifa,

Text ɗin Tahir da ya shigo. yana gaya min in karɓi girki ya sa ni miƙewa zuwa kitchen a yanda na fahimta ni kaɗai ce a gidan, sai yamma sosai suka dawo Halima ta fara shigowa can sai ga Latifa wadda ta sha Glass ɗinta banda firar su Halima da na saurara zan ɗauka na gayu ne kawai dan ba karamin armashi ya ƙara ma fuskarta ba.

Ana idar da Sallar isha’i Tahir ya shigo, mun hallara gaba ɗaya muka ci abinci ina lura da shi ba wani me yawa ya ci ba hasalima ba shi da walwala da ka dube shi za ka san akwai damuwar da take damun sa yana kuma kammalawa miƙewa ya yi riƙe da mukullansa sai ya fice,bin shi da ido nayi.

cike da tunanin damuwar da ke damun sa. Ban koma daki ba a falon na cigaba da zama tare da Halima da Latifa, sai ƙarfe goma ya shigo. nayi masa duk abun da ake masa kafin ya kwanta, yana shan black tea da na haɗa masa idonsa na kan TV Latifa da Halima da ke zaune shiru Halima ta gyara zamanta.

“Idan ka kammala ina son magana da kai.” ta fadi sai ta miƙe zuwa ɗaki,

ni da Latifa muka bi ta da ido. shima ya miƙe ya bi bayanta. Jin shiru shiru raina ya soma ɓaci ganin wannan ai cin fuska ne aka yi min, girkin nawa ya tsallake ni su shige daki a bar ni shanye da baki a zaune, wata zuciyar nata zuga ni da in yi ɗaki in datse ƙofata.

wata kuma na bani haƙuri, da na saci kallon Latifa sai na rasa wane hali take ciki ita ma kishin ke mintsininta koko murna take da abin da aka min. Jin tashin muryar Halima yasa mu maida ido wurin. Tahir ya fito a fusace ya haura saman sa, na miƙe dan zuwa in yi shirin barci Halima ta fito tana cigaba da bambanci.

“Wallahi ban zama ka mayar da ni sakarai dan rashin adalci waccan tana kwance kana kisan kuɗi,wata ma ta ƙirƙiri ciwon idon ƙarya dan ta tatseka duk baka damu ba sai ni dan na nemi ka bani kuɗi in kashe matsalar gabana shi ne za ka gaya min bani da tunani to za ka san ban…

Dirowar Latifa gabanta cikin masifa ta katse ta, “Idan kina neman bala’in ki Halima ki kiyaye ni, ni nan da kika gan ni ba kanwar lasa ba ce, dama saka ma ciwon idon nawa idanu kika yi? kina baƙin ciki an mini magani, to sai dai wallahi ya kashe ki”

Nan suka dirar ma juna. kamar za su cinye kansu ni dai da na gama shirina tsayawa nayi jiransu su gama dan kar in je in samu ya rufe kofa dan yanda na ga ya fusata,

ba zan rasa wadda za ta yaɓa min baƙa ba na je turaka miji ya rufe kofa.

Ganin basu da niyyar dainawa na zo gabansu ina basu hakuri ba wadda ta saurare ni kamar yadda na zata maganar da Halima ta faɗi ma Latifa ita ta raba faɗan

An zo tsiya tsiya ba dole a kirkiri ciwon karya a samu na sayen kayan ɗaki,

ga shi nan har an fara samun na labulai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 2Wa Gari Ya Waya? 4 >>

3 thoughts on “Wa Gari Ya Waya? 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×