Skip to content
Part 35 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Takawa ya yi zuwa ƙofarta, ya ranƙwashi kofar shiru ba a buɗe ba, ya ƙara nan ma ba labari ya yi magana ba a buɗe ba. Wajen matan yi juya “Nawa ne kudin? “Dubu dari uku ne.” Kansa ya jinjina “Bani acc no da lambar waya” ya ciro wayarsa ta fada mishi ya sa “Ku je zan yi magana da ita in kuɗin haka suke zan tura maku.”

kwarjinin sa yasa ta kasa mishi musu suka juya, layin wayar Halima ya kira bata ɗaga ba ya tura mata text message Idan bata buɗe ba, za ta sha mamakin hukuncin da zai dauka a kanta.

Nan take kuwa sai ga kofar an bude ya danna kai ciki, ta zauna kawai tayi tagumi da hannuwanta biyu, dubanta ya yi surkullen da tayi mishi yasa shi kasa buɗe baki ya yi mata bala’in da ya kudurta, zama shi ma ya yi sai ya fara mata magana cikin lalama “Wai dan Allah, Halima me kike da kudi? da har wadanda nake ba ki basu isarki sai kin ciyo bashin mutane kin wulaƙanta ni.

A iya zamana dake ban san iya bashin da na biya miki ba me yasa Halima? dan kin san in ba ke din ba, ba macen da zan ɗauki wannan tozarcin daga gare ta. Ya numfasa “Nawa take bin ki? Kamar ba za ta tanka ba ta furta “Dari uku ne” transfer ya yi wanda ya yi sa’a bai samu matsalar network ba, ya kira layin da matar ta ba shi ya ce ya saka kudin.

Ta ce “E yanzu ta ga alert za ta fara godiya ya kashe wayarsa. Duban sa ya kai kan Halima “Na biya ta” sai ya mike ya bar dakin Latifa kawai ya samu a falo ni dama tun da ya soma saukowa na koma kitchen, ina fitowa kitchen din yana isowa mun kalli juna ni da shi na wuce ta gefensa shi ma ya bar falon. Yana zama cikin motar addu’ar da Kawu Attahiru ya turo mishi ya shiga karantawa yana dafe da kansa cikin matukar takaici na tozarcin da Halima ta ja mishi sunayen Allah ya shiga kira kafin ya ji zuciyarsa tayi sanyi sai ya yi wa motar key ya bar gidan.

Halima na ganin fitar sa ta janyo wayarta, malaminta ta kira ta kora mishi bayanin abin da ya faru da tsoron da take kan hukuncin da Tahir zai yanke mata, dan rashin yin fadan sa ba shi zai bata damar sakankancewa ba zai ci mutuncinta ba. Sai da ya gama sauraren ta sai ya yi dariya “Yanzu ya yi miki fadan ko cin mutuncin?

Ta ce “Ba ko daya, sai ma maganar da ya yi min kamar yana rarrashina. Ya ce “To ki saki jikinki, ko uwarsa kika zaga haka za ta kasance, ki yi abin da kike so ba ki da matsala”, dariyar jin dadi ta yi suka yi sallama tana kara jinjina kyan aikin malamin nan a iya kwanakin nan yanda take so take yi a gidan, dan ma wannan matsiyaciyar ta zo ta tozarta ta a gaban kishiyoyi, amma daga miji na hannunta duk wadda ta nemi yi mata maganar banza rufe ido za tayi ta ci mutuncinta, tana nan zaune cikin dakin har lokacin da Laraba ta iske ta ta ce mata abinci ya kammala, mirsisi ta fito ta ci abincin ta duk da wani kallo da Latifa ke mata.

Ni dai ban fito cin abincin ba, wanda nayi na adana abi na na ƙara ci, na shiga kitchen din dan yin girki kamar yanda Ogan ya ce na fara kenan Halima ta shigo “Me kike min a kitchen ranar girkina? Kallonta nayi da kyau “Megidan ne ya ce in yi.”

“Lallai ma da kyau, to ki faɗa mishi sai na karasa girkina a yau ɗin nan dan jiya na fara” ban ce mata uffan ba sai wuƙar hannuna da na ajiye na bi ta gefenta sai na fita kitchen din. Ina komawa daki text nayi mishi na ce zan dan fita ayi min kitso” shi ma sakon ya turo min Girkin fa idan na fita?

Na tura mishi matarka ta iske ni kitchen ta ce sai ta karasa kwana ɗayanta. Jin shirun sa na gane ya bar ni, na ajiye wayar ina jan tsaki, sai da na ƙara kintsawa sai na fito dan samun direba in shaida mishi za mu fita, jawo motar ya yi har inda nake tsaye ina shiga kiran Asiya ya shigo wayata na shaida mata na fito ga inda na nufa ta ce mu haɗu a can.

Dan haka ina zama sai ga ta, gyaran jiki aka yi min sai aka yarfa min kitso, sai daf da magrib na baro wurin. Washegari da wuri na soma shirin karbar girki da dakinsa na soma sai da na gyara komai ya min yanda nake so kafin na shiga kitchen girki na musamman nayi kuma ban yarda na matsa daga inda nayi ba sai da na gama, gaba ɗaya ƙamshin ya bi ko’ina ya isa hancin kishiyoyina, cikin wata drower da ke kitchen din na adana abincin na zare key da ba a cire shi a jiki sannan na bar kitchen din, ko Laraba da Indo ban bari sun ga inda na adana ba. Sai da na gama shiri na na fito na shirya tebur kuma nayi zama na a falon.Ina ƙare girkina na kwana biyu Latifa ta karba…

Na dawo daga islamiya riƙe da littafin bulugul maram zan shigo na haɗu da wata mace da na ji maigadi na ma tambayoyi haɗa idon mu sai wata me kama da Tahir na gani Ina ta tunanin inda na san ta har muka gaisa sannan na tuna Hadiza ce autar su Tahir da aka ce tayi aure Niger fara’a ta ta karu na ce,

“Baba ƙanwar megidan ce” tayi min duban mamaki shi kuma baba maigadin ya shiga gaishe ta na ce ta zo mu shiga ina ce mata “Autar Hajiya yaushe a gari? Murmushi tayi “Sati na guda kenan” ta fadi mamaki kwance kan fuskarta na san bai wuce na yanda ta ga na gwada na santa, na ce “Wa ya rako ki ko kin san nan ɗin?

Ta ce “Na manta nan ɗin, tare da yaya lawal muka zo yana gidan Kawu Attahiru.”

A main falo muka zauna na kawo mata ruwa dan ta ce ba za ta ci abinci ba ta ci gidan Kawu. Mun dade kafin muka fito tare zuwa gidan Kawun na gaishe da Yaya lawal can muka samu Tahir nan na bar ta na ce sai ta zo, suna hira Tahir da Yaya lawal ita kuma ta samu wuri can kasa ta raɓe.

Jin shiru ba Hadiza yasa nayi tunanin ko can za ta kwana har sai da na fito cin abinci sai na gan ta zaune a falo, kusa da ita na zauna ina takalarta da hira na dan jima sannan sauran matan gidan suka fito, ogan ne ƙarshe an zauna wurin cin abinci na ce ma Hadiza taso mu je” girgiza kai tayi na ce,

“Haba dan Allah ki tashi mu tafi” kiyawa tayi har na ga Tahir ya dubi inda muke gane dai ba za ta yarda ba sai na isa inda ake cin abincin na debo mata dan dama ni kam ba ci zan yi ba na kawo gaban ta na ce “To bismillah” ta fara ci tana duba na “To ke kuma fa?

Kai na girgiza. “Ke dai ki ci” ta ci har ta koshi ogan ya fara miƙewa wai kansa na mishi ciwo ya haye sama, Latifa ta take mishi baya, wayata da ake kira na duba Yaya Sani ne, na ɗauka ina murmushi na ce wa Hadiza ina zuwa bedroom ɗina na shiga mun gaisa tare da yar hira sai ya ba matarsa Aunty Rahma muka gaisa hada yaransa.

Kamar hadin baki muna aje waya kiran Yayata Aunty Wasila ya shigo ita kam hira sosai muka sha har tana faɗa min haihuwar ƙanwata Aimana, nayi murna na ce zan turo sako dan na san ba zai bar ni zuwa ba, ta ce dama duka yaushe na tafi muna ta hira har kuɗaɗen wayata suka kare sai na kira ta wani barci da ya shiga idona sai jera hamma nake ita da kanta ta gane hakan ta ce “Bari in barki yar ƙanwata na ji alamar barci kike ji.

Muna ajiye wayar anan na bingire na gyara kwanciya, wani irin barci na shiga yi wanda ban tashi samun kaina sai uku da rabi na dare shi ma wani irin fitsari da tun samun cikina ya zame min jiki bana riƙe shi sam ga yinsa akai akai ya kulle min mara a gigice na mike zuwa toilet ina fitowa ƙofata na zo na duba Allah ya taimake ni ban sakaci da rufe kofar, sallah nayi raka’a biyu sai na koma na kwanta ina karanto addu’o’i bayan na cire kayan jikina, ban jima ba wani barcin ya kwashe ni.

Ta da Sallar Asuba ya farkar da ni na kuwa duro gadon da hanzari duk da jikina ya soma nauyi, ga cikin kullum kara wani irin girma yake. Alwala nayo na zo na kabbara Sallah sai da na idar da Sallah sannan karatun Alkur’ani ya biyo baya, azkar nayi karshe akan sallayar barci ya yi awon gaba da ni, ja min ƴan yatsun kafa da ake yi yasa ni farkawa ina buɗe idona Tahir ne tsugunne gabana, mun kalli juna kafin na yunkura na tashi zaune ina gaishe shi.

“Me yasa in anyi abinci ba ki ci? Ya jeho min tambayar yana tsare ni da mayatattun idanuwansa kumatu na kumbura “Ina dafawa ina ci” “Kina son jawo min wata maganar a gida ko? Ƙara turo baki nayi na ƙi magana “To ki riƙa dai cin abinci kin ga ba ke kadai ba ce.” na daga mishi kai “Zan fita yanzu ki fito ki nemi abin da za ki ci” kan na kuma ɗagawa miƙewa ya yi yana saka hannunsa aljihu kuɗaɗe ya ciro ya miƙo min ina amsa ina neman karin bayani da idona.

“Kin je Sallon ban samu na ba ki komai ba” godiya na shiga yi mishi ya juya sai na bi shi da addu’a. Fitarsa ke da wuya sai na tuna ina son tambayarsa za ni Tudun Wada in gaishe da yan tsofaffin nan in kuma ga ƴan biyu, sai na biyo shi ko hijab din jikina ban cire ba, na ratso falon Hadiza da na gani kwance a kujera ga falon ya dauki sanyin raɓa ga sanyin safiya ta kudundune da hijabin jikinta.

“Hadiza, a falo kika kwana? Na fada cikin mamaki ina kashe A C jin maganata yasa Tahir rage saurin da yake zai fice “Tashi mu je dakina wallahi barci ne ya kwashe ni sam na shafa’a” ta mike “Ina kayanki?

Na tambayeta wata leda me layi layi ya nuna min a bayan kujera dauko mu je na ce mata ina yin gaba ta dauko ta biyo ni, Tahir da ke tsaye cak tun soma maganar mu ya ja ajiyar zuciya sai ya bar wurin cikin sauri.

Muna shiga bathroom na ce ta shiga tayi wanka dan ta ce min ta roki masu aiki ta zagaya bayin su tayi Alwala, wani abu na ji ya daki ƙirjina jin zancenta ta shiga wankan ta bar ni cikin tunani ta fito na dube ta.

“Anya Hadiza? Ko da yake ina zuwa.” Bathroom din na shiga na hada mata turarukan wanka sannan na fito na ce ta shiga ta kara wankan. “To Aunty” ta ce min duk da za ta dan girme ni ko kadan ne.

Wankan ta kuma shiga ta fito sai shinshina jikinta take wai ƙamshin da ta ji tana yi na kai ta gaban mirror na nuna mata mayukan da za ta shafa da wanda za ta shafa ma sumarta da ta wanke gashi me yawa take da shi amma rashin gyara yasa duk ya dankare, sai da ta gama ta buɗe jakar ledarta za ta canza kaya, kayan duk tsummokara ne dan haka na ce ta ajiye su doguwar riga na samo mata cikin kayana na ce ta saka sai na fita zuwa kitchen na ce mata ina zuwa me aiki tana aikinta ni ma ina nawa farfesun kaza nayi sai kwai da na soya, na dafa ruwan zafi na shirya su a katon tray na wuce ɗakina, tare muka karya ta fita da kayan zuwa kitchen ni kuma na shiga gyaran wurin, da ta dawo tare muka ƙarasa.

Ni ma nayi wanka sai muka fita zuwa islamiyya tare, sai da muka dawo muka shiga kitchen ina yi mana girki tana taya ni, Latifa da ke da girki ta shigo dan duba yanda Laraba ke gudanar da girkin dan Ogan ya kusa shigowa ganin mu ta wani sha mur Hadiza ta dauki tray da na jera mana kayan abinci ni kuma na ɗauki jug din dana haɗa mana juice sai muka fito.

“Dakata Malama” Latifa ta fadi da kaushin murya cak! na tsaya sanin da ni take “Ba fa zai yiwu ki rika shigo mana da kowacce tarkace kitchen ba tana daƙuna mana kayan abinci.” Wani kallo nayi mata “Lallai an samu wuri, amma in ba haka ba ke da ba ki buɗe baki kin kira ƙanwar wanda ya ajiye ki da tarkace, ba ki kuma nuna kyamar ta alhali kayan da kike gadarar za a dakuna muku, dan’uwanta ne ya saya.”

Wannan shi ne baki in ka san abin da za ka fadi ba ka san abin da za a mayar maka ba. gaba daya ta taso min tana naɗe tabarmar kunyarta da hauka dan na lura su ɗin yan rainin hankali ne kana kyale su sai su mayar da kai takalmin kafar su. Muka wuce ta ina cewa,

“Wannan da kike gani ta zo kika wulakanta ta maigidan nan zai iya sake ki, ita kuwa ba zai iya sake ta ba, sai ki bar gidan ita kuwa babu me korarta. Tsawar da aka daka min har kamar zan zubar da abinda ke hannuna na daga kai Tahir ne “Wuce zuwa ɗakinki” na wuce Hadiza ta biyo ni.

Wannan kenan abin daure kai bayan abin da ya faru tsakanina da Latifa kan Hadiza, da yamma Halima ta karbi girki Hadiza ta fita mayar da wani mug da muka yi amfani da shi Halima tayi knocking budewa ta sai kashedi tayi min kan taɓa musu kayan amfani da nake sa Hadiza tana yi.

Fitowa nayi sosai ita ma na wanke ta kamar yanda nayi wa Latifa ita ma rasa abin fadi tayi, Tahir na zaune a falon da laptop ɗinsa, namma tsawa ya min na koma daki. Da komawata kuka na ji ina yi kasa daukar bakin cikin nayi, na rasa wa zan kira in fallasa bakin cikin da yake cin raina Aunty Kulu ta faɗo min wayata na janyo ina kuka na shiga rattafa mata Tahir ba wadda zai rika tozartawa a gaban kowa cikin matansa sai ni.

Haƙuri tayi ta bani da kalaman kwantar da hankali da falalar hakuri da sakamakon sa ga duk wanda ya yi shi, ina mata kuka. Muryar Kawu Attahiru na ji yana fadin “Yi shiru ki yi haƙuri ki saurare ni, Uwar alkhairi” shirun nayi ina shashsheka.

“Ki yi hakuri ki rika wa mijinki uzuri kin ji? A duk yan kwanakin nan mafarkinsa nake addu’a kawai nake tayi dan kar ya zamto abin da nake ganin ya zam gaskiya da kuma za ki san a halin da aka saka shi da kin gane ba ƙaramin kokari yake ba wurin kula ki, dan kowacce tsaye take tana son ta karbe shi ita kadai albarkacin addu’a kike zaune har yau an kasa ganin bayanki, ina addu’o’in da na aiko miki ina fata kina amfani da su na ce “E Kawu.”

“To ki ci gaba da izinin Allah za mu ga waraka, ko kin taba jin an ce gaskiyar wane ta ƙare? Na girgiza kai kamar yana ganina “Sai dai ace karyar sa ta kare ko? To in sha Allah nasara na tafe, cikin jikinki sai ta Allah in sha Allah za ki sauka lafiya.” Haka dai ya yi ta min kalaman kwantar da hankali har na ji na nutsu na share hawaye na.

Sai dai ina fitowa falo nayi kicibis da Hadiza ta cire rigar da na bata, ta mayar da kayanta ga lilliɓinta a kanta.

Tana ganina ta sunkuyar da kanta “Ni zan wuce, Allah ya saka miki alheri bisa karamcinki a gare ni, ba zan taba mancewa da ke ba, kin karɓe ni a lokacin da kowa nawa ya juya min baya, domin na cancanci hakan a laifin da na aikata musu.

<< Wa Gari Ya Waya 34Wa Gari Ya Waya 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×