Na taho wurin Yaya Sodangi ne dan ina tunanin so da kaunar da ya gwada min a rayuwa, shi zai iya yafe min, ya dube ni. Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.
Na ce “Ya isa Hadiza, abin da nake so da ke ki yi hakuri, bari in je in samu Yayan naki in….. Katse ni tayi “Dan Allah kada in sa ayi ta cin mutuncin ki, na gode bisa alherinki a gare ni, na gode na gode, za ta fice na ruko ta ina hawaye “Dan girman Allah, ko za ki tafi, ki jira ni in dawo.”
Komawa tayi ta fadi kan kujera tana kuka. Ban damu da hawayen da ya damalmale min fuska ba ballantana in tsaya sharewa na fito dakin. Latifa da Halima na gani zaune a falon, sun dube ni a tare step na fara takawa zuwa sama, ina tura ƙofar ba shi a falon na wuce bedroom din yana kwance rigingine ya dubi sama, ya yi pillow da hannayensa. Motsin shigowata bai sa ya ɗago ba, kukan da na fasa yasa shi tashi firgigit! shedar ya fada zurfin tunani.
“Me kenan kake yi haka Tahir ? Yar’uwarka da kuka kwanta ciki daya ta zo gidanka har ka gwada matanka sun fi ta, ka bari a ci zarafinta kana kallo, ko kana tunanin su akwai wadda ta ta ƴar’uwar za ta zo ta bari ka wulaƙanta ta? Gara ni, na san ni ba komai ba ce a wurinka amma yar’uwarka fa? Koko abin da suke baka, dadin da suke jiyar da kai yasa kake ganin sun fiye ma ita?
Ban san tashin sa ba, sai dai isowar sa gabana na gani ya daga hannu zai mare ni, ko gezau ban yi ba, ya sauke hannun. Cikin zubar da hawaye na ce “Ka mare ni mana ai na saba” janyo ni ya yi sai gamu bisa gado ta bayana ya rungume ni duk da cikin jikina na shiga damben kwacewa ya ce “Ki bari fa, ina irin wannan halin ki bar yi min musu, kin san dalilin da ya sa na share Hadiza?
Shiru nayi Ita ce sanadiyyar samun hawan jinin Hajiyarmu. Lokacin da ta ƙare karatun makarantar unguwar zoma da ke Malumfashi, ta fitar da miji an sa rana bai fi saura wata daya biki ba ta tayar da kayar baya bata san wanda za ta aura kuma kin san waye? Bai jira amsawa ta ba ya ci gaba “Ƙanen Halima ne.” Saurin juyowa nayi na dube shi ya daga kai. “Kwarai Halima da kika sani ta gidan nan, bayan makotaka da ke tsakanin gidan mu da nasu, akwai zumunci ga kuma surukuta Halima na gidan mu, wanda kuma ta kawo ba a ko san asalin sa ba an ce dai mutumin Niger ne, an kada an raya amma yarinyar nan ta ki sai ma ƙara da ta kai gidan Hakimi wai za a yi mata auren dole.
Mun zauna an kafa mata sharadi cewar indai ta aure shi mun bar masa ita, ta ma manta tana da wasu yan’uwa da iyaye, ta ce ta amince, ranar Auren ta Haj ta yanke jiki ta fadi dan duk ta fi tsanar al’amarin muka nufi Hospital da ita inda aka tabbatar jininta ya hau, Haj na Asibiti aka daura Aure, yarinyar nan ko gezau ta bi mijinta suka tattara a ranar ya dauke ta suka bar garin.
Bayan fitowar Haj da ganewar da tayi yar’autarta ta tafi ta shiga wani hali jinin da aka samu ya sauka ya kara hayewa, dole muka mayar da ita Asibiti. Da kyar muka samu Haj ta hakura ta rungumi ƙaddara. To me za mu yi da Hadiza? Ni me zan ce mata? Nisawa nayi lallai bata kyauta ba, amma hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar, haka nan za ka yi hakuri.”
“In na ce miki ban ji dadin ganin ta ba nayi karya amma dole in yi mata abin da nayi mata dan ta gane abin da tayin, duk da dai da ganin ta duniya ma ta biya mata karatun.” Ji nayi ya zura hannunsa cikin rigata, ga kansa ya sanya saman wuyana yana sunsuna ta, jin ya sanya jikina shiga wani hali yasa na fara kiciniyar kwacewa sai dai da alama ya soma nisa riga ya cire min yana gaya min maganganu cikin fitar hayyaci, “Kina cikin abin da nake matukar so Ummulkhairi, ke wata aba ce me daraja a wurina, bana so kina shiga cikin fadan da ake min a gida, a duk lokacin da na ga ana yi da ke, na fi jin zafin naki, saboda matsayin da kike da shi a zuciyata.
Ki taimake ni in samu kwanciyar hankali ta bangaren ki.” bai bani damar magana ba yasa bakina cikin nashi. Nayi mugun kaduwa ganin abin da yake shirin aikatawa sai dai bai yin ba, gama jagulani ya yi ina mishi kuka daga bisani ya tsallake ni ya shiga bathroom, na tashi zaune ina lalubar rigata tuna Halima za ta iya shigowa dan na shigo mata a ranar aiki yasa ni ciccibawa sai ga shi ya fito, ba tare da na dube shi ba na ce “Ga ta can fa za ta tafi.”
“Kina nufin Hadiza? Na daga mishi kai na sa kai dan barin wurin, na soma taka step na ji shi bayana tun fitowar mu Halima da Latifa wadanda dama zaman da suke hankalinsu na gare mu da Halima ta ce ita fa za ta je ka ta gani ka da aci amanarta, sai Latifa ta hana ta ta ce “Ke ba ki ga da yanda ta tafi ba, daru za su kwasa mu kuma mu sha kallo, yanzu ko kina zuwa ƙarshenta fadan ya koma kanki.”
Ganin yanda muka fito sai ya kulle musu kai Halima ta mike tsaye ta zura mana ido mu kuma muka wuce su zuwa ɗakina. Mun tarar da Halima zaune tana ta razgar kuka wani kallo da Tahir ya yi mata yasa ta zama sosai ta hadiye kukanta “Ke yanzu kina da bakin kuka ko? Mu kin manta sanda kika tafi kika bar mu muna namu kukan?
Ina sane na bar ki a gidan ana nuna miki iyakarki, ban da wannan, ya nuna inda nake tsaye “Da ta je tana min koke koke, barin ki na so yi sai gama gane kuranki, ban da kina Shashasha Namiji za ki zaba ki bar uwar da ta kawo ki duniya? Kika tafi kika bar Hajiyarmu, kin san halin da ta shiga bayan barin ta da kika yi?
Ita dai kuka kawai take ni ce nake bada haƙuri “To yanzu da kika tashi kankarar za ki koma ki karasa mana uwa, koko inda kika fito za ki koma? Ya ja dogon tsaki sai ya juya ya bar dakin. Ina ta bata haƙuri ta share hawayen ta, “Na cancanci duk abin da za su yi min, bayan na tsallake na bi Rabe, bamu zame ko’ina ba sai magarya da ke karkashin yankin Damagaram a ƙasar Niger.
Zaman wata uku muka yi ya tsallake ya bar ni wai ya tafi neman kuɗi ya bar ni tare da iyayensa da yan’uwansa wadanda suke nuna min banbanci ƙarara bayan wahalhalun ayyuka da nake na mutanen ƙauye wanda ban saba ba, kafin ka ce me na canza na fita hayyacina, sai da ya shekara biyu ya juyo, da ya dawon wata guda ya yi ya kuma komawa, yana kara dawowa ya dawo da shirin auren yar’uwarsa nan fa gaba ɗaya suka juya min baya ba a riga an yi auren ba mahaifiyarsa ta ce ya sallame ni, ba bata lokaci ya yi min saki uku da kyar na sai da wata akuya da diyarta da na mallaka na kamo hanya zuwa gida.
Jinjina kai nayi cikin tausaya wa wannan kaddara ta ta. na ce “Ki yi hakuri kaddara ce, ke taki kaddarar haka ta zo ki yi ta addu’a har yan’uwanki su sauko su yafe miki”. Ta share hawaye “Tun dawowata ƴan’uwana suka sani gaba, Haj kuma hawan jininta ya tashi ganin yanda na koma, yaya Lawal ne kawai bai zafafa min ba yake tausayina ganin halin da na ke fuskanta yasa ya ce in shirya ya kai ni gidan Sodangi, kila can zan ɗan fi samun sakewa har komai ya daidaita.
Shi ne ya rako ni. Na ce “Ki saki ranki ki yi hakuri, In sha Allah za su haƙura suna nuna miki kuskurenki ne, dan Allah ki cire kayan nan.” Ta tashi ta cire ta mayar da wadda na bata. Halima suna shigewa ta tashi ta haye upstairs cikin sassarfa ta faɗa bedroom ganin yanda aka yamutsa shimfida ya kara daga hankalinta.
Nazarin gadon ta shiga yi har zargin ta ya tabbatar mata da an yi abin da take gudun, kuka ta fasa ta fadi dabar tsakiyar ɗaki wani kishi ya tokare mata kirji. Kamar an zabure ta sai ta miƙe wurgi ta shiga yi da duk abin da hannunta ya hau kai kafin ta yayo zanin gadon ta yo ƙasa tana kuka. “Wallahi ba zan yarda da wannan cin amanar ba a ranar girkina a kwanta da wata, to wallahi ta fito ko ni ko ita a gidan nan.
Kalmomin da suka shige kunnen Tahir kenan da fitowarsa daga dakin Ummulkhairi. Zanen gadon ta wurga mishi a fuska “Ni za a yi ma cin fuska a wulakanta? To wallahi ba a haifi ƴar ba.” Duban sashin da Indo me aiki ke goge goge, Laraba na shirya abinci, ban da Latifa da ke zaune cike da jin dadin wannan Film me daɗin kallo.
Takowa ya yi inda take mu je dakina” fizgewa tayi tana ci gaba da maganganun da basu dace ba, Please ki yi hakuri mu je dakina.” ya kara rokonta akaro na biyu dan ba abin da yake gudu irin kanwarsa ta ji dan dai masu aiki ta gama wulaƙanta shi gaban su. Sai dai fatan shi bai ci ba dan Hadizar ya gani tana kokarin komawa ciki ta karfin tsiya yake jan ta amma ta kwace saman ya haye ganin yanda ta maida mai daki ya kara tunzura shi sai ya sauko “Kin kure hakurina Halima, dan haka na datse igiyar aurena biyu dake na sake ki Halima pen din da ta ga yana kokarin cirowa yasa tsayawa cak daga iface ifacen da take.”
Ko zuciyata bata da kashi ya kamata in ji zafin abin da kike min, kuma ko ke ɗin ta gwal ce ya kamata in hakura da ke. Dan haka na datse igiyar Aurena da ke. Wani ihu ta yanka tana faɗin ta bani ta shiga uku.