A ranar dai gidan shiru ya yi kowacce ta nabba’a ɗakinta. Maigidan kuwa ba wadda za ta ce ta san lokacin da ya shigo, Halima ma ɗakinta ta shiga ta datse ta kira malaminta da daukar shi kuka ta fasa yana tambayar lafiya?
Ta ce “Tahir ya sake ni” jimami ya shiga kafin ya ce “Aikin Mijinki yana da wuya, domin yana da tsayuwar dare, ba kowane lokaci ake samun sa’a akansa ba, idan ma an dace ba a wani daɗewa abin zai warware” ta gasgata abin da ya ce domin ko’ina ta je hakan ke faruwa “To yanzu ya zan yi” ta tambaya cikin marairaicewa. Wani aikin za mu ɗora, amma fa ki sani haka za a yi ta yi, muna yi ana warwarewa, dan na ga ma akwai wani tsaye kansa.
Da sauri ta ce ƙanen mahaifiyarsa ne, shi ya rike shi, sai kishiyar tawa cikin sai girma yake, so nake ya zube, kuma ayi mata saki uku. “Ba ki da matsala, duk da dai ita ma yarinyar ba a zaune take ba” Halima ta ce “Haba ko da na ji amma shan gabana a wurin Tahir ai da mamaki indai ba asirin ba.” “Za mu yi iyaka kokarin mu, za ki turo kudin aiki kamar na wancan karon.
Suka yi sallama. Da safe Tahir ya nemi ganin mu a falonsa, mun hallara ya shaida mana shi ya kammala course ɗinsa, dan haka gobe idan Allah ya kaimu zai koma Lagos tare da Ummulkhairi, da ƙanwarsa Hadiza. Daga Latifa har Basma shiru suka yi dan ba fuskar da za su a mayar da abin da ke ransu. Yana gama fadi yasa kai ya fice kowacce ita ma ta mike zuwa ɗakinta, sai dai suna shigewa Latifa ta fito daga nata dakin ta faɗa na Basma bayan tayi knocking Basman ta taso ta bude mata, a hannun kujera ta zauna.
“Yanzu Basma haka za mu zura ido ayi mana wannan rashin adalcin, sai a ce da waccan yarinyar zai fara tafiya? Baki Basma ta taɓe. “To ke yanzu ba fa tafiyarki aka dauka ba, idan ma ya ce girma zai bi daga na har ke ba wadda za a ɗauka.”
“In ji wa? Latifa ta tambayeta da sauri ba tayi magana ba sai zura mata ido da tayi. “To tun jiya kika koma uwargida, dan an yanka wa Halima red card, lallai Basma ke duk wannan buduri da aka sha ke kam me kike? Mamaki Basma ta ji a cikin ranta amma bàta bari fuskarta ta nuna ba. “Shi kenan ya kike so mu yi yanzu? Ta tambayi Latifa.
“Yawwa” Latifa ta muskuta Kawu Attahiru ,za mu kira kin san ba wanda Sweety ke jin maganar sa irin sa, sai mu fada mishi.” Kafada Basma ta kaɗa “Shi kenan” “Yawwa to mu kira shi yanzu” cewar Latifa “Ba ni da lambar shi ni dai” in ji Basma, “Ni ina da ita” Latifa ta fadi tana danna wayarta.
Ta soma kira ya dauka, sai da ta gaishe shi sai ta mika wa Basma ita ma ta gaida shi, sai ta amsa tayi mishi bayanin abin da Tahir ke shirin yi na daukar Ummulkhairi zuwa Lagos.” Haƙuri ya bayar ya ce zai ma Tahir magana. Godiya Latifa tayi sai suka yi sallama. Ta mike ta bar dakin tana kitsawa a ranta, ko da ba yanda za a yi tafiyar ta faɗa kanta kasantuwar ta ta karshe, amma da dai ta bari Ummulkhairi ta tafi ta gwammace wannan huhun ma’ahun ta tafi.
Tahi gr na kwance rigingine cikin tunani ya ji kukan wayarsa. Sai da tayi har ta tsinke bai tada kai ba, jin ta kuma ɗaukar ɓurari yasa ya tashi a fusace ya kashe ta gaba ɗaya sai sunan Babana ya gani yana yawo kan screen ɗin, ajiyar zuciya ya fidda kafin ya daga bakin sa dauke da wata makalalliyar sallama jin yanayinsa yasa baban yi mishi nasiha kam muhimmancin hakuri kafin ya dora da tambayar sa dalilin sa na daukar matarsa ta uku a farkon tafiya. Bai ɓoye mishi ba ya ba shi labarin rabuwar sa da Halima. Jimamin sa ya nuna kafin ya fadi mishi.
“Su mata haƙuri ake da su ba a biye masu, amma yanzu ya yi adalci a tsakanin iyalan nasa, ya fara tafiya da babba, daga nan sai ya soma canji. Bayan doguwar nasiha sun rabu.Sauka kasa Tahir ya yi ya kuma tara iyalin nasa, ya ce Tafiya yanzu ta koma kan Basma, dan haka sai ta shirya zuwa gobe. Kuɗaɗe ya miƙo min, ki samu lokaci ku shiga kasuwa da Hadiza ta sayi kayan amfanin ta. Ya kuma miƙo min wasu “Wadannan kuma anjima za a kawo mata suturu, idan kun fita sai ku bayar da ɗinki. Godiya sosai nayi masa kamar ni ya yi wa.
Ya ciro wasu kudin ya bamu ni da Latifa, Halima da ke leƙe ta kafar mukulli ta janye tana jan tsaki. Da ya mike dakin Halima ya shiga ya ce zaman me take mishi bayan ya sake ta? Ta yi shiru ya ce “Ai dama gadarar mace da duk wani rashin arziki da za ta yi maka idan ka ce kana yi ne da ka ce ba ka yi ka datse igiyar shi kenan dan haka ban san ki ƙara kwanar min a gida. Ya sa kai ya fice.Tilas a ranar ta fakaici idon kowa ta bar gidan. Na koma daki na nuna ma Hadiza kuɗaɗen da dan’uwanta ya bayar a kai mata ɗinki da sayayyar da ya ce a yi mata.
Can da rana kuwa sai ga Jakunkuna biyu cike da kaya na zamani, muka yi ta dubawa ni da ita cikin jin daɗi, ita kam har tana ƙwalla, ta ce min mu dan saurara da kai ɗinkin a ɗan kwana biyu ko za ta dan yi kumari. Na ce “E hakan ma ya yi, amma za mu je Sallon a gyara miki kanki. Washegari Tahir suka wuce shi da Basma. Na mayar da hankalina wurin gyara Hadiza, sati daya muka dauka sai da ta sauya, muna waya da Tahir sosai kullum abin da yake gaya min in kula da kaina in kula mishi da cikin jikina. Sai yanzu na gane ba ƙaramin so yake wa ƙanwar tasa ba, baya nan amma kuɗi kawai yake kashe mata, bayan rantsatstsiyar wayar da ya saya mata kullum kuma cikin tambayarta me take so yake kwanaki goma da tafiyarsa aka maido Halima wadda wasu dattawa maza suka maido ina barci lokacin sai bayan na tashi Hadiza ke bani labari.
Da muke waya da Maman Ummi kuma take labarta min ai jama’a kala kala aka yi ta tura wa Tahir da Hajiyarsa da yan’uwansa, dan ya mayar da Halima, Tahir kuma ya ja ya kafe ya ce sam, har yan’uwanta aka tada zuwa Lagos suka ba shi haƙuri amma basu ciyo kansa ba, karshe dai Kawu Attahiru ya rarrashe shi, wanda sai da ya yi wa Halimar faɗa sosai kan ta gyara zamantakewar ta da mijinta, wannan shi ne na karshe da zai tursasa Tahir a kanta. To ta dai samu ta dawo amma bata da hus a gidan ko habaice habaicen Latifa ya ishe ta, dan ma bata cika zama ba.
Saura kwana biyu zuwan Tahir sai ga Aunty Laila gidana. Tun da muka yi waya ta ce sun shigo garin na fita harabar gidan ina dakon isowar su, direban da ya kawo ni ne ya tuko ta. Motar na tsayawa na nufe su, zan rungume ta ta rike ni tana kallona “Haka kika zama? Na ce “Kai Aunty laila, za ki fara daga zuwan ki? Muka wuce ciki riƙe da hannun juna mun shiga falon ta coge tana kare mishi kallo ina “Aunty Laila zo mu je” ta kama ƙugu “An gaida Namijin duniya, wato memakon ya yi wa kowacce part ɗinta, sai ya tara ku a falo daya yanda za a gwabza kishin da kyau a kansa yana kallo, da kyau jarimin maza.
Na kamo hannunta “Zo mu je Aunty Laila” Latifa da ta fito daga kitchen ta dube mu, Halima ma da ke daukar ruwa a fridge ta saci kallon mu, su kansu daga duban Aunty Laila sun san ita ɗin bata wasan yara ba ce, ta girmi duk wata wayewa tasu.Washegari na tambayi Tahir muka fita zuwa gidan Asiya, wuni me daɗi muka yi a gidan ta, dan tuni su ukun sun saba, Hadiza Laila, da kuma Asiyar. Har Sallon muka biya aka wanke min kai ni da Hadiza, na so yin kitso yamma tayi daga na lura Tahir na so. Ranar da Tahir zai zo bayan Hadiza har Aunty Laila sai da ta taya mu yi mishi ƙayataccen girkin tarba, na kuma zage na gyara mishi wuri nasa ƙamshi.
Duk da nayi wanka me kyau na tsala kwalliya sai dariya Aunty Laila take min, “Wai wannan tulelen cikin shi zai bata amarcin da za a sha yau. Baki na tura “Ba abin da zai hana.” Na fadi a hankali ban tunanin ta ji ba sai dariyarta na ji.”A dai bi a hankali Hajiyata.
Jin bude get yasa ni leka window, motar da na ga ta shigo na ji dadi ya lullube ni, ban motsa ba har sai da na ga fitowarsa ya yi kyau ya hadu karshe cikin shigar kananun kaya, glass ɗinsa na manne idonsa. Basma ma ta fito mai wanki da me gadi na ta fito da kaya, “Wai me kike kallo ne? Aunty Laila da ta ji na dauke wuta ta taso dan ganin me ya dauke min hankali ganin Tahir dariya tayi.
“Amarya ango ya iso kenan? Harara na bata ina ɓata fuska Na ce “Allah Aunty Laila kin sa ni a gaba” na daga kafa zan bar dakin ta ce “Sai ina? Na ce “Ta ran Oga” ruko ni tayi “Dan saurara Hajiyata, sai sun gama zuwa sai ki je karshe kai gyaɗa mata sai na koma bakin gado. Tsadaddun turaruka masu sanyin ƙamshi Aunty Laila ta shiga sa min tana kara gyara min zaman rigata.
Atamfa ce ɗinkin riga da zane da suka zauna ga cikina ya bi jikina ya zauna das. Nayi kyau a yan satikan nan, dan na samu lafiya ga kwanciyar hankali da gidan ya samu kwana biyu ba fitina, daidai da Hadiza ta murje har mamakin yanda ta koma nake cikin kankanen lokaci. Tana can kitchen tana tsaron abincin mu dan yanda Latifa ke ta shiga tana fita. Da shigowar sa falo ya zauna iyalai na kawo gaisuwa, Basma ta wuce ɗakinta. Takalmi na saka na fito Tahir na zaune a kujerar da ke kallon ƙofata, idona na lumshe kafin na buɗe su fes akansa wata kaunar sa da son kasancewa tare da shi na sauko min. Shi ma kallona yake har na karaso, na zauna ina gaishe shi kafin na miƙe zuwa kitchen ganin ba wadda ta kawo mishi ruwa ruwan na hado inda na tarar da Hadiza kallona take.
“Kin yi kyau Aunty” murmushi nayi “Kyau Hadiza da wannan katon cikin? yar dariya tayi “Da gaske Allah kin san ai ba ma wasa” na ce. ” To shi kenan, gara ki fito ki yi wa yayanki barka da zuwa, sai mu fitar da abincin. Ta amsa sai ta miƙe tana bayana muka fito ya fara shan ruwan suka yi ido huɗu da Hadiza murmushin sa me tsada da ba koyaushe yake yi ba ya saki “Dan Allah Hadizata ce ta koma haka? Lallai dole in yi miki babbar kyauta, Ummulkhairi.”
Hannunsa ya mika mata ta kama ya zaunar da ita gefensa na dama dan Latifa na zaune a gefen hagunsa. Halima dai a one sitter aka dake an zuba tagumi, da murmushi a fuskata na koma kitchen Abincin na soma fiddowa Hadiza ta isko ni tana taya ni. Na ce “Ban fa faɗa maka ba Aunty Laila ta zo tana gidan nan” fuskarsa ce ta washe “Dan Allah? amma ba ki kyauta min ba, da ban yi wa Ahmad godiyar zuwa mana baƙunta ba.
Ya mike “Bari in je mu gaisa” matansa gaba ɗaya suka buɗe baki suna mamakin ita wannan baƙuwa wane irin muhimmanci take da shi. Sai ga ta ta fito fara’arsa ta karu suna ma juna Barka da zuwa sun gama gaisawa ta faɗa mishi Ahmad na Kano sai ya dawo zai biyo su tafi tare.
Wayarsa ya zaro Ahmad ɗin ya kira sun gama wayar na ce “Wanka za ka fara yi ko abinci za ka fara ci? Idanuwansa ya lumshe “Zan fara wankan” ya mike ya fara takawa zuwa sama zan bi bayansa Aunty Laila da ta mike ta fara tafiya zuwa ɗaki ta kira ni mun shiga a tare wata yar kwalba ta ciro “Yi maza ki dan shafa kadan” dan matsawa nayi “Me kuma za a yi yanzu da rana? “Ba mu da lokaci ki yi yanda na ce idan kika dawo sai mu yi magana” fuska na narke “To bari sai dare ” juyawa tayi na ce “To bani” ta miƙo min bathroom na shiga na shafa sai na fito. Ban same shi falo ba sai na wuce bedroom Ya cire kayan jikinsa, daga shi sai boxers hannayensa dafe da kansa yana zaune bakin gado. Na ce “Yi hakuri na bar ka zaune kana jirana” jin shuru yasa na ce “Lafiya? / idanuwansa ya bude wadanda duk sun kada ya ce “Kaina ke ciwo” saurin zama nayi gefensa jikina har rawa yake ina jera mishi sannu, na yunkura dan samo mishi magani na ji ya ruko ni, jikinsa ya sanya ni, ajiyar zuciya ya shiga fiddawa mun dan jima a haka kafin ya mike ya shiga wanka sai na sauko kasa latifa kawai ke zaune sai Hadiza da na san gadin abincin mu take.
Ba jimawa ya sauko sai a ka ci abinci basma ma ta fito aka ci tare da ita anan na yi mata sannu da hanya Latifa dai fuskarta kamar hadari ta daure ta tamau idanuwanta sun kada cikin tabaranta.
Halima kallon da ogan ke mata yasa ta barin falon ta gudu dakinta. Ko da aka kammala kowa ya bar falon sai Tahir da ya kira kanwarsa suna hira. Dakina na koma na hau gado muna hira da Aunty Laila kiran salla da aka fara yasa mu mikewa sai ga Hadiza ta shigo duban ta nayi Yayanki fa? Ta ce ya fita zuwa masallaci ” gyada kai nayi munyi sallah na gyara fuskata, muka fito na shiga kitchen tuwo nayi niyyar yi wa Tahir sanin yana so, dan Basma ban ma yi tsammanin ta iya ba.