Skip to content
Part 38 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Tahir daga masallaci wanda tare suka fito da Kawu Attahiru, shi ma Kawun jiya ya zo. Gidan Baban suka wuce, falonsa na musamman suka shiga. Duban dan nasa yake cikin tsantsan son da yake mishi,

“Ya ka samu gidan naka? Murmushi Tahir ya yi yana shafa sumarsa “Lafiya Baba Alhamdulillahi” murmushi Baban ya taya shi yana jin daɗin farin cikin da ya ga dan na shi ciki. Haj Hajara ta shigo da kwanonin abinci, Tahir ya shiga gaishe ta tana tambayar sa saukar yaushe? Da fitar ta baban

Ya ce “Sauko mu ci abinci.” girgiza kai ya yi da murmushin da ya ki barin fuskarsa “Na ci abinci Baba.”

Baban ya shiga cin abincinsa, “Yaushe za ka koma? “Kwana biyu kaɗai zan yi Baba.” “To yanzu da wa za ka koma? Kai tsaye ya ce “Da Ummulkhairi” murmushin su na manya baban ya yi “Ba ka mayar da uwargidan ka ba? Bai yi magana ba sai kallon baban da ya yi “Da ita za ka tafi” ɓata fuska ya yi sosai bai yi magana ba. “Ba na so ka bari iyalinka su fahimci wa ka fi karkata a kanta, ka bar komai a ranka, duk kan su kai ka ajiye su, ka yi kokarin kwatanta adalci a tsakanin su.”

Sai da ya ji baban ya yi shiru ya fara magana “Ina iyaka kokarina Baba, ba wai rashin adalci yasa zan tafi da ita ba a wannan karon, na ajiye Halima a gefe na bar ta sai ta gane kurenta, rai fa tana son me kyautata mata Baba, yanzu zuwan Hadiza ba wacce ta saurare ta hasalima a falo suka watsar da ita.

Ita ta ɗauke ta zuwa ɗakinta, ba wacce bata ci mata mutunci ba saboda Hadiza, ni ma sai da ta same ni da kukanta kan na wulaƙanta yar’uwata har ga shi na bada dama matana na wulaƙanta ta. Kai dai baba ka san yanda ta rike Hajiyarmu a zamanta ƙanƙara, yanzu haka ita ta tunasar da ni har hankalina ya kai kan yanda ƴan’uwana na gida ke rayuwa, taimakon da nake yi musu kullum cikin yi min addu’a suke.”

Baba da ke ta murmushi ya ce “Ni ma na ce Allah ya shi mata albarka, ka samu mata Tahir, irin wadda ko wane Namiji ke fatan samu ta so ka kai da kowa naka ta so ka a kai din take so, ba kaɗan na ji daɗin samun wannan alheri da kayi ba, dan mace ta gari ita ce rabin addini, ka samu sai kayi ta kokari yanda za kayi adalci a tsakanin su, amma yanzu ka ɗauki babbar ba sati uku bane?

Ya gyaɗa kai “Jiya na zo da addu’ar nan ta ruwan zamzam sai ka je mata da ita, zumar ce dai ba a kawo min ba har na taho, daga me kyau a ke so” Tahir ya yi godiya ya ce zai sanya a cincika mishi zumar a nan. Sun jima suna tattaunawa har sai da suka je sallar magrib suka dawo sannan ya yo gida. Ina karakainar shirya abinci, Latifa ta kunna mp 3 a falo tana ta cashe rawarta, sai shilla dan kwankwasonta take, tana juya yan ƙananun mazaunanta masu kama da mara tana wakar.

“Mu dai igiyar mu uku uku zama dam zama dam. Ba zato sai shigowar Tahir muka gani ji nayi kamar in saki dariya dan yanda masu igiya uku aka yi wuri wuri, ai kau faɗa ya rufe ta da shi yana fadin ba ya son wannan shashancin za ta kunnawa mutane kida tana rawa, ya wuce sama.

Sai da ya dawo sallar Isha’i aka zauna cin abinci, Halima bata fito ba sai da aka kammala yasa Latifa ta kira ta, sai da ya daure fuskarsa tamau bai taba dariya ba, kafin ya ce “Kwana biyu zan yi, jibi zan koma dan haka Ummulkhairi za ta yi girki yau, Latifa tayi gobe, jibi za mu wuce tare da Halima.” Cikin ladabi Halima ta amsa ta mike ta koma ɗaki.

Tana shiga kujera ta faɗa wani irin farin ciki ke ɗawainiya da ita, wanda ta rasa da wa za ta raba shi sai ta kira malaminta, tayi mishi albishir ɗin za a tafi da ita Lagos. Ya ce aiki ya yi mata sosai wanda yanzu ma akwai kuɗaɗen da za ta bayar dan a ƙara kama shi da kyau. Suka ajiye waya tana tunanin inda za ta samu kuɗaɗe dan ajiye tan nan da Tahir ya yi ba ƙaramin jin jiki take yi ba duk dan abin da take da shi ta miƙa wa malamai, sarkarta da Tahir ya saya musu ta fado mata ita kawai za ta kai kasuwa a bata kudinta, ta san yanzu da sun shirya kudi ba za su zama matsalarta ba. Ni ma Halima na tashi na mike zuwa ɗakina, wanka na faɗa Aunty Laila na zaune kan gado Hadiza tana falo ta ki shigowa ciki wai kar ta takurawa baƙuwa.

Na fito na zauna gaban mirror ina yan shafe shafe na, sai da na ji na dauki ƙamshi kafin na zura rigar barci doguwa har ƙasa, duk da take mara nauyi ba me bayyana surar jiki ba ce, hijab na sa iyakacin sa ƙirjina, na jawo kujerar mirror na zauna ina fuskantar Aunty Laila “In dan ni da kin yi tafiyar ki Mrs Tahir.”

Girgiza kai nayi “Kina sa ni jin kunya Aunty Laila ni barci nake ji, sosai nake cikin gajiya” “Ai kina ma kokari cikin ya yi girma” kwalbar dazu ta ciro “To dan ƙara gogawa” fuska na bata “Abin ma ko tausayi Aunty Laila, so kike a kashe ni” “Da dai kin karba, dan wallahi za ki zo da kudinki kina roƙo na in nemo miki shi, abin nan ina me tabbatar miki ko matar gwamna aka siyar mawa ba za a ji kunya ba, kin samu a arha kina wani basarwa.

Na ce ” Ba haka bane Halin da nake ciki za ki duba Aunty Laila” ƴar dariya tayi “Ni dai yanda na ji masu ciki ma sun fi son abun” kare fuskata nayi da hannuna na mike ta kara miƙo min kwalbar na amsa na shige cikin bathroom na shafa kadan dan fari ne kamar mai. Ina fitowa ban ko dubi inda Aunty Laila take ba na fice dakin, sai da safe nayi wa Hadiza har lokacin Basma da Latifa na zaune tare Tahir, kallo ɗaya nayi wa inda suke sai na wuce su na haye sama. Shigata kwanciya kawai nayi dan ba abin da nake so irin kwanciyar, ban sa ran shigowar Tahir a lokacin ba sai dai ina fara lumshe idanuwana na ji shigowarsa shirin barci ya yi kafin ya hawo gadon bayana ya kwanta ya rungumo ni ta baya yana shafa cikina “Cikin nan ya yi girma da yawa, ko dai yara biyu za ki haifo min?

Da sauri har ina kaɗa hannu na ce “A’a daya ne” Duk yadda na so yin barci Tahir bai bani damar haka ba, wahala sosai ya bani har na ga kamar ya manta da cikin jikina. Dan haka ina idar da Sallah nayi niyyar guduwa ɗakina dan rama barci ko da yau zan koma Asibiti shigowarsa daga masallaci ya hanani umarnin in hau gadon in kwanta ya bani, sai da ya kare azkar ɗinsa ya hawo ya kwanta ya rungume ni ta baya muka shiga barci. Karfe Tara na safe na farka gabana ya fadi lokacin da na dubi agogon, tuna ina da baƙuwa ban je na ga halin da ta tashi ba, kokarin tashi na fara yi ya ƙara kwantar da ni a hankali na ce “Lokaci fa ya tafi” idanuwansa ya buɗe “Ina za ki?

“Ban duba Aunty Laila ba, kuma yau zan koma Asibiti” Bathroom ɗinsa ya nuna min “Shiga nan ki yi” ban cika son in ta yin musu da shi ba, dan miƙewar kawai nayi na shiga wankan na fito daure da tawul dinsa, na shafa man sa duk yana kwance ya yi matashin kai da hannuwansa yana kallona, narai narai nayi da fuska, shi kuma ya mike inda jakar da ya zo da ita take wata doguwar riga me matukar kyau kalarta danyen kore gaban kirjin caccabe da kwalliya ya miƙo min na sanya ba kaɗan ta karbe ni ba, damma katon cikina nayi rolling da gyalen rigar. Sai da ya gama kallona ya mike zuwa Bathroom “Ki shirya mu je Hospital din, idan muka kammala breakfast” kai na gyaɗa mishi.

Ban yi mamakin ganin matan gidan su duka uku a falon ba, daki na wuce bayan na hada su nayi musu jam’un gaisuwa, zaune na samu Aunty Laila na zauna kusa da ita “Har kin tashi Aunty Laila? “Ba dole ba daga kin gudu ba dole mu nemawa oganki abin breakpast ba”. Ido na buɗe “Kai Aunty Laila dan Allah ha da ke a shiga kitchen? “Allah kuwa ki je ki samu Hadiza tana kitchen din” na juya sai na isa kitchen din, cikin mutunta juna muka gaisa da Hadiza muka kuma gaisa da Laraba da Indo.

Mun jera abincin Ogan ya fito bayan an gama karyawa ya ce in je in shirya na samu Hadiza da Aunty Laila a ɗakina suna karyawa, fuskata na shiga gyarawa na canza doguwar rigar zuwa less, Aunty Laila za ta je unguwar Rimi wurin wata cousin dinta tare za su da Hadiza ni ma dan saboda Asibitin da zan koma da tare za mu, kiran Tahir da ya shigo wayata yasa ni miƙewa dama na kammala na sallame su na fito har ya zauna cikin motar, na zauna a front sit Ina satar kallonsa dan sosai ya min kyau.

Yana tare da ni har aka yi min awon ya dauko ni maimakon mu koma gida, gidan da yake ginawa ya wuce ya shiga da ni ko’ina sosai na sha mamakin irin ginin da ake tamfatsawa Naira kawai ake ba kashi. Daga nan sai wani wurin shakatawa muka dan huta sai yamma ya dawo da ni dan ko shiga bai ba sauka kawai nayi ya juya kan motar.

Na samu su Aunty Laila sun dawo. Washegari Tahir ya koma tare da Hali dubu kafin wucewarsa kuɗaɗe masu yawa ya bani ya ce in saya ma Aunty Laila tsaraba a ranar Asiya ta zo muka wuni. Sati guda Aunty Laila ta yi mijinta ya zo suka wuce mun rabu kan sai na zo bikin ƙanwarta Amira wanda Tahir ya ce zuwan da tayi ne kawai zai sa ya bar ni na kira Aunty Kulu na shaida mata batun zuwana birnin Ikkon.

Na ci gaba da renon cikina da ke ta kara girma. Wata safiya Hadiza na zaune riƙe da wayarta na fito Bathroom wayar ta miƙo min “Ga Hajiyarmu” na amsa ina murmushi sai da na zauna na soma gaishe ta godiya take ta min da sa albarka kan rikon da nake wa Autarta. Kwanan Laila goma da wucewa tafiyata biki Lagos ya zo ta jirgi za mu yi tafiyar ni da Hadiza saboda halin da nake ciki.*

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 37Wa Gari Ya Waya 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×