Mun isa Kankara lafiya. Na sha mamaki da na ga ginin da Tahir ya yi a jikin gidan su, dan kwata kwata zuwan mu na ji yana maganar sayen gidan da ke jikin gidan nasu an gama shi tsaf sai maganar shiga. Mun bar Tahir tare da jama’a muka shiga ciki, cikin ba masaka tsinke, har Haj Hajara ta Iso, Kawu Attahiru ne dai da Aunty Kulu ba za su zo ba.
Dakin Haj na kai mu daga Latifa zuwan ta na farko kenan, gyara sosai aka yi wa wurin nata, an maida shi two bed room flat an buda flat dinta ya zama katon gaske an kuma kayata shi da kayan more rayuwa. Nan muka ci abinci muka yi sallah. Latifa da na hanga tana rada wa wata yarinya ta sasan yaya Lawal ina ne part din Tahir?
Ya sa ni dan guntun murmushi, mikewa tayi tayi wa Haj sallama. Ina nan har sai da nayi sallar Isha’i Haj ta ce “Ki tashi ki je ki huta ga gajiya, ga halin da kike ciki.” Ban musa ba mikewa nayi Hadiza ta ce “Allah ya huta gajiya, sai da safe” na ce “Za ki sani ne, ina nan dawowa ki ma matsa min, wanka kawai zan yo.”
Dariya tayi “Ina za ki tsafa da wannan uban cikin? gara ma kin yi kwanciyarki wurin ku.” Na samu falon ba kowa sai candle da aka kunna kofar dakin Tahir na tura dan ba abin da nake so irin in gasa jikina da ruwa me dumi, jakata da na zubo kayan amfanina na dauko, ina bude su ina tunanin komai nawa ya kusa karewa duk da nayi waya da Aunty Kulu bayan isowar mu da na samu labarin ba za ta zo ba.
Na ce komai na amfanina sun kusa karewa ta ce sai na haihu za ta taho min da su ta ware min wadanda nake saye. Latifa na gani baje bisa gadon, wani murmushi ne ya subuce min su Latifa manya, ashe saurin da take dan ta zo ta shige dakin ogan ne, dan dama Hadiza ta saurari hirar su da Halima tana gaya mata muddin Basma bata je ba, idan tayi wasa aka zo da ni kankane komai zan yi ta rasa wurin zama.
Wayarta take latsawa ga kida ta kunna a wayar, kallo daya nayi mata na wuce bathroom sai da na hada ruwan wanka da turarukana na wurin Aunty Kulu masu dadin kamshi da kwantar da hankali kafin na gasa jikina dadi na ji sosai na dauro katon tawul dinsa na rufa da karami, sai na fito, na wuce ta zuwa falo wata kwafa ta saki “Ko da wannan fitinannen kamshin ta karbe miji, ballantana a zo batun girki sai dai hassada ta sa ka kasa yaba mata, ga dirin jiki na masifa da ko ke mace sai ta burge ki, bare namiji.
Tayi duk iya yinta ta samu hanyar shiga dakinta dan ta ga sirrinta, amma hakan ya faskara. Gyara kwanciyar tayi cikin matukar takaici. Sai da na fiddo mayukana na shafa sai na bi da turare, wata doguwar riga me bin jiki na zura na rufe kaina da gyale komai na maida shi inda yake na rufe jakar da dan karamin kwadon da nayi guzuri, na jefa dan key a hand bag dita.
Sallamar da na ji cikin wata makalalliyar murya ta sa ni daga kai ina amsawa Tahir ne, “Yaya madam ke kadai ga duhu? Murmushi nayi na ce “Ba komai, mu da za mu shiga barci” Ya ce “Gen din ya samu matsala ya ki tashi, amma me gyara ya zo ana duba shi.” Da yake ya saya musu katon Gen a gidan. Na ce “Dama solar ka sanya musu” ya ce “Shawara me kyau, sai dai yanzu sasan su nake so a maida musu na zamani, ayi wannan din daga baya.” na fadada fara’ata.
“Allah ya kara budi na alheri ya kara daukaka, dan sashin Hajiya ba karamin kyau ya yi ba.” Bai ce komai ba sai ya ce ” Ina Latifa? Da hannu na nuna mishi kofar dakin ya mike ya isa kofar ya tura ya shiga da sallama zaune ta tashi tana fara’a, “Ba ki yi barci ba? “Ban yi ba ka san bana barci da wuri.” ya ce “Haka ne, to sauko ki ci nama, kina ta fama da duhun kauyenmu.”
Fara’ar ta kara tana saukowa “Ai wallahi garin ya min.” “Ashe ki ce idan zan maido ki nan din ba zan samu matsala ba? Shiru tayi tana tauna naman da ta sa ka bakinta, tana ta ci tana korawa da lemo duk yana kallonta, dadi ya gama kume ta sanin ya baro Ummulkhairi falo, rigar jikinta ta yaye tana mishi wani irin salo na jan ra’ayi murmushi kawai ya yi sai ya mike tsaye.
“Daga kin gama zo mu je falo mana” ba ta so hakan ba, amma ba yanda ta iya ta mike ganin har ya kai kofa. Ina zaune a inda ya bar ni sai dai kishi da ya turnike ni kamar ya kashe ni, sai nayi kamar in tashi in yi tafiyata sasan Haj sai kuma in ba kaina magana in daure, zama ya yi ita ma ta zauna kusa da shi tana ta salo kamar za ta hada jikinta da na shi.
Dakin ne ya gauraye da haske mikewa ya yi ya kunna TV sai ya canza wurin zama “Ummulkhairi ina ganin ki je sasan su Umma (Mmn Ummi) za ki fi sakewa” da to na amsa mishi duk da wani takaici da ya kulle ni, dan yana so ya kasance da matarsa shi ne zai kore ni.
“Ki dauki abin da za ki bukata saboda safiya” nan ma to din na kuma ce mishi tashi nayi na suri jakar da na zubo kananan abubuwan amfanina ina mai da na sanin zuwana indai wannan nuna iyakar za a yi min.
“Ke kuma Latifa ki shiga ki kwanta zan turo Hadiza ta taya ki kwana” “Kai kuma fa? Latifar tayi saurin tambayarsa “Mutane sun yi yawa gidan.” “To ina za ka kwana” “Kar ki damu da inda zan kwana ni da garinmu.”
Wata boyayyiyar ajiyar zuciya na fidda “Idan kin tashi akwai komai da za ki bukata a kitchen” ya ce wa Latifa ina ficewa na ji yana ce mata sai da safe, bata amsa ba sai wani kallo da ta bi shi da shi na zallar takaici ranar da ya koma kaduna daga kawo Ummulkhairi bai kwana ba jirgi ya bi ya koma Lagos yau kuma yana zuwa suka dauko hanya tana murna yau ita ke da miji dan sharri ya tafi ya bar ta.
“Ummulkhairi” na ji muryarsa a bayana ya yin da na dauki hanyar sasan maman Ummi jama’ar gidan da yan biki kowa ya nabba’a dan hadarin da ya hadu wanda a kowane lokaci ruwa zai iya sauka. A inda nake na tsaya cak ban waiwayo ba sanin kowaye. Har ya karaso inda nake hannuna ya kama ya kuma karbi jakar hannuna hanyar waje ya kama bi ni dai bin sa nake kamar raƙumi da akala har waje inda ya adana motarsa, buɗe ta ya yi ya kuma ba ni umarni in shiga sai da na shiga na zauna ya juya ya koma cikin gidan ya bar ni da tunanin ko me hakan ke nufi?
Kofar Hajiyar su ya tsaya sai ya kira Hadiza a waya ta fito ta same shi umarni ya bata ta je part ɗinsa ta kwana a falo da to ta amsa tana tunanin dalilin yin hakan. “Idan kuma Latifa ta tambaye ki Ummulkhairi ki ce tana wurin su yaya lawal.” Kai ta daga mishi sai ya juya ta bi shi da sai da safe. Na muskuta gami da gyara zamana “Na bar ki zaune ko? Ya fadi yana wa motar key murmushi nayi ban yi magana ba.
Muna tafiya ina tunanin inda za mu na ga mun isa gidan kajin sa gidan maabocin dogayen bishiyoyi ya yi horn aka buɗe mishi wani madaidaicin gini ya shigar da ni duk kuwa da cewa cikin haduwa ya yi ta karshe wani niimtaccen dakin barci ya kai ni, bakin gado na zauna bayan shigarsa toilet fitowarsa gani na zaune ya ce,
“Ba ki kwanta ba” kai na daga mishi “To zo mu je falo” na mike na bi bayansa leda ya bude gasassar kaza ce ya turo gaba na ya tashi kunna Tv tare muka ci ina gamawa na ce barci da hannu ya nuna min ƙofar bedroom na miƙe da kyar na wuce ina shiga kwanciya nayi ina jin wani sanyi dan hadari da ya taso gaba ɗaya har ruwa ya fara zuba sai ga shi ya shigo blanket ya ciro me matuƙar laushi ya lullube ni,har wata ajiyar zuciya na fidda, sai ya tuna min Ummata zuwan nan da nayi idan na kwanta ita ke lullube ni, ya kashe fitilar me haske, ya kunna bed side lamp, sai ya hawo gadon bayana ya kwanta ya rungume ni ta baya fuskarsa yasa a kan wuyana “Nayi kewarki Ummuna.”
Abin da ya rada min kenan wani lokaci ya dauka yana abu daya sa’adda na samu ya sarara min sai marata ta dauka da ciwo.