Haka na daure har sai da na ji ta lafa min sai na shiga barci. Gabanin Asuba na farka marar ce ta ci gaba da tsungula min Tahir na kan sallaya ya yi sujjada ga mahallicinmu.
Har ya fita sallah ban samu na tashi ba, da kyar ta sakan nayi wanka hade da alwala, sai da na gabatar da Sallah na zauna nayi kwalliya Atamfa nasa ɗinkin doguwar riga.
Sa'ilin ya shigo "Lallai ma me cikin nan akwai kokari har kin yi wanka kin sha ado? Murmushi nayi ina gyara daurin dankwalina na gaishe shi ya jani zuwa bakin. . .