Wanka na ci gaba da yi cikin tsantsar kulawar da nake samu. Dauri dai yaran nan sun sha shi, ni kuma na sha maganin sanyi har na gaji, wurin Aunty Kulu turaruka na saya, na jiki da na tsugunno masu asalin tsada, dan ita kayanta yammatan gaya ne ga kyau ga kudi.
Tahir bai samu dawowa duba mu ba saboda yanzu aikin nasa ya koma tafiye tafiye, har sai da muka yi wata guda Allah ya yi wa Malam na tudun wada rasuwa daga gidan gaisuwar ya iso Kankara, cikin jimami yake kwarai na rashin tsohon kwana daya ya yi ya koma.
Ya ce wa Hajiya da nayi arbain din da ta ce zai turo a tafi da mu, Hajiyar ta ce ba zai yuwu ba dan ban je gida ba kuma akwai biki a gidan mu na yayana Mustafa da diyar Babbar yayar mu za ta aurar da diyarta ta farko. Ana gobe zan yi arbain kuma ranar da zan yi arbain din zan wuce Dutainma, mun yi wankan safe Haj ta goya Areef ta ce in goya Mimi, in sa lullubina in biyo ta, fita muka yi daga gidan wata mota da ban san sa’adda ta kira me ita ba muka shiga, tafiya sosai muka yi zuwa wani kauyen fulani, ya sauke mu muka shiga rigar Haj ta ce ya jira mu. Sai lale ake mana aka yi mana shimfida, sai fillanci suke da Haj, aka kawo mana nono kindirmo, ni dai da ban iya shan shi haka ba, sai ban sha ba.
Wani dogon bafulatani aka kira, a fuska yana kama da Haj, faraa sosai yake ganin Hajiyar suka gaisa cikin fulatanci ni kuma na gaishe shi da Hausa.Daga yanda suke kallona na gane maganar ta shafe ni. Ta kwance goyon da ke bayanta ta mika mishi ni ma ta ce in yi yanda tayi. Sai duban yaran yake yana murmushi magana ya fara min ganin ina nonnokewa ya ce “Ki saki jikinki ki saba da ni, ni kane ne wurin Haj, kakanninmu daya.”
Murmushi nayi sai na sunkuyar da kaina, wata da nake kyautata zaton matarsa ce ya kira ta iso cikin sauri magana ya yi mata ta amsa sai ta juya sai ga ta ta dawo dauke da wata kwarya ta ajiye gaban sa wasu sake saki ya ciro ya miko min, “Ki wanke wannan sai ki jika ku rika sha da yaranki, kar ki wasa.”
Na karba ina ta mishi godiya wasu ya ciro “Wannan kuma dafawa za ki yi kuna sha shi ma ke da yaranki.” Haj ta mike za ta kewaya sai da ya bi ta da kallo ya ga shigewar ta kafin ya ciro wata kwalba ita ma sake sakin ne a cikinta “Ki zuba turare kalar wanda kike so ki shafa ya yin tafiyar ki wurin me gida, in sha Allah za ki yi godiya ba kowa nake ba shi ba, amma ke saboda yanda Haj ta fada min halayyarki da muamalarki shi yasa na ga ya kamata in taimaka miki.”
Zagewa nayi sosai na shiga mishi godiya. Haj ta dawo na ce “Me zan bayar sadaka? Ta ce “Abin da Allah ya hore, dan bayar da sadakar yana da kyau” yan dari biyar na ciro na ajiye gaban sa, amma sai ya yi murmushi ya dauki daya. Wata mata me tsananin kamanni da shi ta shigo, fara’a sosai ta shiga yi ganin Haj ta zauna aka gaggaisa ita kam hausa ce a bakinta radam.
Haj ta ce “Yaushe kika dawo? Dan’uwanta da na lakanci Baffa ake kiransa ya ce “Ga ta nan ta dawo bata iya cimar mu” Haj ta ce “Allah sarki” ta dauki yan biyu Haj ta ce mata yaran Sodangi ne ta ce “Shi bana Sodangi ya ga kwansa mu ne dai ni da Yaya Atta ba mu samu ba.”
Ta ce “Kuma Allah bai manta da ku ba ta” Ta goya Mimi ta saba Areef ta fita Haj ta bi ta da kallo kafin ta juyo wurin dan’uwanta “Ko Wodile za ta gidan Sodangi ta taya Ummulkhairi kula da yaran nan? Daga ita din me son yara ce, kuma za ta samu cimar birni da ta saba da ita, Ummulkhairi bata da matsala, haka ita ma wodilen.”
Kira ya kwala wa yar’uwar tasa sai ga ta ya yi mata bayani ta ce “Ita bata da damuwa za ta je. Ya ce a kira Sodangin a gaya mishi, murmushi Haj tayi “Kar ka damu daga dai Wodilen ta amince zan gaya mishi. Sai da muka mike za mu tafi Haj ta sa a ka bude boot buhun shinkafa ne da kwalin taliya da na makaroni sai sabulai na wanka da na wanki da omo.
Yaran gidan suka kwashe zuwa ciki sai muka kamo hanya. Mun yi nisa Haj take ban labari “Wannan kanwar Baffa ce, a Abuja tayi aure tana auren me gadin wani kusan gwamnati, Allah bai bata haihuwa ba, ga shi mijin Allah ya yi mishi rasuwa, na zaba miki ita.
Ummulkhairi mace ce me kirki da zumunci, za ki ji dadin zama da ita, tana da son yara ga tsafta. Sai da na kara sati guda na tafi Dutsinma dan Haj ta ce sai mun sha maganin nan kar in je can in watsar. Murna sosai gidan mu suka yi da gani na. Mun sha biki har guda biyu rawa sosai na taka a wurin bikin dan ni ma yanzu ko Tahir bai bani ba ina da abin da zan yi hidima, Akwati na hada wa yayana mustafa, Yaya Maimuna kuma na saya ma yarinyar ta kayan kitchen, nayi ma iyayena alheri da sauran yan’uwana, hada Hafsa da tilon yarta. Na koma Kankara Tahir ya yi wa Haj maganar komawa ta ta ce ya bata nan da sati guda, sai tayi mishi maganar Wodile wadda na ji su Hadiza na ce wa Daada, sai ya ce zai yi magana da Hajiyar tudunwada ta ba shi Hassana ko Hussaina daga yasan ba za ta yarda ta rabu da yaran duka ba sai su taya ni kula da yaran dan Hadiza muna dawowa makaranta zai mayar da ita. Shiri sosai Ummata tayi na komawata mutum biyu aka tado da za su yi min rakiya Matar yayana sai Yayata Aunty Wasila.
Anan gidan su Tahir Maman Ummi ce sai Uwargidan Babban Yaya, motar da Tahir ya turo ba za ta ishe mu ba sai da aka hada da motar babban yaron Yaya babba, motar Tahir ne ya yi mishi kyautarta. Karfe goma na safe muka kamo hanya. Mun shiga ba mu samu kowa a falon gidan ba Hadiza ta bude dakina bata kuma zauna ba ta soma gyaran wuri, duk wata kura suka goge ta ita da Mmn Ummi suna shirin shiga kitchen sai ga sakon abinci daga Asiya dan su laraba dama sun ce basu san da dawowar mu yau ba.
Tahir ma baya nan sai gobe zai shigo. Nan kowa ya ci ya koshi, sai dare matan suka dawo kuma a tsaitsaye suka leko a ka gaisa Basma ma da ke gidan sai washegari muka sa ta ido. Gari na wayewa suka soma shirin tafiya duk da jin da nake kamar kar su tafi, Ko da basu ga Tahir ba sakonsa ya iske su. Na samu Daada mace me kwazo da tsafta ga juriyar dawainiyar yara dan haka na samu saukin goyon.
Ni zan yi girki dan haka zagewa muka yi muka gyara gidan hada su laraba, na gyaro wurinsa abinci da na san yana so nayi mishi nayi kwalliya sosai cikar da nayi tun ta haihuwa tana nan har yanzu nayi dam dam, nayi mamakin ganin matan su uku suna maganar da tayi kama da ta sirri, a sanin da nayi su biyu ke irin wannan zaman Halima da Latifa to yau har da Basma, na ji ba dadi dan ba yarda za a yi ka ji dadi idan aka ware ka.
Amma sai na kama addua nayi tayi har na samu na manta da lamarin su, na ci gaba da sabgata.Yamma sosai Tahir ya shigo, ya zauna a falo yana makale da yaran idan ya dauki wannan sai ya ajiye ya dau wannan ya kasa daina fadin girman su, da wayon da ya ga sun yi masa. Har daki ya shiga suka gaisa sosai da Daada. Da daddare cikin tsoro na shirya zuwa turaka dan ina ganin yara har biyu gare ni ya kamata a daga min kafa, har su kara wayo damma sauki na daya ba su kukan dare, gaba daya ma basu da rigima.
Daada nake jin kunya da wuri ta shige dakina dayan da na bar mata, ni kuma mu zauna da Hadiza. Mimi na saba a kafada na wuce, yana zaune daga shi sai guntun farin wando black tea da na kawo mishi yake kurba a hankali idonsa na kan TV yana kallon labarai a tashar CNN a gefe na ajiye ta na koma dauko Areef ina dawowa na samu Mimi tana kuka abin da bata cika yi ba.
Na ajiye Areef na zare dogon hijab din da na dora saman rigar da na sa yar yala yala ce me hannun shimi iyakarta gwiwa na zauna ina bata nono Areef ma ya tashi ya fara kuka duk sai na rikice ya dora min shi ya zauna daf da ni ya hade jikinsa da nawa yana rada min maganganun da suka sa na rufe ido, ba su jima ba suka koma na kwantar da su gefe daya. Ina waiwayowa ya jani zuwa gado, al’amuran da suka faru a wannan dare masu tsayawa a rai ne, dan sambatun da Tahir ya rika yi na san idan haka nan ne ba zai taba yarda ya furta min su ba.
Yana tafiya sallar Asuba na gudu dakina wanka nayi da ruwa me dumi na gasa jikina, na idar da sallah ina azkar ya shigo sai da ya leka Daada suka gaisa sai ya shigo jikin gado na boye fuskata dan samun kaina nayi ina jin kunyarsa. Ya leka yaran da ke ta barci sai ya fita ya koma saman sa. Karfe tara ya tasa ni wurin rumfar ajiye motoci bayan na shigarsa guda biyu, akwai na Basma su ma biyu sai ta Hali dubu, wasu kuma sababbi na gani dal guda biyu fara da baka ya ce “Zabi daya.”
kallonsa nayi sai ya dage min gira na ce “Wai hidima bata yi maka yawa? Kafadarsa ya noke “Daga Allah ya hore meye amfanin su? Anan inda ka same su nan za ka bar su.” Na gyada kai sai na shiga godiya katse ni ya yi “Kin fi karfin komai da nake da shi Ummulkhairi, dama na yi deposit na motocin na ku, haukan da Latifa tayi min yasa na fasa saye sai wata shekarar, amma giyar dare da aka shayar da ni tilas in bada tukuici.”
Sunkuyar da kaina nayi duk kuma maganar da yake ban dago ba. “Ki zaba ” ya maimaita, farar na nuna ya kwantar da kansa jikin motar yana min wani irin kallo “Mu maza wadda zuciyar mu ta kwallafa ita take son kasancewa da ita idan ba ita din muka samu ba ko me za mu samu ba ma gamsuwa nayi kewarki Ummuna.”
Ban ce komai ba sai hanya da na kama ina tafiya a raina ina saka ni fa tsorona Allah tsorona munafuncin maza, su yi ta zura ka kai kuma kana hauka kana ce gaske ne, duk da dai Tahir ba mai fade fade bane amma daga daren jiya na rasa abin da ya hau kansa. “To jira ni mana.” na ji muryarsa a bayana kin tsayawa nayi ido muka hada da Halima wadda ke fitowa a lokacin ina zuwa inda take na ce mata Ina kwana sai na wuce ciki.