Skip to content
Part 45 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

“Wace yar’uwar tamu? Halima ta tambaye shi. Shiru ya mata sai ma wayarsa da ya zaro ya soma amsa kira har kuma suka isa gida bai ajiye wayar ba ballantana su samu damar tambayarsa yana kuma ajiye su juya kan motar ya yi bai ko shiga ba.

An yi haka da kwana biyu da rana na fito kitchen, na ji ana knocking komawa nayi na bude, kallo daya na gane matar duk kuwa da cewa sau daya na taba ganin ta ga dadewa da aka yi tunda na gan tan ko da yake abin da ya taimaka min wurin gane ta bai wuce hoton ta da na dade ina gani a Dp dinta na WhatsApp dan na dade ina da lambarta kafin rashin ji daga gare ta yasa na gogeta.
Ba wata ba ce illa Haj Shema’u da ta taba zuwa har ta bani maganin mata farko farkon zuwa na Kaduna.

Murmushi nayi mata “Sannu da zuwa Haj.”

Ita ma murmushin tayi min “Yawwa kamar Amaryar Kankara ko? Kai na daga mata “Ikon Allah kin canza kamar ba ke ba, ya kwana biyu? Na ce “Sai alheri, ki shigo mana” na fadi ina bata hanya sai da ta zauna na kawo mata lemon da cincin din da nayi ta tambaye ni Halima fa? Sai da na duba motarta na ga tana nan sannan na ce “Kin yi sa’a tana nan ta dawo” mikewa tayi na nuna mata kwanar da kofarta take dan na ga kamar ta manta.

Da kallon mamaki tayi ta bin Halima ganin katon cikin da ke gabanta. “Ikon Allah, Halima ke ce da ciki? Murmushi tayi “Ai kuwa dai kin gani.” labari suka shiga tana bata labarin kishiyoyin da aka yi mata da yanda take neman hanyar da za ta wargaza su duk kan su, amma dai muna tare da wadda kika gan mu tare duk da itam ma ba barin ta zan yi ba, yanzu dai wadda tafi rike min wuya matarsa ta uku, Ummulkhairi dan ya fi san ta.”

Kama baki Haj Shema’u tayi tana sauraren ta. Wayarta ta janyo ta kira Latifa ba bata lokaci sai ga ta ta zo sun gaisa da Haj Shema’u sannan suka roki ta taimaka musu kan yadda za su yaki Ummulkhairi ta ce, “Akwai mafita wani kasaitaccen me bada magani ta ba su labari, suka shirya ranar zuwa har sun yi sallama ta fito sai ta koma ta ce musu “Kuna da labarin tana da kasaitaccem wurin dinki na zamani? Zura mata ido suka yi cikin kaduwa ita kuma ta juya ta fice cikin jin dadi dan dama takaicin su take so ya karu.

Ina harabar gidan ina neman Indo in ce mata ta je makarantar su Hussaina ta dauko min ita na hango fitowar Haj Shema’u da fara’a na tare ta “Har kin fito Haj? “E wallahi ” na ce “Ina zuwa ciki na wuce na dawo rike da kudi dan yanayin da na gan ta na gane za ta bukaci kudin na mika mata ina fadin “Ki shiga mota Haj.” godiya sosai tayi min ta fita gidan tana zagin Halima a zuciyarta.

“Marowaciyar banza bata iya gane rayuwa ta canza min ba ta temaka min, na zo ko na mota sai neman ta hada kai da ni a cuci baiwar Allah. Ai ba zan taba mancewa da cin amanar da kika yi min ba, Halima kin kuma kawo kanki yanzu, sai na rama.

Halima na zaune inda Latifa ta barta bayan sun gama juyayin bakin labarin da Haj Shema’u ta basu, bata ma da niyyar tashi a haka Tahir ya shigo ya same ta ganin ta a birkice yasa ya ce “Ya ya dai lafiya? Ta dube shi da fuskarta me kamar za ta fasa kuka “Yanzu Tahir adalci kenan? Ashe har akwai macen da za ka daga ka fifita sama da ni? Cikin rashin fahimta yake duban ta “Me nayi kuma? Wace macen na daga sama da ke? “Ummulkhairi Tahir, ka bude mata wurin dinki na zamani ni ko oho” wani duba yake mata ta cikin farin glass dinsa.

“Gaskiya ne Halima Ummulkhairi tana da wurin dinki na zamani yanzu haka ma aiki ya yi nisa za ta bude wani dan wannan din ya bunkasa, sai dai za ki dauko kur’ani zan yi rantsuwa ba kudina a bude shagunanta ma’ana ba ni na bata ba, na yarda dai ta tattala abin da nake bata sai ta bude. Wanda tun kina ke kadai nake so ki tattala abin da nake ba ki dan ki tsaya da kafarki amma hakan ya faskara sai ma masifar cin bashi da kika dora ma kanki wanda na rasa ta inda na kuskuro ki.

Ki tashi malama ki yi alwala ki rantse. kan ni na bude mata ni kuma zan rantse kan bani bane na gaji da rainin hankalinki, ki tashi! Ya kare cikin daka mata tsawa har sai da ta zabura bed room dinta ta shige ta datso kofar ya ja mummunan tsaki sai ya bar dakin.

Kwana biyu da zuwan Haj Shema’u an zauna cin abincin dare. Tun da na shaki kamshin girkin Basma wanda aka saka ma kifi na ji hankalina ya tashi, cikina ya shiga yamutsawa amma son ganin yanda za ta kaya da Halima wadda ke ta salo bata son abincin sai maigidan ya fita ya nemo mata abinda za ta ci dan bata son wanda aka girka a cikin gidan ya hanani tashi sai da na ji amai zai zubo min na mike cikin sauri, a falona na wuce Hadiza da ke karatu dan gaskiya bata wasa da karatunta.

Bathroom na shige na yi ta kwara amai gaba daya sai da na amayar da abinda na ci. Wanke fuskata nayi sai da na gama maida numfashi sai na fito Hadiza ta dago ta dube ni “Aunty na ji kamar kakarin amai? kai na girgiza “Amai dai? Kai a’a.” Daada ta fito rungume da Mimi muka dube ta a tare, ta miko min yarinyar. “A bamu nono mu je mu kwanta.”

Murmushi nayi na karbe ta sai na soma shayar da ita muna dan taba hira har ta saki dan kanta barci ya dauke ta, ta dauke ta suka shiga daki, dama yanzu haka take musu yau idan wannan ya kwana wurinta gobe kuma sai ta dauki dan’uwansa, ta koya musu cin abinci bayan madara dan haka basu damu na da tsotso.

Ni ma ban jima ba wurin Hadiza dan ita kam sai ta raba dare tana karatu. Wani sanyi sanyi na soma ji da ya sanya ni kashe fanka sai nayi shirin barci na kwanta Areef na gefena. Nayi barci sosai farkawar da zan yi wani amai na ji na shirin zubo min na tashi da sauri nayi aman kamar zan amaye yan cikina kafin na dawo daki, Hadiza na gani zaune “Aunty dama ke ke amai dazu? Ban samu amsar bata ba dan jin wani sabon aman na koma ba komai a cikina da zan amayar kakarin kawai na yi tayi na wanke fuska zan koma daki na ga Hadiza tsaye a bayana “Sannu Aunty” ta fadi tana dubana da tausayawa kai na daga muka koma daki, ina kwanciya na kuma jin wani. A wannan daren dai haka nayi shi a wuya ce tun muna yi daga ni sai Hadiza har ta tado Daada, ba yanda Hadiza bata yi da ni ta kira Tahir ta waya na hana ta.

Zuwa Asuba nayi laushi matuka, ina yin sallar na kwanta ina jin shigowar Tahir ya dauki Areef ina ganin Hadiza ta ji rokon da nayi mata kar ta sanar mishi, juyawa ya yi da yaron a kafadarsa yana fadin “Madam yau me barcin safe ce kenan? Na dade ina jin shi da yaron kafin barci ya dauke ni. Tabawar da na ji Hadiza na min ta sa ni bude ido, “Kin ji yadda jikinki ya dauki zafi Aunty? Ki tashi ko tea ki sha mu je Hospital.”

Maida kaina nayi “Zan ji sauki Hadiza” bata bi ta kaina ba ta fice Tahir ta samu suna breakfast Basma na tare da shi da Latifa, Halima na zaune a daya daga cikin kujerun falon wai ba za ta iya zama ba kafafuwanta kunbura suke asibiti za ta. Ya ce ta bari zuwa anjima sai su je tare. Ta ce “A’a” dan Allah kadai yasan abin da ta karba a wurinsa tunda ta gane tana da ciki, bata kawai yake kamar bai san me take ba, dan a halin yanzu ba shi da bukatar hayaniya da ita tana dauke da cikinsa, fata kawai yake ya ga ta haihu lafiya.

A rikice Hadiza ta isa gabansa “Yaya Sodangi, Aunty fa bata da lafiya.” “Me ya same ta? Ya tambaya cikin sauri “Amai ta kwana tana yi, yanzu kuma zazzabi ne jikinta me zafi.” “Shi ne da na shiga kika kasa fada min? Ya fadi yana ture kujerar da yake zaune cikin zafin nama ya nufi dakina Hadiza ta bi shi a baya.

Jin labarin Amai ba karamar kaduwa yasa matan ba, Halima da Latifa suka dubi juna Latifa ta kyafta ma Halima ido sai ta mike ta fara takawa zuwa dakin sai da Halima ta harari kofar Ummulkhairi kafin ta mike ta bi bayanta, Basma ta noke kafada kamar tayi tafiyarta dakinta sai dai ta yanke ta bi su.

Suna shiga idanunsu na kyakykyawan gani, Tahir na tallafe da Ummulkhairi wadda jikinta ya yi matukar gashewa ya karbi mug ya danna min a baki dan ya yi ya yi in sha na ki na ce idan na sha amai zan yi, ba shiri na shiga sha sai dai yana shiga cikina na maido shi gaba daya na bata ma Tahir jiki, na kwace jikina daga hannunsa na kwantar da kaina kan fillow rigar ya cire ya kamo hannuna “Zo mu je ki yi wanka” ya dauko wayarsa ya mika wa Hadiza da ta shigo lokacin “Kira min Dr Muhammad, ki ce ina son ganin sa yanzu, Ummulkhairi zai duba min.

Ta karbi wayar “Tashi mu je” ya kuma bani umurni kamar sun hada baki suka dan basu san me zasu gani ba idan suka fito kila ma a kirji zai dauko ta, Hadiza ta fito falon tana dariyar mugunta kasa kasa dan ta san sun ji abin.

Sai da na fara wankan ya fita dan zuwa ya canza kayansa da fitowa ta Hadiza na samu ta gyara inda na bata falo na wuce na kwanta bayan da na sa jallabiyar da Hadiza ta ajiye min. Tahir ya dawo, Daada ta fito dauke da Mimi tayi mata wanka ta shirya ta cikin wasu riga da wando farare masu taushi, ta raba mata sumar ta biyu kafin ta dora mata hula. Ganin uban sai ta fara zallo za ta wurinsa ya mika hannu ya dauke ta, ta karbi Areef a hannun Hadiza dan ta je shi ma ta yi mishi. Sannu ta min ta juya Tahir ya kuma kiran Dr ya ce yana hanya, a kafada ya sa Mimi ya fita daidai step din da ake takawa a shiga main fallow na gidan ya tsaya yana sauraren ta inda zai ga Dr Muhammad ya bullo, hancin motarsa da ya kunno kai ya zura wa ido, su biyu shi da wani abokinsu da suka dade basu hadu da Tahir ba suka fito suka nufo inda yake tsaye hannu suka ba shi suka gaisa.

“Kwana biyu Lawal? Tahir ya fadi ma wanda suka zo tare da Dr “Muna gefe Kankara, wannan yarinyar fa? Ya fadi yana miko hannu dan daukar Mimi wuyan uban ta makale duk da cewar ba kyuyar take ba gara ma Areef ya kan dan taba. “Yan biyun da aka haifar mishi ne” Dr ya ba Lawal amsa “Wow! ka ce wata beautiful babyn na ciki? /gaskiya ka more mutumina, duk yadda aka yi in ba balarabiya ka auro ta haifa maka wadannan zuka zukan yaran ba to Shuwa ce.

“Duk da Tahir ba shi cikin yanayin son magana sai da ya ce “Kai dai ba ka da mutunci, to in fada maka yarinyar nan mahaifiyata ta dauko sak, dan an ce a duk fadin zuriarta ba a samu wanda ya biyo ta har kuma yaran da ta haifa duk kuwa da tana cikin shekarun girma sama da wannan yar tawa. Dan’uwan haihuwarta namiji ne shi kuma kamar mu daya da shi, ku mu shiga daga ciki” Cikin suka shiga a falo ya bar su ya shiga ciki wurina sai da ya ce Hadiza ta dauko gyalen rigar ta rufe min kaina sannan ya koma tare suka shigo da Dr, Hadiza ta ce min kwana tayi amai ga zazzabi?

Kai Tahir ya daga mishi “Sannu Madam” ya ce yana nazarina, karin ruwa ya sa min wanda ya zuba wa allurai sai kuma ya debi jinina ya tafi dan gwajin, abokinsa da suka zo tare dai tun da ya ga yan biyu ya ce Dr ya je ya dawo, ya zauna ya tasa su yana musu wasa dan ya samu Mimi ta yarda da shi, sai fadin yanda suka burge shi yake ni dai barci nayi sosai.

Dr Muhammad na dawowa da result Tahir ya tare shi da son jin abin da ke damuna kai tsaye ya ce “Congrats Kankara ka Kara jefa kwallo a raga, madam dai juna biyu ne sai dai karami ne kwarai.” Suna ta maganar su Lawal da ke wa yan biyu tafi ya dago “Amma watan su nawa har ake maganar wani cikin? 8 month” Tahir ya ba shi amsa maganar da suke tayi da dariya yasa su Halima san sanin sakamakon duk da ba sa son tabvatuwar zargin su.

Latifa ta tari Tahir bayan tafiyar su Dr duk abin da ya kamata ayi ya bar shi a hannun Hadiza ya ce sai zuwa yamma za su dawo tare da Asiya, wadda ita ma tayi nauyi sosai “Amma wallahi Maman twince tana jin jiki, hala typhoid ne? Murmushin sa me tsada ya yi mata “Yan biyu ne za su samu kanne.” juriya me yawa ta sa wurin yin murmushin yake “Amma ba ku yi wa yan biyu zalama ba?

Wuce ta ya yi ba tare da ya ce komai ba, bata saurari Halima ba dakinta ta wuce ta datse kuka tayi hada birgima kafin ta ci alwashin ko za ta tafi tsitara sai ta ga bayan kishiyoyinta Ummulkhairi da halima dan sune suka rike mata wuya suka sha gabanta musamman Ummulkhairi.

<< Wa Gari Ya Waya 44Wa Gari Ya Waya 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×