Skip to content
Part 48 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Tun daga ranar ya fita harkar Halima. Dakinta da yake shiga ya duba ta ya daina, sai da aka kwana biyu a haka a na gobe yan Kankara za su koma Halima da ke daki ta rasa abin da ke mata dadi, dan mahaifiyarta tun wannan tonon silili da suka yi wa juna Halima da Latifa ta tattara nata ya nata ta sulale, ta bar gidan ko Tahir bata yi wa sallama ba sai dai ya ji bakin Hadiza.

Ga Tahir idan za ta kwana tana kiran sa bata shiga wanda take jin faduwar gaba idan tunanin ya saka ta a black list ya darsu a ranta. Kanwarta bazawara ta kalla “Kai ni wajen Tahir Zabba’u.” “Ki ce da shi me Aunty? Ke dai da kika samu bai kore ki ba ki rufa wa kanki asiri ki rabu da shi.” da masifa ta taso mata “In za ki kaini ki kaini.” kanwarta budurwa wadda suke cewa Baby ta dago kai daga kwancen da take kan three seater tana danna wayarta, tare da Allah Allah kar auntyn tasu ta ce ita dan bata dade da fita ba ta je kai kayan da aka zubo musu abinci, ta ga yan Kankara duk suna nan zube a falon. Kan ba yadda Zabba’un za ta yi ta gungura ta suka fito sun ratso falon kowa da ke ciki ya bi su da ido ba wanda ya ce su ci kansu, Tahir ma da ke zaune yana cin abinci dauke kansa ya yi, ran Halima ya yi mummunan baci ta ce kanwar ta ta ta mayar da ita. Sun koma daki ta dubi Baby “Kira min Tahir Baby” Ita ma gwada bata son zuwa tayi ta kwakwkwara mata zagi dole ta mike ta fita tana tura baki, tana gaya mishi dama ya kammala abarkacin idon mutanen wurin ya ce yana zuwa sai ya bi bayanta yana shiga suka dubi juna shi da ita, su kuma kannen nata suka shige bed room har yanzu zaune take kan wheel chair an dora mata danta kan cinyarta hannayensa ya nade a kirji ya tsare gida “Ga ni lafiya? Ta cije lebe sai hawaye “Jarabtar da aka yi min ita za ta sa ka wulakanta ni Tahir?

Abinda dai kika dauko wa kanki Halima, ke yanzu ba ki ji kunyar daura wa jarabawa da kika yi ba? Sakamako ne dai na abinda kika shuka ban kuma wulakanta ki ba dan da na wulakanta ki da tun a ranar da na san ko ke wace ce ba za ki kwana min a gida ba kuma b….

Ta katse shi cikin kuka “Kuma wallahi ban zama anan ina kallonka da wasu matan yayin da ni na zama mara amfani, ni ka sake ni in koma Kankara.

“Wani shegen murmushi ya sakar mata “Halima kenan, ai tun ranar da na saki Latifa ke ma na karasa miki saki dayanki domin ganin ki ma bana so Halima, girman iyayenki yasa kika kawo war haka a gidana, ki kara hakuri za ki tafi ina so in sallami yan Kankara sai in kira iyayenki su ji halinki in yaso sai su tafi da ke.”

Yana kai karshe ta mike tsaye hannunta akai tana famar kuka Tahir ya rufa mata asiri dan ta da ke bisa cinya ya fado ya tsala ihu cikin zafin nama Tahir ya cafko shi ya sa shi a kafada sai ya bar dakin da shi, ya wuce yan Kankara a falo bedroom dina ya yi wa tsinke ya shigo na fito daga bathroom daure da tawul wanda yake daga kirji zuwa cinyoyi, dan kullun zan kwanta ina shiga ruwan dumi mun zuba wa juna ido ni da shi, dan rabon da muyi wa juna wani dogon gani tun kafin wannan bahallatsar ta Halima da Latifa yaron hannunsa ya miko min na kai hannu na karbe sa ina jijjiga shi.

“Gwada ba shi nono mu gani.” Saurin duban sa nayi jin abin da ya ce sai ya kara maimaita min na dan yi jim, gane ba zan samu wani karin bayani ba a wurinsa sai na zauna bakin gado na balle tawul din na dunguna mishi nonon ya kama har yana sarkewa dan yadda yake ja da karfi kamar za a kwace mishi.

Tahir na tsaye yana kallon mu, “Na ba ki yaron nan Ummulkhairi, ki hada su shi da Sudes ki shayar da su.” Wani razanannen kallo nayi masa sai kuma nayi kwal kwal “Ya za a yi ka raba uwa da danta? Alhali ba mutuwa tayi ba, wane irin zagi kake so ayi min ka karbe mata da ka bani?

Sai na fara hawaye.”Ba zan so ayi min haka ba ballantana har ni in yi wa wata.” “Na saki Halima! na cikashe mata igiyarta daya.” barin kukan nayi nayi saurin duban sa “Ina so ki rike yaron nan ki shayar da shi nononki, ina jin tsoron ya dauko halayen uwarsa.” “Addu’a dai kawai za a yi, amma daga jininta ne ta haife shi ba ka da makankara da ita.” “Ko dai meye ne ki taimake ni ki rike min shi bana so ya tashi karkashin tarbiyar Halima.”

“Wannan fa duk ba shi bane ita Halimar ta ta mahaifiyar haka take? Takowa ya yi zuwa gadon ya zauna sai ya rungume ni kalamai masu dadi da yabon halayena yake yi yayin da yaron ya saki nonon ya zura min ido, kamar su daya da Sudes har rashin hasken fatar sai dai Sudes ya gwada mishi girma kadan dan shi an haife shi watanninsa ba su kai ba. Ba mu ji motsi ba sai dai bude kofa muka ji, Hadiza da bata san da shigowar Tahir ba ta fado dauke da Sudes saurin juyawa tayi ni kuma nayi saurin janye jikina daga Tahir ina tura baki.

“Ka ja min in ta jin kunyar Hadiza” na kwantar da yaron sai na mike sai na isa gaban wardrobe ina neman kayan da zan sa in kwanta, har na sa yana zaune “Ki zo mu je falo yarinya kin koyi zaman daki tun da kika haihu.” na dan langabe “Da barci zan yi.” “Ke wa ya ce miki kana bako ka riga shi kwanciya? Sai na ga gaskiyar sa dan haka a baya na bi shi muka fita dakin shi bai zauna ba wurin Kawu Attahiru ya ce min za shi.

Na zauna cikin bakin ana hira, Hadiza ta kawo min Sudes ta karbi Sadiq. Kwanan da yaron ya yi wurina yasa suka gane Tahir ya bani shi Hadiza ta tambaye ni na bata labari sama sama ai kuwa suka shiga magana daga me fadin babu me bata dan kishiya ta rike ya girma ya ce da wa Allah ya hada shi ba da ke ba, sai me cewa ni yanzu duk cutar da Halima tayi min da mugunta a rayuwa har in amshi danta in rike? Ni dai amsa daya nake basu.

“Da na Tahir ne, kome zan yi dan shi zan yi kuma da zuciya daya zan yi. Sai dai dagowar hantsi suna ta shiri Tahir din ya shigo yana fadin Halima ta bar gidan nan me gadi ya fada mishi dan haka shi zai wuce Kankara idan motocin da za su mayar da su sun zo su taho. Yana fita suka balle ka ce na ce “Ko har yanzu surkullen da wannan me kama da tukunyar bai sake shi ba? In ba haka ba me zai kuma yi da wannan me bakin halin, abu ma ta riga ta tashi aiki, in ma ya rike ta sai dai ya taimake ta. Ko ni ma sai da na ji zafi wai shi har wane irin so yake mata jiya fa ya ce min ya sake ta amma yau ta bar gidan ya bi ta a kidime. Har suka gama shiri suka tafi ina jin zafin abin da Tahir ya yi wanda na san shi ne kishin.

Tahir na isa gidan su Halima ya zarce sai da iyayenta da yayyenta suka zauna sannan ya fadi abinda ta aikata har ta tsinci kanta a halin da take ciki a yau, da gore goren da suka yi wa juna ita da Latifa wanda yasa ya sahale mata aurensa, gaba daya suka yi kan Halima ban da mahaifiyarta da ke ta faman kuka. Yayanta wanda take bi ya yi tsalle ya karyo iccen bishiyar dalbejiya da ke tsakar gidan ya kwada mata ya daga zai kara mata wata gwoggon su da ke zaune cikin gidan ta tare amma duk da haka sai da ya kara hambare ta ta fada cikin wata kwata da ke tsakar gidan, ta kuwa fashe da kuka dan azabar da ta ratsa ta ga ta duka ga ta ciwonta da ta fama.

Tahir ya mike ya bar gidan dan yadda gidan ya hargitse a tsaitsaye ya shiga gidan su sai ya dauko hanya duk da haka sai dare ya iso. A bedroom ya same ni yaran sun ruda ni, Daada tana dakin su ita da su Mimi, Hadiza bata gidan sun fita da Kamal. Barka da zuwa nayi masa sai ya karbi Sadiq na zauna ina ba Sudes nono, sai da ya koshi na karbi Sadiq ina gama ba shi goya shi nayi muka fito na ba shi abinci ya tambaye ni Hadiza na ce tana wurin mijinta ya ce, “Ke ma ki bi naki mijin mu je mu yi kwanciyar mu.”

Na ce “A’a sai da ya raka ni har daki, muka kwanta tare da yaran sai shi ma ya tafi ya kwanta, Hadiza bata shigo ba sai da na soma barci. Da safe na fito gaishe shi yana zaune a falo da kofin tea a hannu yana kurba ganin yana waya sai na samu wuri na zauna abinda na fuskanta da mahaifin Basma yake wayar ya ce ta dawo dan zamu tare sabon gidan mu, amma sai mahaifin nata ya ce A’a ba za ta dawo ba dan kayan dakinta da aka yi order ba su zo ba zai yi tafiya sai ya dawo sai ta dawo.

Da ya gama wayar murmushin da ya yi min da gani na karfin hali ne gaishe shi nayi ya tambaye ni ya muka kwana na dan jima wurin sa kafin na tashi na koma dakina. Kwanakin da suka biyo baya shiri muke tayi na gyaran jiki ni da Amarya Hadiza wadda na lura yanzu wani irin so take wa angon nata, ni dai ce Tahir yaki barin gyaran nawa ya dire kulllun kawo min hari yake.

Tashin mu kuma ya ki fadin rana ya ce mu zama cikin shiri kawai dan haka na shishshiga makota da ake gaisawa na kuma yi wa yan ajin mu na islamiyya. Wata na guda muka sha bikin tarewar Hadiza wanda Kamal ya matsa ya kasa hakurin in yi arba’in kamar yanda ta ce ni kuma nayi taro sosai har yan gidan mu sai da suka zo ba a maganar yan Kankara wadanda suka zo kwai da kwarkwata, mun mika amarya dakinta kokari sosai Tahir ya yi wurin shirya mata daki.

Basma bata dawo ba har lokacin ranar da aka kai ta washegari duka bakin suka koma gidajen su, ina bedroom dina Tahir ya shigo ya same ni “Shirya ki raka ni wani wuri.” da mamaki na dube shi “Ina zamu? Bai tanka ba ni ma sai na ci gaba da shirina ganin na gama ya ce “Mu je” na bi bayan sa har inda motarsa take muka shiga ya ja muka bar gidan. Mamaki na ji ganin sabon gidan mu ya kawo ni, tamfatsetsen gida ne me part hudu sai wurin masu aiki, daga cikin sashen kowaccen mu aka yi mishi nashi wurin, wanda ya ce shi ne nawa ya bude muka shiga na shi ne farko daga ka shiga shi muka fara shiga, kafin muka fito muka wuce nawa three bedroom flat ne daga an wuce falo sai bedroom na farko a wata kwana yake sai biyun sune a tare suna kallon juna na farkon muka fara shiga wanda yake babba ne sosai bayan gado ha da kujeru aka shirya a ciki ya ce in bar wa Daada da yara na ce “To” sai muka wuce sauran guda biyun sai mamaki nake a raina wai wannan uwar dukiyar da aka shirya har ana hangen wadda ta fita, ina nufin mahaifin Basma wanda ya ce ayi mata wanda ya fi namu duk da su bai riga ya sa furnitures din ba suka kara mai. Ya dube ni “Wadannan kuma sune namu” dan kallon sa nayi “Naku kai da wa? ba ga naka can ba.”

Kai ya girgiza “Na daina raba daki, daga raba dakin ne yanzu ya cuce ni yau kwananki nawa da haihuwa amma guduna kike kin ki dawowa dakina da kwana? Wancan a suna yake nawa amma nayi shi dan Hajiyata ne zan dauko ta ko da ba za su bar min ita duka ba akalla ta rika zuwa tana hutawa” ganin yana nuho ni yasa na soma ja da baya jikina na rawa dan tsanar da nayi wa ciki da goyo, sai dai shi ma din abin a tausaya mishi ne mata hudu ka dawo ba ko daya dole ya shiga wani hali.

Ban ankara ba na kai bango ya iske ni ya matse ni rokona yake in tausaya mishi in ba shi hakkinsa kan ba yadda zan yi na sallama ya yi gado da ni biji biji ya min ya kuma tsallake ni ya je ya tsarkake jikinsa da ya fito ne yake ce min zuwa anjima iyalan gidana za su dawo saurin bude idanuwana nayi daga lullumshesun da na fara.

“Kamar ya za su dawo? Ya ce, “Ke kin dawo kenan” saurin tashi nayi sai ga ni zaune “Wane irin tashi ne haka ba a yi sallama da kowa ba ko Haj Hajara sai dai ta ji na tafi? Ya dubi agogon hannunsa “Idan an kwana biyu kya je ki yi musu, ni fita zan yi.” ya fice na bi kofar da fita da kallo cikin tunani. Na tashi nayi wanka na tsaftace jikina, su Daada suka iso a wurin ta nake ji da ta shiga yi wa Haj Hajara sallama bata same ta ba ta fita. Har wata boyayyiyar ajiyar zuciya na fidda, Indo da laraba suka yi girki wadanda sune suka goyo min yaran.

<< Wa Gari Ya Waya 47Wa Gari Ya Waya 49 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×