Skip to content
Part 49 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Sai washegari Hadiza da Asiya suka zo min wuni. Ni kuma da aka kwana biyu na koma can tsohon gidan na kwaso suturuna, da yan abubuwan da nake so. Kayana na yanke rabawa yan’uwana, kamar yanda Tahir ma yan’uwan na shi ya ce su kwashe na shi.

Basma ta dawo kafin dawowarta sai da aka zo aka shirya mata wuri ta dawo da masu yi mata aiki su biyu, ba laifi an samu canjin zama tsakani na da ita, na kan shiga wurinta mu gaisa duk bayan kwana biyu, to ita ma ta kan shigo jefi jefi.

Kawu Attahiru ya shawarci Tahir bayan na Asibiti da ake wa Basma kan rashin haihuwarta su gwada addu’a ko Allah zai sa a dace daga likitocin da suka duba ta sun ce za ta iya yuwuwa ta haihu. Kawun ke yo addu’ar a ruwan zamzam, Tahir kuma ya kawo mata. Ni dai sai addu’a nake Allah ya tsare ni da yin gwarne duk da dai iyakata wahalar ciki sai nakuda raino ina da masu taimaka mini, ga yaran na samu ba masu rigima bane musamman Sadiq yana da matukar hakuri ko yaushe hannunsa na cikin baki.

Ban kuma ga fuskar tunkarar Tahir in ce zan yi tsarin iyali ba alhali ya dade bai samu haihuwar nan ba. Wata rana na fito kwashe shanyan kayan yaran da Indo tayi musu ta fita zuwa kasuwa bata kwashe ba, igiyar bayan dakin Basma take, daidai saitin windon bedroom dinta, ina kwashe kayan ina ninkewa muryar Basman na rika jiyowa da wata da ban san kowace ce ce ba.

“Matsala gare ni Fauziyya, wadda ban taba sanar ma wani ba, ita ta ja min na zama koma baya wurin miji. Ina tunanin kin taba jin ana fadin wasu kyawawan matan kyan zahiri ake basu ba a basu na badini? Kamar yanda wasu munanan matan ake basu kyan badini” sai na ji muryar abokiyar hirar ta ta ta ce,

“Me kike son gaya min Basma? “Abinda nake son gaya miki ba ni da ni’ima ta yaya mata Fauziyya, Tahir ya taba bani misali da kaza a dafa ta ba gishiri ba Maggie.” “Cabdijam! shi ne kuma kike zaune haka ba ki amfani da magunguna? “Tahir ya nema min na Islamic amma haka nan dai nake ba canji.”

“Lallai Basma ke wace iri ce shi ne kika zauna a haka cikin kishiyoyi? Saurin barin wurin nayi cikin wani madaukakin mamaki da ya rufe ni dakina kawai na wuce na hau gado dama shi yasa Tahir bai damu da Basma ba cikin matansa, duk da kasancewarta macen sakawa a gaban mota? dan duk cikin mu babu wadda tayi kyanta. Wani tausayinta na ji ya kama ni gaskiya Basma tana cikin jarabawa me girma.

Sai kuma na ji Tahir ya kara burge ni a karo na barkatai dan ba kowane namiji za ki kasance da wannan matsalar ya yarda ya zauna da ke ba wulakanci, ko wani banbanci. Motsin da na ji yasa ni daga kai “Tahir ne rike da hannun Areef da Mimi yanda na dubi fuskarsa ba walwala ni ma sai na tsuke tawa, yaran suka hawo gadon suka haye ni suna tumurmusa ta, shi dai yana tsaye yana kallon mu.

“Ki shirya gobe mu je Dutsinma ki wuni sai mu wuce Kankara mu kwana jibi mu dawo.” Ban amsa shi ba dan wani takaici da ya kulle ni shi ma daga haka juyawa ya yi yaran suka sauka da gudu suka bi shi. Tun haihuwata ban je gida ba. Kullun fama nike da Tahir yana cewa in saurare shi, har Sudes ya yi wata hudu da ban da yanda zan yi da shi sai na fara mishi fushi a satin nan, shi ma sai ya share ni dan haka a yan kwanakin nan ni da shi ba me shiga harkar wani, wai kuma yanzu ya zo yana gaya min wuni daya zan yi, hawaye na ji na taho min na share har kanwata Aisha ta haihu sun yi sabon gida sun tare, dadi daya na ji gobe sunan matar yayana Isuhu zan ga yan’uwa gaba daya a gidan sunan. Wayata na janyo na kira Ummata labarin zuwana a gobe na bata, sai na kira Hafsa da muka ajiye waya shiri na soma.

Washegari sammako muka yi muka kama hanya bamu tafi da Daada ba dan mun bar mata Areef da Mimi daga Sadiq sai Sudes muka tafi da su sai Hussaina dan ta taimaka min da hidimar yaran. Mun shiga Dutsinma tara na safe kai tsaye gidan mu muka sauka, mun shiga tare da Tahir daga bisani ya fita ya bar ni nan Hafsa ta zo ta same ni sai muka tafi gidan sunan tare.

Bayan na shiga gidan su na gaida mahaifiyarta. Na shiga cikin yan’uwana ana ta hira sai Aisha ce bata zo ba an ce ciwon nono take fama da shi, na ce idan zamu wuce zamu biya in gaishe ta in mata barka.

Na idar da sallar La’asar ina gyara fuskata kiran sa ya shigo in fito nayi sallama da kowa Nura kanena da Aunty Wasila ta kira a waya ya kawo mata sako na nemi mu je tare ya nuna min sabon gidan nasu, sai da na shiga motar na zauna sai na fada wa Tahir mu dan biya gidan kanwata da ta haihu in yi mata barka in kuma gaishe ta dan tana fama da ciwon nono, agogonsa ya kalla.

“Ban san magrib tayi min a hanya” na ce “Ba dadewa zan yi ba” na leka na ce Nura ya shigo shi ya nuna mana hanya har muka kai gidan kofar gidan akwai shaguna gaban shago daya a ciki maza ne zaune su uku.

Mun fito ni da Nura ina sakale da da Sadiq a kafadata Nuran ya dauki Sudes, daya daga cikin mazan da ke zaune ya taso a take na gane shi, duk da jiki da ya yi akan yanda na san shi shekarun baya Abakar irin dogayen mazan nan ne masu alamar karfi farin bafulatani, nufo ni ya yi ni kuma nayi saurin shigewa cikin gidan gabana na faduwa, sai ya karbi Sudes hannun Nura ya kuma hana shi tafiya yana mishi tambayoyi game da ni.

A cikin gidan na samu Aisha ta samu sauki hira kadan muka taba na mike sai godiya take min kan sakon da na aiko mata lokacin da ta haihu, ta sa hijab ta biyo ni dan ta gaida Tahir har lokacin Abakar na dauke da Sudes, Nura ya karbe shi muka karasa gaban motar.

Tahir ya sauke glass suka gaisa da Aisha ta koma ciki Nura ma yaron ya miko ma Hussaina ya ce ba sai ya bi mu ba mashin zai hau zai shiga kasuwa. Na zauna gabana ya kuma faduwa ganin yanda fuskar Tahir ta koma, ya ja motar muka bar wurin text na tura ma Nura na tambaye shi sun yi wata magana da Tahir ne raply ya maido min duk kan su sun tambaye shi.

Gabana na ji ya tsananta bugu, na lumshe ido ina jero addu’ar ALLAHUMMA LAA SAHLA ILLAH MA JA’ALTUHU SAHLAN WA’ANTA TAJ’ALUL HUZNA IZAA SHI’ITA SAHLAN Kukan Sadiq yasa ni bude idona jin kuma Tahir bai ce mu ci kan mu ba ya kara tabbatar min cikin fushin yake har na samu yaron ya yi shiru.

Wurin Haj muka fara sauka har aka yi sallar Isha’i ina wurinta sai ga Hadiza ta shigo dan suna garin sun zo duba uban mijinta da ya karye sai da muka gama hira ta wuce gida ni ma muka tafi namu gidan ni da Hussaina shirin kwanciya muka yi muka kwanta na dade barci bai dauke ni ba jin shiru Tahir bai shigo ba, sai da na farka cikin dare na gan shi kwance a falo kan kujera.

Ko da muka karya da safe shirin tafiya muka fara, karfe tara na safe muka fita zuwa sasan Haj, yaran ta ce a dora mata kan cinyarta tana mana maraba ina cikin gaishe ta Tahir ya shigo shi ma cikin shirin tafiyar yake ya zauna ya fara gaishe ta ya ce, Ku shirya Haj yanzu zamu wuce” ta dube shi “Amma ka daure ku shiga ku gaida malam Hashimu, na gaya maka mashin ta kade shi ya karye a kafa.”

Dan bata rai ya yi. “Kin dai matsa Haj, na bada sako a ba shi, amma ko abinda zai tuna min da Halima ban so ballantana in shiga gidan su in gan ta.” Ta ce “Ka dai daure, ai ba dan ita za ka shiga ba.” ya dauki Sudes ya mike Haj ta min “Ke ma tashi ku je tare.” na mike dan dama ina son zuwa dakin Hadiza na gidan amma ban san yanda zan yi in shiga gidan su Halima ba.

Yana tafe ina biye da shi Hussaina na rike da Sadiq, a tsakar gida karkashin bishiya aka yi ma tsohon shimfida, mutan gidan suna ta sannun ku da zuwa, muka zauna a tabarmar da aka shimfida mana muka gaida tsohon yana ta shi ma Tahir albarka da sakon da ya aiko mishi suka karbi Sadiq sai murnar ganin sa suke, mahaifiyar Halima ta karbi Sudes sai sannan na lura da Halima kan wata shimfida nesa da uban gaba daya ta dada fita hayyacinta kanta a kasa yake kanwarta baby ta je ta dora mata Sadiq a cinya, ni dai mikewa nayi na shiga wurin Hadiza mun gaisa nake tambayarta yaushe za su dawo?

Ta ce da dai ta roke shi ya bar ta sai wani weekend din idan ya shigo sai su koma tare, amma daga zamu tafi da Haj gobe da safe idan zai yi sammako za su koma tare. Tare da ita muka fito ban ga Tahir ba na san ya fice na ajiye wa baban Halima kudi gefen shinfidar sa nayi musu sallama muka tafi tare da Hadiza, mun samu Haj ta kintsa sai muka yi sallama da mutanen gidan muka kama hanya.

Kamar yanda Tahir ya ce da isar mu dakin shi na bude nayi wa Haj iso, su Laraba suka tarbe mu da abinci, har lokacin Tahir fushin sa yake sai da muka zo kwanciya ya yi min tas! Dama ina son ganin tsohon mijina dan in wulakanta shi na ja shi ya je ya gan shi. Duk rantse rantsen da nake mishi bai sa ya saurare ni ba, nayi kuka me isa ta har sai da na ji kaina ya fara ciwo na kwanta lamo zuciyata na min zafi.

Kwana biyu ya dauka yana fushin ana ukun na kwanta sai mutum na ji bayana na san ya huce kenan, kwace jikina nayi na sauka na bar mishi gadon dayan dakin na shiga sai dai abin mamaki babu key din kofar jiki dole na fito da na rasa ina zan nufa sai na shige dakin Haj zaune take kan kujera rike da carbi, gadonta na haye na kwanta ta ce “Ina yaran?

Na ce “Sun yi barci” sai ga Tahir zama ya yi suna hira sama sama kafin ya ce ki zo mu je mu bar Haj ta samu ta kwanta.” in bangon da ke dakin ya tanka ni ma na tanka Haj ta ce “Tashi Ummulkhairi kin baro yaranki na ce “Ki yi hakuri nan zan kwana.” haba ta rike “Wane irin nan? To akwai abinda kayi wa yarinyar nan me hakuri Sodangi, har ka kure hakurinta.

Yi hakuri, Ummulkhairi ki je wurin yaranki.” kuka na kama yi dan bakin cikin azabtar da ni da ya yi na rashin magana da baya min. Haj ta rufe shi da fada ta inda take shiga ba nan take fita ba karshe ta rarrashe ni na sauka gadon ina goge fuskata da dankwalin kaina na fita dakin na yi sa’a yaran ba wanda ya motsa, na kwanta can karshen gado Tahir ya hawo gadon ya kamo ni yasa a jikinsa albarkacin hakurin da Haj ta bani na hakura rarrashina ya shiga yi har ya ciyo kaina na hakura zuwa safiya mun shirya radam.

Sati guda da dawowar mu sai ga yayyin Tahir su biyu, yaya babba da yaya magaji, a dakin mahaifiyar su suka yi masauki ni kuma na tsaya tare da su Laraba muka shirya musu abincin tara me kyau. Sun zauna tare da Tahir da mahaifiyar su wai daga gidan su Halima ne suke ta aike suna rokon a basu Sadiq, dama na ji wurin Hadiza ta ce tun zuwan mu Halima ta ga danta ta tashi hankalin kowa wai a karbo mata danta idan yana hannunta Tahir zai rika daukar dawainiyarta.

To duk yadda suka kai ga bugawa basu ciyo kan Tahir ba a ranar suka juya. Sati daya tsakani aka kara tado wasu dattawa hada tsohuwa dan yadda ta birkice musu nan Haj ta zaunar da Tahir ta ce ya basu ba’a jayayya kan da. Allah ya raya shi, cikin matukar bacin rai ya zo ya karbe shi a hannuna ya kai musu.

Duk da sabo da nayi da yaron kowa san barka yake min da aka karbe shi. Wata guda kuma da karbarsa ya kamu da bakon dauro wanda ya yi mishi mummunan kamu suna ta aike a bada kaza a bada kaza na magani Allah ya karbi ransa wanda aka ce Halima dan karamin hauka tayi.

Allah ya taimake ni har sai da Sudes ya shekara uku sannan na samu wani cikin, cikin hukuncin Allah kuma tare muka samu da Basma yammata muka haifa duk kan mu, inda na hada yarana hudu, Tahir ya sauya mana gida sai ya bada wannan haya ya gina wani can kusa da gidan su Asiya ya ce wancan saboda part biyu da ba mutane ka da su lalace zaman mu lafiya da Tahir har Basma dan ita din ba me matsala ba ce.

Tsakani na da Ubangiji sai godiya bisa ni’imominsa a gare ni Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah.

Godiya ga Allahu subhanahu wataala da ya bani ikon kammala wannan labari. Kuskuren da ke ciki ina neman Allah ya yafe min ina fata za a dauki abu me amfani a watsar da mara amfani. Bissalam

Taku Maryam Ibrahim litee alumfashi Mu hadu a RANAR NAKA.

<< Wa Gari Ya Waya 48

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×