Tahir wanda ke kwance bisa gadonsa, idonsa yana kallon sama ya tada kai da hannayensa, a zahiri za kayi tunanin kyakykyawan rufin dakin nasa yake kallo, amma a baɗini tunani me zurfi ya faɗa. Matan da ya tara, kowacce da irin matsalarta, saboda rashin dace da samun me aikin da ta iya girki, yasa shi saka dokar kin amincewa da ƴan aiki su girka abincin da zai ci.
To matan nasa ma, Basma da Latifa sai godiya, abincin suka kwabo maka shi, sai dai ka ci kar ka mutu, Ummulkhairi da Halima ne kaɗai ya dace ta. . .