Kwance take idanunta a lumshe fuskarta fayau. fara ce amma ba za ka ce mata sol ba, eyelashes ɗinta zara-zara kwance luf a saman idonta dake lumshe, hannuwanta da kafafunta sun sha ƙunshi ja da baƙi Wanda da ka gani ka san na amarya ne ko ba a faɗa maka ba.
Gefe daya kuwa mahaifinta ne zaune dirshin a ƙasan tiles sai kuka ya ke kamar ƙaramin yaro, a ɗayan gefe mahaifiyarta ce an rirriƙeta tana kuka tana fizge-fizge kamar wacce ta kamu da cutar hauka domin ta gama fita a hayyacinta, ga jami'an. . .