Zaman da Yaya Almu ya sani na yi a sashin Umma ya sa baki ba su yanke ba a wurin, kowa ya zo nan din dai yake sauka tamkar tana nan.
Hakan sai ya sani a cikin kidima da ayuka masu yawan gaske, don sai na zamo ni ce mai karbar su, sai na sauke su anan sannan na ke kai su wajen su wato masaukın su ni ke tsayawa in ga an kai musu wadataccen abincin da zai ishe su, kuma akan lokaci in kuwa gari ya waye ina idar da sallah zan je in ga na ba. . .