Washe garin ranar tun da sassafe kafin ma'aikatan asibitin su fara zuwa na tattara yan kayayyakina da niyyar sulalewa na gudu amma sai nayi tunanin idan na bar nan ina zanje sai kawai nayanke shawarar zama amma zanci gaba da bincikena a sirrince.
Haka naci gaba da zama ina bincikena a hankali na kuma cigaba da bin duk wata hanya da zanbi na tabbatarwa Dr Aminu cewa Hafsat fa gaskiya ce da wannan tunanin nawa kuwa watarana bayan mun hadu da ita na faki idonta na dauke wani USB cable a cikin jakkarta dan na nuna musu nabbatar musu. . .