Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Wani Rabon by Deejasmaah

She’s so sweet 1

Tunda muka dawo gida ba mu wani zauna ba fad’i tashi kawai mukeyi daga wannan zuwa wannan, hidima sun taru sunyi min yawa saboda komai ni ce a gaba tun ba a shiga hidimar sosai ba har na fara gajiya irin haka ina ga in an shiga bikin ai ina ganin bazan ganu ba tun daga lokacin na fara jinjina bestie da irin k’ok’arin a hidindimu na bata tab’a nuna gajiyawarta a lamura ba.

Lefe ake shirin kawowa tun safe ta gudo gidanmu wai kunyar ‘yan gidansu take ji ganin zuwanta yasa nima na kwanta a kusa da ita dama gidansu nai niyyar zuwa to tunda ita tazo sai na fasa fira muka duk’ufa yi kamar an dad’e ba a had’u ba,  girki muka yi tare da sake gyara gidan muka sake kwanciya kamar marasa mafad’a.

“Bestie wai me ye amfanin kwanciyarki a nan ?” Ta tambaya tana mai kallo na hararar ta nayi tare da cewa “in ban kwanta ba goya ki zan yi” itama hararar tawa tayi tareda cewa “in ma kika goyani ai ba laifi kika yi ba besides, yanzu ni ‘yar lallashi ce.” Ta k’arashe da zolaya

Dariya na k’yalk’yale dashi tare da cewa “lallashi indeed, amma ai ba nawa ba ko sai dai na Yaya Sahal” na fad’a ina mai kashe mata ido d’aya “dallacan ni ki tashi ” ta fad’a cikin son gujewa maganar domin yanzu da an d’auko tad’in auren gocewa take yi wai ita tana tsoron aure.” Wai in na tashi me zan miki ?! To na tashi menene ya faru?”

Gyara zama tayi tana fuskantata ba tare da tace komai ba sai bakinta da yake motsi ba tare da fitar harafi ko d’aya hakan yasa k’irjina ya fara bugawa jijjigata nayi tareda cewa” what’s wrong bibti? ” ajiyar zuciya tayi kafin tace ” Nothing is wrong babe…it is just something that is worrying me…But ina so ki fahimceni please…kar ki min bahagon fahimta ” kallonta nayi da kyau kafin nace “OK inajinki” Ina mai tattara hankalina kaf a kanta.

Ehmmm….lemme ask you first…Hmmmm what do you think of Sahal?” ta tambaya tana mai kallon idanu na shiru nayi don ban ma san me zance ba wannan wani irin tambaya ne kuma daurewa nayi tareda cewa” ban gane me kike magana akai ba…What about him?”

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na barkatai kafin tace” Ina nufin me za ki iya fad’i akan Sahal when someone ask you about him and how much can you rate him as a husband” kallon tsaf nai mata kafin nace ” Sahal is a nice person,yana d’aya daga d’aid’aikun mazan da na sani a rayuwata kuma zan iya bada shaida akanshi a koina. Shi d’in mutum ne mai tsananin kirki da kulawa ga girmama lamuranki da duk abinda ya shafe ki sannan kuma yana da ibada ilimi da kuma wayewa. Muna mai fatan ya kasance miji Nagari domin dukkan hali da d’abiun shi sun nuna hakan”.

Murmushi tayi kana tace” kina ganin cewa nayi dace da miji kuma abokin rayuwa?” dafe kaina nayi don tambayoyin ta sun fara yawa. “Uhmmm ba ma ke ba ko wata mace burinta miji irin Sahal domin ya tara duk wasu characteristics na muradin mace ga mijin aure, so ba abunda za mu yi miki sai tayaki murna domin Allah ya baki mijin da za ki yi alfahari dashi a matsayin miji uban y’ay’a kuma abokin rayuwa na har abada.” Na bata amsa Ina fatan hakan ya zama tambayar k’arshe don ban k’aunar su ko kad’an.


“Yauwa za ki iya auren namiji irin Sahal?” Ta sake tambaya a gajarce na bata amsa da “eh mana.” murmushi ta kuma saki kafin ta ce “then marry him…Let him be our husband…”

A firgice na mik’e ina mai kallonta jikina har wani rawa yake yi ‘kaiiiii! This girl can’t be normal cos lafiyayyen mutum ba zai yi hakan ba’ tambayar kaina nayi. “Shin ko dai Aljanu gareta ne?”

(“In ma aljanu take da ke ce ta farkon da zaki fara sani ai)”.

Katse mini tunani tayi ta hanyar takowa gabana tare da rik’e hannuna.” Are you sick or possessed?” Na tambaya ina mai tab’a wuyanta, ture hannuna tayi tare da cewa “babu abunda yake damuna lafiyata k’alau. Damuwarki ce kawai damuwa ta….” Katse ta na yi a hasale

“Noosrah Maikwanoni kinga alamun ina cikin damuwa ne? How on earth za ki yi wannan tunanin? Is it because banda miji ko kuma saboda ban samu damar aure bane? Shin na tsufa ne har haka shiyasa kika fara jin tausayina ko me? Ke ma kina tunanin ba zan auru ba ko?!” Hawaye ne suka fara sunturi a kunci na ban tab’a tunanin rana irinta yau zai zo gareni ba, saboda Allah baiyi zan yi aure ba shine Noosrah zata b’ullo da wannan maganar lallai kam!!! Dafa ni tayi itama tana hawaye.

“Dama akwai randa za ki zargeni da miki shagub’e ko gori ?! Kar ki manta cewa ke d’in jinina ce abar alfaharina kenan yi miki gori daidai yake da yima kaina…”

Ture hannunta na sake yi tareda hayayyak’o mata, “in ba hakan ba to menene? Ehhhh nace menene ? Kallon cewa yanzu banda wani madafa a rayuwata kike yi ko?”


Kuka ta fashe dashi tare da duk’awa a wurin juya mata baya nayi Ina mai k’ok’arin tsaida hawayen da yake zubo min amma na kasa don sai k’ara zuba yake yi babu alamar zai tsaya juyo dani tayi tana mai cewa,” this is actually not what I mean…….ta ya za ki yi wannan tunanin Babe, Babu komai a zuciyata sai alkhairi. Burina Inga kema kin samu natsuwa kamar kowacce mace shiyasa nace ki auri Sahal ba dan komai ba…”

“Me yasa kike tunanin cewa zan iya auren mijinki, ko mutuwa kika yi bana fatan hakan, ko na so haka shi Sahal d’in ya ce mi ki zai iya auren mace irina ne? Kar ki manta da abunda ya faru a can baya da irin mazan da suka rabu dani…”

Na fad’a cikin sanyin jiki murmushi tayi itama kafin tace ” Sahal is a family zai iya aurenki in har na mai magana what matters is yarjewa da amincewar ki besides mazan da suka rabu dake a baya saboda ke d’in ba ajin auren ki bane, I believe Allah yana miki tanadi mafi alkhairi and I somehow believe that Sahal might be the man for you…”

Dariya na k’yalk’yace dashi tare da cewa “sannu hajiya, but I can’t marry him, so you can rest, in dai har kin yarda cewa Allah has greater plans for me then believe that Sahal can’t be the man for me, for he’s been yours since from the beginning, if I can’t add to your happiness then ba zan zama reason da zan rage miki jin dad’in rayuwa ba, so kar ki sake tada wannan maganar please.”

Gyad’a kai kawai ta yi ba dan ta amince ba sai dan ba yadda ta iya dani gyalena na yafa tare da cewa “ni na tafi wurin kawo lefe” ban bata damar magana ba nai waje bayan na d’auki wayata, baki ta sake tana kallona wato avoiding d’inta nake yi domin tuntuni na gaya mata cewa bazan je wurin kawo lefen ba amma daga wannan maganar har na tashi.

Gidansu na nufa ina mai sak’e-sak’e a zuciyata na tarar dangin ango har sun tafi masha Allah nake ta fad’i domin kayan sun had’u ba a magana mutanen dak’in na gaisar kana na nemi wuri kusa da Anty Nafeesah yayar su Noosrah na zauna muna bud’e kayan tare muna yabawa

“D’auke min kaya ku kai min cikin d’aki naga harda masu bak’in jini a wurin kayan.” Shi ne maganar da ta katse mana firar da muke yi k’asa-k’asa Mama ce ta fad’a tana mai nunawa wasu almajirai kayan duka d’akin suka d’ago suna kallonta tashi Anty Nafeesah tayi tare da cewa “haba Mama wannan wani irin magana ne?”

“Auuuu Allah!? Wato so kike mu zuba ido yadda wasu suka kasa samun miji itama d’in ta kasa samu ko?” Ta fad’i tana mai rik’e baki jikina fara rawa yayi domin ba yau ta saba mun habaici ba ta cigaba da cewa “ku zo ku kwashe kayan nan nace!!” Da sauri ko suka taho izuwa kan kayan kwashe su tass suka yi suka nufi ciki dasu.

Kallona Anty Nafeesahr tayi kana tace “Mama dan Allah ki dunga karantawa mana bai kamata ba wallahi ba fa a k’addarar ko wata mace bane aure da wuri ba…” Da sauri ta katse ta da cewa “dallah can rufe min baki sakarya kawai da kike wannan maganar ni na hanata tai aure ina ce bak’in fentin da yake bin gidansu ne yake sa mazan guduwa? In ma haushi za a ji sai aji na uwarta ba nawa ba…”

Ban tsaya jin me zata k’arashe fad’i ba na nufi k’ofar gidan a guje hawaye nake yi ba na ko ganin gabana gidanmu na nufa ina mai tsiyayar hawaye hakan yasa na nufi d’akin Fav kawai na kwanta ina jin kaina yana wani irin sarawa kamar zai tsage gida biyu…

Mamar nan fa ba uwar bari ba ce

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wani Rabon 2Wani Rabon 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×