Skip to content
Part 1 of 18 in the Series Warwara by Haiman Raees

Jagaba

Bismillah da sunan Rabba,

Wannan da ya yo ‘yan Maraba,

Ya aiko manzo mai haiba,

Muhammadu bai taɓa ƙarya ba,

Allahu kai na saka a gaba.

2.

Tsira da aminci mai girma,

Ga Manzon nan mu yo hidima,

Ina roƙon ai mini alfarma,

Dominka in samu ni’ima,

Ranar kowa ke neman alfarma.

3.

Allah ka san ban zaɓa ba,

Kuma dama ban yi niyya ba,

A zuciya ban yi zato ba,

A mafarki ma ban hango ba,

Sai ga shi na samu Jagaba.

4.

Mun yi addu’a kafin mu zaɓa,

Kuma mun je har mun zaɓa,

Allahu kuma shi Ya zaɓa,

To Allahn za mu saka a gaba,

Butulci sam ba za mu yi ba.

5.

Allahu yau ga jagaba,

Wannan da Ka sa ya shige gaba,

Tabbas yau shi ne a gaba,

Muna rayuwa yau yana gaba

Biyayya kau ba za mu ƙi ba.

6.

Tunda Allah shi Ka zaɓa,

Haiman ko ba zai yi butulci ba,

Biyayya ba za na ƙi ba,

Du’a’i ba zan daina ba,

Akan mulkin nan na Jagaba.

7.

Fatanmu ya zamo Uba nagari,

Ya canza salo har ma tsari,

Na mulkin nan maras tsari,

Da cin hanci da yai tsauri,

Mu gudo rafi ga tsandauri.

8.

Ƙiyayya ba za mu nuna ba,

Goyon bayanmu ga Jagaba,

Yana nan har zuwa a gaba,

Tunda Allah shi ka sa a gaba,

Bore mu sam ba za mu yi ba.

9.

Shugabanmu kuma Jagaba,

Allahu ya kai ka can gaba,

Ka jamu mu je zuwa gaba,

Al’umma mu yi ta ci gaba,

Da zaman lafiya ba gaba.

10.

Allahu Ka sanya alheri,

A cikin wannan zaɓi,

Ya Rabbi Ka tunkuɗe sharri,

A tsarin wannan mulki,

Muna bayansa Jagaba.

Warwara 2 >>

1 thought on “Warwara 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.