Skip to content
Part 13 of 18 in the Series Warwara by Haiman Raees

ALKALAMI

Jama’a ina sallama,

Ni ne nan alƙalami.

Batu yau nake shirin yi,

Ga ɗalibai har malami.

Ni ne abin tsoro wurin jahili,

Kuma kayan aikin malami.

Ko’ina in har ka je galibi,

Ka ga ana amfani da ni.

Musamman ma wajen ɗalibi,

Balle Uwa Uba wajen malami.

Ban ɗauke wa kowa ba sahibi,

Hatta liman bare na’ibi.

Ko tarihi idan ka duba,

Ni ne farkon halittawa.

Kuma ni aka ba wa umurni,

Komai da komai in rubuta.

Duk abinda zai zam kasancewa,

Ni aka fara ba damar rubutawa.

Shi ya sa in ka lura da kyau,

A ke ɗauka ta da muhimmanci.

Jeka kotu inda ake hukunci,

Ko fada inda ake shugabanci.

Ni makamin ƙare dangi ne,

Mai iya shafe gari ko jahilci.

Wasu na amfani da su raba dangi,

Wasu kuma wajen yaye ƙangi.

Wasu su yi amfani da ni wajen saki,

Wasu kuma su yi wajen rubuta sadaki.

Wani lokaci a yi aiki da ni a yi cuta,

Wasu kuma su yi da ni su bada kyauta.

Ni alƙalami ɗan baiwa ne,

Don haka kowa sai ya gane.

Allah ne Ya zaɓe ni,

Na rayuwa tsawon zamani.

Jama’a da yawa na amfani da ni,

Likita, direba haɗa jami’i.

Ga shi dai arha ce da ni,

Amfani kuwa kamar magani.

Kowa na iya mallaka ta,

Ba bambanci kamar tozali.

Kai dai kawai idan ka siyan,

Ka yi aiki da ni wisely.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Warwara 12Warwara 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×