Bayan sun sallami Boka da kud'i ma su tsoka su ka kama hanyar Adamawa ko da su ka isah gidan yayan shi su ka fara zuwa don mayar mai da motar shi da su ka ara, kai tsaye su ka nufi gidan don sun dad'e da komawa sabon gidan su, Halima su ka tarar zaune a falo Sallamar da su ka yi ta amsa, "ina wuni antyn mu" cewar Buhari yana zama a kujerar murmushi Halima ta yi tace "lafiya lau", "ina yaya?", cewar Buhari "bara na kira shi", Halima ( Afnan) tace ta na nufar d'akin shi. . .