Skip to content
Part 10 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Bayan sun sallami Boka da kud’i ma su tsoka su ka kama hanyar Adamawa ko da su ka isah gidan yayan shi su ka fara zuwa don mayar mai da motar shi da su ka ara, kai tsaye su ka nufi gidan don sun dad’e da komawa sabon gidan su, Halima su ka tarar zaune a falo Sallamar da su ka yi ta amsa, “ina wuni antyn mu” cewar Buhari yana zama a kujerar murmushi Halima ta yi tace “lafiya lau”, “ina yaya?”, cewar Buhari “bara na kira shi”, Halima ( Afnan) tace ta na nufar d’akin shi miti2 se ga su sun fito, gaishe shi Buhari ya yi Saleh ma gaishe shi yayi, Sannan yace “yaya dama motar ce na dawo maka da ita” “haba Buhari ni ai kyauta na baka bawai aro ba, akwai wata ma ita na so ba ka amma ka ba matar ka wannan se ka d’auki d’ayar” dad’i sosai Buhari yaji, sanna su ka mi’ke zuwa wajen da su ke aje motoci, wata sabuwar mota ce nai kyau da tsada ya nu na wa Buhari yace “gashi nan”, tare da bashi key d’in, murna sosai Buhari yayi sannan Yace bari ya gwada ya ga ko aikin mallam ya yi yace “yaya da ma ina bu’katar 3millon ne ina so na fara sana’a ne to muje na rubuta maka check se ka cire ko” “to yaya nagode sosai”, “ka dai na min godiya kai fa ‘kanina ne guda d’aya da na ke da shi komai nawa na ka ne”, da haka su ka yi sallama bayan ya rubuta mai check d’in.

Kai tsaye kud’in su ka je su ka cire, Su ka raba dai-dai sannan Saleh ya nufi Jigawa wajen iyalen shi, don yau satin shi biyu da barin gidan don ma matar shi akwai hakuri.

Bayan shekara biyar, abubuwa da dama sun faru cikin kuwa har da rasuwar Al-amin, Abubakar ya ji mutuwar Mahaifin na su, yayin da Buhari ko a jikin shi tun da ya samu Naira ga kuma gadon Baban su da ake shirin rabawa, Bilkisu ma ta haifi wata ‘ya mace ta ci suna Asma’u yayin da ta na da wa ni cikin yanzu, Afnan kuwa har yanzu shiru hakan kuma be da mu Abubakar ba ko yayi tunanin ‘kara aure ba.

An raba gadon Al-amin kowa an bashi na shi, Khadija ta bar garin Adamawa ma ta koma can Jos dangin mahaifiyar ta kud’i sosai ta ke da shi yanzu, don Al-amin yabar dukiya mai tarin yawa da kadara ko khadija ta samu gida biyu da fili biyu, banda Tsabar kud’i ma su yawa, Safiyya ma haka yayin da ta koma d’aya daga cikin gidan da ta gada ta ke she’ke ayar ta, Abubakar da Buhari su ma ba ‘karamin dukiya su ka samu ba da kadara, duniya sabo ya bud’e wa Alhaji Buhari don yanzu ya zama Alhaji daga shi har matar shi Jamila sun je makkah, har Bilkisu ma ya kaita makkah ita da Baba Lami don matar na musu ‘ko’kari sosai, wani had’ad’d’en gida ya gina mu su kamar a ‘kasar waje, yanzu Bilkisu na cikin hutu, don baza ka taba gane ta ba don ta zama wata babbar mace yanzu ta na da shekara 25 kenan, Buhari na le’ka su lokaci zuwa Lokaci, don ya na ƙaunar matar shi uwa ƴaƴan shi.

Bayan shekara biyu

Bilkisu ta haifi ‘yar ta mace ta ci suna Fatima inda tace kuma ita ce autar ta gata sosai yaran su ke samu awajen mahaifiyar ta su ga tarbiya me kyau, duk da kullum cikin maganar Dad su su ke, duk san da Hajiya Bilkisu ta yi mai magana se sun yi fad’a har ta gaji da dena amma tace baza ta fasa yi mai maganar ba.

Bangaren Abubakar kuwa har yanzu ba’a samu rabo ba, shiyasa kullum su na cikin zaga duniya shi da sahibar ta sa, ba su wannan ‘kasar ba su wancen, yau ma kamar kullum sun shirya zuwa Kaduna wajen Abokin shi Ummar don yanzu ma yaran shi hud’u, Fiddauseey ita ce Babba, se Muhammad wanda su ke cewa, Amir, se kuma, Aisha, se Ibrahim su na cemai khalil, sun je anyi zumunci sosai don yanzu ma Halima da Bilkisu sun saba sosai kamar ‘kawaye na tun asali, ko bata je ba tana kwaso yaran ta su je su ayi zumunci.

Alhaji Buhari yanzu ya yi ma kan shi fad’a ya fara sana’a inda ya bud’e shagon atamfofi, a wajen da Baban su ya ke siyarwa ya sa ka wani yaro a wajen, ya bud’e gidan mai kuma sannan kuma ya fara gine-gine, yayin da Hajiya Jamila ma yanzu ta na da wa su kadarori na ta don wankan shi ta ke da taimakon bokan ta, don ba ta raga mai ko kad’an ga zallar rashin mutun ci da rashin girmama wa.

Bara mu waiwaya bangaren Ahmad da momin shi,

Ahmad ya yi aure shi ma ya auri wata ‘yar ‘kanwar momin shi mai suna Aisha momin shi ta nemo mai ita, Aisha yarinya ce mai kimanin shekara 23 akwai hankali hakuri kyau biyayya ga uwa-uba Ilimi du ka boko da Islamiyya su na zau ne ne a India don har yanzu Ahmad be cika zaman Nigeria ba aikin shi ma yana can ne, yayin Halima ta na zuwan har can ta gaishe da Dad ta su na mutun ci sosai kuma da matar Baban na ta Aisha, momi yanzu ita kad’ai ta ke zaune, amma maimuna ta bata ‘ya guda d’aya, don tà dingà ta yà ta wasu aiyukan don momi bata son mai aiki, ga tsufa kuma ya fara kamata, kuma tana jin dad’in yarinyar.

Bayan shekara d’aya Hajiya Safiyya ma ta rasu mahaifiyar Alhaji Buhari, yanzu Khadijah kawai ta rage mallam Bashir ma mahaifin khadija ya ra su, ita dai har yanzu ta na Jos don tana jin dad’in zaman garin.

An raba gadon ta an ba wa mahaifan ta, da kuma Alhaji Buhari don shi kad’ai ne d’anta. Buhari kud’i sun zauna mai sosai yanzu don ga kud’in ga kadara, Shi kan shi Alhaji Saleh yanzu ya zama mashahurin mai kud’i Kakar su ta rasu har yayan shi ma ya rasu, se matar shi Habibah, idan ya ga dama yana waiwayen ta idan kuma ya ga dama kuma ya barta ta na zaune agidan su.

Bayan shekara d’aya, Alhaji Buhari gidan man shi ya ‘ko ne gidan shi ma guda d’aya shima yayi gobara hankalin shi ya tashi sosai don dama duk kud’in da ya ke da su ba su ishe shi ba, Ana haka kuma shagon shi ma na kaya ya ‘kone haka yasa hankalin shi ya ‘kara tashi, hakan ya sa ya kira abokin shi Alhaji Saleh yace su je wajen Boka, sunyi gobe za su ta fi.

*****

Washe gari Su ka yi sammako su ka nufi Zamfara, har wajen boka, bayan sun gaishe shi yace “me ke tafe da ku?”, Buhari ne yace, “boka duk abun da na mallaka se ‘kare wa su ke yi ga shi wa su ba sa shigowa na rasa yanda zanyi ga yayana yasan ina da kud’i yanzu baze bani ba, nima yanzu Lokaci ya yi da zan tara nawa ma su dinbin yawa”, bayan boka ya gama jin bayanin yayi wani mugun dariya sannan ya kalle shi yace, “Buhari kenan Baza ka ta’ba tara dukiya su zauna ba indai yayan ka na doran ‘kasar nan ko ka tara wani abun ba ze ta’ba zama ba, don Taurarin arzi’kin ka sun yi duhu sosai, kuma abu d’aya ne ze haskaka su a yanzu”, cikin tashin hankali, Alhaji Buhari yace, “Menene boka?, ka fad’a min ko ma miye ne zan yi”, “ba wani abu ba ne se dai ka auri matar Yayan ka Halima”, cikin tsantsar tashin hankali Alhaji Buhari ya mi’ke tsaye yace “boka ta yaya zan auri matar Yayana, bayan irin son da ya ke mata”, cikin fushi boka yace, “Ku fita ku bani waje kawai!”, Alhaji Saleh ne ya ba shi hakuri sannan ya kamo Alhaji Buhari ya zaunar da shi, boka ne ya cigaba da cewa “Taurarin arzi’kin yayan ka ya zarce na ka sosai kuma a nawa binciken in dai Yana da rai ko da ace zaka auri matar shi za ka samu dukiya amma ba kamar idan ya mutu ba”, “to yanzu boka se mun jira har lokacin da ya mutu?”, cewar Alhaji Saleh, “ya rage na ku wannan amma ni dai ina jiran ku kuzo da Halima ni zan d’aura mu ku aure”, “to” su ka ce sannan su ka nufi Sokoto don yanzu ya na yawan zuwa, don yaran shi na kiran shi wataran har da Kuka ma dole ya ke bari koma me ya ke yi ya tafi, don wani irin so yake wa yaran nashi da Momin su Hajiya Bilkisu don be ma Hajiya Jamila rabin son ma.

Bayan yaje Sokoto ya yi sati d’aya1 sannan ya koma Adamawa bayan ya yi ya dawo ne kuma ya nufi Jigawa don su san na yi, a gidan shi da ya gina a jigawa su ka sauka don su na shirin tarewa ne, don Hajiya Jamila ta matsa mai don dama da ‘kyar ta yarda ta zauna a Adamawa.

Alhaji Buhari da Alhaji Saleh su na zaune su na tattaunawa don akan maganar boka, Buhari ne yace “yanzu ya kake gani za’ayi, ya za’ayi na auri sadiya bayan Yayana na son shi?” “ba se yana raye tukuna zai hana ka auren ta ba, to abun da boka yake nufi kawai ka ga bayan shi sannan ka auri matar shi kuma dukiyar shi ta zama naka shine kawai zaka samu jin dad’in rayuwa,” wani irin dariya Buhari yayi yace “lallai kam se yanzu na hasaso hakan gaskiya ne ka yafe ni yayana, amma dole ka ba ni waje ka gama cin duniyar ka se nawa”, dariya su ka yi shi da Alhaji Saleh haka su kaci gaba da shirin su har su ka gama su kayi Sallama.

Alhaji Abubakar na zaune a gidan shi kamar kullum shi da matar shi Hajiya Halima su na hira, Halima ne tace, “my dear kwanan nan na ga gaba d’aya ka canza ba yanda na saba gani ka ba, ka dawo shiru ba walwala gashi kullum se ka shiga d’aki shiru, ni abun ya fara damuna”, murmushi yayi sannan ya jawo ta jikin shi yace “ki yi hakuri my wife wallahi kwanan nan bansan me ke damuna ba, banajin dad’i jiki na kamar ina mu ku ban kwana”, ku ka Halima ta fashe da shi tace “don Allah ka daina fad’in haka, kar ka sa zuciyata ta buga”, “to na dai na kin ji” “to” gobe ki shirya muje Jos na gaishe da momi na, tsalle ta daga ta rungume shi ta na jin dad’i don yadda ta ke masifar son Momin, dad’i sosai Abubakar ya ji ganin yadda matar shi ke son mahaifiyar sa sosai kamar ita ta haife ta.

Washe gari sammako su ka yi na tafiya Jos don kafin azahar ma sun isa sosai momi ta ji dad’in ganin su ta yi ta saka musu albar ka da fatan samun zuri’a d’ayyiba, kwanan su uku acan su ka dawo da tsaraba mai tarin yawa wanda momi da ‘yan uwan ta su ka ba su, Momi ta na jin dad’in ganin yaron na ta sosai don tun da ta dawo Jos wannan ne zuwan shi na uku, shi ma yana son zuwa wajen da ta ke, Kasancewar ba su fito da wuri ba, se gabanin magrib su ka iso Adamawa, Sallah su ka yi su ka zauna cin abinci don ya saya musu a hanya don yasan ta gaji sosai baza ta iya girki ba.

Washe gari Hajiya Halima ta tashi da matsanan cin zazza’bi, inda su ka nufi asibiti, bayan aune-aune, aka gano Halima na da ciki wata biyu, murna a wajen Alhaji Abubakar ba’a magana, kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, yayin da kulawa ya ke bawa Halima sosai, har su momi da Ahmad sun samu Labari sunji dad’i sosai.

Yau Alhaji Abubakar ya yi shirin zuwa Kaduna wajen abokin shi Ummar.

Zuwa ‘karfe shabiyu12 ya isa Kaduna, da ya ke, sammako ya yi, bayan sun gama gaisawa da Bilkisu su ka shiga d’akin Ummar bayan sun zauna, Abubakar ya bud’e jakar da ya zo da ita, wa su takar du ya fito da su ma su yawa ya ba shi yace “wannan takardun Gidaje na ne da na Gidan mai da filaye na wanda ba kowa ma ya san da shi ba, se kai, to gashi da sa hannu na na mallakawa abun da Halima ta haifa, akwai wa su ma zan kawo maka duk ka na mallakawa abun da za’a haifa min”, “haba Sadiq wai meyasa ka ke irin wannan maganar”, cewar Ummar, “baza ka gane ba ne, Kwanan nan ina yawan yin mafarke-mafarke wanda ba ze fad’u ba, kuma naje gun wani malami ya fassara min cewa akwai wa ni na kusa da ni ne da yake bina da sharri, ze iya yuwuwa ma ya ga baya na”, “Subhanallahi!, Wannan wanene haka”, “ni dai ka bar shi ko ma waye ne, Allah na ganin shi kawai ka bari ba se na yi wani bincike ba kawai”, “to shikenan Allah ya shige mana gaba” “Ameen” cewar Abubakar ya na mi’kewa ya na fad’in “bara na ko ma kar yamma ta yi min” “to a gaida gida”, “to gida ze ji” Abubakar yace yana fita d’akin, har bakin gate Ummar ya raka shi se da ya fita sannan Ummar ya koma gida zuciyar shi ci ke da Mamakin wannan abu.

*****

Gabanin magrib Alhaji Abubakar ya isa gida, don gudu ya dinga yi ya dawo duk da Halima bata nan taje gidan su don Dad ta yazo shi da matar shi.

Alhaji Buhari da Alhaji Saleh sai shirin su su ke na ganin bayan Alhaji Abubakar har sun samo wa su ri’ka’k’kun mutane da za su yi musu aikin inda su ka saka nan da kwana biyar ma su zuwa, Yau Lahadi sun bar shi zuwa Juma’a ne su far masa.

Alhaji Abubakar ya kira d’an uwansa Alhaji Buhari in da ya shaida mai komai akan abun da ke faruwa amma be fad’a mai komai akan dukiyar da ya bawa Ummar ba, inda ya ‘kara da cewa “d’an uwanan idan na maka lefi ka yafe min don Allah”, Alhaji Buhari, abun ma dariya ya so ba shi saboda yanzu zuciyar shi ta ‘ke’kashe, yace “yaya ni ba abun da kamin se dai ma ni ina neman yafiyar ka idan na maka wani abun” murmushi Alhaji Abubakar ya yi sannan yace “ba abun da ka min idan ma ka yi na yafe”, “to nagode sosai”, cewar Buhari sannan su ka yi Sallama.

Washe gari kuma sammako ya yi na zuwa Jos don ya gaishe da momin shi inda ya shirya ya ta fi shi kad’ai momi ta yi farin cikin ganin d’an na ta bayan sun gama gaisawa da ‘yan uwan momi ne ya shiga d’akin momin na shi in da ya tarar da ita akan sallaya da alama sallah ta idar, “momi na a dinga samu a addu’a”, shafa addu’ar ta yi sannan ta kalleshi ta na murmushi tace “ai kullum kafin na yi wa kai na addu’a se na maka”, “to momi Allah ya amsa”, gyara zama ya yi sannan ya shaidawa momi duk abun da ya ke faruwa, sosai hankalin momi ya ta shi, amma se ta danne don kwantar mai da hankali shi ma, “Saddiq insha Allah ba abun da ze faru se alkhairi ka ji” “to momi Allah ya sa amma momi idan na miki wani abun don Allah ki yafe ni”, “ba abun da kamin idan ma kamin Saddiq na yafe maka, duniya da Lahira” “na gode momi”, yace sannan ya ce “zan zo na koma na bar Halima ita kad’ai” “ai kuwa ya kamata ya jikin nata” “yayi sau’ki”, “to Allah ya sauke ta Lafiya” “Ameen Abubakar yace sannan ya yi mata sallama ya kama hanyar Adamawa.

Yau Laraba yau ne kuma Alhaji Abubakar ya shirya komawa Kaduna wajen abokin shi.

Da misalin sha d’aya11:00 ya isa don sammako ya yi, bayan sun gaisa Alhaji Abubakar ya ciro mai wa su ta’kardu su ma duk na fili ne da kuma kud’i ma su yawa wanda sun kai 40millon sannan yace, “Ummar bawai a aboki na d’auke ka ba, a jinin jiki na na d’auke ka, ba wanda yasan sirrina sama da kai amini na, don Allah ko bayan rai na kar iyali na su wula’kan ta shiyasa na baka wannan kud’in ka kulan min da Halima na, da kuma abun da zata haifa kar su yi marai ci Ummar wannan kamar wasiyya na ke baka” Ummar da kwalla su ka fara fita a idanun shi ya kalli Alhaji Abubakar yace “don Allah ka dai na fad’in haka muna nan zamu rayu tare kuma kai za ka kula da iyalen ka da yardar Allah”, “da hakan ze kasance da na fi kowa jin dad’i, ko ba komai zan so na ga abun da Halima za ta haifa min”, “in Allah ya yarda ma za ka gani” “to nagode sosai” yace sannan ya mi’ke ya nufi waje kamar kullum har bakin gate Alhaji Ummar ya raka shi sannan ya dawo gida.

Washe gari Halima se shiri ta ke don yau zata gidan su don an gaya mata Anty Aisha ba lafiya, bayan ta gama shirin ta tsaf Alhaji Abubakar yace shima ze je ya gaishe ta, tare ko su ka je sun gaishe ta sannan su ka gaisa da Ahmad, Ahmad yanzu girma ya zo kamar ba shi ba ne ke zuwa zance wajen khadija ba amma abun ba wuya gashi har da ‘ya yana shirin samun jika ma Allah kenan.

Sun dad’e agidan sannan su ka je gidan maimuna ma su ka gaishe ta, sannan su ka nufo gida.

Washe gari ta kama ranar Juma’a Alhaji Abubakar bayan ya dawo Sallar Juma’a zazza’bi mai zafi ne ya rufe shi don yana kwance ma har bayan sallar la’asar ma da’kyar ya iya yi, har bayan magrib yana kwance, sallar magrib ma da’kyar ya yi shi sannan ya koma ya kwanta duk da ya sha magani amma ina se ‘karuwa ma yake yi Hankalin Halima ya yi masifar ta shi ta na zaune akan gado shi kuma Abubakar ya na kwance akan cinyar ta bacci ne ya d’auke shi gashi ta na so ta tashi amma kuma bata so ta tashe shi, awannan lokacin da bacci ya d’auki bawan Allah, be san a lokacin ana can ana shirin yanda za’a ga bayan shi ba don Alhaji Buhari da abokan aikin shi su na can sun shirya komi kawai lokaci su ke jira.

Halima na zaune har yanzu don be tashi ba agogo ta du ba har ‘karfe goma na dare, hakan yasa ta d’an motsa don ta tashi hakan yasa Alhaji Abubakar tashi, bata so hakan ba don bata so ta katse mai bacci ba, Murmushi ya yi mata ita ma ta mayar mai, sannan tace “ya jiki?”, “naji sau’ki sosai”, “to masha Allah”, bayan ta gama abun da zata yi ta dawo, kan gadon ta kwanta, muryar Abubakar ta ji yana cewa “Halima idan na ta’ba miki lefi ki yafe min kin ji”, “don Allah ka de na irin wannan maganar” “to idan kina so na de na kice kin yafe min”, “to na yafe maka duniya da lahira da wanda ka yi da wanda ba kayi bama”, murmushi ya yi sannan tace “to na gode sosai my wife” hira su ka cigaba da yi, Abubakar ne “Halima idan mace ki ka haifa asa ka mata khadiha, idan kuma Namiji ne asa mai Al-amin kinji?” shiru ta yi mai, “Halima baki ji ba ne?”, “na ji, amma kace ka dena fa” “to afuwan ya kamata ki yi bacci dare yayi duba har 12:00” “to”, kashe fitilar d’akin su ka yi sannan su ka kwanta har sun fara bacci Halima ne ta mi’ke ta fito don kamar motsi ta ke ji, falo ta fito ta ji ‘kara ana buga falon alamar ana son ballawa da sauri ta dawo ta samu Abubakar ta fad’a mai, ta so wa su ka yi su ka nufo falon su na fitowa ana balla kofar wa su ne su biyar duk sun rufe fuskar su ko idon su ba’a gani don sun saka glass, kuma dukkan su ri’ke su ke da bindiga, d’aya ne ya nufi Abubakar ya seta shi da bindiga tare da nu na mai hanyar cikin falon, ba musu ya biyo shi yayin d’ayan ma ya ta ho da Halima du ka su ka gurfana a ‘kasa, “Don Allah kar ku cutar da mu ku fad’i abun da ku ke so za’a ba ku” cewar Halima, d’ayan ne ya d’auke ta da wani gigitaccen mari wanda se da ta kusa fita hayyacin ta, Alhaji Abubakar cikin fargaba yace “don Allah kar ku cutar min da mata duk abun da ku ke so zan ba ku” d’ayan ne ya nufe shi tare da sha’ke mai wuya Halima ne ta tashi da gudu zata nufi wajen, d’aya daga cikin su ne ya ri’ko ta, kuka ta ke ta na fad’in “don Allah ku bar shi ba shi da lafiya don Allah kar ku cutar da shi”, d’ayan ne ya d’aga bindiga Abubakar ya se ta harbi ya sakar mai a kirji, ihu Abubakar ya saki na a zaba, wani ya ‘kara sakin mai,ihu Halima ta yi tare da fisgewa daga ri’kon da d’ayan ya yi mata ta nufi wajen shi da gudu Naushi d’ayan ya kawo mata dai-dai ta tsuguna ta taro Abubakar da ke shirin Fad’uwa ƙasa hakan yasa naushin ya same ta a ciki wani razananniyar ihu ta sa ki tare su ka kai ‘kasa da Abubakar tanajin ya na furta kalmar shahada sannan ya cika ita ma suma ta yi a wajen, su kuwa d’akunan su ka shiga, bayan sun cire lullu’bin fuskar su Alhaji Buhari ne da Alhaji Saleh se wasu uku amma ba shi ya yi harbin ba.

Ke! duniya ina zaki damu, ace d’an uwa ya kashe d’an uwan shi kuma agaban shi akan wani abun duniya da zamu tafi mu bar shi, lallai Allah ya kawo mu WATA RAYUWA CE da kowa kan sa kawai ya sani.

d’akunan su ka shiga su ka d’auko abun da ze musu amfanin ciki har da sar’ko’kin Halima na gwal, sannan su ka d’auki Halima su ka tafi da ita wanda har yanzu bata farfad’o ba, Wuta su ka cinnawa gidan anufin su wai ace gobara su ka yi sannan su ka nufi gida.

Washe gari ‘yan anguwa su ka tashi su ka ga wuta ya cinye gidan duk da be gama mutuwa ba har yanzu, kai tsaye gidan su Ahmad su ka nufa don sun san nan ne gidan ‘yan uwan masu gida, su ka fad’a mu su hankalin su ya yi mummunan ta shi, hakan yasa su ka kira ‘yan san da aka nufi gidan Ahmad ne da Dad shi, cikin gidan su ka nufa komai ya ‘kone amma abun mamaki gawar Abubakar na nan ba abun da ya ta’ba shi fuskar shi d’auke da murmushi ga kuma shatin harbi biyu da aka mai a kirji nan su ka shiga neman Halima, lungu da sa’ko duk ba su ganta ba, hakan yasa su ka dawo falon inda su ka bar su Dad Ahmad su ka shaida mu su, cewa ba su samu matar ba ‘kila ta ‘kone ne, jin haka yasa zuciyar Ahmad ya wani irin bugawa luuu! Ya tafi ze fad’i ‘kasa Dad shi ne ya taro shi, amma ina! se da ya kai ‘kasa sumamme, hankali Dad ya yi masifar ta shi ruwa ya samo ya yayyafa mai amma shiru da sauri su ka sa shi a mota da taimakon ‘yan sandan aka kai shi asibiti, Emergency aka wuce da shi, don ba shi taimakon gaggawa yayin da Dad ya bar wani d’an sanda a asibitin ya dawo don shaidawa su momi halin da ake ciki a hankalin momi yayi masifar ta shi da jin mutuwar Abubakar ga kuma jikar ta da ba’a tabbatar da inda ta ke ba, lambar momin Abubakar ta nemo don dama ta na da number su na d’an gaisawa ta kira tare da bawa Dad ya yi mata bayani don baza ta iya ba, tashin hankali sosai momi ta shiga da jin mutuwar d’an nata d’aya tilo, inda tace kar a kaishi ga ta nan yanzu za su biyo jirgi su zo, Sallama Dad ya mata ya kashe wayar maimunat Momi ta ‘kara kira itama aka shaida mata abun da ya faru hankalin ta ita ma ya tashi sosai, ko minti talatin ba’a yi ba se ga ta agidan don bata da nisa dama. momi ne tace ta je asibiti ta zauna da Ahmad ita da A’isha, matar shi, su kuma za su je don A d’auko Abubakar a dawo da shi nan, haka ko aka yi maimunat sun tafi asibiti, duk da hankalin momi na kan d’anta amma su ka nufi gidan Abubakar, mutane su ka tarar sosai a kofar gidan kowa ya ji mutuwar Abubakar se hankalin shi ya tashi barin ma ace wai kashe shi aka yi mutumin da ba ruwan shi da shiga sabgar kowa ga mutunci girmama manya ga kyauta duk wanda ya kwana a Adamawa ba zama gaba d’aya ba ya san da Labarin Alhaji Abubakar don shi na kowa ne, da’kyar su momi su ka samu su ka shiga, su na shiga momi ta hango gawar Abubakar kuka sosai ta saki Dad ne ya kamata ya kaita cikin mota sannan ya dawo ‘yan sanda na nan su na bincike, Dad ne ya mi’kawa babban su hannu su ka gaisa sannan yace “ya ake ciki”, “gaskiya Alhaji munyi iya bakin binciken mu mun gano tabbas ba matar agidan ko sun kaita wani waje sun kashe ta ko dai tana wurin su har yanzu don tabbas da ita su ka tafi yanzu abun da ya fi shine ku bada hoton ta ayi cigiya ko Allah ze sa adace”, “to Nagode sosai zan baka hoto zuwa anjima” d’aukan Abubakar su kayi aka fito da shi don sa ka shi a mota a kai shi gidan su Ahmad ko da aka taho da shi sosai mutane ke le’kawa don su ganshi wa su sun ganshi wa su kuma ba su samu ganin shi ba,.

Gidan su Ahmad aka nufa da shi su na zuwa aka shiga da shi wani d’aki, ba jumawa momin shi ta ‘karaso ita da ‘yan uwan ta da yawa, lokacin ma har an masa wanka shiga ta yi tare da bud’e shi wani irin kuka ne ya kwace mata, kuka take sosai ta na fad’in “Yanzu Abubakar waye ya maka wannan aiki Allah ya to ni asirin su” ta dad’e ta na kuka wata daga cikin ‘yan uwanta ne da su ka zo tare ta dafa ta tare da cewa “kiyi hakuri anty addu’a ya kamata ki yi mai don Allah ki dai na kukan nan”, share hawayen ta ta yi ta fara yi mai addu’a yayin da wa su hawaye ke ‘kara zubowa ta dad’e ta na yimai addu’a sannan ta tashi.

dai-dai lokacin kuma Ummar ya ‘kara so, don abokin su da ke nan garin ya fad’a mai, idanun shi jazur da ganin shi kasan ya ci kuka tare da matar shi su ka zo, wajen gawan ya je ya bud’e tare da yi mai addu’a.

Su Buhari kuwa ko da su ka bar asibitin wani gidan shi su ka nufa, sun watsa ma Halima ruwa amma ta ‘ki farfad’o wa hakan yasa su ka barta da nufin da safe su kaita asibiti.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 9Wata Rayuwa Ce 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×