Skip to content
Part 3 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Kallon Momi ya yi, Ya ce”Momi kin kira ni kuma kin yi shiru”

Carab Auta, Ta ce”Laaa! ba ka san yau Dad ze dawo ba?”

Ya ce”ina ruwan ki? Ni ban yi magana da mai kukan kitso ba”

Had’e rai ta yi sosai don ta tsani a ce mata mai kukan kitso dama ya yi haka ne don ta yi mai shiru.

Momi ce Ta ce “Abbas yau Dad d’in ku ze dawo mun yi waya ma da shi yace min zuwa 2:00pm insha Allah ya na sokoto”

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Abbas, Ya ce”Shine Dad ko ya fad’a min, ai dama ina fushi da shi bari ya zo dai”

Murmushi Momi ta yi sannan, Ta ce”kun fi ku sa ai bazan shiga ba anjuma nan ku zo ku bani kunya”

Dariya ya yi sannan ya juya zuwa d’akin shi domin ya ci gaba da karatu, in da Momi kuma Ta ce”Auta je ki kara taso min Asma’u kice zan zane ta idan bata zo ba”

Mi’kewa ta yi da gudun ta domin ita ba abun da ke mata dad’i irin tashin mutum da safe, domin bata ‘kaunar baccin safe ita tsabar fitina.

‘Dakin Asma’u ta nufa ta din ga tashin ta har se da ta tashi.

Ta ce”Je ki zan yi wanka na fito yanzu nan”

“Minti nawa?”

“minti 10”

“Laaa! minti goma ya yi yawa”

Ta ce”To minti 5″

“To”

Tace tare da tashi ta fita.

Da sauri Asma’u ta rufe d’akin ta domin ta san wannan yarinyar yanzu zata iya dawowa, murmushi ta yi na takaici.

“Wai minti nawa? se kace wata irin uwan nan tawa”

annan Ta ce”fati se de Allah ya shirya mana”

Se da ta kwashe minti 20 sannan ta fito kai tsaye falo ta nufa in da ta san Momi na nan, Momi na zaune har yanzu suna fira da autar ta tana bata labarin wani malamin su na makaranta.

Asma’u ne ta shigo yarinya ce me kimanin shekara goma 10 a rayuwa fara ce sosai sannan kyakykyawa ce ta karshe su biyu ne fara re acikin yaran momi daga Asma’u se Abbas, amma auta baza a kira ta da fara sosai ba se de a ce mata choculate color, kuma ita ma kyakykyawa ce sosai.

Da sallama ta shigo falon, Momi ne ta amsa sannan ta samu guri ta zauna kusa da Momi amma a kasa wanda wannan al’adar su ce in dai babba na saman kujera to su a kasa za su zauna, kallon momi ta yi

Ta ce”Momina kin tashi lpy??

Murmushi ta yi sannan, Ta ce”Lafiyar lau”

Sannan ta rankwashe ta, Ta ce”Sannu da bacci don na san ma ba karatu kike yi ba, kina can ki na bacci ko don kin ga anyi hutu ko? Next week za’a koma se mu gani”

Murmushi ta yi, Ta ce”Momi to ai shi yasa nake hutawa kin san fa idan aka koma ba hutu 7:30 mun fita se kuma ‘karfe 3:00pm sannan kuma ga islamiyya fa”

“To ke hutu kika zo yi ne?”

Auta ce Ta ce “Momi fad’a mata dai

Dariya su ka yi dukan su sannan Momi, Ta ce”Bari na wuce d’aki na huta kafin Baba Lami ta zo, idan ta zo se ku yi min magana”

“To” su ka ce sannan ta mi’ke ta shiga d’akin ta.

Sokoto

Bayan Momi ta wuce d’akin ta tabar su a falon suna fira, Auta ce ta ce.

“Anty Asma’u muje compound d’in gida mu yi wasa kinji”

Mi’kewa su ka yi suka fito wajen gida, se yanzu na ‘kare wa gidan ma kallo, gida ne had’ad’d’d’e sosai wanda fad’in had’uwar shi ma kusan ‘bata baki ne.Gidan yana da girma sosai ga komai na more rayuwa akwai, tafiya su ke yi acikin gidan har su ka iso inda a kayi swimming pool a wajen gefe kuma lambu ne, shuke-shuke ne sosai a wajen, ‘bangaren kayan marmari can gaba kuma wajen wasa ne a kayi, kayan wasa ne sosai awajen, abun dai se wanda ya gani.

Sun dad’e su na wasa a wajen, kuma suna yi suna duba baba lami, amma bata zo ba, har su ka gama, su ka koma falo su ka sa ka kallo.

Auta ce Ta ce”Anty Momi fa ta ce muyi mata magana ko kin manta ne?”

“Ina sa ne mana, ba ta ce se idan Baba lami ta zo bane?”

“Kin ga fa yanzu har 12:00 ta kusa, ni dai na tafi na tashe ta”

“To, se kin dawo”

Mi’kewa ta yi ta nufi hanyar d’akin momi, ita kuma Asma’u taci gaba da kallon ta.

Koda ta isa ‘kofar a rufe taji ta, bugawa ta fara yi tana fad’in.

“Momi ki bud’e, momi!! Momi!!”

Kamar a mafarki ta ji a na kwala mata kira bud’e ido ta yi ta mi’ke tare da yin salati, idon ta ne ya sauka akan agogon bangon dake manne a d’akin wanda ya nuna 11:47, mamaki ta yi sosai, ashe har bacci ta yi haka ba ta sani ba, kawai ta kwanta ne ta na jiran baba Lami ta ‘kara so.

Mi’kewa ta yi ta isa bakin ‘kofar da har yanzu Fati bata bar bugawa ba, ‘karasawa ta yi tare da bud’e ‘kofar.

Auta ce Ta ce”Momi baba Lami d’in ma bata zo ba”

“Ok to muje falo”

Fitowa su ka yi falon Asma’u na zaune har yanzu tana kallon ta.

Momi ne Ta ce”Asma’u ki kashe kallon nan mu je kicin ki taya ni wani abun, tunda kin ga baba Lami bata zo ba, da ma tace min ba lallai ne ta zo yau ba, Gaskiya ta na ‘ko’kari sosai ma wallahi”

Kashe kallon ta yi tare da mi’kewa suka nufi kicin d’in domin had’a abincin rana ga kuma Dad su na hanya, su ka bar Auta a falo ta na kwance nan bacci ma ya d’auke ta.

Kaduna

Washe gari

Wanda ya yi dai-dai da kwanan sadiya shida a gidan Baffa.

Kowa ya ta shi lafiya a gidan Baffa in da kowa ya shiga yin harkar gaban shi, Inna ta na had’a musu abun kari, Baffa kuma tun da ya dawo sallar asuba su ka fara karatu kamar yanda su ka sa ba, bayan sun gama ne su ka zo kowa ya karya, sannan yace Garbati da Bashir su ta fi kiwo shi kuma ze tafi gonar sa ya duba domin jiya an yi ruwa sosai a garin, Haka ko akayi, se da yaga fitan su sannan shima ya fita.

Ita kuwa Inna ta na aikace-aikacen da ba’a rasa ba na gida tana goye da Ilham, Maman ta kuma ta na d’aki tana bacci kamar kullum, ya yin da su Hassana su na makarantar Boko Primary da ke garin, da yake su basu gama ba, Bashir ma be dad’e da gamawa ba, Garbati ne dai ya gama tun tuni, in da kuma ya so a kaishi Birni ya ci gaba da karatun shi, kasancewar Garin na su ba secondry, amma Allah be nu fa ba.

Sokoto

Cikin sauri-sauri Momi ta ke aikin ta ganin yanzu ma har kusan 1:20, nan da nan kuma ta kammala aikin nata tas ta fita tare da cewa Asma’u ta gyara kicin d’in ta wanke abubuwan da aka ‘bata, ita kuma d’aki ta koma ta yi wanka tayi sallah, sannan ta shirya ta dawo falo ta zauna.

Lokacin ma Asma’u ta gama aikin du ka, Auta kuwa har yanzu bacci ta ke kwasa, tashin ta Momi ta yi tare da ce musu su je suyi sallah.

Mi’kewa suka yi suka nufi d’akin su.

Abbas ne ya shigo falon sanye da wani shadda sky blue, ya yi masifar yi mai kyau se ‘kamshi ke tashi domin Abbas ba ba ya ba wajen son turare, ‘karasowa ya yi.

Ya ce”Sannu Momi”

D’agowa ta yi ta kalle shi sannan.

Ta ce”Sannu My Son, hala bacci ka ke yi tun d’azu fa gashi yanzu har 1:45″

Murmushi ya yi, Ya ce “Wallahi Momi ina cikin karatu bacci ya kwashe ni, Ba ni na tashi Ba se karfe d’aya 1:00, shine nayi wanka na fito masallaci ma za ni”

“To ai se kayi sauri Don na ji kamar ma an tayar”

Cikin sauri ya fita, da ya ke masallacin gidan su ne ya na fita ya tarar ma har sun tayar, ya bi su.

Bayan su Asma’u sun idar da sallah, Asma’u ne ta shiga ba yi ta yo wanka ta zauna ta tsara kwalliyar ta dai-dai yadda ta iya da ya ke Asma’u akwai son kwalliya.

Auta na zaune ta na kallon ta ta yi shiru se da Asma’u ta gama kwalliyar ta tsaf, sannan Auta ta mi’ke ta yi hanyar ba yi, Asma’u ne Ta ce”Ke!, me za ki yi a bayin nan?”

Ba tare da ta kalle ba, Ta ce”Wanka zan yi”

Tare da shiga bayin, Asma’u ne ta ta so da sauri, Ta ce”Ba Momi ta hana ki wanka da kan ki ba kin iya ne ma?”

“To ina ruwan ki da ni, ai ba ki yi niyyar yi min wankan ba, kuma ki na kallo na kika yi na ki har da kwalliya, amma kin ‘kyaleni, ba se na yi da kai na ba”

Dariya sosai ta bawa Asma’u, ai ko tayi mai isar ta.

Abun ya ‘kara ‘kular da Auta kawai se ta fashe da kuka ta na fad’in wallahi kuma se na fad’a wa Momi”

“Ki yi ha’kuri Autar Momi zo na miki”

“Ba’a so d’in”

Auta ta fad’a tare da kama hanyar fita d’akin, da sauri Asma’u ta kamo ta tana bata ha’kuri, da’kyar ta shawo kanta za ta yi mata wankan.

A zuciyar ta tace “Auta ikon Allah wa to kallon da ta ke yi min na in yi mata wanka ne, tsabar fitina baza ta ce in yi mata ba, kuma da cewa na yi Auta zo in yi miki wanka baza ta zo ba, Allah ya shirye ki”

A haka su ka ‘bata lokaci sosai, ta yi mata wankan ta shirya ta tsab sannan suka fito d’akin.

Falo su ka nufo, Abbas su ka gani zau ne gefen shi kuma Dad ne, ai da gudu Auta ta ruga ta fad’a kan Dad ta na fad’in.

“Dad yaushe ka dawo?”

Murmushi ya yi ya d’aga ta sama ya cafe, Ya ce”Ban jima da shigowa ba”

Asma’u ne ta ‘karaso ta rungume shi, Ta ce”Dad we are welcome, we are happy to see you”

“Yauwa sannu Husna ya karatu?”

“Alhamdulillahi Dad”

Auta ce tace “Dad amma baza ka koma ba ko? Ni nafi son ka zauna a nan kuma ma idan baka nan Yaya da Anty su na dukana, d’azu ma Yaya ya rankwashe ni, ita kuma Anty tace baza ta yi min wanka ba kuma ma……..”

Momi ne ta katse ta tare da, Ce w”Daddyn Abbas ga abincin ka can, idan ka biye na wannan yarinyar har labarin da ya faru shekaran daya wuce duk zata ba ka”

Murmushi ya yi, Ya ce”Ki ‘kyale su ‘yar Dad za su ga abin da zan musu in dai suna ta’ba min ke, yanzu muje mu ci abinci ko”

Mi’kewa suka yi dukan su su ka nufi Dinning in da Momi ta gama musu shirya mu su abinci.

Zuba mu su ta yi, kowa ya yi Bismillah!, tare da fara ci, se da kowa ya ci ya ‘koshi lokacin an fara kiran la’asar Dad da Abbas ne su ka mi’ke su ka nu fi masallaci, ya yin da Momi ta wuce d’akin ta don ta yi sallah suma su Asma’u d’akin su suka nufa don su yi sallah.

Ni ko abun ya d’aure min kai se nake ga kamar Alhaji Buhari ne Dad su Abbas idan ba ido na ke yimin gizo ba, ba ma mamaki tabbas Alhaji Buhari ne Ba me kama da shi ba! Lalle kam!, akwai rikici!.

Bayan sun dawo sallar ne su ka zauna su na fira Dad ne ke tambayan su akan karatun su da kuma abun da su ke son su zama.

Auta ce sarkin surutu, Ta ce”Dad ni dai Ina son na zama ‘kwararriyar likita ne”

Dariya su ka yi du ka sannan Abbas, Ya ce”Wa ya ga su auta an zama likita! kai akwai fama fa”

‘Bata fuska ta yi, Ta ce”Dad ka ganshi ko”

Dad ne Ya ce”Abbas zan sa’ba maka fa”

Dariya ya yi sannan Ya ce” Ka yi ha’kuri Daddy, Ni dai Dad law na ke so na yi”

“Masha Allah ai se ka da ge da karatu sosai kaji”

“To dad ai karatu munanan muna dage wa”

“To Allah ya taimaka, Husna fa?”

Murmushi ta yi sannan Ta ce”Ni kuma aikin jarida na ke so Dad”

Murmushi ya yi sannan Ya ce”To Allah ya taimake ku, kuma ya bada abun da ake Nema”

Tare su ka amsa da “Amin”

Har gaf da magrib suna Hira se da aka kira sallah sannan su ka mi’ke kowa ya yi d’akin shi su Dad su ka yi masallaci se da a kayi isha’i sannan su ka dawo gida lokacin ma su Momi duk sun yi sallar su suna zaune suna kallon Labari na a tashar arewa24.

Su Dad ma su ka shigo aka cigaba da kallo da su suna fira suna kallo.

Har wajen goma 10:30 sannan Momi Ta ce”Su tashi su tafi su kwanta”

Mi’kewa su ka yi kowa ya nufi d’akin shi, se Momi da suke fira da Dad, Momi ne ta kalli Dad.

Ta ce “Dad Abbas amma ka dawo kenan ko?”

Kallon ta ya yi Ya ce”A’a, Ranar laraba zan koma”

Ran Momi ne ya yi matu’kar ‘baci, Ta ce”Yanzu Dad Abbas hakan da ka ke yi ya kyau tu kenan a ce kabar matar ka da ‘ya ‘ya ka ta fi wani gari ka zauna, idan ma a ce kasuwan ci ne ka ke yi ai zaka iya dawo dashi nan garin tun da ba wani aikin gwamnati bane kawai business, amma se ka kama hanya ka tafi wataran ma ka na fin Wata d’aya1 a can gaskiya yaran ka ba su jin dad’in rashin ka kusa dani ko badon ni ba kodon ‘yaran ka, domin idan ta ni ne ka je ka zauna a can kar ka dawo ma”

Ta ‘kari she maganar had’e da mi’kewa tsaye.

Kallon ta Dad ya yi sannan, Ya ce”Ke har ki na da hurumin za’ban min a in da zan yi business, wacece ke!, to ina so ki dawo hankalin ki ki sani ra’ayi na ne zama a can d’in”

Murmushin takaici Momi ta yi sannan, Ta ce”Ni ba kowa bace, kuma bani da kowa yanzu a duniya da ya wuce kai, kuma dole na yi maka biyayya domin aljanna ta tana ‘kar’kashin kafar ka ne, amma don Allah ka fad’a min me kake yi a Jigawa”

Cikin tsawa Dad, Ya ce”Kke! bance kar ki ‘karamin irin wannan tambayar ba, to da ga yau idan kika ‘kara min kwatan-kwacin wannan tambayar a bakin auren ki!”

Sosai maganar ta daki zuciyar Momi, kuma ya tono mata tsohon jinyar da ke cikin zuciyar ta, ko shakka babu zata yi murna idan aka ce yau sun rabu da Alhaji Buhari, amma baza ta iya tafiya tabar yaranta ba, kuma idan ta tafi ma ina zata je? Bayan ta gama tunanin nan ne ta durkusa.

Ta ce”Ka yi ha’kuri Dad Abbas idan tambayata ta ‘bata maka rai”

Sannan ta mi’ke ta nufi d’akin ta hawaye na bin fuskar ta, ko da ta shiga d’akin kwanciya ta yi ta ringa tunani yan da ta ga rana haka taga dare, don bacci ya ‘kauracewa idon ta, wato shi Dad Abbas in dai zan mai mgana akan tafiyar shi to zan ga ‘bacin rai amma idan na ‘kyale shi se mu zauna lafiya, lallai daga yau na yi al’kawari bazan sa ke yi mai maganar ba ko da ze je ya yi shekara a can ne, maganar da take yi kenan acikin zuciyar ta, ta na cikin wannan tunanin ne ta ji kiran sallar asuba, ba ta yi mamaki ba don ta san lokacin ya yi.

*****

Shi ko dad tunda ta shiga d’akin, tsaki yaja sannan shima ya wuce nashi d’akin ya yi kwanciyar shi, ya na tunanin kalaman matar na shi, a zuciyar shi ya ce “lallai baza ki ta’ba sanin ina da mata a Jigawa ba, saboda tsaro amma nasan ko na fad’a miki ma ba abun da za kiyi”, ha ka dai yayi ta zance zuci be dad’e ba Bacci ya d’auke shi, bacci yayi sosai harda munshari don se da ma ya makara be tashi da wuri ba.

Shin waye Alhaji Buhari ne, sannan waye, Sadiya da ta ke zaune a gidan Baffa, wai kuwa Jamila tasan da Maman Abbas, duk ku biyo ni domin samun amsoshin tambayoyin ku.

ASALIN LABARIN

WAIWAYE ADON TAFIYA

ADAMAWA CIKIN ‘KAUYEN YOLA

Malam muhammad Sani ya kasance haifaffen garin yola cikin wani d’an ‘kauye, yana da mata biyu Saudatu itace amarya se Maryam uwar gida, tun da yake da maryam ba ta ta’ba Haihuwa ba Hakan ya sa, ya ‘kara aure ya auri Saudatu.

Saudatu ta na da hakuri sosai da kawaici, sa’banin Maryam da duk ‘kauyen akayi ma ta shaidar masifa, domin Masifaffiya ce ta karshe.

Saudatu ta na da yara biyu2 ‘Daya Namiji ne mai suna Al-amin, se macen sunan ta khadija, suna zama ne cikin wahala da gallazawar Maryam domin ta tsani saudatu ganin ta shigo daga baya tana da yara biyu2, amma ita bata da ko d’aya hakan ya sa ta ‘kara tsanan saudatu, ita kuma saudatu ta na hakuri da dukkan abun da maryam ke yi mata ita da yaran ta.

Ana haka ne saudatu ta kara samun wani cikin, mallam sani yayi murna sosai domin yana da son yara arayuwar shi sosai, shiyasa ya d’auki son duniya ya d’aura ma Saudatu, duk da ya na ‘ko’karin yin adalci a tsakanin su, kuma yana da rufin asirin shi domin ya na sana’ar shi ta sayar da kayan marmari.

Cikin saudatu ya shiga wata na tara 9 haihuwa ko yau ko gobe, sosai mallam sani ya ke bata kulawa, maryam abun yana matu’kar ‘bata mata rai.

Wata ranar Juma’a ne saudatu ta tashi da na’kuda tasha wahala sosai in da ta haifi kyakykyawan yaron ta.

Minti 10 da haihuwar ta Allah ya kar’bi ranta, mallam sani yaji mutuwar matar nashi sosai kuka sosai ya yi khadija da Al-amin ma sunji mutuwar Maman su sosai, haka aka dawo da ita gida akayi mata sutura aka kai ta gidan ta na gaskiya.

Mallam sani sosai mutuwar saudatu ta kad’a shi don da ya tuna se yayi ‘kwalla, haka kuma yake ta rarrashin yaran nashi, tare da ce musu suyi wa maman su addu’a domin ahalin yanzu addu’ar su ta ke bu’kata.

Bayan kwana 3 da rasuwar saudatu jaririn da ta haifa shima ya bita.

Sosai su Al-amin ke kewar mahaifiyar ta su.

Bayan wata uku da rasuwar Saudatu maryam ta shiga azabtar da su Al-amin, duka yaran kuma sun d’auko Halin mahaifiyar su, akwai hakuri da kuma kawaici, duk abun da Maryam za ta musu, ba su ta’ba fad’awa Baban su ba, shi kuma mallam sani ya d’auki son duniya ya d’aura wa yaran nashi domin duk soyayyar da yake wa mahaifiyar su se ya koma kansu, abun da kuma yake ‘batawa Maryam rai kenan ta yi duk wani makirci na ta na ganin mallam ya daina son yaran nan amma abun yaci tura, haka ta gaji ta dena, amma ta d’auki alwashin se mallam ya tsani yaran nan.

Maryam ta na da ‘kawa a’kauyen mai suna ladidi, gaskiya ne!, se hali yazo d’aya ake abota domin kuwa halin su d’aya da maryam shiyasa su ka zama aminan juna, abu d’aya ne kawai suka sha bam-bam Ladidi ta na bin malamai sosai don duk wa ni ba’kon malami da akayi to ta san da zaman sa.

Da taimakon Ladidi maryam ta yi wa mallam asiri wanda ya ji baya son gani yaran nasa, wataran ma yakan manta dasu aduniya, abun da ya d’aga wa Al-amin da khadija hankali kenan ganin baban su da ya ke son su ya ke share musu hawaye shima yanzu ya juya musu baya, su na cikin damuwa sosai kuma ba wanda za su fad’awa damuwar su, ko za su ji da d’i a zuciyar su.

Ana hakane kuma gaba d’aya mallam sani karayar arzi’ki ta same shi yanzu baya wani samu don se ya fita ya wuni be fi yayi d’ari uku 300 ba, abun da a da yakan yi dubu biyar ma arana, gashi kayan nashi duk idam ba’a siya ba se su ru’be se de ya zubar dasu.

Maryam ganin bata samum kud’i sosai a hannun mallam ya sa ta fara d’aurawa khadija talla, arana se ta yi mata talla sau uku.

Da safe idan ta tashi se ta d’ibo ruwa ta yi wanke-wanke, sannan ta share gidan ta share d’akunan gidan sannan kuma ta dama kunun da zata je tallan shi, haka zata fita tun safe har se ta kai ‘karfe 11:00, tana tallan kunun wataran ma se ta wuce.

Tana dawowa kuma, ta da fa shinkafa da wake wanda zata d’auka ta tafi tallan rana, a wannan shinkafar ne kuma ake sammu su suci, gaba d’aya khadija ta canja ta fita hayyacin ta, ta yi baki amma da fara ce sosai ga ta kyakykyawa son kowa ‘kin wanda ya rasa, Bayan ta dawo tallan shinkafar kuma bayan magrib ta d’auki tallan tuwo, Al-amin ba yanda ya iya ne baya ‘kaunar tallan nan musamman ma na dare shiyasa ma yake rakata ba tare da sanin Inna ba, har ta siyar su dawo gida tare, wataran ma sukan kai 11:00 na dare, idan sun dawo wani lolacin ma Inna tayi bacci se sun tashe ta, ta ‘kar’bi kud’in ta koma baccin ta hankalin ta kwance, su kuma su koma d’akin su su kwanta, haka washe gari ma su mai-mai ta abun da sukayi, rayuwar ga ba d’aya ba ta musu dad’i har sun gwammaci mutuwa ma.

******

Bayan shekara 3 da rasuwar mahaifiyar su, har yanzu dai ba abunda ya canza ta ‘bangaren talla ma har yanzu khadija tana yi gashi se girma take yi don yanzu tana da shekara 15 aryuwar ta yayin da Al-amin yake da shekara ashirin 20, shima yanzu ya dena zaman banza ya samu aiki a wajen abokin Baban shi, wanda ya ke sana’ar kafinta ya na ‘kera kujeru, gado, da sauran kayan katako, sosai kuma mallam Bashir ya ke jin dad’in aiki da Al-amin, domin sosai Al-amim ya ke ‘ko’karin koyan aikin, ba ya wasa, kuma yanzu ya kware sosai don sosai Mallam Bashir ya ke hutawa domin Al-amin yana mai aikin me kyau duk da ba shi kad’ai ba ne a wajen, amma ya fi jin dad’in aikin da Al-amin sosai kuma ba ya yimai mugun ta a rana idan sun tashi aiki yakan ba shi dubu uku 3000 wataran ma ya kan fi haka, domin su na samu sosai a aikin, amma Al-amin se yace ya ri’ke ya tara mai idan an tashi ya rin’ka bashi dubu d’aya kawai, shima don innan ta na tambayan shi ina kud’in da ake ba shi ne, se ya bata d’ari biyar da bata yarda ba , se ta je ta tambayi mallam Bashir nawa yake ba wa Al-amin ya shaida mata d’ari biyar ne domin ya riga da yasan komai don Al-amin ma ya gaya mai, shiyasa kullum idan ya ta shi se ya bata d’ari biyar wataran se ta d’auko Naira d’ari ta ba shi tsabar rashin imani, idan duka kud’in ma ya ba ta haka za ta yi mi shi, shiyasa ya ke yin haka raguwan d’ari biyar d’in kuma se ya siyo musu abinci mai rai da lafiya, idan kuma inna ta basu ya ishe su se ya aje a haka d’ari biyar d’in da yake ajiye wa ya ta ru koda ya du ba dubu biyar 5000 ne, nan ya bawa khadija dubu uku ta sayi dukkan abun da take so na bukatun ta, khadija ta ji tsoron ‘karbar kud’in saboda inna, amma kuma se ta kar’ba ta siyo sabulun wanka se man shafawa da omo ta wanke kayan ta da sauran abubuwa canjin kuma ta ‘boye saboda watarana.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yanzu dai da d’an sau’ki suna d’an hutawa don idan inna bata ba su abinci ba Al-amin ya kan siya musu, su ci su koshii, sede har yanzu Baban su Ba ya kula su don yanzu ma baya zama a gari maryam ta yi mai hanyar wani aiki da mijin Ladidi ke yi a lagos, in da suke tafiya tare wataran ma su kanyi wata biyu2 ba su dawo gida ba, amma mallam sani yana cikin matsanancin damuwa da ka gan shi zaga gane haka domin yanzu gaba d’aya ya rame ya Lalace sosai.

Yauma kamar kullum Al-amin ne ke zaune a wajen aikin na su ya na ta aiki Khadija ce ‘yar mallam Bashir ta yi sallama tare da ajiye ma Al-amin kulan Abincin da ta kawo mai ta nemi guri ta zauna, su ka sha hirar su, sosai domin shakuwa ce sosai ke tsakanin su da Khadijan wanda za’a iya cewa soyayya ce mai ‘karfi a tsakanin su.

Bayan wata biyu

khadija ce zaune bayan sallar magrib don yau Allah ya taimake ta ba ta je tallan daren ba domin yau Baban su ya dawo kuma ya cika inna da kud’i sosai hakan yasa inna tace yau ta huta, Wani yaro ne ya shigo gidan, yayi sallama yace wai ana kiran khadija, khadija da tasan waye mai kiran nata tace kaje kace bata nan, inna ce ta fito da gudu daga d’akin ta tace “kai yaro zo nan ” ‘karasowa yaron yayi inna ta ce “wa yake kiran ta?, yaron yace “wani ne a mota, kuma Yace sunan shi Ahmad” murmushi inna ta yi tace “kaje ka ce ta na zuwa ka ji” “to” yaron yace sannan ya fita ya je ya ce wai tana zuwa,

‘Dari biyu 200 Mutumin ya ciro a aljihun shi ya mi’ka ma yaron ya ta fi yana murna.

Inna ce ta ce “tashi ki shirya kije” khadija ta kalli inna ta ce “inna ni fa ban san shi ba kuma ba a garin nan yake ba fa inna”, tsawa inna ta daka mata tace “baza ki tashi ki wuce ba kika barshi se ya gaji ya tafi ne” khadija badon ta so ba ta d’auki kod’ad’d’en hijabin ta ta sa ka tare da wucewa ta fita karasawa ta yi inda yake da sallama, bayan sallamar kuma bata ‘karacewa komai haka yiyi ta magana ta yi banza da shi, da ze iya hakura da yarinyar nan da tuni ya hakura da ita amma kuma so da kaunar ta acikin ranshi ya ke tun ranar da ya fara ganin ta, ta dawo d’iban ruwa a rijiyar gidan kakan shi da ke garin na su.

Ahmad shi ba a ‘kauyen nasu yake ba yana cikin gari ne kakan shi ne wanda ya Haifi maman shi yake zaune a nan ya zo ziyarar shi ne ya had’u da Khadija ta zo d’iban ruwa, da kan shi ma ya d’ibo mata ruwan ya kawo mata har ‘kofar gidan duk da bawai ya saba da wahala bane amma bashi da girman kai ko kad’an da talaka da mai kud’i duk d’aya ne awajen shi, tun alokacin ya bayyana wa khadija soyayyar shi inda kuma ta bayyana mai bata son shi, don ita ba soyayya agaban ta yanzu.

Ahmad ya kasance kyakykyawan saurayi shi ba fari bane amma za’a iya kiran shi black beauty don kyakykyawa ne na karshe su biyu mahaifan su su ka haifa daga shi se kanwar shi maimunatu, iyayen shi basu da wani buri da ya wuce su ga yaron nasu yayi aure domin yanzu ya shiga shekara 30 a rayuwar shi, shi kuma bai ta’ba had’uwa da macen da tayi mai ba se yanzu Allah ya had’a shi da khadija wanda ya d’auki son duniya ya d’aura mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 2Wata Rayuwa Ce 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×