Yaro ne ya shigo gidan Yace "ana sallama da Al-amin", inna ce tace "inji waye?", "wani ne awaje" dai-dai nan Al-amin ya fito don yaji abun da yaron yace, "muje" yace wa yaro, koda suka fito ga mamakin Al-amin se yaga Ahmad ne, 'karasawa yayi su ka gaisa, ya tambayi mai jiki shiru Al-amin yayi sannan yace "jiki sede ace da sau'ki", "subhanallahi!, amma me ze hana mukai ta asibiti ne", shiru Al-amin yayi sannan yace "to bari mu fito se mu wuce", Komawa gida yayi yace wa khadija ta taso su je. . .