Skip to content
Part 5 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Yaro ne ya shigo gidan Yace “ana sallama da Al-amin”, inna ce tace “inji waye?”, “wani ne awaje” dai-dai nan Al-amin ya fito don yaji abun da yaron yace, “muje” yace wa yaro, koda suka fito ga mamakin Al-amin se yaga Ahmad ne, ‘karasawa yayi su ka gaisa, ya tambayi mai jiki shiru Al-amin yayi sannan yace “jiki sede ace da sau’ki”, “subhanallahi!, amma me ze hana mukai ta asibiti ne”, shiru Al-amin yayi sannan yace “to bari mu fito se mu wuce”, Komawa gida yayi yace wa khadija ta taso su je asibiti dakyar ta mi’ke ta zira hijabinta suka fito dakyar take takawa don ko ganin gaban ta ma bata yi, kawai saka kafa take yi yayin da Al-amin ke ri’ke ta hannun ta, har suka fito waje, sun zo dai-dai inda Ahmad yayi perking d’in motar shi, ya bud’e mata, Al-amin sakin hannun ta yayi yana sakin hannun ta Tayi luuu ta fad’i kasa sumammiya, cikin firgici da tsantsar tashin hankali Al-amin ya d’ago ta yasa ta amotar shima ya shiga, da sauri Ahmad ya zagaya ya shiga shima tare da jan motar da gudu su ka nufi asibiti,

Gudu Ahmad ke yi sosai har suka isa asibitin Al-amin ne ya d’auke ta suka shiga ciki, emergency room akayi da ita, yayin da su Al-amin ke tsaye akofar, wata nurse ce ta fito tace musu “su je can su zauna domin ba’a tsayawa akofar”, tashi su kayi suka je su ka samu wani waje suka zauna amma idon su yana kan kofar, acikin su bansan wanda yafi wani shiga tashin Hankali ba,

Har awa2 likitan nan bai fito ba yayin da duk minti d’aya tashin hankalin su ya ke karuwa, suna zau ne suna jira wayan Al-amin ya shiga ringing ko da ya duba Nombar malam Bashir ne, d’aga wayar yayi tare da gaishe shi ya amsa sannan yace mai “lafiya yau baka zo ba kasan muna da aiki sosai, kuma yau za su ‘kar’ba”, “wlh ba lafiya ba ‘kanwata khadija ne bata da lafiya, yanzu ma muna asibiti ne”, “subhanallahi!, to ya jikin nata”, “da sau’ki”, “Nima yau bana jin dad’i ne ban fito shagon ba gashi nayi musu al’kawari yau zan ‘karasa musu, gashi ance min bakaje ba shine na kira ka, nasan da ace kaje da yau za’a gama aikin”, “to Mallam idan ta ji sau’ki ko anjima ne zan le’ko” “to” mallam ya ce tare da kashe wayar, Ahmad ya kalla yayi mai bayani abun da ogan nasu yace, Murmushi Ahmad yayi yace “abokina kaje aikin ka Insha Allah zan kula da ita komi za’a bukata”, Al-amin ne yace “a’a zan zauna kawai”, Ahmad ne ya matso tare da dafa kafad’an Al-amin yace “Baka yarda dani bane ko soyayyar da nake mata ne ba ka yarda da shi ba?”, “a’a” ba haka ba ne, na yarda da kai, kuma idan akwai wanda zan ba wa khadija to kai ne kar ka yi haufi”, murmushi Ahmad yayi yace “na gode yayan mu” dariya Al-amin yayi sannan ya juya ya fita, be juma da tafiya ma Aka bud’e d’akin da khadija ke ciki, da sauri Ahmad ya zo wajen, ofis likitan ya nufa tare da ce wa Ahnmad ya biyo shi, Zama likitan yayi sannan ya cire glas d’in fuskar shi, ya kalli Ahmad yace “yarinyar da aka kawo miye naka?” Jim! Ahmad yayi, sannan ya kalli likitan yace ” ‘kanwa ta ce”.

Likitan ne yace “‘kanwar ka ta na fama da typod ne da maleria wanda yaci karfin ta da yawa, yanzu ga wannan takardar magani ne ka je ka siyo kayi sauri harda ruwa yanzu za’a saka mata”,

Ahmad kar’ba yayi sannan ya tashi ya fita direct wani phermacy ya nufa ya siyo maganin da ruwa leda shida6, ya dawo asibitin ya kaiwa Likitan, sannan yace “zan iya shiga na ganta”, “ehh ba matsala”, tare suka jero zuwa d’akin da khadijan ke kwance, suka shiga, har yanzu tana kwance bata farka ba ruwan likitan yasa ka mata sannan su ka fito waje, se lokacin Ahmad ya duba agogon da ke manne ahannun shi da ya nuna 12:40, mamaki yayi sosai gashi ya fito be gaya wa momin shi ba, ciro wayar shi yayi yaga 3three miss call daga momin shi, kafin ya gama tunanin ya ji wani kiran ya shigo dubawa yayi ya ga momin ne cikin sauri ya d’aga tare da cewa “Assalamu alaikum, momina don Allah kiyi hakuri na fita ban fad’a miki ba”, daga can momi ta ce “kana ina ne to?”, “momi ina nan cikin gari wlh khadija ce aka kwantar da ita a asibiti yanzu ma ina can”, “subhanallahi!, ya jikin nata to?” “momi wlh har yanzu ma bata farka ba” “Allah ya bata lafiya”, “amma ka fita baka fad’a min ba, zamu had’u ai”, “kiyi hakuri momi na, wlh ban zaci zan dad’e ba ne”, “to shikenan, zan turo maimuna ta kawo muku abinci”, “to momi an gode”, su kayi sallama ta yanke wayar.

Al-amin tunda ya fita kai tsaye wajen aikin nasu ya nufa ya tarar da yaran na aiki su ma suna ganin shi su ka fara murna dan sun san aikin nan Ba ze dad’e ba zasu gama, aiki ya fara yi sosai yayin da hankalin shi na asibiti amma haka ya daure yayi aiki, ba su suka tsaya ba sai wajen karfe 2:00, domin suyi sallah, Wayan shi ya ciro a Aljihun shi ya kira Ahmad da ya ke ya bashi number shi d’azu kira d’aya kuwa Ahmad ya d’auka ya tambaye shi ya mai jiki ya ce mai “da sau’ki yanzu ma an saka mata ruwa ne”, “to” yace sannan yace “Nima ina ga nan da ‘karfe 4:00 na dawo, domin aikin ma saura kad’an ne”, “to” Ahmad yace sannan su kayi sallama, Al-amin ya shige masallaci dama yayo alwala.

‘Karfe biyu momi ta kira Ahmad ta ce ga maimuna nan a hanya ka kira ta ka mata kwatan cen asibiti, “to” yace sannan ta yanke wayar, nombar maimuna ya kira yayi mata kwatance, minti 20 se gata a asibitin da kulan abinci har guda biyu, Fitowa yayi ya shigo da ita cikin asibitin, kai tsaye su ka wuce d’akin da khadija ke ciki “Masha Allah!” maimuna ta furta lokacin da ta ga khadija, khadija da bata dad’e da tashi ba se zare ido take yi maimuna ce ta karaso, tace “sannu anty khadija”, “ya jikin naki?” murmushi khadija, ta yi duk da bata san maimuna ba tace “da sauki”, se yanzu Ahmad ya shigo mamaki sosai khadija ta yi ganin Ahmad, murmushi ya ke mata yace “gimbiyata ya jikin” “da sau’ki” ta ce ba tare da ta sake kallon shi ba, “ga ‘kanwata nan maimuna zata zauna da ke, yayan ki ya fita amma ya kusa dawowa, kad’a mai kai kawai ta yi ya fita domin yaje yayi sallah.

maimuna ce ta mi’ke ta d’auki filet tare da cewa “anty me zan zuba miki,akwai tuwon shinkafa, akwai fried rice, wanne zaki ci?” “Na koshi!” tace ata’kaice, “haba anty nasan baki ci komai ba don Allah ki ci kinji”, “na koshi ne!” khadija ta sake fad’a, “matsowa kusa da ita maimuna tayi ta dafa kafad’ar ta tace “haba anty kinsan me wlh momi da kanta ta dafa abincin nan don kawai matar yaya kin ga idan baki ci ba se na fad’a mata, ko na kira yayan na fad’a mai”, murmushi khadija tayi tace “lallai mutumin nan wato har gidan su yaje yana bada labarina, ko ba matar yaya ba ta fad’a a zuciyar” sannan tace “to shikenan azubomin tuwon”

murmushi maimuna tayi sannan cikin sauri ta tafi ta zu’bo mata tuwon lafiyayye da miyar d’anyen ku’bewa yaji man shanu se ‘kamshi yake yi ‘karba khadija tayi ta fara ci ba’a magana domin tuwon yayi dad’i sosai maimuna na gefen ta tana zaune, ita ko khadija tuwon ya mata dad’i sosai se ci take yi, ta d’ebo tuwon zata kai lemo kenan aka turo kofar d’akin Ahmad ne ya shigo kallon ta ya tsaya yi ita ko kunya ne sosai ya kamata ga tuwo a hannun ta ta rasa yadda zatayi, da ya lura da haka se ya juya ya nufi wani kujera da ke d’akin ya zauna, ta can bayan ta khadija cigaba ta yi da cin tuwon ta har ta koshi, Ahmad ne ya ce “maimuna zuba min abinci to yaya tace tare da mi’kewa, tace “me zan zuba maka?”,

“tuwo”

yace atakaice, d’aukan d’ayan filet d’in tayi ta zuba mai ta ajiye mai da cokali,

cokalin ya d’auka ya fara ci, be wani ci da yawa ba ya ajiye tare da mi’kewa ya fita maimuna ce ta biyo shi abaya tace “yaya ina zaka je ne?” yace “yanzu zan dawo ki zauna da ita”, “amma yaya tun d’azu ban ga wani na ta yazo asibitin ba”, kallon ta yayi sannan yace

“marainiya ce bata da kowa se yayan ta Mahaifiyar ta ta rasu mahaifin ta baya garin nan yayan nata kuma tare da shi mu ke, an kira shi awajen aikin shi, shine ya bar min amanar ta ni kuma na baki amanar ta yanzu, zan je gida ne nayi wanka don bana jin dad’in jikina tun da safe da nayi wanka, gashi yanzu har ‘karfe 4:15, shima yayan nata ya kusa dawowa”,

“to”

tace sannan ya juya ya shiga motar shi ya wuce gida.

maimuna koma wa d’akin ta yi, ta tarar da khadija ta koma bacci, zama ta yi tana kallon ta ci ke da so da tausayim ta, a zuciyar ta tace ” lallai kyakykyawa ce Allah ya ba yayana ita”, tana cikin zancen zuci ne aka turo kofar Al-amin ne sallama yayi ta amsa masa ko ba’a fad’a mata ba tasan yayan khadija ne yadda su kayi kama sosai, shima Al-amin kallo d’aya yayi mata yasan ‘kanwar Ahmad ce don Ahmad ma ya biya ta wajen aikin nashi ya fad’a mai za shi gida amma ya bar ‘kanwar shi tana can, Maimuna ce ta gaishe shi ya amsa sannan yace

“ya mai jikin”

“da sau’ki!, ta ci abinci ma sannan ta koma Bacci yanzu”,

“to mun gode sosai”

yace sannan ya koma ya zauna akan kujerar da ke d’akin, tare da ciro wayar shi yana latsa wa, maimuna ma wayar ta ta ciro acikin jaka ta kira momin ta, gaisawa su kayi sannan momi tace “ya mai jiki” “da sau’ki momi, yaya ya dawo gida ko?”,

“Ehh ya dawo yace min ze yi wanka ya dawo, dad ku ma yazo yana tambayar ki nace mai kina wajen surukar mu, yace a gaishe ta da jiki ‘kila zuwa gobe ma mu le’ko asibitin”

“to momi”

tace sannan su ka yi sallama, dai-dai nan kuma khadija ta tashi, sannu da jiki Maimuna ta ‘kara mata sannan ta fad’a mata sa’kon dad murmushi kawai khadija ta yi, Al-amim ne ya ta so yazo, tare da cewa “khadija ya jiki?” murmushi ta yi tace “da sau’ki sosai yaya, yaushe ka dawo?”, “ban jima ba naje wajen aiki ne”, “to yaya amma kaci abinci kuwa?”, murmushi yayi sannan yace mata, “na ci”,

“kai yaya ban yarda ba wallahi!”, “dagaske nake yi”

“to”

tace sannan ya fita domin ya kira likita domin ruwan da aka saka mata ya ‘kare, be fi minti2 da fita ba su ka shigo tare da Likitan, ruwan ya duba sannan ya cire ya fito mata da magungunan da zata sha yanzu sannan yace “anjima za’a ‘kara saka mata ruwa bayan magrib sannan ya fice”, maimuna ce ta mi’ke tare da d’aukan flet fried rice d’in nan ta zubowa khadija yaji vegetable ga nama sosai aciki, mi’ka mata ta yi tace “ki ci, se kisha maganin” “a ‘koshe nake fa ban dad’e da cin tuwo ba zaki ‘kara min wanna”,

“Don Allah kici”

Al-amin ta kalla tace “yayan mu ka mata magana ta ci abinci”, Al-amin ne ya ce “khadija kici mana se ki sha maganin”, jawo filet d’in ta yi ta fara ci wani filet d’in maimuna ta d’auka ta zuba shinkafar sannan ta mi’kawa Al-amin tace “Bismillah!, yayan mu”, murmushi yayi yace,

“to nagode”,

Dai-dai nan Ahmad ya bud’e d’akin ya shigo, maimuna ce tayi mai sannu da zuwa sannan ya wuce kan d’ayan tebur d’in da ke d’akin ya ajiye kayan da ya zo da su, sannan ya ‘karasa wajen Al-amin yace “ya ka tasa abinci kuma ka’ki ci” murmushi yayi yace “na ‘koshi ne”, “a haba baza ayi haka ba, maimuna zo ki d’auki abincin nan ki ‘karo mana tare zamu ci”, da sauri maimunat ta d’auka taje ta ciko musu sosai ta ajiye musu Ahmad ne ya kalli Al-amin yace “mallam ka d’auki cokali muci abinci fa”

murmushi Al-amin yayi sannan ya aje wayan dake hannun shi ya d’auki cokalin su ka fara ci, sosai Abincin yayi mai dad’i fiye da yanda ya zata, maimuna ce taje wajen kayan da Ahmad ya shigo da su ta duba drinks ne kala-kala, se kuma snaks da faro drinks d’in ta d’ibo da ajiyewa khadija d’aya sannan ta ajiyewa su Ahmad suma, ita kuma snak d’in ta d’ibo ta had’a da drink d’in taci don yunwa ta fara ji , ita dama ba gwanar cin abinci bane ko agida se de irin mara nauyi kamar snak d’in.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 4Wata Rayuwa Ce 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×