Skip to content
Part 7 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya abangaren khadija har yanzu shiru Don yanzu ma karatu take yi sosai don Al-amin ya saka ta makaranta, maimuna ta yi aure don yanzu ma yaran ta 2 mustapha da sadiya wanda suke kiran ta (ikram) don sunan momi ne.

sosai khadija ke zuwa gidan maimuna su shan hirar su. Yanzu shekara sha biyu12,da auren su shekaran ta ashirin da takwas 28 yanzu amma idan ka gan ta baza ka ta’ba cewa ta haura ashirin d’in ba.

Abubakar sosai su ka dage da karatun su ba wasa, Buhari ko se abun da yaci gaba,Don yanzu rashin jin nashi gaba yake da taimakon uwar shi safiyya don tace adaina takura wa d’an nata.

Se da khadija ta cika shekara sha13 da aure sannan ta samu ciki murna a familyn ba a magana sosai su ke murna su na fatan Allah ya sauke ta lafiya.

Bayan wata shida khadija ta haifi ‘yar ta mace bayan dogon nakuda Allah ya kar’bi abun sa, tashin hankali ba’a sa maka rana sosai su ka shiga tashin Hankali sosai Ahmad yana jin labarin ya suma har aka dawo da ita daga asiti bai farfad’o ba, Yayin da Al-amin yanacan be san me ake yi ba, Dad Ahmad ne ya kira shi ya fad’a mai shima suma yayi yayin da akayiwa khadija sutura aka kawo ta gidan su domin Baban ta yayi mata Addu’a sunyi sa’a yana garin kuka sosai Baba yayi yana ganin be kyauta ba be cika amanar da matar shi saudatu tabar mishi ba.

Haka aka kai khadija gidan ta na gaskiya sede muce Allah yasa muma mu cika da imani, Ameen.

Wasa-wasa har kwana3 Ahmad da Al-amin ba su farfad’o ba.

Abu kamar wasa har sati d’aya yayin da likita ya shaida musu Ahmad ya samu buguwar zuciya, amma da yardar Allah ze dawo dai-dai, Idan aka d’aura shi kan magani, Al-amin ya farfad’o yayin da ya shiga matu’kar tashin hankali da mutuwar ‘yar uwan na shi, guda d’aya da yake gani a duniya ya ji dad’i farin cikin shi, ba shi da aiki se kuka yana yiwa ‘kanwar na shi addu’ar samun rahamar ubangiji.

Gidan su Ahmad cike ya ke da ‘yan uwa, ko wa yaji mutuwar khadija, Musamman ma momi da take jin ta rasa ‘yar ta ga kuma Ahmad na asibiti abun ya had’u mata biyu, maimuna ma sosai take zubda kwalla ita ma abun biyu ya zama mata, ba yanda su ka iya se hakuri Don Allah ba ya barin wani don wani ya ji dad’i, idan lokaci yayi se an tafi, Allah ka sa mudace.

Ahmad be farfad’o ba se bayan kwana goma10 da mutuwar Khadija ko da ya farka ba abun da ya ke se kuka yana fad’in akai shi wajen matar shi, hakuri akayi ta ba shi amma ina! Se abun da yayi gaba, yau kuma aka sallame su su ka dawo gida momi da dad sun yi mai Nasiha sosai akan ya yarda da kaddara, ga likita yace ya daina sa ma ran shi damuwa indai ana so zuciyar shi ta dawo dai-dai.

Inna Maryam da Baban su Al-amin ma sun ji mutuwar Khadijah,don Inna har ta je ta nemi gafarar Al-amin akan abun da ta mu su, sannan ta na ta addu’a da neman gafarar Khadijah na.

Bayan Mutuwar Khadijah da wata ɗaya, Mallam Sani ya shirya koma wa Lagos in da ya ke aiki, inda Inna Maryam tace za ta bishi idan yaso se ta dawo don ta na son zuwa garin, sun shirya tsaf, Al-amin ya ba su na mota don sun faɗa mai tafiyar, sunyi Sallama, su ka kama hanyar Lagos, a hanyan ne su ka yi hatsari duk motar na su ba wanda ya fita duka sun mutu, ta wayar Mallam Sani aka kira aka shaidawa Al-amin.

Al-amin ya je ya ɗauko su, anyi mu su sutura, an kai su gidan su na gaskiya, se dai mu ce Allah ya sa mudace, Ameen.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya ba dad’i aban garen Ahmad da Al-amin, yau wata biyu2 kenan da rasuwar khadija, amma kullum kamar yau su ke ganin abun, yarinyar khadija ta ci suna Halimatu- sadiya, su na kiran ta Afnan, sosai mutuwar khadija ya ta’ba Ahmad don yanzu Ahmad gaba d’aya ya lalace ya rame don baya cin abinci ma se momi ta yi da gaske,Ahmad da aka san shi mutum mai fara’a, surutu, da faran-faran amma yanzu ya dawo shiru-shiru, kafin ka ga dariyar shima aiki ne yanzu.

Bayan wata biyar da rasuwar khadija Afnan sosai take samun kulawa ta ko ina yarinya se wayo take yayin da kamannin mahaifiyar ta ne sosai a fuskar ta, kamar an tsaga kara, abangaren Ahmad ba abun da ya canza se gaba lamarin ke yi, sosai ake yimai Addu’a.

Al-amin ya fawwala wa Allah komai amma abun yana ran shi a duk sanda ya tu na kuma se ya zubda kwalla, khadija sosai ta ke ‘ko’karin Bashi farin ciki domin ya manta da abun, amma tasan baze yiwuba se dai ta yi iya ‘ko’karin ta.

Bayan shekara 3,

Su Abubakar sun gama karatun su kuma sun fita da result me kyau yayin da gwannati ta ‘kara d’aukan nauyin su zuwa England don suyi karatu, sosai Al-amin yayi ma d’an nashi fatan Alheri da mai nasihohi akan Rayuwa da kuma addinin shi, yayin da Buhari abun nashi ke dad’a ta’bar’bare wa ya ke don yanzu Abubakar yana da shekara ashirin20 shi kuma yana da sha bakwai16, tun da aka samu ya gama primary da’kyar be yarda ma an saka shi secondry ba don ya fad’a wa baban nashi ko ya saka shi baze yi karatu ba, yace shi Sana’a ze yi, Al-amin be hana shi ba yabar shi, se yayi kwana2 ba shi agidan su na tare da Iliya abokin shi, wataran sun sun shirya shi da Iliya za su rafi don su yi wanka, ko da su ka isa rafin Buhari ne ya fara shiga yayi sannan ya fito Iliya ne ya shiga shima da yake yafi Buhari iya ruwa se yake ta wasa aciki se ya nutse ciki sosai sai yayi minti2 kafin ya fito, Buhari har ya gaji yace ya fito su tafi, yace bari na kara yin ko sau d’aya se na fito, yin kasan shi keda wuya ruwan ya fara jan shi ihu Iliya ya fara yi yana neman taimakon Buhari ruwan sosai ya ke jan shi tsorata sosai Buhari ya yi, yace a zuciyar shi sede ka mutu kai kad’ai don bazan shigo ba dama ba wani iya ruwa nayi ba, yana ji yana gani ruwan nan ta cinye Iliya ya koma gida shi d’aya.

Iyayen iliya ne su kayi ta neman shi har wajen Buhari su ka tambaya amma se yace musu ma baisan in da yake ba ya dad’e ma rabon da ya ganshi haka su ka hakura don sunyi neman sun bada cigiya amma ba labarin Iliya Buhari kuma yayi shiru da bakin shi.

Bayan shekara2, Afnan ta yi wayo sosai don yanzu tana da shekara 6 sosai yarinyar ke ganin ‘kauna awajen dangi kowa yana son ta, momi kuma ta na kawo ta gidan Al-amin akai-akai, Ahmad dai yanzu Alhamdulillah za mi ce don ya fara dawowa, yayin da momi ta yimai maganar ya nemo mata don zaman shi Haka baze yuwuba, to kawai yace mata, amma a zuciyar shi ba ya tunanin kara aure yanzu.

Bayan mutuwar Iliya Buhari ya shiga wani hali don bai da wani aboki a garin kowa tsoron abota yake yi dashi, hakan yasa ya had’a wani munafurcin, ya je ya samu Baban shi da maganar ze yi karatu akai shi bording school, sosai Al-amin ya ji dad’i, yayin da ya tura shi wani bording da ke zamfara, acan ne Allah ya had’a su da Saleh wanda shi d’an jigawa ne iyayen shi sun rasu yana wajen kakan shi ce, shi ma tantirin shaid’ani ne don gara ma Iliya so dubu akan shi, abota sosai su ka ‘kulla yayin da su ke she’ke ayar su don anan Buhari ya koyi shaye-shaye ma don yanzu ba abun da baya sha yayin da su ke shirin guduwa daga makarantar ma don ba karatun ya kawo su ba,

Yau watan Buhari shida da zuwa makarantar yayin da kuma halayen shi su ka ‘kara ta’bar’barewa ya kira Baban su ya shaida mishi ana neman kud’i dubu d’ari uku a makarantar, ba tare da tsanan ta bincike ba Al-amin ya tura mai don ba shi da wani buri da ya wuce Buhari ya shiryu yayi karatu, yayin da Buhari shiri ne kawai yayi wa Baban nashi, Don sun gama shirya wa gobe za su gudu su bar makaran tar.

Washe gari kamar yadda su ka tsara Bayan dare yayi su ka fito da kunshin kayan su su ka nufo gate, ma su gadi su biyu suna nan A bakin gate d’in don dole su bi ta gate don katangar baza ta hauru musu ba.

Koda su ka ga masu gadi basuyi Bacci ba komawa su kayi su ka d’auki wasu manyan ‘karafuna, da gudu su ka nufo wajen su, ma su gadin ba su kawo komai tun da sun ga ‘yan makarantar ne se de ma hankalin su ya tashi kar ace wani abun ne ya faru, basuyi yun’kurin fito da bindiga ba, koda su ka karaso, ‘karfe nan su ka buga musu a kai nan take du ka su ka gad’i makullin kofar su ka ciro a aljihun d’aya daga cikin su tare da cire bindigogin jikin su su ka saka acikin kayan nasu fita su kayi har da key d’in ta waje su ka rufo kofar sannan su ka cillo key d’in cikin makarantar sunyi haka ne gudun wata matsala da zata je ta dawo.

Koda suka fita tafiya sukayi ta yi acikin daren Har su ka gaji wani garin su ka isa sunyi nisa sosai da makarantar, wani wajen su ka samu su ka kwanta, har safiya ta yi, sannan saleh yace yana da wani aboki su je gidan shi, aiko kama hanya su kayi, su nufi gidan yayin da ya musu masauki mai kyau.

Al’amarin masu gadi kuwa ko da gari ya waye hukumar makarantar ta ga wannan abu sosai hankalin ta ya ta shi, ta ke aka kira ‘yan sanda Nan aka duba d’aya ma har ya mutu domin ya bugu sosai jini yayi ta zuba sosai akan shi, d’aya kuma ya samu buguwa shima amma be mutu ba, bincike sosai akeyi yayin da aka gano Buhari da saleh ne su ka daki masu gadi su ka gudu, kud’i sosai aka saka wanda ya kawo su, yayin da ‘yan sanda da hukumar makaranta su ka tafi Adamawa garin su Buhari har gidan su, ko da su ka shaidawa Al-amin ga abun da d’an shi yayi a take anan ya suma akayi asibiti da shi, yayin da khadija ta shaidawa ‘yan sandan tun da Buhari ya tafi makaranta ko ziyara be kawo gida ba.

Komawa su kayi, aka cigaba da bincike, Har gidan tv se da aka saka hotunan su ana neman su.

Su buhari kuwa su na gidan abokin saleh sun samu wurin zama don za su ci mai kyau su sha mai kyau, wataran su na kallon tv su ka ga hotunan su ana neman su, tsoro sosai su kaji suka cewa abokin nan nasu ya ara musu kud’i ko dubu d’ari biyu ne su bar garin kafin ‘kura ta lafa, be yi musu ba ya ara musu don akwai kud’in, ko da ya ba su su ka had’a da na Baban Buhari ya tashi suna da dubu d’ari biyar.

ɓaddakama su kayi su ka bar garin su ka nufi sokoto d’aki su ka kama haya su biyu yayin da su ka cigaba da she’ke ayar su, kamar kullum su na zaune ad’akin da su ka kama, Buhari ya kalli saleh yace “wai kai baka maganar komawa gida ne?”, saleh ne yayi dariya sannan yace “Ehh se san da nayi ra’ayi zan koma kuma bara kaga ba abun da ze faru da murna ma za’a tare ni” Buhari ne ya ce “to meyasa?”, yace “akwai wani malami da muke zuwa wajen shi da abokina kafin ya mutu magani ze baka, wlh ko Shekara goma zaka yi da murna ma za’a tarbe ka”, dad’i sosai buhari yayi, yace “lallai kai ka cika tantiri”, dariya saleh yayi yace “to ni na wasa ne akace maka”, se da su kayi wata biyu a sokoto sannan su ka nufi zamfara wajen Malamin da Saleh ya fad’awa Buhari, sosai Buhari ya tsorata ya za ci malami ze gani da Qur’ani se yaga boka, sosai ya tsorata, laya boka ya ba shi, yace ya d’aura ahannun shi kar ya bari ya fad’i.

Bayan sun ‘kar’bo layar kuma su ka ko ma sokoto, amma ba anguwan da su ka sauka da farko ba, wani anguwa ne, ‘kauye ne ma, su ka kama wani d’aki, su na zaune su da wani d’an garin ne shi amma shi ma duk irin su ne.

Wata rana su na zaune, a bakin kofar d’akin wata yarinya ta zo wucewar ‘yar fulani, Nan Buhari ya ji ta kwanta mai a rai ya bi ta amma ta ‘ki kulashi, ya dawo ya tambayi abokin su wacece wannan, nan ya fad’a mai komai na ta sunan ta Bilkisu, kuma ba ‘yar asalin garin ba ne zuwa su ka yi da iyayen ta ya shaida mai kuma su na zau ne a gidan haya ne ma, Buhari ne yace “to yanzu ya za’ayi na same ta?”, “abu mai sau’ki indai ka na da kud’i to ba matsala don babanta Abashe akwai shegen son kud’i”, dariya Buhari ya yi na samun nasara, yace, “yanzu dai ban da wa su kud’i amma zan samu ran ce da na koma na aiko ma ka da shi”, “Ehh sosai kuwa” cewar Mansur abokin na su. “to yanzu dai ina da dubu d’ari biyu ya za’ayi kenan?”, “ka fara kashe mu su kafin na ba ka nawa”, “to nagode, amma yaushe za mu je wajen ta?”, “kar ka ko ma wajen ta don baza ta saurare ka ba, don ba ta kula Kowa, ko a garin nan, abun da za’ayi kawai mu je mu samu Baban na ta”, “naji dad’i sosai cewar buhari”.

Da yammacin ranar su ka je su ka samu Baban Bilkisu, inda su ka shaida mai abokin su ya na neman izinin fara zuwa wajen ‘yar sa da fara’a ya tarbe su, ya tambaye shi, shi d’an ina ne? Yace shi maraya ne iyayen shi sun rasu kud’i kawai su ka bar mai, dad’i sosai Abashe ya ji jin an ambaci kud’i don shi neman su yake yi, yace “yanzu kun sa mu yarinyar ne?”, ya tambaya, “Ehh amma ta ‘ki ta saurare mu”, cewar Saleh, “lallai ma dole zata saurare ku, bara na turo mu ku ita” yace tare da, mi’kewa, kud’i Buhari ya ciro kimanin dubu Hamsin ya bashi, washe ba ki yayi yana godiya, ya ‘kar’ba tare da cewa “bara na kira muku ita”, ko minti biyar ba’ayi ba da shigar shi se ga Bilkisu ta fito fuska a had’e duk da haka be hana tsantsar kyaun ta fitowa ba, da sallama ta zo wajen da su ke, Buhari ne ya washe ba ki, ya na fad’in “sannu da zuwa ranki shi dad’e”, banza ta yi da shi, se surutun shi ya ke kasancewar su Saleh sun ba shi waje sunyi gaba, har ya gama yace ze tafi amma Bilkisu bata yi mai magana ba, kud’i ya ciro a aljihun sa ya bata ‘kin ‘kar’ba ta yi ta shige gida.

Bayan sati biyu da had’uwar Buhari da Bilkisu kullum se ya je gidan yayin da Bilkisu ko ganin shi bata son yi, Baban ta ko har yace ma ya bashi ita, don kud’i sosai Buhari ke kashe mai don ya ari kud’i sosai a wajen Mansur, ana maganar sa ka rana ne ma.

Su Buhari kamar kullum su na zaune a d’akin su, Buhari ne yace, “Saleh kasan fa tsohon nan yace ya ba ni yarinyar nan kuma ina son ta wallahi auren ta zanyi gashi mun d’auko abun da ‘karya ya za’ayi?”, “Kar ka damu indai kana tare da ni ba wata matsala akwai wa su kud’i da na ke tara su za su kai ‘kimanin 2miillon, zan ara maka su se ayi shagalin biki” “kai amma na gode abokina”, cewar Buhari.

An saka ranar auren Buhari, wata d’aya1 yayin da Bilkisu da mamanta ba su so ba don tace du ka ‘yar nata nawa take yanzu ta shiga, shekara sha shida, haka dai Baban ta ya dage.

<< Wata Rayuwa Ce 6Wata Rayuwa Ce 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×