Bismillahir Rahmanir Rahim
Tafe nake a kan hanƴata na komawa gida, zuciyata cike da saƙe-saƙe babban tashin hankalina bai wuce abin da zan je na tarar a gidan ba. Bayan layinmu na biyo ko Allah zai sa a dace na samu abin da na fito nema. Yau ma kamar kullum babu kowa a wajen, da yake unguwace ta masu hannu da shuni.
Masifar ta kawai nake tunowa, take wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo min a kuncina,gefen hijabina na kamo na share hawayen.
Wani tank’ameman gida na zo giftawa cak naja na tsaya ina kallon wata dattijuwar mace, wace ak’alla shekarun ta bazasu hau ra 45 ba, kai daga ganin ta ba sai an fad’a ba ka san kud’i sun zauna duba da irin kayan dake jikin ta, masu tsadar gaske ga wasu manƴan gwalgwale dake manne a wuyanta da hannunta masha Allah nace zuciyata cike da sha’awa.
Ɓangaren ta na hagu na hango wani had’ad’an gay a kusa da ita ya wani neke fuska tamkar k’aramin yaro, gaskiya ya had’u sosai fari ne kar da shi fuskar nan cike da saje, me dan k’aramin baki ko ba’a fad’a min ba na san babu abinda yasa a lips din sa kawai hallintar sa ce a haka, gani zasu shige mota ne nayi saurin isa inda suke murya na rawa nace” Asalam alaikum.”
Cikin daddaɗar muryata wacce ko ni ina alfhari da ita, cikin biyayya da girmamawa zuciyata cike da tararabin yanda zasu amshe ni na sake k’ok’arin furta ” ina wunin ku hajiya? dan Allah taimako nake nema?..” suka juyo cike da mamaki suna min wani irin duba wanda sai yanzu na gane tsantsar wauta ta, muryar dattijuwar nan ce ta daki dodon k’unne na cikin azama na sake gyara tsayuwata ina sauraron ta.
Ta ce “ƴan mata wani irin taimako kike nema a tsakar ranan nan?” ta ida maganarta tana mai k’arasa shiga motar.
Na bude baki zanyi magana kenan yayi saurin rigani da cewa” ohh Daddah! kin fa san sauri nake irin wannan mutanen babu abin da suka iya sai k’anzan k’urege, ki bata wani abu kawai tunda kinyi niyya bazan hanaki ba..” ya fad’a cikin murya sa me sanyi da shegan dadi, wai haka a masifance yayi maganar ikon Allah, duk da banji dadin yanda ya k’atse ni ba amma haka na daure banyi magana ba.
Cikin wasa da manƴan taka ta ce “Allah ya shirya ka yasa ka gane, jakata babu canji bata wani abu to” ta fad’a cike da zolaya.
“Daddah! bana so fa.” domin maganar ma bason yin ta yake ba.
“ANNUWAR nace kaba ta wani abu, in ba so kake yanzu ka ga b’acin raina ba..”ita ma ta fad’a cikin isa da izza.
Gudun b’acin ranta yasa shi zaro d’ari biyar yana shirin jefe mata, Daddah! tace” hannu da hannu nake so ka bata, sannan kuɗin sunyi kaɗan ka ƙara mata” ɓoyayyen tsaki ya saki, kana ya ƙara mata yawan kuɗin cikin fushi ya zaro rafa din d’ari biyar biyar ya miƙa mun a wulaƙance fuskarsa na kallon gefe ran nan nasa a had’e…
Na kasa amsa jikina ya ɗauki rawa domin tunda uwata ta kawo ni duniya ban taɓa ganin kuɗi masu yawa haka ba, hajiya ta dube ni a tsanake take ta hango tsantsar tsoro da firgici a kwayar idona, sai hakan yayi mata daɗi sosai cikin nuna kulawa da kamewar mutuncin ta tace” amsa mana ba taimako kike nema ba? ai kin samu amsa sai ki mai godiya..” ta fad’a tana fad’ad’a yalwatacen murmushi.
Hannuna yana rawa na amsa cike da girmamawa da nuna jin daɗi nace” na gode Allah ya ƙaro arziki da wadata, ya ƙara lafiya da nisan kwana na gode sosai hajiya..” na fad’a har ina goge hawayen da suka sub’uce min.
Kafin ta bani amsa saurayin nan yaja motarsa da ƙarfi saura ƙiris ya bankaɗeni, na daka tsalle na koma gefe a zuciya ina tsine mai, a zahiri kuma na ce ” an baƙin ciki kawai duk da haka ai ka bayar…”
Cikin tsanannin murna da annashuwa na nufi hanyar gida, yau duk masifa baza’a dake ni ba, na samo mafita, kafin nayi kwanar layin mu, na tsaya gidan wata ƙawata mai suna Aisha!, nayi sa’a na same ta cikin nutsuwa na gaida mama dake zaune a tsakar gida tana fifita, cikin murmushi ta ce “ƴan mata kenan ana ganinku? Yanzu nan mutuniyar taki ta koma ciki, shiga ki same ta.”
Kai na a ƙasa nace ” to mama amma ina so za muyi magana dake ne.”
Allah sarki baiwar Allah me tausayi da nuna min kulawa, ta d’auke ni tamkar yar cikin ta sai ta ajiye mafici cikin nutsuwa tace “matso kusa da ni y’ata.”
Cikin biyayya na matsa amma ban rab’i jikinta ba, zanina na ɗan kwance na fiddo da kud’i dana samo, cikin nutsuwa nayi mata bayani yanda akayi na same su kana nace “tunda kullum innah! d’ari biyu nake samowa me zai hana a biya min kud’in makaranta dashi in yaso sai na ci gaba da zuwa, Allah bar shi abin da ya rage na ringa amsa da kad’ai-kad’ai ina kai mata har su k’are na cigaba da barar.” ta kai k’arshen zancenta da hawaye masu d’umi bisa fuskarta.
Mama tausayi na yasa ta kawar da kai gefe, cikin rauni tace” MUNIBAH!! ki fad’a min tsakanin ki da Allah da manzonsa a Ina kika samo kud’i masu yawa haka? shifa mutunci ƙwaya ɗaya ne tak kuma kamar madara take in ya zub’e ƙasa bai tab’a d’ibuwa har abada, ki riƙe maraicin ki, ki kama kan ki da nutsuwar ki, kina tunanin zaki kawo min kud’i ne na sa hannu na amsa haka kawai ba tare dana bincike ba, a’a ba haka nake ba , yanzu nan ba sai anjima ba tashi zaki yi muje gidan da aka baki kud’in nan naji batun gaskiya, rayuwar yanzu ba dabba ake kiwo ba d’an mutun ake hari, tashi muje yanzu naji gaskiyar abin da ya faru aka dauki kud’i masu yawa aka baki…” ta fad’a tana d’aukar mayafinta dake kan igiya a rataye.
Dama na san za’arina, banyi mata musu ko kaɗan ba na miƙe na wuce gaba tana bina a baya, kamar munafika har muka isa gida, ƙofar wajen a rufe take cikin nutsuwa na kwankwasa ƙaramar ƙofar gate din, ta ciki aka ce waye?
Cikin nutsuwa nace nice, ba’a sake magana ba sai buɗe k’ofar da akayi, ganin baƙin fuska ne yasa shi fitowa gaba d’aya waje yana bin su da kallon mamaki can ya ce “ke bake ce yanzu hajiya tayi ma alheri ba? shine kika sake dawo wa dan son abin duniya, duk kud’in da aka baki bai isheki ba har da sake jajibo wata ma?”
Ya ida maganar Yana watsamun harara.
Mama tayi saurin cewa “malam ba wannan ya kawomu ba,zuwa nayi naji dalilin da kuma abin da tayi aka loda mata irin wa’innan maƙudan kud’in, tunda a gaban ka akayi to ina jin ka.” ta fad’a cikin sigar rarrashi.
Ganin ba yanda yake tunani bane, sai kunƴa ta kama shi cikin sunna kai ya shigayi mata bayani kamar yanda nayi mata babu ko tuntunɓen harshe, jikinta yayi sanyi hankalinta ya kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa, bata sake mai magana ba ta kama hannuna muka dawo gida, bata bari na shiga ciki ba muka tsaya a bakin k’ofar ta dauko d’ari biyu a gefen zaninta ta bani had’i da amsan kud’in hannuna tace” kije gida yanzu in malam ya dawo zanyi mai bayani insha Allah ranar littinin dake za’a koma makaranta.”
Murmushi nayi har cikin raina naji dadi, cikin biyayya nace” na gode mama Allah ya jikan magaba ta, ya ƙaro lafiya da nisan kwana na gode kwarai da gaske… na fad’a ina hawayen tausayin kai na.
Murmushi kawai Hajiar ta sakar mun kafin ta ce “àmeen ngde.”
*****
Da sallama a bakina kamar yanda na saba na ƙarasa shiga cikin gidanmu, babu kowa a tsakar gidan gudun kar nayi laifi, sai na dauki tsintsiya na fara shara cikin sauri da kwarewa, ina gamawa na had’a kayan wanke-wanken dake watsi a gidin rijiya, can gefe na hango ruwan sabulu, ɗauka nayi na wanke su tass sannan na nemi wajen zama na fara hutawa, ba jimawa sai gata ta shigo cike da masifa hannunta cikin na Hannatu dake share majina cike da k’azanta.
Jikina na kyarma nace” Sannu da hanya Anty.” Daga haka naja bakina na ɗinke.
Bata amsa mun ba hannu kawai ta mik’o min, cikin sauri na ɗaura mata d’ari biyun hannu na ina cewa” yau da kyar na same ta har na dawo gida wani mutun ya kirani ya bani.”
“Tambayar ki nayi a ina kika samo ta? Faɗi ba’a tambayeki ba, ki kiyayeni mai sunan aljanu, Allah yaso ki yau wallahi da sai kin ganewa aya zaƙi a gidanan, tashi kiyi aikin da kika saba banza kawai.” ta fad’a a hasale.
Naja jikina baya kaɗa kaina nayi na ce “na gama komai ai,” ta ce “har girkin kin gama?” ta jeho min tambayar cikin isa.
Kai na girgiza alamar a’a cikin faɗa ta ce “ba kida baki ne kike ɗaga min kai kamar ƙadangaruwa?”
“Ai ban san abin da za’a daura ba ne, kuma tunda na shigo ban shiga d’akin ba.” bata amsa mata ba ta wuce ciki abin ta, sarai ta san me take nufi cikin sauri ta bi bayan ta, har cikin d’aki taliya ta ɗauko guda d’aya tal ta ce ” ungo ita zaki dafa, ki tabbatar komai yaji wallahi ki sake abincin nan yayi irin na jiya sai nayi miki tsinanniyar duka a cikin gidan nan, ki bar gani kwana biyu na ɗaya miki ƙafa!”
*****
Dafe goshi hajiya tayi cikin jin haushin sa ta ce “ANNUWAR wai me yasa kaf cikin jikokina kafi kowa tsanar talakawa ne ? karfa ka manta wannan kud’in da kake ganin ubanka na dashi, shima da farko talaka nee na k’arshe, da sannu Allah ya d’aga darajarsa, ban san meyasa uwar ku tayi muku mummunar raino ba, to wallahi daga yanzu duk wanda zaizo neman alfarma a gidan nan zan kafa doka ku ne za ku riƙa bayarwa, domin wannan yaron yana matuƙar ƙoƙari dan son faran tamin gaba d’aya ni ya ɗauko a komai da komai, ba kamar ku ba da kuka dauki halin banza, zamu dawo zan saka doka naga wanda ya isa ya karya ta a cikin gidan nan.”
Ranshi ya sake ɓaci sosai, can ƙasan maƙoshi ya ce “Allah ya taimaki hajiya Daddah nifa banyi da wata manufa ba, amma in ranki ya ɓaci dan Allah kiyi haƙuri za’a kiyaye gaba” ya fad’a hakan dan gudun b’acin ranta dan abin da ta ce zatayi ya san tsaf zata aikata sa.
*****
Tana tsaka da aikin Abba yayi sallama cike da nutsuwa, cikin sauri ta mik’e da sauri ta nufo shi fuskarta cike da annuri, hugging ɗin sa tayi sannan ta ce “sannu da zuwa sanƴin idaniyata.”
“Yauwa mamana ina fatan kuna lafiya?”
kafin nayi magana ta rigani da cewa” lafiyar mu ƙalau ai wannan maman tamu ta cika son jiki, tun safe tana kwance a ɗaki sai yanzu ta fito shima sai da na matsa mata” ta fad’a tana dafa kafad’ata had’i da matse min, inda sabo na saba sai kawai nayi murmushi ina me amsar kayan hannun sa, cike da dabara ta amshe laidar tana cewa” ba shi ya kamace ki ba Mama na maza je ki duba mana abinci kinga Abban ki ya dawo da wuri yau.”
Ji nayi idanuna sun cicciko da ƙwalla gudun kar ya tafi na ci bugu, sai nayi saurin juyawa ina tafiya inda ta fakaici idonsa tana zuba min harara.
Alhamdulillahi Allah na gode maka da ka sake bani dama a karo na babu adadi, na sake dawo muku da sabon novel dinna me cike da sak’akiya, tausayi alajab’i rud’ani makirci soyayya da hargitsi, ku ci gaba da kasancewar dani danji yanda zata gaya, comments din ku shine kwarin gwiwa ta.
Like, comment and share, please!